Showing 39001 words to 42000 words out of 62424 words

Chapter 14 - BILKISU BOOK COMPLETE By Mrs Aliyu.txt

19 Aug 2025

2856

ne, ban taɓa yin zina"


Mama Amarya ta ce "Ƙarya kike irin mazan da kike kaiwa gidan mijinki ki ne, wannan cikin cikin ɗaya daga cikin kwartayen ki ne"


Bilkisu ta fashe da kuka cikin kuka ta ce "Allah ya isa tsakani na da ke, tun a duniya Allah zai saka min, kuma idan kinje lahira zaki gani "


Me Napep din yazo ya kalli Alhaji ya ce "Alhaji tun bansan tsakanin ku ba, amma yanzu na sani, kuyi haƙuri ku barta ta kwana zuwa da safe"


Mama Amarya ta ce "Kaima ban yadda da kai ba, hala kwarton ta ne ma, ka gama abin da zaka yi da ita ka kawo ta"


Juyawa yayi ita ma ta bishi a baya ya kalleta ya ce "Kije ki shege ta gefensa"


Ta tafi kai tsaye zata shege ta gefe Abba yasa ƙafa ya tokareta ta faɗi, ta mike ta ce "Abba wai ka manta ni wacece, Bilkisun ka ce fa"


Turota waje yayi ya rufe ƙofa.


Tashi tayi tayi gun me napep din ta ce cikin kuka "Badan kuɗin ka ba da nace kaje kawai amma yanzu kayi haƙuri ka kaini wani gidan zan haɗa maka kuɗin ka duka"


Ya ce "Hajiya ba kuɗi bane damuwata, inda zaki kwana, gashi kina mace, muje can ɗin idan suma sun hana zan kaiki gun Mamana"


Ta ce "Nagode Allah ya saka maka da Alheri"


Ya ce "Kada ki damu, Hajiya dole mu taimaka wa irin ku"



Suna zuwa gidan su Umma kuwa shiga tayi saboda gidan ba ƙofa taje jikin ƙofar ɗakin Umma ta buga kofar sosai daga ciki Umma ta ce cikin muryan barci "waye"


Ta ce "Umma Bilkisu ce"


Ta ce "Wace Bilkisun kuma"


Ta ce "Adda Bilkisun ki ce, ƙanwar su Ya Abubakar "


Shiru taji sai kuma taji buɗe kofar, Umma na ganin ta ta ce "Innalillahi wa inna'ilaihir raju'un, daga ina haka"


Kuka ta fashe da shi ta ce "Mu shiga ciki"


Ta ce "Aa ki bani kudi na kaiwa mai Napep yana waje"


Umma ta ɗauko ɗari biyar suka fito tare suka same shi Umma ta miƙa masa ya ce "A'a dama na jira ne naga idan ba'a karɓeta ba, Allah ya kiyaye gaba"


Bilkisu ta ce "ka amsa"


Ya ce "Hajiya kada ki damu kawai kimin Addu'a "


Ya juya kan Napep dinsa ya tafi.

Komawa ciki suka yi, Bilkisu tana kuka tana faɗa mata abin da ya faru, Umma kuwa tayi ta lallashinta tana bata baki, har barci ya ɗauke ta, ita ma Umman ta kwanta.


Washe gari Sassafe bayan sin karya Umma ta ce "Zaki bar garin nan, gun Adda Bilkisu zaki je a Kaduna ki haihu a can, yanzu ki tashi kije gidan Umar ki ɗauko kayan ki"


Ta ce "Ta sani ne"


Ta ce "Bata sani ba amma kuma yanzu zan kira ta, yanzu ki tashi kije ki ɗauko kayanki, idan ya hanaki kizo ki faɗa min ina dai dai da su daga su har iyayen nashi da duk wani mai goye masa baya"


Kuɗin Abin hawa ta bata sannan ta tafi, gidan a buɗe yake da alama tunda ta fita ba'a rufe ba, falon ma a buɗe ɗakinta tayi tana shiga ta ganshi yashe a ƙasa sai sharan barci yake. Ta ɗauki takarda da biro ta masa rubutu kamar haka _Umar ka cuce ni, bai kamata ka rabu da ni a cikin halin da nake ciki ba, kuma duk da haka bai maka ba saida ka kore ni a gidanka saboda matarka, sai da ka tura min sonka a cikin zuciyata kai kuma kazo ka ƙimu nida gudan jinin ɗanka, da kake faɗan irin son da kake masa. Nasan tuntuni dama baka sona daga baya kazo kace kana sona, ashe ba so bane, duk salon ƙiyayya ne, ka tura min sonka ni kuma ka guje ni, to ni na tafi Kaduna zanje na haihu a acan kuma kamar yadda ka zabi sunan da za'a saka wa ɗanka shi zan saka masa_


