Showing 57001 words to 60000 words out of 63585 words
Chapter 20 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
ce
"Bakiji me nace bane!?
masu aikin ne bana so su tab'a komai nawa, idan kika sake gigin gayyato su nan wallahi! sai kin raina kanki,
akwai kofa ta can sakanin inda kike da waje ki bud'e surika shigo miki ta can, ban yadda na gansu a area'n nan ba!
fita a d'akin nan yanzun nan!!."
yakuma buga mata tsawa, ta juyo da sauri dafe da fuska tayi waje tana fad'in
"Ka mare ni Abdurrahim."
tsaki yaja ya shige bathroom.
Yana fita ya tarar da Missed call d'in Mommy a wayar sa.
yana saka kaya ya fita ya tafi sashin Hajiya.
Hajiya na ganin sa ta ce
"Yauwa abikin turawa da ma yanzu nake kan cewa Kulu ta kira min kai,
ciwon gwuiwan nan ya sako ni gaba kwana biyu."
zama ya yi yana fad'in
"Muga kafar."
ta ja zani saman gwuiwar tana cewa
"Ka ganshi nan zugi kamar ya kwana biyu hanani bacci yake, yanzu ko na sha na shafa maganin da ka banin nan baya dai na zugin."
yatsar sa ya d'aura kan gwuiwar yana d'an daddannashi sannan ya d'ago ya gyara zaman sa ya ce
"Za'a canza miki magani, anjima zan kawo miki."
"Yauwa ai gara a kawo min wani, wannan gwuiwa ya sako ni gaba."
bai kuma magana ba sai wayarsa daya zaro yana daddannawa.
Hajiya ta gyara zama ta dube shi tana rike hab'a tare da fad'in
"Wai ni kam abokin turawa har yanzu banji
ana fad'in yarinyar nan Kuraiba ta d'auki ciki ba, ko baku fad'a bane? to ai ko baku fad'a bama za'aga alamar ciki tare da ita,
akwai cikin kuwa?."
baki ya tab'e batare da ya ce komai ba.
Hajiya ta ce
"Ni halina da kai ke nan, ana ma magana kayi banza da mutane, gara ka fad'a tun da wuri a sani a nemo maganin tsari a sunkuya bata,
dan gidan nan yanzu ya zama abun da ya zama miyagu suna son kafa sansanin su,
ban san me ke damin Abubakar ba wannan yarinyar Feeryal ba abin a zauna da ita a guri bane,
bari zanyi tattaki naje Yelwa na karb'o mata magani a rufa idon makiya akan abun cikin,
idan ta bar gidan ba shike nan ba kowa ma ya huta, wannan karo ko ba'a gama bincike ba zata koma,
iya shegen banza kawai ina gashi nan ni ina ganin ku ina jin dad'i,
shine bazai so ganin jikokin sa ba, idan aka barta tayi wa cikin wani abu fa tun da su dama jinnu sunfi son karnin jini,
kafin a sake samin wani ai sai an kuma yin wani watannin,
ba gara a tare ko mai tun da wuri ba, bari Abubakar zai zo ya same ni."
d'ago idon sa ya yi daga kallon waya ya kalle, wato ita a lissafin ta ciki Kuraiba take da shi.
baki ya tab'e ya mike yana fad'in
"Da ma tana da ciki ne?."
"Yo iyashegen banza ai kai kafi kowa sani in tana da shi ko babu, kardai kuyi irin abun zamanin nan aure kusan wata 6 ai yaci ace yanzu tana da cikin wata 5 ko shidan ma."
takalmansa ya zura ya fice
daga nan ya wuce masallaci...
Bayan wata biyu da cire cikin Siyama
Bilkisu da Saddiqa suna zaune a d'aki wanda dama su biyu d'akin su d'aya,
Rahma da Nabila suma d'akin su d'aya, Siyama nata daban.
Saddiqa da yawu ya cika mata baki ta mike taje ta zubar a toilet ta dawo.
jim kad'an ta kuma zuwa ta zubar.
ta kuma mikewa zataje zubarwa Bilkisu ta ce
"Ke dalla kin dami mutane da tofe-tofen yawu, wai ba dama mutum ya zauna kusa da ke sai yawu,
wani iskancin saran da kika samu kwana biyun nan ke nan, kibi ki ishi mutane da yawu da kakarin amai."
Bilkisu bata rufa baki ba Saddiqa ta kuma mike wa da gudu ta shige toilet tashiga kakarin amai.
Bilkisu ta mike tsaye ta taho bakin kofar toilet d'in ta ce
"Ke Saddiqa wai me ke damin ki, baki da lafiya ne bazaki fad'a a kira Family Dr ya zo ya duba ki,
ko kije ki gayawa Ya Abdurrahim ya baki magani ba."
