Showing 15001 words to 18000 words out of 62424 words
da ya iya sakin Amanar da aka bashi. Yana tafiya Mama Amarya ta fito ta ce "Oya maza a koma daji"
Ummi ta juya ta fara haɗa kayanta Bilkisu tana kuka Khadiyo nayi Ummi ta tafi, ana haka ta tuba bata ci komai ba tayi kicin dan ta ɗebo ta fara ci tana kuka ji tayi an ƙwace abincin tana ɗaga kai taga Mama Amarya, bata ce komai ba ta koma ɗaki ta kwanta ta kuma wani sabon kukan, har barci ya kwashe ta, cikin barcin ta taji ana dukanta a cinya ta tashi ganin Mama Amarya tayi ta ce "Ki tashi kije ki ɗora mana Abincin dare. Ta tashi a hankali tana jin jiri taje ta fara shirya Abinci tana gamawa ta ɗibi nasu ita da Khadiyo suka yi ɗaki suna ci su Abubakar suka shigo ɗakin tana ganin su ta saki kuka Abubakar yayi ta lallashin ta, Khadiyo ne take faɗa musu komai, komai a kunnen Mama Amarya ake Lalle akwai sauran aiki a gaban ta tunda yanzu akwai wanda zai lallashi Bilkisu, ta fi so ta kasance bata da kowa, tunda yarinyar bata da kunya kuma ta lura Alhaji yafi son ta duk cikin yayan sa.
Tana wannan tunanin Sauda ta shigo gidan, suka shiga Ɗaki Mama Amarya ta ce "Albishirinki"
Ta ce "Goro"
Ta ce "Yanzu Hali tayi waje "
Mama Sauda tayi shewa ta ce " Yanzu kika kasance Hajiyar Alhaji"
Mama Amarya ta ce "Ban kasance ba tukunna dan akwai sauran rina a kaba"
Mama Sauda ta ce "Menene"
Ta ce "Su Abubakar bana son su kasance da ita, nafi son sai Bilkisu ta raina kanta duk da yanzun ma ta raina ina son ta kasance a wulaƙance ne"
Mama Sauda ta ce "To ki koma gun boka ya watsa su a duniya mana "
Ta ce "Ay ita ma Bilkisun hankalin Alhaji ya Fara komawa kanta, dan ina haɗawa da kissa ne yasa dai yake dan ɗage mata kai amma wata rana kinsan komai zai iya lalacewa"
Ta ce "Ay gun boka kawai zamu tafi komai ma yayi Ya ƙara dulmiyar da Alhajin sannan ya watsa kan ƴaƴan suje can su lalace, kinga baƙin cikin zai kashe uwarsu in yaso daga baya Bilkisu ma san yadda zata yi ta bar gidan"
Mama Amarya ta girgiza kai, ta ce "Bana son tabar gidan nan saboda yarinyar akwai iya girki, ban taɓa cin girki mai daɗi irin nata ba, ko na uwarta, kinga tunda na kora uwar ay ita din ta zauna ko dan gyaran gida da yin girki, amma duk da hakan ina son Alhaji ya yadda da zance na kan cewa tana bin maza"
Ta ce "Eh haka ne kan kin kawo shawara kinga ko ta nan ma ya tsane ta, "
Dariyan ƙeta Mama Amarya tayi ta ce " To ya maganan Ruky da Umar ɗin"
Nan da nan Annurin fuskan Mama Sauda ya canja, Mama Amarya ta dano ta dan haka ta ce "Sauda muna tare da ke amma baki son ki haɗa zuri'a da mu"
Ta ce "Wallahi ba haka bane, kin san saboda bai zo min da maganan ba amma ni idan na koma zan masa maganan, haba ya za'ayi na ƙi Ruky ay Ruky ƴata ce"
Mama Amarya kan bata aminta da zancen ba dan haka dan haka cikin ranta ta ce "Zaki gane kuren ki, koma ko kinƙi ko kin so sai Umar ya auri Ruky "
Ita ko Mama Sauda tana tunanin irin rashin mutuncin da zata yi wa Umar da har ya yarda yake Soyayya da karuwar yarinya irin Ruky.
Mama Amarya ta ce "To tashi muje gun bokan muyi yadda za'ayi"
Ta miƙe suka tafi.
