Showing 12001 words to 15000 words out of 63585 words
Chapter 5 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
cikin matukar damuwa.
Mom d'in sa ta waro ido ta ce
"Wlh karya ne bazai yiwuba dole a wanke zargin da aka maka a gaban kotu, daga zuwa niman aure dan baza'a baka ba sai a bika da mummunar kazafi,
to wlh bazan lamunta ba sai mun d'au mataki."
ta d'aga waya ta kira lambar Dad d'in sa ta sanar masa abin da ke faruwa.
baya kasar amma yace sabo da faruwar haka zai dawo, dan ya ce bazai lamunce wulakanci da tozarci kan d'ansa d'aya tilo ba.
amma da jin ko a wani gida lamarin ya faru ya ce
bazai dawo ba amma zai nimi Alhaji Abubakar d'in da kansa,
dan yana ganin mutuncinsa dan yasan shi mutum ne mai mutunci.
nan da nan ya nimi Daddy a waya, Daddy yana hanyar dawowa gida daga office kiran Dad d'in Ibrahim ya shigo wayarsa.
Umma Karima najin shigowar Daddy, ta nufi sashin Mommy da sauri, tana shiga ta isketa a parlour tun kafin ta karaso take fad'in
"Hajiya Halima taso maza muje naji shigowar Alhaji kafin wancan makiran matar can tasa,
ta rigamu zuwa ta je ta kitsa masa makirci yahau ya zauna a kai,
gara a yi ta ta kare yau 'yar nan ta bar gidan nan,
badun Hajiya bata gari ba, ai da anyi ruwa an d'auke."
"Ai kuwa maza muje dan ni tun da nake ban tab'a ganin makirarriya irin Hajiya Fatima ba,
tagama da Alhaji gaba d'aya wlh ji nake kamar ta mutu na huta."
"Hm kyale munafukar can taurin rai gare ta amma ajuri zuwa rafi saura kiris tulu ya tarwatse."
cewar Umma Karima tana jinjina kai.
suka fita suka nufi sashin Daddy.
Daddy na zaune a parlour'n sa dan da ya shigo a parlour ya zauna bai shige ciki ba.
har suka shigo suka sami guri suka sauna bai d'ago ba yana abinda yake yi.
suka had'a baki sukayi masa sannu da dawo wa, ya amsa, batare da ya d'ago ba.
Umma Karima ta d'an tab'a Mommy tayi mata alamar ta fara magana.
Mommy ta gyara zama tare da fad'in
"Alhaji mun zo gurin ka ne, yanzu fisabilillahi Kai kaji ka amince 'ya'yan ka su zamo tambad'ad'd'u ta sanadiyyar 'yar da ba'a san asalinta ba ma,
bafa zai yuwu ba yazama dole a kawo karshen lamarin,
iskancin yarinyar nan ya tashi a waje ya dawo har cikin gida kana sane kayi shiru,
bari Hajiya ta dawo dan wlh mu bazamu zuba ido muna gani tarika shigo mana da 'yan'iska cikin gida,
ga 'ya'yan mu mata suna cikin gidan ba."
Umma Karima ta ce
"Ato gaya masa dai,
yarinya tasan ta rika kawo 'yan'iska cikin gida suna iskanci ai abin nata ya girmama ya kai makura,
da idanuna na gansu a tsaye a bakin get d'in sashin Hajiya Fatima, ya shige cikin hijabinta suna shagalin su,
ni tun da nake ban tab'a ganin tambad'ad'd'iya irin aljanar yarinyar can ba."
Daddy ya d'ago yana dubansu rai b'ace,
ya nuna Umma Karima tare da fad'in
"Sai da nayi sammanin daga gurin ki maganar nan zai fito, da Alhaji Shitu Abdu ya sanar min,
ke Hajiya Karima ki kiyaye ni wai me ke damun ki ne kam Hajiya Karima?
kin san waye Alhaji Shitu Abdu kuwa?
to bari kiji taken sa mai kud'in shari'a, ba'a tab'a takasa a share lafiya sai ya yi shari'a da koma waye,
me ya kaiki shiga lamarin sa ina ruwanki;
badun yana ganin mutuncina ba da yanzu kinji sammaci daga kotu,
idan kiyi wa Fad'imatu kin share, ko ince ni tunda Feeryal a gurina take nine ubanta,
to Alhaji Shitu Abdu bazai jure tozarta masa d'a ba,
ki dawo hankalin ki nagaya miki ke nan!."
Daddy ya mike rai b'ace ya kwashi wayoyin sa ya nufi bedroom yana cigaba da fad'a.
