Showing 45001 words to 48000 words out of 63585 words

Chapter 16 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

shi mai cike da tarin wahala.
kamar yadda ya saba munanan mafarkai masu cike da rud'ani da firgici yanzu ma haka ya soma, sai dai na yau ya girmi na sauran lokutan.

Wasu halittu ne masu ban tsoro suke binsa zasu kamashi abaya gudu yake basa samin nasarar kamashi,
yau kam duk iya gudun sa sai da suka cimmasa.
suka d'ad'd'aure shi da igiyar wuta,
jikin wani katon itaciya wacce kasan ta, rami ce mai zurfin gaske wuta yana ci ba kakkautawa.
ga mashi gami da kifiyoyi a hannunsu suna ihu mai firgitarwa da haniniyar zasu kashe shi.
ga igiyar wutan tana shiga jikinsa tana cin namar jikin sa.
wad'annan dodannin halittun kuwa,
sun d'aga wata kifiyar wuta suna daf da caka masa.
ya zabura tare da yin salati ya mike zaune jiki na kyarma.
ya had'a zufa sharaf hatta tafin kafarsa zufa yake.
hannu ya kai ya dafe kirjin sa da yake ji kamar zasa fito.
kallon gefen sa ya yi yaga Mommy na kwance tana sharar baccin ta.
da kyar ya mike yana jin jiri na d'ibansa ya fad'a bayi ya yi al'wa ya fito.
ya shinfid'a sallaya yasoma gabatar da sallah a daddafe.
har wajen karfe hud'u ya sallame ya kwanta kan sallaya bacci na d'aukar sa yakuma yin wannan mafarkin.
kiran salla ce ta taimake shi wajen farkawa daga mummunar mafarkin nan.
ranar Daddy bai iya fita masallaci ba a gida ya yi salla.
Mommy na idar da sallar ta taja kafarta ta koma side d'in ta, babu gaisuwa bare tambayar sa ya yakwana da jikin nasa.
Daddy na zaune har wani lokaci a kan sallaya dare d'aya ya jijjiga har ya fara fita a hayyacin sa.
ya mike da kyar ya nufi sashin Aunty.

Aunty na zaune parlour tana saurarar karatun alkur'ani a TV ya shigo.
duban sa tayi tana sakar masa murmushi,
shima murmushin karfin hali ya yi mata.
ta ce "Yanzu nake shirin zuwa sashin ka naga har wannan lokacin baka shigo ba, na ce ko lafiya."
murmushin yakuma yi mata yawuce bedroom d'in ta.
ta mike ta biyo bayansa, taga ya haye gado ya kwanta.
rike baki tayi
"Daddy kazo ka kwanta kuma bafa a nan kake ba."
tayi maganar tana karasowa bakin gadon, ta zauna tana dubansa cikin kulawa.
da d'an mamaki ta ware ido a kanshi ganin yadda fuskarsa ta zabge kamar dai mara lafiya.
hannun sa ta ruko tana fad'in
"Ya ya dai Daddy me ke faruwa ne baka da lafiya ne?."
tayi maganar cikin nuna damuwa sosai.
hannunta ya kankame yana gyad'a mata kain.
gaba d'aya ta damu ta ce
"Me ya same ka Daddy ba dai ciwon ka ba, sannu kaji yanzu ina ne ke maka ciwo, Abdurrahim ya sani kuwa? bari na kirashi ya zo ya duba ka."
ido ya rumtse kana ya bud'e ya ce
"Banyi bacci ba jiya Fad'imatu ina jin kirjina da kaina kamar zasu fashe."
"Subhanallahi sannu Daddy, kuma kasha maganin ka kuwa, ko dai kwana biyu baka sha ne? bari na d'auko maka na nan kasha sai na kira Abdurrahim."
ido ya rumtse yana jin yadda kai da kirjin suke masa.
ta mike da sauri taje ta d'auko maganin sa datake ajiyewa a gon ta wanda idan yana gurinta da kanta take basa yake sha.
ta had'o da gorar ruwa tazo ta bashi ya sha.
ta mike tana fad'in
"Bari na d'auko waya nakira Abdurrahim."
ya ce
"Barshi tukunna Fad'imatu idan bai lafa ba zuwa anjima sai a kirashi."
kai ta gyad'a cike da matukar tausaya masa.
ta gyara zamanta gefen sa tana ta yi masa sannu.
ta bud'e tafin hannunta tana karanto addu'o'i ta tofa ta shafa masa a kai d'in zuwa jirjin sa.
a hankali ya lumshe idanunsa yana jin nutsuwa na shigarsa, duk da yana jin ciwon amma yaji matukar jin dad'in nutsuwar da ya samu wanda jiya zuwa yau da safiya bai samu ba.
a hankali a hankali bacci ya tafi da shi.
ganin yasamu bacci Aunty ta tafi kichin domin ta shirya masa abincin da ta san yafi so idan ya tashi ya ci.
ita da Feeryal da Baba Rabi ne a kichin.
Feeryal na taimaka mata da wasu abubuwan in da Baba Rabi kuma ke ta aikin gogewa da wanke duk in da yab'aci da duk abin da akayi amfani da shi aka aje zata d'auka ta wanke ta goge sannan ta maida shi gurin zamansa.