Cikin kursumin daji suka shiga suna ta tafiya gaba daji baya daji har Mama Sauda ta fara tsorata dan bata taɓa zuwa irin dajin ba, suna zuwa gurin Mama Amarya ta ce "To daga nan zamu fara rawan tsohon mawaƙin nan Michel jockson"
Mama Sauda ta zaro Ido sai ga Mama Amarya ta fara, itama ta fara lakwashe lankwashe dan ba iyawa ta yi ba, suna isa bukkan sai gashi ya fito yana yin rawan shima saida yazo gaban su ya zauna, suko suna tayi, ya daka musu tsawa saida Hantar Mama Sauda ya kaɗa ita ko Mama Amarya taci gaba da yi sai da ya ce "Zauna Hajiya ya isa amma kuma daga yau kada ki sake zuwa min da wannan sakaryar dan bata iya rawan ba"
Ta ce "Za'a koya mata ay"
Ya ce "To me ke tafe da ku, ya kike da Bilkisu nasan zaki ce Hankalin Mijinki ya koma kanta, kuma kina son yayyenta su shiga duniya, kuma kina son Mijinki ya yadda Bilkisu tana bin maza ko mu sata tabi mazan"
Mama Sauda kuwa Mamaki fal cikin ta, Mama Amarya ta bashi kuɗi ya ce "Kuje za'ayi komai, kwanan nan Alhaji zai kora ƴaƴan sa, sannan Bilkisu zata fara bin maza, kuma zai tsane ta, nasan akwai abin a ranki kuma Sirri ne zan miki Aiki a kan sa shima"
Mama Amarya tasan maganan Ruky da Umar ne dan haka ta ce " To Sheɗanina"
Zasu tafi ya ce "Yau baza ki bani ba, kinsan idan baki bani ba aiki bazai yi ba"
Ta ce "Ay naga kaine baka yi magana ba"
Ya ce "To Mu shiga ciki"
Mama Amarya ta shige bukkar shima ya bita, suka rufo ƙofa aka bar Mama Sauda a gurin.
Sun daɗe sosai a ciki kafin suka fito Mama Amarya tana gyara zanin ta, Mama Sauda tana ganin ta ta gane sunyi Zina ne. (Wa iyazibillah)
Boka ya kalli Mama Sauda ya ce " Idan kina son zuwa nan kije ki koyo rawa sannan, dan da rawa ake zuwa"
Da sauri ta ɗaga kai dan a tsorace take. Suka tashi suka fita a gurin suna rawan, yayin da Sauda take ta lankwashe lankwashe.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 23-24
Har suka isa gida Mama Sauda Hankalin ta a tashe tunani kala-kala take a zuciyarta, ita dai tasan duk iskancin ta baza ta taɓa bawa wannan ƙazamin bokan kanta ba, kuma ma ko ba shi ba baza ta iya ba, ita dai barta da iskancin ta da hassada.
Har tabar gidan tana mamakin ta, ita ko Mama Amarya ko a jikinta harkokin ta take yi kawai.
Sun dawo daga gun Sana'an su, kai tsaye ɗakin da Bilkisu take suka shiga suka ganta kwance tasha aiki ta gaji, yayin da Khadiyo take danna mata ƙafa, Usman shima ya zauna bakin gadon ya sa hannu yana danna mata ya ce "Sannu ko Sister kin sha aiki ko, Allah ya baki lada, nasan mijinki zaiyi farin ciki da ke.
Murmushin jin daɗi tayi ta ce " Yayana kenan kuka nasan matan ko zasuyi farin cikin samun ku"
Abubakar ya ƙarasa hawa kan gadon ya shafi fuskanta ya ce "Kiyi haƙuri da irin zaman da kike a gidan nan na ƙunci, Allah zai dube mu"
Hira suka yi daga bisani suka suka fito ta fito raka su, suka ga Ruky ta fito zata fita, wani mini sket ne a jikinta tasha kwalliya, wanda kwalliyar kwata-kwata bata yi kyau ba, ta gansu sarai amma kuma ta taho ta bangaje Usman, ya yi mata mungun kallon ta kalle shi ta ja tsaki, ya kai mata duka Bilkisu ta riƙe hannun, Ruky ta ce "Barshi ya ja ma kansa bala'i dan ubansa"
Fizge hannunsa yayi ya je ya bugeta ta faɗi ƙasa warsar, da sauri Bilkisu ta tura shi waje har ɗakin su sannan ta dawo dan ta san Ruky zata iya musu wani sharrin.
Ita kuwa da taga ba kowa sai ta tashi ta bisu ɗakin Bilkisu ma ta bita, tana shiga ta samu sun cire kaya suna ƙoƙarin kwanciya ta kama Usman da kokuwa, shi kuma ya ɗauki charger na fitila ya ringa zuba mata a baya dama gashi jikinta ba ishashen kays ba, sai ihu take Bilkisu tana ƙoƙarin hana shi.