Saddiqa ta mike tana kuma tofar da yawu.
Bilkisu ta harare ta tana kuma fad'in
"Wlh ni ni yanzu bamma yadda da ke ba, jiya maganar me kike sakan dare a waya,
duk da a bacci na tashi amma na fahimci akwai wani abun da kike b'oyewa."
ta juya da sauri tafita a d'akin ta nufi d'akin Umma Karima tana shiga ta ce
"Wallahi Umma ban yadda da Saddiqa ba, ki kirata ki binciketa wlh kamar ciki take da shi, tabi ta dame ni da amai da zubda miyau."
Umma Karima ta zabura tare da buga kirji ta ce
"Ciki! nashiga uku ina Saddiqa'n ta ke."
ta mike a haukace tayi waje tana kwad'awa Saddiqa kira.
Saddiqa ta fito da sauri jiki a sanyaye.
Umma Karima ta dubeta sama da kasa tana haki sannan ta ce
"Biyo ni nan maza ki bani fitsarin ki na gwada in dai ciki ne kin gama da ni Saddiqa."
Bilkisu Rahma Nabila Siyama duk suka rufa musu baya.
Kulu mai aikin Hajiya da tazo karb'awa Hajiya hayaki gun Umma Karima, taja ta tsaya tare da rike baki tana binsu da kallo har suka shige d'akin Umma Karima.
Umma Karima ta d'auko tsinken gwajin ciki ta mika mata d'an karamin kwantena ta sata gaba suka shiga bayi tana tsaye a kanta tayi fitsari ta bata.
ta saka PT ciki taja ta tsaya tana fifita da d'an kwalinta.
bai mata ba ta fito parlour rike da PT, gani tayi d'akin ya kasa mata.
'ya'yan nata suka biyo ta.
wani uban ashar Umma Karima ta mulmulo ganin amsar tana da ciki sinken gwajin ya bayar.
ta sake shi a kasa ta sa hannu akai tana fad'in
"Nashiga uku ni Karima Saddiqa kema cikin kikayi!
a ina kika samo ciki wani d'an kutumar uban ne ya miki ciki!."
Kulu ta waro ido ta juya sad'af-sad'af ta yi waje tana kama baki.
Saddiqa tayi kasa da kai jiki na rawa.
Umma Karima ta buga mata tsawa
"Dan uban ki ina tambayarki uban wa yamiki ciki zaki gaya min ne ko sai naci kutumar uban ki."
Saddiqa ta zabura murya na rawa ta ce
"Um..mu...."
sai kuma tayi shiru.
Umma Karima tayi kukan kura tayi kanta da sauri ta b'oye bayan Bilkisu tana fad'in
"Zan gaya miki Umma."
"Zo nan gaba na ki gaya min."
ta fad'a tana huci.
ta zo jiki na rawa tashiga kame-kame ta na fad'in
"Um..um..saurayin Aunty Siyama ne."
Siyama da Umma Karima suka waro ido a tare.
Umma Karima ta ce
"Au tsinanne tambad'ad'd'e, d'an akuya sabo da shi ya zamo bunsuru yabita ya barbare ta yakuma biyoki ke ma,
sabo da wancan karon ban d'auki mataki a kan saba, shine bari ya kuma b'ulluwa ta hanyar baya ya d'ura miki ciki ke ma,
ke Siyama d'an gidan uban waye ne shi da yake binku yana barbarar ku,
sai na ga uban sa Wallahi."
su Nabila suka waro ido dan dama basusan da na Siyama ba.
Kulu da saurinta ta shige sashin Hajiya.
Hajiya na ganin ta babu aikan da ta mata ta ce
"Ke Kulu ina hayakin dana aike ki karb'a?."
Kulu ta ware ido ta rike hab'a ta ce
"Hajiya wlh akwai babban matsala a gidan nan, wannan yarinya Saddiqa 'yar wajen Hajiya Karima ciki take da shi, ciki tayiyo wlh Hajiya yanzun nan aka gano tana da ciki."
Hajiya ta saka salati tana fad'in
"Wasayyawu ni jikar mutane hud'u Saddiqa'n ce tayiyo ciki, ciki dai acikin gidan nan,
maza kirawa min Abubakar da abokin turawa."
Kulu ta d'au wayar Hajiya ta kira lambar Daddy yana d'agawa ta mika mata.
ta karb'a ta kai kunne tana ta ce
"Abubakar kasan musifar dake faruwa agidan nan kuwa, maza kazo yanzu ina niman ka."
ta kashe ta ce wa Kulu kira min abokin turawa.
wayarsa tayi ta ringing bai d'aga ba.