Suna kammalawa Aunty ta d'auko lafiyayyen girkin da tayiwa Daddy,
Feeryal kuma ta d'auko nasu shima kayataccen breakfast da abinda tafi muradi wato cake d'in da ta had'a da kanta, da yoghurt mai sanyi.
ta fito ta haura da shi dinning.

Aunty na shiga ta hango Daddy jikin sa na b'ari ya had'a gumi sharkaf, idanunsa kuma a rufe.
da sauri ta dire tray'n abincin hannunta kasa, da sauri mai kama da gudu ta hayo gadon ta rirrikeshi tana jijjigashi da kiran sunan sa
"Daddy Daddy Daddy!."
da karfi ya ware idanunsa da sukayi mugun ja ya sauke wani nannauyan ajiyan zuciya.
ya kankameta numfashin sa na sama-sama ya ce
"Fad'imatu zasu kashe ni!."
a hargitse Aunty da kwalla ya fara zuba mata ta ce
"Su waye Daddy ina suke!? innalillahi wa innailaihirraji'un."
"Dan Allah Fad'imatu kar ki bari na sake yin bacci, ina kuma yin bacci nasan yanzu kam zasu kashe ni, kirjina da kai na zasu fashe Fad'imatu."
Aunty data shiga mummunar tashin hankali hawaye d'aya na bin d'aya
ta rungume shi tana fad'in
"Bazaka mutuba Daddy bazaka mutu ba."
ta mike da sauri ta fita ta d'au wayarta ta daddanna ta tura kira wa lambar Abdurrahim.
wayar tayi ta ringing bai d'aga ba, takuma mai da kiran shima sai da yakusa yankewa kafin ya d'aga.
murya a hargitse Aunty ta ce
"Abdurrahim kayi sauri kazo ciwon Daddy ya tashi!."
ta kashe wayar da sauri ta koma ciki.
Daddy na zaune dafe da dai-dai kahon zuciyarsa d'aya hannunsa na dafe da kansa sai jan numfashi yake da kyar tamkar zai fita yabar jikin sa.

Ba ayi minti 10 ba Abdurrahim ya shigo rike da jakar kayan aikin sa.
yawuce bedroom d'in Aunty kai tsaye.
ganin halin da Daddy yake ciki sai da ya firgitashi, sai dai bai nuna a zahiriba cikin gaggawa yasoma bashi taimakon gaggawa.
ganin ya had'a allura yana shirin masa, Aunty ta share kwalla cikin raunin murya ta ce
"Abdurrahim bazai sa shi bacci ba dai allurar ko, ya ce baya so ya yi bacci in dai zai sashi bacci kar kayi masa."
"Dole ne sai an masa ana bukatar ya sami bacci yanzu."
Aunty tayi shiru tana kallon Daddy daya lumshe isanunsa ya yin da bakin sa ke motsi da alama addu'a yakeyi.
sai itama ta soma karanto ayoyin Allah cikin ranta.