Alhaji yana daga ɗakin Mama Amarya ya jiyo ihunta a tunanin sa ma Bilkisu ne, yana fitowa falo Mama Amarya tana biye da shi a baya, cikin ranta tana cewa Allah yasa kwarto ne a ɗakin Bilkisu, yaji a ɗakin su Usman ne ya fito zai shiga yaga Ruky ta fito da gudu tana sosa jikin ta, Mama Amarya ta rungumeta ta na cewa menene, shima Alhaji ya zuba mata ido yana jiran jin amsa, Cikin kuka ta ce "Ba Usman bane ya ce In kawo masa ruwa shine na kai masa, shine suka rufe ƙofa shi da Abubakar suka haɗu suka cire min kaya wai zasu min fyaɗe, shine naƙi yadda, shine suka zane ni, kuma Usman ya min fyaɗen bayan nan Abubakar ma wai zaiyin shine yake ta zane ni wai idan na galabaita sai yayi"
Daga ciki suke jinta, daga su har Bilkisu da take tsaye a gurin, kasa magana suka yi.
Abba ya kalli Bilkisu ya ce "Adda me gaskiyar maganan faɗa min"
Lokacin ta samu daman yin magana muryanta na rawa ta ce "Wallahi Abba ba haka aka yi ba ita ce..."
Mama Amarya ta katseta ta hanyar cewa "Yi min shiru munafuka kawai, duk halin ku ɗaya ne, to bari yau zamu bar muku gidan ku sannan sai na kaisu koto lalata min yarinya da Usman yayi"
Ya ce "Ba inda zaku je, su zasu bar min gidan dan banga amfanin zama da ƴan iska irinsu ba"
Bilkisu ta ce "Haba Abba ƴaƴanka ne fa kafi kowa sanin halin su baza su iya aikata haka ba"
Kiran su yayi suka fito, ya ce "Ku tattara ku bar min gidana"
Abubakar zaiyi magana ya dakatar dashi da hannu haɗi da cewa kuje can kuje kuyi iskancin ku, amma ba a nan gidan ba"
Usman ya ce "Abba kayi haƙuri dan Allah ina zamu je, bamu da gurin da ya wuce nan"
Ya daka musu tsawa a tare suka tashi zasu koma ɗaki ya sake daka musu tsawa "Kada wani ya shigar min ɗaki"
Usman ya ce "Kalli jikinmu Abba ba kaya zamu sa kayan mu ne"
Suka shiga kaya suka saka suka ɗauki jakan kayan su suka fito, zasu wuce Bilkisu taje ta rungume bayan Abubakar tana cewa "Ina zaune ne a gidan nan dan ku nima binku zanyi Wallahi bazan zauna ba"
Abubakar ya kalle ta yayin da Usman ya sa hannunsa a fuskarta ya ce "Ba inda zaki ce, kedai ki ci gaba da Addu'a, wata rana sai labari"
Ta ce "Dan Allah zan biku duk inda zaku je Yaya bazan iya sake zaman gidan ba"
Ji tayi Alhaji ya riƙota ya bata wani gigitaccen mari har sai da taga walƙiya, Abubakar ya kalle shi kanar zaiyi magana sai kuma ya juya yayi hanyar fita, Usman ko sai da yayi magana, ya ce "Ita kuma me tayi? "
Sake bata mari yayi a ɗayan gefen, ta faɗi ƙasa sai kuma ta miƙe, ya ce "A gaba na kike cewa kina zaune ne saboda ƴan iska, har kina cewa zaki bisu"
Zata yi magana cikin kuka, taji Khadiyo ta riƙe mata hannu ta jata ciki, suma basu ƙara magana ba, suka fita waje.
Suna Fita Usman ya ce "Ina zamu je yanzu"
Abubakar ya ce " Muje gun Umma mu faɗa mata sannan muyi gun Baba Jafar dan bamu da inda ya wuce gun sa"
Gun Umma kuwa suka wuce har tayi barci amma saida aka tashe ta, suka faɗa mata komai tayi Mamaki, sannan ta ce "Gwara da kuka zo nan, kuma ba inda zaku je, Karatu zaku tafi kuma ba'a ƙasar nan ba, domin ina son ku tsayu da ƙafar ku, ku wuce wulaƙanci"
Suka jinjina kai duka,
Ta ce "Yanzu Ina Bilkisun"
Abubakar ta ce "Tana gida saidai tana buƙatar Addu'a Umma so suke su nakasa yarinyar nan"
Umma ta ce " Baza su nakasa ta ba, tana tare da Allah "
***************
Haka rayuwa taci gaba da tafiya Bilkisu ko yaushe tana fuskantar ƙalubale, tun tana ganin hanya ko zata ga yayyen ta amma babu su, Khadiyo kan tunda taje gidan Kakanninta ta faɗa musu halin da suke ciki, Kakarta ta hana ta dawowa, tunda ta tafi kuma Alhaji bai nemeta ba, Bilkisu kuwa da yake tasan inda take bata damu ba ma.
yanzu an hana ta zuwa makaranta ma tun tana Ss 2 aka hana ta daina zuwa.