Umma Karima ta d'a murya ta nad'e taburman kunyarta da bori
"Eh da ma ai zaka ce haka tun da ni mai jinin kule ne, yazo ya yi sammaci na mana muzuba mugani da ni da shi wazai fad'i a shari'ar,
in shi mai kud'in shari'a ne ni mai bakin kare kai ne,
haka kawai ga gaskiya muraran a nimi rufa gaskiya da bayan hanu."
ta mike fuu ta bar parlour'n.
ta bar Mommy nan zaune dan dama ita ce da Daddy.
Koda Umma Karima ta fito zata koma sashin ta can ta hango,
motar Abdurrahim da shigowar sa ke nan yana kokarin gyara parking a babban parking lot.
ta karaso, dai-dai sanda ya fito daga motar ya maida marfin motar ya rufe,
waya na rike a hannunsa yana kokarin tura kira.
ta ce
"Sannu da dawowa Abdurrahim ya aikin dai."
"Alhamdulillah."
ya fad'a a takai ce yana kokarin barin gurin.
Umma Karima tayi saurin fad'in
"Da ma yanzu nake shirin kiranka idan na koma ciki,
na ce da kai idan ka dawo kazo ina niman ka."
bai yi magana ba sai kiran da ya katse yana son jin abin da ke tafe da ita.
ganin hakan ya sata fad'in
"Abdurrahim ace kana cikin gidan nan, abubuwa da yawa suna ta faruwa a matsayin ka na babba a gida, kana ji baka d'au wani mataki ba,
a kaf gidan nan fa daga alhaji sai kai,
ko kannensa Alhaji Sulaiman da alhaji Tukur sai dai su biyo bayan ka su jira umurnin ka,
dan kaine Alhaji karami.
amma ace sanannen gida kamar wannan a aje tukururuwar karuwa aciki tana d'ebo 'yan'iska tana shigo wa da su har cikin gidan nan,
ba'a taka mata burki ba;
ai ko dan gudun gurb'acewar kannen ka zakayi wani abu, kafin ta kai ga lalata musu rayuwarsu suma,
wannan yarinyar da Hajiya Fatima ta tsinto annoba ce a gidan nan,
sam ba yar arziki bace irin tambad'ad'd'un aljanun nan ne,
haka shekaran jiyan can ta ja su Ameerah ta kaisu gurin party, haka ta tsaya a bainin nasi tana rungume rungume da maza,
ga video a wayan Ameerah kowa ya gani iskanci muraran,
yau har gida abokin iskancin nata ya biyo ta,
aka kamasu hanu da hanu,
haba ina amfanin sa abin nata ya yi yawa."
"To ni meye matsala ta da hakan Hajiya Karima?
ki sanarwa Aunty'n da ta kawo ta mana, inaga zai fi."
ya yi maganar yana picking na call d'in da ya shigo wayar sa,
ya kai wayar kunne ya fice a parking lot d'in.
Umma Karima ta bi bayansa da mugun kallo a fili ta ke fad'in
"Wannan d'an iskan yaro har gobe bazai canza halinsa ba,
in banda tsabar rashin daraja,
ni da na zauna shekara da shekaru da uban sa da Hajiya Karima ya ke kirana, sai wancan juyar yake kira da Aunty,
a sannu duk zaku dawo karkashin ikona kai da uban naka."
tayi kwafa a fili, ta juya ta nufi b'angaren ta.
Har ya d'au hanyar sashin sa sai kuma ya juya ya nufi b'angaren Mommy.
a bakin kofar parlour ya tsaya, su Ameerah da Sumayya suna zaune cikin parlour'n ko wannen su da waya a hannunsa suna chatting.
suna ganin sa kowa ya shiga taitayin sa, duk suka aje wayoyon suka shiga gaishesa.
batare da ya amsa gaisuwar tasu ba ya dubi Ameerah fuska a murtuke ya ce
"D'auko wayar ki ki zo nan!."
da sauri ta mike ta d'au wayar ta tako gabansa kirjinta na dukan tara-tara
hannun ta na rawa ta mika masa.
ya amsa tare da kuma tamke fuska ya daddana zuwa can ya d'ago tare da nuna mata screen d'in wayar ya ce
"Uwar me kika ajiye sa kike yi da shi a wayar baki goge ba?."
da sauri tayi kasa da kanta tashiga kame-kame dan irin kallon da yake jifan ta da shi tasan babu ko shakka zata iya samin tsarabar duka.