Feeryal ta fito daga bedroom d'in ta d'aure da towel a kirjin ta kanta babu d'anwali, ta nad'e gashinta ta tufkeshi a sakiyar kanta kamar Donut.
kofar Aunty ta nufa ta d'aura hannu kan handle tana kokarin murd'a handle d'in cikin muryarta mai fita da yanayin shagwab'a takuma karo ainihin shagwab'ar ciki tana fad'in
"Ammie wai yanzu ma sai na sa bra, ina breakfast fa bacci zanyi, Ammie kar na sa ko..."
da sauri ta janye hannunta daga kan handle d'in jin an bud'o kofar tun kan takai ga rufa bakin ta.
arba da tayi da shi ne ya sanyata had'iye ragowar maganar ta.
ta matsa gefe ta bashi hanya yasa kai ya fita.
Aunty ta ce
"Feeryal koma ki sa kaya ga Daddy bayida lafiya."
da sauri ta koma ta sako kaya ta zo d'akin Aunty lokacin har bacci ya d'auke shi.
Aunty na zaune da kur'ani tana karantawa a dai-dai saitin kansa.
wannan bacci ya yi shi cikin salama dan kuwa baiyi mafarkin ba,
hakan kuwa baya rasa nasaba da karatun ALQUR'ANI da Aunty take a kansa.
bata gusheba har sai da ya farka da kansa.
ya damke hannunta cikin nashi yana mai dad'a jin girma da kaunarta cikin ransa.
sannu tarika jera masa bayan ta taimaka masa ya yi wanka ta zubo masa abinci ya ci.
Abdurrahim ya kuma shigowa duba shi bayan ya bashi wasu magungunan yafita.
Ajmal ya kira ya ce yarika zuwa yana duba jikin Daddy'n a side d'in Aunty yana sanar masa yanayin jikin nasa, zai tafi asibiti yanzu.
Ajmal dake sashin Hajiya ya mike da sauri yana tambayar dama Daddy'n bashida lafiya ne.
kashe wayarsa ya yi batare da yabashi amsa ba.
Hajiya da taji an ambaci Daddy ba lafiya itama ta mike da sauri tana cewa
"Kai Ajimi Abubakar d'in ne ba lafiya?."
ya ce "Eh Ya Abdurrahim ne ya kira ni wai naje narika duba jikin Daddy yana sashin Aunty."
da sauri Ajmal ya fita hajiya tabi bayan sa tana fad'in
"Au Abubakar d'in ba lafiya arasa wanda zai zo ya gayamin a cikin gidan nan akwai wanda ya haifa min shine, zancen banza kai."
bala'i Hajiya tarika har suka isa sashin Aunty.
Aunty na jiyo hayagagarta ta yi sauri ta fito tana fad'in
"Hajiya sannu da zuwa ga Daddy'n ta nan."
"Eh ba shakka anya Fatima ni da d'ana ma amma wai yana ciwo ban saniba kamar bani na haifa ba,
kin kakabeshi cikin d'aki sai ya mutu tukun kifito min da shi, kice kwana ya kare ko me."
Feeryal da ta mike zata shige d'aki ganin Hajiyar, karaf suka had'a ido aiba shiri ja ta tsaya cak....!



Mommyn Twins ce





22
Hajiya ta yaguna fuska da baki ta ce
"Um gayyar tsiya ana tare da mayu a gida taya za'a zauna lafiya."
Feeryal ta sunkiyar da kai bata d'ago ba sai da Hajiya ta shige d'akin Aunty, kafin tayi hanzarin shiga bedroom d'in ta.
Hajiya na shiga ta rike hab'a tana cewa
"Kai Abubakar ya jikin naka, to mene ne amfanin kakabeka da akayi a cikin d'aki,
kana kwance ciwo na karuwa babu sauki."
ta kalli gefen da Aunty take ta kuma yaguna fuska tana cigaba da fad'in
"Kazo ka kwanta a nan alhalin gacan uwargidan ka, in kwanciyar jinya ce idan bazaka iya yin sa a d'akin ka ba, sai kaje d'akin uwargidan ka,
kafin ka fara sanin kowa ita ka fara sani,
'yar'uwar ka uwa d'aya uba d'aya da mahaifinta da naka,
jinin ka ai sai yafi kula da kai fiye da bare, to banjiba ban gani ba ka tashi ka koma can shashin uwar gidan ka kaje kayi jinya,
mu haka muka sani a hausance baza'a kawo mana wani iyayin zamani ba."
Aunty tayi murmushi tare da girgiza kai.
Ajmal ya ce
"Haba Hajiya sai wani surutu kike ko a ina in dai jinya ce ai za'ayi, surutun nan na damin Daddy kiga yadda yake rumtse ido."
"To ai sai ka rufa min baki ka hanani magana, ina ganin gaskiya a zane bazan sallaka ba."
Ajmal ya masa kusa da Daddy yana masa sannu.
sai a sannan ita ma Hajiyar ta maso tana cewa
"Abubakar ya jikin naka abokin turawa ya baka magani kuwa, to ma wai ina yatafi ne kai kana nan a kwance,
yaran yanzu wai tausayin iyaye ma babu a ransu,
na dai gaya maka maza ka tashi ka koma d'akin uwar gidan ka, mu a al'adarmu ta hausa haka muka ni, miji ya yi jinya ad'akin uwar gida,
kai dama Allah yasa 'yar'uwar ka ce uwar 'ya'yan ka."
cikin muryar ciwo Daddy ya ce
"To naji Haji amma anan nafi samu nutsuwa."
"Nutsuwar hofi na dai gaya maka maza ka tashi ka tafi, kafin kasan nan d'in can ka fara sani,
me ya kashe ka dacan, zancen banza kai, kana tare da mayu guri guda ina jiki zaiyi sauki."
ta juya tayi waje tana masifa.
Ajmal ya ce
"Kai wannan mata akwai fitina, gara da kika tafi ma, ki bar mutane suji gari,
Daddy ciwon kan na nan ko yana d'an sauka?."
Daddy ya ce "Da sauki."
Ajmal ya fita yana kiran Abdurrahim a waya ya sanar masa da sauki.
Aunty dake gefe tana tsaye, Daddy ya kirata da hanu.
ta karaso in da yake.
ya ruko hannunta murya a raunace ya ce
"Kiyi hakuri Fad'imatu."
da sauri ta ta tare numfashin sa
"Daddy gaskiya Hajiya ta fad'a can ne ya kamata ka zauna ba nan ba."
"Kinfi so naje na mutu a can d'in bazaki cigaba da taimaka min ba?."
kai ta girgiza zuciya cike da rauni ta ce
"Bazaka mutu ba Daddy sai in kwanan ka ya kare, amma fa ka san da cewa idan bakayi abin da Hajiya ta fad'a ba za'a sami matsala."
ido ya rumtse bai kuma cewa komai ba, tabbas anan ne kad'ai yasan zai rika samin sassaucin abin da yake ji.