Tana gamawa ta ajiye ta fara tattara kaya sai ya farka, ya kalle ta ya ce "Baki tafi ba dama"


Ta ce "Kayana zan ɗauka"


Ya ce "Ba abin da zaki dauka dan haka ko ki tafi ko in miki duka"


Fita tayi ta tare me napep ta koma gun Umma ta faɗa mata komai, Umma ta ce "Munyi waya ta ce Yanzu ki shiga motan haya kije Kaduna, da na faɗa mata kin tafi ɗauko kayanki ta ce da ban tura ki ba, saboda haka yanzu muje tasha in saki a mota"






_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/3, 9:20 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




_*Nafisa Isah Musa Allah ya sauƙe ki lafiya*_





*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 51-52





Suna zuwa tasha suka samu mota Umma ta biya kuɗin motar saida taga tashin su sannan ta koma gida.


Suna isa a cikin tashan kawo aka sauƙesu ta fito, tana kalle-kalle sai yanzu gashi bata san gidan da zata je ba.


Tana kalle-kalle sai taji murya ta bayanta "To Ƴar ƙauye kallon me kike"


Tana juyowa taga Aliyu ta ce "Lah Ya Aliyu"


Ya ce "Ina kayanki muje gacan mota"



Ta ce "Muje kawai bani da kaya"



Bude mata gefe yayi yayi ya shiga gurin driver ya ja suka tafi, suna isa gidan yayi parking a gurin Adana motoci saida ya kashe motar sannan ya buɗe ya fito sannan ya buɗe mata ta fito ya rufe yayi gaba ta bishi a baya suka shiga falon Adda Bilkisu ta fito ta rungumeta tana jinta a jikin Adda Bilkisu sai ta saki wani kuka mai ban tausayi. Adda Bilkisu ta yi ta bubbuga bayanta tana cewa ya isa haka duk wanda ya zalince ki Allah zai saka miki, yanzun kan komai ya ƙare ay, ki kyale kowa da halin su, kuma ba Babban mai laifi irin Umminki da ta kyale ki, bana son ki faɗawa kowa kina nan ki kyale su, "


Ta gyaɗa kai.


Wani ɗakin ta kaita ta haɗa mata ruwan wanka a bayi ta ce "Ki shiga kiyi wanka "


Ta shiga tayi wanka tana fitowa taji bata da wata gajiya kuma, Sallah azhar tayi.


kaya ta gani akan gado ta ɗauka ta saka mai kawai ta shafa sannan ta zauna bakin gado, ba jimawa sai ga Adda da Abinci harda flask din ruwan zafi, ta fara haɗa mata tea ta ce "Ki fara shan wannan dan hanjinki ya warware ko"


Ta amsa tana sha a hankali ita kuma ta fita, bayan ta shanye ta zuba abincin faran shinkafa ne da miyar Alayyahu da naman rago a ciki kaɗan taci taji ta ƙoshi.

Adda ta shigo ta tattara kayan ta fita da su. Sannan ta dawo, ta ce "Ki kwanta ki huta ko"



Maryam ce ta shigo da gudu ta rungumeta Adda ta faka mata duka a baya ta ce "Baki da hankali ne, bakya ganin yanayin yadda take ne"


Maryam ta ce "Momy ni fa ban gani ba"


ta juya ga Bilkisu ta ce "Ina shigowa Yaya ya faɗa min Wallahi, ke kice munyi kusa haihuwa, yeeeee" sai kuma ta fara tsalle.


Momy ta ce ", To ki kyale ta ta huta mana"


Ta shafi cikin ta ce "Babynmu ka huta lafiya kaji"


Sannan ta fita da gudu kuma, ita dai Bilkisu murmushin ta take ta yi, Mommy ta ce "Bansan yaushe Maryam zatayi hankali ba, kwanta kinji"


Tana kwanciya kuwa barci ya kwashe ta.




*** *** ****




Zai fita kenan ya duba kan gadon ba wayar sa, ya kalli matar tasa ya ce "Ina wayata kuma, ni da na ajiye a gefena da zan kwanta"


Drawer ta buɗe ta miƙa masa ya ce "Ya akayi ta mutu bayan da caji"


Bata ce komai ba ta fita ya buɗe wayan yaga Miscall da baƙuwar number da massage ɗaya ya buɗe ya karanta saƙon Bilkisu ya duba da sauri ya fita ɗakin Mama Sauda yayi ya ce "Me yasa kika kashe min waya saboda Bilkisu ta kira ni ko, tana buƙatan taimako kin sani amma kika ƙi taimaka mata a cikin tsohon daren nan ina zata shiga, yau idan wani abu ya samu yarinyar nan daga ke har ɗanki sai na ɗaure ku tunda baku da mutumci"


Fita yayi kamar wani zararre ya shiga mota yayi gidan Umar.