da sauri ta ce
"Dama..dama.ban..bansan yana nan ba nayi zaton na goge tun ranar."
wani mugun kallo ya wurga mata ta kuma shiga taitayin ta da kyau.
ya mai da idanunsa kan wayar kana ya d'ago ya ce
"Ina video yake?."
da sauri ta d'ago ya tsare ta da ido, baki na b'ari ta ce
"Babu wani video hoto ne kawai."
ganin yadda ya tsare ta da ido murya na rawa ta soma rantse-rantse
"Wlh Ya Abdurrahim iya hoto ne kawai na rantse da Allah babu video kuma ka duba ka gani ma."
bai kuma magana ba sai idon da ya tsare ta da shi.
cikin dakika guda ya karanto iya gaskiyar take gaya masa.
wayar ya wurga mata kad'an ya fad'i kasa tayi saurin taro sa,
ya nuna ta da yatsa tare da kad'a yatsar yana mai taune gefen lips d'in sa alamun gargad'i,
kana ya juya ya fita.
Sumayya da ke zaune cikin ta ya d'ura ruwa.
tana ganin fitarsa ta mike da sauri ta na fad'in
"Ina ga irin ta ina kinga abinda nake guje miki,
hoto kawai kika d'auka a kaci ubanki da duka ina kuma ga kin yad'ashi wa media,
ai wlh da baki da wata mafita gun Ya Abdurrahim zai ce dama aikin ki ke nan, yad'a hotunan bad'ala;
Allah ya taimake ki."
Ameerah ta dalla mata harara tana cewa
"Ke nifa bana son munafurci ina ruwan ki, ai na rantse bazan kyale yarinyar nan ba sai nasa an mata dukan tsiya shegiya mai idon mayu,
ai tun da aka bige ni a kan laifin ta wlh itama sai ta sha duka."
"To Allah ya taimake ki Ameerah ni dai in zaki bi ta tawa da kinyi hakuri kawai."
"Anki a bi takin Sumayya ke nifa bana son shishigi."
Sumayya ta juya ta nufi bedroom d'in su tana fad'in
"Kar ki fasa Ameerah."
cikin d'aga murya Ameerah ta ce
"Ai dama bazan fasa ba, na rantse sai ta duku."
Sumayya bata kuma bi ta kanta ba ta shige bedroom abinta dan tasan halin ta sarai yanzu sai ta huce fushin goge hoton da yayan nasu ya yi a kanta.
Hajiya bata nan taje ta'aziyya a yelwa, sai da tayi kwana uku kafin ta dawo,
tun bata hutaba labari ya isar mata.
ta ce wa Ajmal da ya shigo yi mata sannu da dawowa ya kira mata Daddy.
shiko ya mike ya nufi kofar fita yana fad'in
"Kijira ya dawo mana."
"Kai Ajimi iya shege zaka kawo min, ka kira min uban ka ka ce na jira shi, gaka min iya shegen banza,
ban san me Abubakar yake nufi ba,
daga ce ta d'an zauna na wani lokaci kafin a gama bincike,
shike nan sai ta shari gindi ta zauna har malikiyaumiddini, to bari ya dawo ya same ni zaman nata ya isa haka ta kara gaba,
nagaji da gayyar tsiya arna gun idi."
Da daddre Daddy da ya shigo gaishe ta ko zama baiyi ba ta taresa da maganar.
ta ce gobe gobe yasata a mota ta koma inda ta fito.
da kyar Daddy ya samu ya lallab'a ta ya ce saura kiris a gama binciken ana gamawa zata koma, Hajiya ta rika bala'i haka dai ya tashi ya barta
★★★
Yau Feeryal tun da yamma take side d'in su Miemie,
har bayan sallar isha, tun kan magriba taso komawa b'angaren su Miemie ta ki barinta.
har dai da sukayi sallar isha kafin suka fito ta rako ta.
suna tafe suna d'an hirar su, suka taho ta kofar b'angaren su Ajmal.
Zaraddin da tun fito warsu a kan idon sa yana hango su ta saman bene, kafin su karaso ya yi saurin sauko wa.
suna isowa ya fito yana wage baki.