Akai-akai Ajmal ke zuwa duba shi kamar yadda Abdurrahim ya ce mishi.
Aunty kuwa time d'in shan magani nayi zata bashi, bayan ta tabbatar da yad'an ci wani abu.

Mommy ta tada bori in da akayi duniya bata yadda ba an d'au kwanan ta a kaiwa Aunty.
taje ta sami Hajiya
Hajiya ta taso ta shigo da bala'i tace dole sai Daddy ya tashi ya koma sashin Mommy, ai batasan yana nan ba tayi zaton ya tafi tun da safe.
dole Daddy ya tashi ya koma sashin sa, sabo da masifar Hajiya, ta ce eh gara ya zauna a sashin nasa bazai zauna a gurin Aunty ba.
har dare Umma Karima bata shigo ta duba Daddy ba tana can tana bidirin ta tana ta shirya yadda abubuwa zasu tafi mata yadda take bukata.

Tun da dare ya yi hankalin Daddy ya yi masifar tashi, ko da Abdurrahim yazo masa allura ya ce kar yayi masa, yana fargabar kada ya yi bacci.
Daddy ya yi ta iya bakin kokarin sa gani bai kwanta bacci ba, amma fa ina bacci b'arawo sai da ya sami nasarar sacesa.
ai kuwa yasha fama cikin bacci,
igiyar wuta tana cinsa suna daf da caka masa mashi.
wani haske yazo yagilma a sakanin su,
duk suka dare.
daga can yaji ana cewa
"Ka kamo haskem can kar kabari ya tsere kayi gaggawan taro shi, shine tsiran ka,
ya zauna cikin rayuwar ka tanan ne zaka kub'uta, idan ya kub'uce shike nan babu tantama zaka mutu a wannan tsekon!."
hasken yatafi can da nisa sannan ya juye zuwa mutum, sai dai an bashi baya baya iya ginin fuskar mutumin.
yana b'acewa wad'an nan halittun suka kuma tasowa suka dawo suka cigaba da azabtar da shi.
dakyar ya farka ya had'a zufa sharaf.
ciwo ya dawo sabo.
Mommy na d'akin amma bata iya taimaka masa da komai ba sai sannu da take ta jera masa.

Har sai washegari Umma Karima ta shigo duba shi, ta koma da karfin gwaiwar ganin aikin ta na tafiya dai-dai yadda take so.

A b'angaren Aunty kusan kwana tayi tana sallah da nima masa sassauci a gurin Allah.
da sassafe taje ta duba shi ganin yadda yadad'a fita hayyacin sa.
ta dawo sashin ta tashiga rusar kuka.
waya ta d'aga ta kira Hajja Umma tana d'agawa takuma saka kuka,
hankalin Hajja Umma yatashi matuka tashiga tambayar ta me yake faruwa,
da kyar ta samu tayi shiru nan take gaya mata abin da ke faru.
Hajja Umma ta sauke numfashi gwuiwa a sanyaye ta ce
"Amma ni a gani na jinyar nan nasa a had'a da na gida, a gani ko za'a dace,
Allah ubangiji ya bashi lafiya, bari Alhaji ya shigo zan sanar masa."
Aunty ta ce to sukayi sallama ta kashe wayar.
tausayin Daddy ya cikata ciwon kwana biyu ya jijjigashi ya fita hayyacinsa gaba d'aya.