*** *** ***



Umar kuwa yau ya kasa fita kwata kwata yana zaune a ɗakin Bilkisu wani azababben ciwon kai ne ke damunsa, ko Sallah ya gagara yana nan kwance a tsakar ɗakin Bilkisu anan fa barci ya kwashe yayi barcin sosai ƙarfe 11:00am ya farka yaji ba wani ciwon kai kuma saidai kuma ya koma tunani dabam wato Bilkisu, fitowa yayi ya Ruky a falo ya ce "Ke Ina Bilkisu kuwa take"


Ta ce "Ba kai ka koreta jiya ba"


Shiru yayi yana tunani duk abubuwan da suka faru ya dawo masa a tsakiyar kan sa. Komawa ɗakin yayi yana kalle-kalle kamar taɓabbe wayarta ya gani ya ɗauka, ga kuma akwatin da ta ɗauka ya hana ta rigar barcin da ta cire ya gani ya ɗauka yana dubawa can kuma ya hango takarda ya ɗauka ya karanta, sai kuma ya yar a ƙasa ya fito falo ya samu Ruky ya ce "Faɗa min ina Bilkisu ta je"


Ta ce "Ka manta da hannun ka ka rubuta mata saki uku"


Tunawa yayi tabbas haka akayi a daren jiya ya rubuta mata saki uku kai ya kama, sai ji suka yi an banko ƙofa Baba ya gani ya miƙe kafin Ya kai ga Magana Baba ya riga shi"


Ina Bilkisu?


Sai shiru bai iya cewa komai ba, Mari Baba ya bashi ya ce "Me ka mata jiya da daddare ka kore ta"


Shiru ba Amsa nanfa Baba Ya ringa dukan sa kamar ya samu ƙaramin yaro, can kuma ya sake shi ya fita, yana fita, Umar ya kalli Ruky wani tsanan ta ne ya kama shi, abubuwan da suka faru suka ringa dawo masa kwakwalwa, ya riƙe mata wuya ya ce "Faɗa min me kika bani naci hankalina ya ɓace kika sa na saki matata"

Shiru tayi tana son ta ƙwace nan fa ya ringa dukanta kamar Allah ya aiko shi, ya kamata ya ɗaga sama ya doka ta jikin bango nan fa hannunta ya karye ta fara kuka ya kalleta, ya ce "Kamar yadda kika sa na rabu da ita kema kin rasa ni, dama can bana son ki, ban san yadda aka yi kika samu nasara a kaina ba. Allah ya isa tsakani na da ke, ki dube ki fa, me zanyi da ke, ƙazama irin, kuma bari kiji baza ki sake fita ko ina ba, kina nan a gidan nan wahala kuma yanzu kika fara gani.


Ɗakin Bilkisu ya kuma komawa ya zauna yana kuka can ya tuna da Sallah asuba ya miƙe yayi alola sannan ya zo ya rama Sallah da ake bin sa ya kuma zauna yana Addu'a neman gafaran Ubangijinsa.



*** *** ***





A firgice ya farka daga barcin da yake ya tashi ya zauna ya kama kai ya ce "Adda na kore ta ni da kaina? Me ke shirin faruwa dani, Tunda na kori su Abubakar ina suka je basu dawo ba, kwanciya yayi Abubuwa suna dawo masa haushin kansa ya fara ji, bai kamata ya kore ta ba, dan kawai ya kama ta da wani a ɗaki, kuma a hakan ta dawo masa da ciki wani ya wulaƙanta ta ya kore ta, me ke shirin faruwa da nine, Mama Amarya ce ta shigo ta ce, ", Ni dalla Malam ka tashi ka shirya ka bar min gidan nan tun safe ka wani zauna"


Kallon ta yayi ta yi "Ta ja tsaki ta ce "Ka wani zauna a gida ni ka fita min a gida mana"


Ya ce "Ina kika tura min ƴaƴana da Matana, Ina Addana, Aisha, Abubakar Usman da Hali da kuma Khadija"


Jin muryan ɗan uwansa yayi a falo ya miƙe ya fito falo yana ganin sa ya ce "Allah yasa Bilkisu tana gidan ka"


Ya ce "Nima ita nazo nema"


Baba ya faɗa masa komai, Shima Alhaji abin da ya sani game da ita ya faɗa, nan fa suka fara jajantawa junan su.


Yinin ranan a gidan suka yini daga bayane Baba ya koma gida yana zuwa ya tarar Mama Sauda tana kuka, ko girki ta kasa yi a gidan abinci ma ta kasa cin sa ya tambaya lafiya.