Soyayya kuwa ta shiga tsakanin Umar da Ruky, saidai kuma Umar sam baya yadda ya taɓa jikin ta, ita ko bata so haka ba, ta so ne suyi soyayyar shan minti, suna kasancewa, saidai ya ce baya ra'ayin wannan soyayyar auren ta yake son yi.
Mama Sauda tayi-tayi ta raba amma yaƙi karshe ma ya daina shigo mata gidan sai dai ya zauna can part dinsa.
Yau tasha aiki ta gaji ta kwanta a Falo tana hutawa sai taji Mama Amarya daga kicin tana waya da Alhaji tana cewa "Ka dawo da wuri zan nuna maka, Ina jin ta tana waya tana cewa ita Kaza zata ci ya kawo mata, ashe kullun idan mun kwanta sai ta shigo da shi su kulle ƙofa, wata rana ma a gidan yake kwana, nidai so nake kagani da idon ka. "
Sam bata fahimci akan waye ake maganan ba, dan haka bai shafe ta ba, idon ta ya fara rufewa dan barci yasa ta tashi, taje ta watsa ruwa sannan tasa kayan barci Tana son ta kulle ƙofan taga makullin ƙofar an balla, bata damu ba, ta kwanta, barci ya kwashe ta.
Cikin barcinta sai taji an shigo, ta tashi ta zauna, taga mutum a gaban ta yana mata murmushi, ya ce "Babyna ga kazar da kika ce kina so, amma kafin nan ki gyara min ki bani daddadan abin da kika saba bani, dan yau a yunwace nazo"
Zata yi magana sai Alhaji ya turo ƙofa Mama Amarya tana bayansa, tana cewa "Munafuka to yau asirinki ya tonu, ƴar iska kawai"
Shiko kafin a ankara yabi ta gefen su ya fita da gudu.
_*Mrs Aliyu ce*_
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/27, 8:30 AM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 25-26
Mungun Kallo Alhaji yayi mata ya sannan ya kalli ledar da Kwarton ya ajiye ya buɗe Kaza ce a ciki gasassiya gashin inji sai ƙamshi ke tashi, ya kalle ta ita ma cikin ledan take kallo tana ganin sun haɗa ido tayi baya dan ta san komai zai iya faruwa, jin muryan sa tayi yana rawa ya ce "Waye shi"
Ɗagowa tayi taga hawaye a idon sa, ta shiga tashin hankali wanda yafi na da, muryan ta na rawa ta ce " Wallahi Abba ban san shi ba, shi... "
Mari ya bata shima muyan na rawa ya ce "Adda Kin cuce ni kin cuci kan ki, dama halin ki ɗaya da yayyen ki, nayi nadama da na bari kika shaƙu da kannen ki, da nasan haka zaki kasance da ko uwarki naki aure lokacin da aka cusa min ita, auren uwarki ƙaddara ce a gurina tunda ta haifo min ke, kije na sallama ki a duniya BILKISU na yafe ki a duniya, baza ki zauna kina min iskanci a gidan nan ba, kije can yawon barikin kije kiyi tayi"
Bilkisu ta ce "Abba dan Allah kada ka kore ni, kaga ko hanyar rigan su Ummi ban sani ba ina zanje, duk kan mu da daddare ka kore mu, Umma ka koreta da daddare tasan inda zata je, haka ma Ummi ita ma tana da gun zuwa, sannan ka kori ƴan uwana, su maza ne ko a Titi zasu kwana ba abin da zai same su, niko Abba ba inda nasan zan nufa kuma idan nace zan kwana a titi Wallahi akwai ɓata gari suna nan zasu lalatani"
Ya ce "Dama kin riga kin lalace dan haka kije can kici gaba da lalacewan"
Ta kalli fuskarsa taga yadda hawaye ɗaya na bin ɗaya ta miƙe ta sa hannu ta fara share masa ta ce "Abba ka daina kuka nasan kana baƙin ciki akan abin da kake zargi, kuma Wallahi ba haka bane, Abba Wallahi ban taɓa yin zina, kuma ban taɓa kusantar ta ba ko sau ɗaya, nasan hukuncin yin zina, kuma nasan irin abin da zan fuskan bayan nayi aure, Abba ka yadda da ni, bana son ka kore ni, idan ka kore ni ina zan je, ina zan fuskanta,