Motar Abdurrahim ne yashigo gidan.
yana gyara parking ya fito yashiga sashin Daddy.
ganin jikin Daddy na yau sai da jikin sa ya d'anyi sanyi, bayan ya bashi kulawar data dace ya fito ya wuce ide d'in sa.
yana tsaye cikin bedroom d'in sa yana rage kayan jikin sa yaji an rungume shi ta baya.
tawani lumshe ido
cikin makirarren murya ta ce
"Sannu da dawowa mijin Kuraiba an dawo lafiya ya aiki."

ta dawo ta gabansa tana wani karairaya
tayi sama da hannunta tana tayashi b'alle boturar rigarsa.
tana gama b'alle boturan ta yi kasa da hannunta kan belt d'in wandon sa, tana kokarin kunce balt d'in.
hannunta ya rike ya kauce gefe ya sa kai ya shige bathroom batare da ya ce da ita komai ba.
bayan sa tabi da kallo tana ji kamar ta bisa cikin bayin.
wani mika ta sake tana matse ido, yau ba karamin magunguna ta d'urawa cikin ta ba,
ba'aje ko nan da can ba ta fara sakin layi.
a hankali ta juya ta fita ta koma d'akin ta.
wanka tayi tasa wasu arnan kayan baccin da babu marabar su da babu.
ta jikin window ta hango shi yana fita daga side d'in, tasan gurin Daddy zai je ta sake labule taje ta d'auko wasu magungunan nata ta cuccusa a gaban ta.
tana zama bada jimawa ba taji ana knocking.
ta mike da sauri ta d'au after-dress ta saka kan kayan jikin ta fito, sai taji knocking d'in ta can ta kofar parlour'n sa ne.
da sauri ta nufi parlour'n dan zaton ta shine ko kafar ta kulle ne dole sai an bud'e ta ciki.
tana isa da saurin ta ta bud'o kofar da zummar ta rungume shi, sai ganin Ajmal tayi tsaye rike da d'an karamin flas da glass cup a hannun shi.
murmushin yake tayi ta ce
"Karamin ango ya akayi ne."
washe baki ya yi ya ce
"Matar yaya barka da dare ai naki shiga kai tsaye ne shiyasa nayi knocking."
"Okay mene ne wannan d'in?."
ta nuna flas da glass cup d'in hannunsa.
ya ce
"Sudan tea d'in Ya Abdurrahim ne ya ce nakawo na ajiye masa."
"Okay to kawo mana bari na karasa da shi."
ya mika mata ya yi mata sai da safe ta mai da kofar ta rufe.
har zata haura stairs wani dabara ya zo mata, sai ta dawo da sauri ta nufi gefen ta, tana shiga d'aki, ta bud'e jakan magungunan ta ta ciro wani magani ta barbad'a a ciki ta mosa shi sosai ta mayar da murfin ta rufe.
ta fita da sauri ta haura taje ta aje masa, ta dawo d'akin ta ta kwanta.

Sai wajen 9 ya shigo ya tub'e jallabiyar jikin sa, ya zauna da gajeren wando.
ya d'au flas d'in ya tsayaya tea d'in cikin glass cup d'in,
kana ya soma sha a hankali.
sai da ya kai karshe yaji d'and'anon sa ya babbanta dana kullum, ido ya zubawa kasan cup d'in ganin abu ya kwanta a kasan shi.
juye sauran tea d'in ya yi nan yakuma ganin da alamun abu a ciki.
ya janyo wayarsa ya kira Ajmal, yana d'agawa ya ce
"Ina tea d'in baka karb'o bane?."
da sauri Ajmal ya ce
"Tun d'azu na karb'o Kuraiba ta karb'a ta shiga maka da shi."
kashe wayar ya yi batare da yakuma cewa komai ba.
ya mike yaje yaja bedside ya d'au wani table yad'au gorar ruwa ya b'are ya sha.
kana ya haye gado ya kwanta, bayan ya yi addu'a.
Kuraiba da ya shigo a kan idon ta bata fita ba sai da karfe 11 ya cika,
lokacin itama ta gama jika ta tsumama.
ta mike cike da confidence ta nufi saman shi.

Tayi mamakin ganin sa kwance da alama bacci yake.
dan maganin da ta saka masa bai isa ya iya rumtsawa ba idan bai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login