Kulu ta ce "Bai d'aga ba Hajiya."
ba'a jima ba Daddy ya shigo da fargabar abin da Hajiya zata ce masa dan yasan maganar Hajiya bazai wuce akan Feeryal ba.
tun kafin ya zauna ta ce
"Abubakar Saddiqa da cikin shege a cikin gidan nan, wace irin musifa ce wannan, acikin gidan ka cikin shege ya b'ullo."
da sauri Daddy da maganar ta duki kirjinsa ya kai hannu ya dafe kirji.
ya zauna kan kujera da kyar hannunsa dafe da kirjin sa.
"Innalillahi wa innailaihirraji'un!."
kalmar data fito daga bakin Daddy ke nan.
Abdurrahim da shigowarsa ke nan yaga kiran Hajiya yana masallaci.
ya karaso da sauri ganin yanda Daddy ke dafe da kirjinsa zaton sa ciwon sa ne ya tashi yasa Hajiya ta kira sa.
ya sunkuya gaban Daddy tare da cire hannunsa dake kirjinsa ya d'aura nasa yana fad'in
"Daddy ya kake jin kirjin ya ke maka."
ido ya rumtse ya ce
"Zafi sosai yake min Abdurrahim."
Hajiya ta ce
"Yo wad'an nan 'ya'ya su zasu kasheka, bansan meye kake jira ace wad'annan gandan-gandan d'in 'yanmata suna zaune a gida babu aure, ba dole su d'auko magana ba,
gaba d'ayan su da an musu aure kan lokaci da yanzu 'ya'ya biyu ko uku suke da shi,
har autar tasu Nabila takai ta haifi d'a d'aya zuwa biyu;
to Saddiqa ta d'auko ciki sauran ma ba'a san in da hali zaiyi ba."
da karfi Abdurrahim ya d'ago ya furta
"Ciki!."
Hajiya ta ce "Kwarai kuwa cikin shege tayi, wannan irin abin kunya ace daga gidan nan ya fito."
wani irin mikewa ya yi damasunsa sukayi wani irin bud'ewa, b'acin rai karara ake iya hangowa kan fuskarsa.
da sauri ya juya yana taka kafafunsa a kasa, kasa tana amsa sautin takunsa
dip-dip-dip!.
ya b'allo reshen fulawa ya nufi sashin Umma Karima.
yadda ya fad'o cikin parlour ba 'ya'yan nata ba hatta ita kanta Umma Karima sai da ta razana..
ya yi kan su su Saddiqa da duka kan mai uwa da wabi, ba ita kad'ai ba har da su Bilkisu Rahma Nabila.
sai da itacen ta karye tayi kaca-kaca a jikinsu.
Siyama ta mike da gudu ta masa bayan Umma Karima dan bulalar sai da ya same ta,
ransa ya kai kololuwa wajen b'aci yayi jifa guntuwar itacen hannunsa,
ya cafko
Saddiqa yana kokarin kuncen belt d'in wandon sa.
Umma Karima ta yi saurin cewa
"Wlh in gaya maka Abdurrahim fyad'e aka mata, fyad'e d'an iskan yaron ya yi mata bada son ranta ba."
wani mari ya d'auketa da shi sai da ta kife kasa.
ya shiga nuna su da yatsa cikin kakkausar muya yake fad'in
"Wallahi! idan kukasa bakincikin ku ya yi sanadiyyar bugawar zuciyar Daddy, na rantse dukkanin ku sai na cire zuciyoyin ku da hannuna!."
ya yi shot da Saddiqa a yadda yake jin kansa idan yacigaba da tsayu zai iya kusan kashe ta da duka......!
Mommyn Twins ce
Abdulrahim na fita Umma Karima tayi kan 'ya'yan ta tana fad'in
"Ai kin gani Saddiqa kin janyo muku duka dukan ku, idan badun nace masa fyad'e akayi miki ba da kinci ubanki a hannunsa,
yazama dole kema aje a cire cikin nan,
dan wlh ban shiryawa abin kunya ba,
'yan iskan yara suna ni man sa ni a bakin duniya."
a b'angaren Daddy kuwa da kyar ya iya mikewa yana jin kirjin sa na yi masa zafi, ya lallab'a ya tafi sashin Aunty.
ganin yanayin sa Aunty ta tare shi a d'an tsorace tana fad'in
"Subhanallahi ya dai Daddy ba dai jikin ba dai?."
ta rike hannunsa ganin yana kokarin zama bakin gado, ya zauna yana mai dad'a kankame hannunta.