Ta ce "Mun cuci Bilkisu "

Ya ce "Me kuma ya faru"


Nan ta fara faɗa masa Abubuwan dake faruwa har zuwa jiya da ta kore ta.







_*Mrs Aliyu ce*_


lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[6/4, 7:04 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com



loadιng...........✍🏻



🌐BILKISU



Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)


Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU



*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*




_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Page 53-54



Girgiza kai yayi ya ce "Wannan wani irin Imani me ta muku haba Sauda, to gaskiya bazan iya zama ci gaba da zama da ke ba, dan haka kije na sake ki saki ɗaya"


Kuka tasa ta ce "Haba Baban Umar kayi haƙuri dan Allah kada ka min tunda baka min haka ba sai yanzu da girma ya kama ni"


Ya ce "Kamar yadda kika koreta, ɗanki ma ya koreta kema ki bar min gidana bana son ganin ki"


Ɗaga kai tayi ta kallo ƙofa taga Umar a tsaye yana kuka yaje ya durƙusa gaban Baban yana kuka yana son yayi magana amma ya kasa Baba ya ce "Kada na sake ganin ka a gida na, kaje kaima na Sallama ka a duniya "


Lokacin tayi magana haɗe da kuka "Baba ban san lokacin da nayi haka ba Baba ka taimaka min dan Allah "


Ya ce "Wai kan na tambaye ka, Bilkisu ba ƴar uwarka bace, ko a gidan wani ta fito baza ka iya riƙeta ta haihu a gidan ka ba, ka koreta a cikin wannan daren kasan ina ta kwana, ga gari da ƴan iska, so kake ta dawo da halinta na baya kenan ta kuma lalacewa"


Ya girgiza kai ya ce "Cikin kuka Abba tun da ma can sharri aka mata amma Wallahi Bilkisu ba haka take ba, bata taɓa zina ba, nine nan shaidan ta Allah ne kuma shaidata, Abba nima kaina nayi mamakin da na samu Bilkisu cikekkiyar budurwa wanda banyi zato ba"


Baba ya duba maganan sa ba rashin kunya illa tsantsan gaskiya da yake faɗa da kuma yanayin da yake ciki, kan sa ne ya sara ya tashi ya fita a gidan mota ya shiga ya kuma yin gidan ɗan uwan nasa yana shiga da mota, yaga wani mutum a rakuɓe jikin bango yaje gurin ya ce "Malam lafiya "


Muryan sa na rawa ya ce "Dan Allah ka haɗa ni da Alhaji "


Ya ce "Me zaka masa kuma, kaga yanzu za'a shiga Sallah Magrib ka bari muyi Sallah mu fito"


Kuka ya fara yi sannan ya juya, Baba ya bishi da kallo kawai, yayi Alola ya shiga masallacin ƙofar gidan Alhajin yabi Jam'i suka gabatar d Sallan Magrib, bayan sun fito ne shima ya haɗu da Alhajin sai ga wannan Mutumin yana takowa a hankali kamar a tsorace yake yazo ya durƙusa a gabansu ya ce "Alhaji na kasa samun Sukuni, komai ma taɓa yana lalacewa, an bani jari da yawa dan nayi sana'a jarin ya lalace, Nayi Aure matar taƙi zama, to sai na tambayi wani Malami yake cewa akwai abin da nayi wa Allah wanda na fusata shi yasa yake jarabta ta da hakan"

Alhaji ya ce "Mu kuma menene namu"

Ya ce "Alhaji na cuci ƴarka Bilkisu dani aka haɗa baki aka mata sharri dan ina neman abin duniya, dan Allah Alhaji a min magana da ita ta min hukuncin da ya dace ko ta yafe min"


Baba ya ce "Bilkisu bata nan, amma me ka mata"


Ya ce "Da daɗewa matar gidan nan, Maman Ruky ta ce nazo na shiga ɗakinta a matsayin Saurayinta wanda muke lalata da ita zata min kyauta me tsoka kuma zata kuɓutar dani na gudu, munyi hakan kuma an samu nasara kuma kwanaki ma naji ance ka kore ta"



Alhaji ya ce "Kenan kaine wanda na kama a gadon Bilkisu, ashe bata san da zuwan ka ba, tayi ta min rantsuwa amma naƙi yadda da hannuna kasa na koreta, tashi kaje, Bilkisu dai bata nan, bamu san ma inda taje ba muma nemanta muke, mu baza mu iya yafe maka ba har sai tazo"


Tashi yayi yana kuka yana Tafiya Baba ma ya faɗa masa yadda sukayi da Umar Ayko Alhaji ya fara kuka kamar ƙaramin yaro, Baba yana lallashin sa.


*** *** ***



Yau sai taji ta tashi da kewan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login