Miemie ta ce
"La Ya Zaraddin ashe kana nan, kwna biyu ina ka shiga ne bana ganin ka."
kirjinsa ya shafa yana bin Feeryal da wani irin mayataccen kallo ya ce
"Tafiya nayi d'azu na dawo."
murmushi Feeryal tayi tana janye idanunta daga kallon da ya ke mata cikin siririyar muryarta mai kama da mai yin shagwab'a ta ce
"Sannu da dawowa Ya Zaraddin ka dawo lafiya."
wani irin lumshe ido ya yi ya wani rungume hannunsa a kirjinsa da ke ji ina ma ace ta fad'o cikin sa,
komai na yarinyar ya had'u babu makusa ko kad'an.
ya karkace kai yana cigaba da aika mata irin kallon nan nasa sannan ya ce
"Daku na fara had'uwa da na shigo ku yakamata ku fara kunce jaka ku kwashi tsaraba,
musamman ke da kikayi min barka da dawowa lafiya."
ya yi maganar idanunsa akan Feeryal.
"Oh lallai ma Ya Zaraddin d'in nan amma ai ni na fara tambayar ka banganka ba kwana biyu."
Miemie tayi maganar tana d'aga kiran Ammah da ya shigo wayarta.
"To Ammah."
ta fad'a tana sauke wayar.
ta dubi Feeryal tana fad'in
"Ki karasa bari naje na bawa Ammah ATM d'in ta zata aiki direba kuma ni na aje mata shi wai bata gani ba, ina zuwa yanzu."
Feeryal ta gyad'a kai.
Miemie ta juya da sauri.
Feeryal ta d'aga kafa tana kokarin barin gurin,
da sauri Zaraddin ya ce
"Ah ina kuma zakije tun baki karb'i tsarabar ki ba,
ai kin cancanci tsaraba mai tsoka ke da kikayi min fatan na dawo lafiya ai dole na saka miki, taho muje ki karb'i tsaraba sai kinso ki samma Miemie."
ya juya ya shige kofar dide d'in su, sannan ya juyo ya ce
"Zo mana zo muje ki karb'a."
ya yi maganar yana gwada mata hanya.
a hankali ta d'aga kafarta da zummar biyo shi.
wata mota da ta shigo gidan yanzu fitilar motar ta hasko mata ido.
da sauri ta kai hannunta biyu ta kare fuskata,dan har jijiyar idanunta sai da ya amsa sakamakon hasken nan.
Tsawon sakanni 20 wutar motar bata janye a kanta ba.
da sauri ta matsa gefe tare da janye hannayen ta kan fuskarta, sai a sannan ta sami damar iya bud'e idanunta.
abin da ya bata mamaki motar tana tsaye batayi gaba ba ba'a kuma kashe wutar motar ba.
maganar Miemie ta juyo a bayan ta
"Feeryal muje gashi har na dawo."
Miemie tayi gaba Feeryal ta biyo ta, da sauri Miemie ta d'an dawo da baya ta ruko hannun Feeryal ta ce "Motar Ya Abdurrahim ce wannan zo mubi ta can.......!
*Babu editing a karanta da hakuri*
Miemie ta janyo hannunta suka bi gefe.
yana zaune cikin motar ya jingina bayan sa jikin sit idanunsa akan waya yana latsawa.
kallo d'aya tayi masa tayi saurin janye idanunta sakamakon jin wani irin mummumar fad'uwar gaba,
sau uku ke nan tun da take gidan ta tab'a ganin sa, had'uwarsu ta farko a sashin Hajiya da yake tambayar ta wai ita aljana ce ko,
sai kuma ranar da sukaje dinner sukayi dare, sai kuma yau.
ganin da tayi masa sau uku duk abu guda take ji mummynar fad'uwar gaba mai had'e da tsoro.
duk da ba su yake kallo ba idanunsa na kan wayar hannunsa, amma gaba d'aya ta rud'e ganin irin dukan da ya yi wa su Miemie ya dad'a kara mata tsoron sa.
da karfi ta damke hannun Miemie ta kara saurin ta.
Suna shiga parlour Aunty ta wani sauke numfashi mai sauti.
Miemie ta dube ta ta ce
"Ya dai Feeryal?."
kai ta girgiza tare da kakalo murmushi.
A parlour suka tadda Aunty da Daddy zaune suna kallo tare da d'an tab'a hira.
suka karaso suka gaishe su, Daddy ya dubi Miemie ya ce
"Mamana mutumiyar taki taci abinci kuwa?."
Aunty ta ce
"Wani abincin cake da yogurt ba tana da abincin da ya wuce su ne."
kai Feeryal ta langwab'e ta ce
"Naci tuwo fa Daddy ko Miemie."
Miemie tayi murmushi ta ce
"Taci Daddy tare ma muka ci."
"Yauwa ko ke fa gara dai a rika had'awa da mai nauyin, idan iska ya taso kinyi nauyi bazai iya kada ke ba."
cewar Daddy cikin zolaya.
dariya duk sukayi.