Aunty tayi kokarin zame hannunta tana fad'in
"Daddy bakasha magani ba ko bari na d'auko maka kasha."
ya dad'a rike hannunta tare da girgiza mata kai ya ce
"Barshi Fad'imatu dan ko na sha ma babu amfanin da zai min."
jikin ta ya yi sanyi sosai ta ce
"Daddy dan Allah kar ka bani tsoro, me kake ji yanzu, ya kirjin ya ke maka."
"Zafi sosai yake min Fad'imatu sai ina ji kamar zafin yafi na baya."
kallon sa ta ke cikin tsoro "Fad'imatu."
ya kira sunan ta murya a sanyaye ta gyad'a masa kai alamun tana jinsa.
hannunta ya dad'a rikewa gam kana ya soma magana
"A cikin gida na ni Abubakar Fiya, aka samu mai yin ciki a waje a cikin 'ya'yana,
Fad'imatu ina jin zafi sosai cikin zuciya ta."
wani irin waro ido Aunty tayi kirjinta ya buga da karfi ta ce
"Daddy wacce irin magana ce wannan maraddad'in ji!?."
kai ya gyad'a mata ya ce
"Tabbas Saddiqa tayi ciki a waje Fad'imatu har haka na gaza a gida na?
me mutane zasuce a kaina."
Aunty ta dad'a jin gaban ta ya tsinke jikin ta ya yi sanyi matuka,
taji rashin dad'in abun ba kad'an ba,
duk da mugun hali irin na uwar Saddiqa bazatayi fatan ace d'iyarta ta kasance cikin wannan halin ba,
jiki a sanyaye ta ce
"Daddy baka gaza ba masu taimako ne aka sami sakaki daga wajen su, uwa ita ke taimakon uba wajen yiwa 'ya'ya tarbiyya, a yayin da uba ya fita nima,
kayi hakuri Daddy jarabawa ce babu wanda yafi karfin kaddara,
mutane zasu fahimceka dan sun san cewa kai tsayayyen uba ne;
ka rungumi kaddara mai imani ne ake jarabtar shi ta ko wacce hanya,
shin Daddy ka mance imanin mutum bazai cika ba har sai ya gaskata ya kuma yarda da wad'annan abubuwa guda shida,
yadda da ALLAH d'aya ne kayi imani da shi, da mala'ikunsa da duk littattafan da ya saukar, da duk manzannin da ya aiko,
da ranar karshe wato ranar kiyama,
da KADDARA mai kyau ko mara kyau;
Daddy kaddarar mu ce bazamu tab'a ketare masa ba, kayi hakuri dan Allah Daddy ka barwa Allah ko mai kaji Daddy."
ta zauna gefen sa ta cigaba da kwantar masa da hankali,
wanda cikin kankanin lokaci yaji nutsuwa tare da shi.
A cikin gidan kuwa labari ya soma yawo kamar dai yadda idan abu ya faru ake kai kawo da shi.
sai dai wannna karo masu yawo da zance kasa-kasa sukeyi dan yau abin maganar daga tushin uwar kai kawo ya fito, wato Umma Karima.
tarika sakaye wa tana cewa ai fyad'e aka mata.
a ranar da abun ya faru da daddare Umma Karima tasa Saddiqa gaba suka ce sashin Daddy.
yana zaune a parlour yana kallon labarai a TV.
Mommy na zaune a gefe san yau ita ke da Daddy.
Umma Karima ta zauna saman kujerar da ke fuskantar sa, Saddiqa ta zauna a kasa.
Umma Karima ta marairaice murya dake nuni da zallar shiga matukar damuwa ta ce
"Alhaji yanzu fisabilillahi kaji abin da ya faru, amma baka zo kaji taya hakan ya faru ba,
shike nan za'a zuba ido a gyale yaron da ya keta mata haddi ya mata fyad'e ke nan, baza'a d'auki wani mataki ba,
ko d'an gidan uban waye baza'a tura hukuma suje su kamo sa ba,
shiru za'ayi da batun ke nan abu tun safe kayi shiru bakace ko mai ba har dare."
Daddy ya dube ta da d'iyar tata da ta sunkuyar da kai ya jinjina kai tare da fad'in
"Me kike so nace a kai bayan ke ce uwan ke ce uban, duk abin da kikaga dai-dai ne kije kiyi Hajiya Karima."
daga nan bai kuma cewa komai ba ya kwashi wayoyinsa da system d'in sa ya shige bedroom d'insa.
Mommy ta ce
"Haba Alhaji bai kamata ka ce haka ba, kamata ya yi ad'au mataki a kan yaron."
Umma Karima ta mike cikin d'aga murya take fad'in
"Rabu da shi Hajiya Halima,
sabo da an gama da kai an wanke an baka, waccen tambad'ad'd'iyar tsintacciyar aljanar ruwan,
ganin ta ne ba'ayi ba kawai da daddare kabi ka d'aga hankali ko bacci bakayi ba, alhalin gurin iskancinta ta tafi sai da akaje aka d'auko ta a hotel gurin samarukan iskancinta,
sai 'yar da ka haifa wani ya sace ta yaje ya mata fyad'e kayi ko oho,
to wlh bazan yadda ba 'ya'yana ba tumakai bane da ko wani d'an iska zai rika hawansu ya share lafiya, zakaga abin da zanyi."
ta ja hannun Saddiqa fuuu sukayi sashin Hajiya.
suna shiga ta fashe da kuka tana fad'in
"Yanzu fisabilillahi Hajiya ace ayiwa yarinyar nan fyad'e, Alhaji ya yi ko oho sai kace zuwa da 'yar nayi gidan nan."
Hajiya ta ce
"Ke da'alla dakata Karima ki na nufin ki ce da karfi akayi mata cikin, ba maza tabi tayi yo cikin ta ba."
Umma Karima tashiga rantse-rantse ta na fad'in
"Ga Saddiqa'n ta fad'a da bakin ta ba saceta ya yi yaje yayi mata fyad'e ba."
Saddiqa ta kama gyad'a kai tana fad'in da karfi ya yi mata har da kukan ta.
Hajiya kuwa ta yadda har tana cewa baza'a kyale yaron ba, kuma zatayiwa abokin turawa magana ya zubar da cikin.
Umma Karima ta koma da kwarin gwuiwa ganin hakarta ya cimma ruwa.
Washegari da safe kuwa Abdurrahim ya shigo sashin Hajiya da shirin tafiya asibiti.
Hajiya ta ce
"Yauwa abokin tuwara da ma yanzu nake shirin niman ka, ka d'auki 'yar'uwan ka kuje asibiti ka cire mata cikin nan karya girma ya zame mana abin gori, duk da fyad'e akayi mata amma mutane bazasuyi la'akari da hakan ba,
gara tun wuri a cire shi tun kafin a busa masa rai ayi zunubi."
wani kallo ya wurgawa Hajiya kana ya juya ya soma tafiya yana fad'in
"Ba dai ni ba ba kuma asibiti na ba."
ya fice ya shiga mota ya bar gidan.
Aunty tashigo sashin Umma Karima ta isketa zaune ita kad'ai sai mai aikin ta da take ta mata hidima.
Umma Karima ta bita da kallon mamakin ganin ta yau a sashin ta, wanda tun ranar da aka kawo ta gidan iyayen ta suka kawota sashin Umma Karima tun daga ranar bata tab'a sake taka kafarta cikin sashin nata ba, duk tsawon shekarun nan sai yau.
Aunty ta nimi guri ta zauna kan kujera kana ta dubi mai aikin nata ta ce
"Bamu guri zamuyi magana."
nan da nan ta juya ta bar gurin.
Aunty ta gyara zama ta kalli Umma Karima wanda da dama ita ma ita take kallo,
Aunty ta yi murmushi sannan ta ce
"Hajiya Karima ke nan kina cike da mamakin gani na yau a cikin parlour'n ki zaune a kan kujerar ki ko?
aje wannan mamakin ki fiskance ni, kin san me ya kawo ni nazo ne na tuna miki abin da kika manta,
yau ga miyagun kalamanki sun fad'a kan d'iyar ki, 'yar da kike kira karuwa ita ta iya tsare kanta da taimakon Allah bata aikata abinda kike ta mata fata ba,
sai gashi ke mai tsoron Allah an samo fasa gurbi cikin koyayen ki;
na dad'i ina jiran rana mai kamar tayau sabo da na mai da miki amsar kalaman ki,
amma kash banso ranar ta kasance rana mai muni irin haka ba,
wlh shine Allah nayi bakincikin abin da ya faru, bana farin ciki dan Saddiqa tayi ciki,
sabo da itama 'yata ce tun da d'iyar mijina ne,
amma ina so ki san da cewa
shi Allah sam baya bacci, shi yasa ya nuna miki ishara idan ke mai hankali ce ki gani,
kina da wasu 'ya'yan mata rai uku bayan Saddiqa ga kuma kanwarki cikon na biyar d'in su;
ki kwanta kiyi nazari kiyi amfani da kwakwalwarki,
kiyi kokarin baiwa sauran tarbiyyar da zai sa su kyamaci zina,
idan kuma ke kasashshiyar uwa ce,