Daddy ya mike ya nufi bedroom ya na cewa
"To sai da safen ku."
zama sukayi suka bud'e sabon hira, har wajen karfe goma kafin Miemie ta yi musu sallama ta tafi.
Feeryal ma ta mike dan bacci ne cike a idanunta ta shige bedroom d'in ta.
Aunty ta je ta kulle kofar parlour kana ta dawo ta kashe TV sannan ta rage wutan parlour ta shige d'aki.
Ta taras da Daddy ya yi nisa a baccin sa, ta rage kayan jikinta ta sa na bacci kana ta shige bayi ta d'auri al'wala ta fito ta haye gadon itama ta kwanta gefen sa bayan tayi addu'a.
wani irin zabura Daddy ya yi ya mike zaune tare da fad'in
"Innailaihirraji'un!."
ya dafe kirjinsa jikinsa na cirawa.
a razane Aunty ta mike ta ruko shi tana fad'in
"Subhanallahi ya ya dai Daddy me ya faru bakayi addu'a bane ka kwanta."
kai ya girguza mata yana sauke numfarfashi tare da share gumin da ya karyo masa.
gaba d'aya Aunty ta rud'e a 'yan kwanakin nan ta lura a duk sanda ya kwanta haka zai farka a birkice.
tsawon shekaru ashirin da d'ori bayan auren su ya yi ta fama da irin wannan matsalar wacce damuwar haka takai ga tab'a masa lafiyar zuciya,
a wancan lokacin bayan auren su da wata biyar yasoma irin wannan mummunar mafarkin,
sai da ya shari shekaru goma yana fama da matsalar,
da taimakon Allah da taimakon addu'o'in da Aunty take tayashi yasami sassaucin lamarin,
damuwa da irin wahalar da yake sha idan ya kwanta bacci,
ta kai ga tab'a masa lafiyar zuciya, da har gobe yake shan magani.
sai gashiga a 'yan kwanakin nan abun ya dawo yanzu ba bu dare babu rana daga zaran ya kwanta bacci zai farka a firgice.
Ganin yadda gaba d'aya hankalin Aunty ya tashi, a hankali ya kwantar da kansa jikin kafad'ar ta yana sauke numfashi.
cikin shiga damuwa sosai Aunty ta ce
"Daddy tashi kayi al'wala muyi sallah babu abin da yafi karfin Allah babu abin da zai faru da yardar Allah."
Tarika karfafashi har ya mike yaje ya d'auro al'wala,
yafito ya taras har ta shinfid'a musu sallaya ta sa hijabi tana tsaye tana jiran sa.
shi ya jasu sallar suna idarwa taje ta d'auko musu Alkur'ani.
sun jima sosai suna karatu cikin suratul BAQARA, sai da ta tabbatar da nusuwa tare da shi,
har yana karatun yana gyangyad'i,
ta gyara ta mike kafafunta ta ce
"Kwanta Daddy."
ya mike kan sallayar yayi pillow da kafarta.
a hankali take karatun cikin kasa da murya tana yi tana shafa kansa, nan da nan bacci ya yi gaba da shi.
ya yi bacci abadan kafin itama ta soma lumshe ido. ta rufe kur'anin kana ta jingina bayan da jikin gado a haka bacci ya d'auketa a zaune.
Har sai kusan asuba ya farka ya ganta zaune tana bacci.
kauna da tausayin ta suka dad'a shigarsa, ya mike ya ciccib'eta ya d'aurata a kan gado,
yana ajeta ta bud'e ido.
murmushi tayi masa cikin muryar bacci ta ce
"Daddy ashe da sauran ka har yanzu tun da ka iya d'aukata."
kumatun ta ya ja ya na fad'in
"Tun da ina da ke kam tsufa bata isa ta matso ni ba."
murmushi tayi masa ta gyara kwanciyar ta.
shiko ya shige bayi ya d'auro al'wala,
yafito ya haye sallaya yasoma gudanar da nafilfili.
sai da aka kira sallar asuba kafin ya tashe ta shikuma ya wuce masallaci.
Aunty na idar da sallah ta je ta tada Feeryal kafin ta koma tacigaba da adhkar.
Feeryal ko bayan ta idar da salla da karatun alkur'ani tayi kamar yanda kullum Aunty ke umurtar ta da tayi, tana shafa addu'a ta haye gado ta koma baccin ta.
ba ita ta farka ba sai wuraren karfe 11 da rabi.
Bayan tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa da ta