Showing 6001 words to 9000 words out of 63585 words

Chapter 3 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

tacigaba da ayyukan ta.



Feeryal ce kwance ke baccin ta cikin kwanciyar hankali,
kiran wayar ta dake karkashin pillow da take kai yata da ita.
mika tayi had'e da salati ta zura hannun ta karkashin pillow ta janyo wayar, batare da ta duba mai kiran nata ba ta kai wayar kunne idanunta a lumshe cikin muryar bacci ta ce
"Hello."
numfashi ya sauke mai sauti ya ce
"Har na cire rai da picking call d'ina, Feeryal me yasa bakya d'aga wayata?
i miss you Feeryal ko sau d'aya ki bani dama mana,
hope kina lafiya."
shiru tayi batayi magana ba, amma ta gane mai muryar.
Major Sadam ya rumtse idanunsa yana jin sonta na zaga jini da jijiyar sa ya ce
"Please Baby let me know kina sona."
nan ma shiru tayi wayar tana kunnen ta.
"Feeryal." ya kira sunan ta.
a hankali ta maida idanunta ta lumshe tana saurarar sa, nanma shiru batayi magana ba.
"Kinyi min izini anjima na kira ki bayan kin gama bacci?."
a hankali ta bud'e idanunta cikin tsiririyar muryar ta ta ce
"Eh."
cikin matukar jin dad'in amsashi da tayi ya ce
"Yes! thank you bye."

Ta sauke wayar a kunnen ta, ta mike zaune tare da yin hamma,
har yanzu bacci ne cike tam a idanunta,
sai dai tana jin yunwa dan daren jiya bata ci ba ta kwanta.
ta kalli agogo karfe 11 har da rabi.
ta zame blanket d'in da ke rufe a jikin ta.
ta zamo bakin gado ta mike ta nufi kofa ta fito,
daga ita sai riga da wandon bacci pink masu samtsi.

Tun daga bakin kofa ta ke fad'in
"Ammie yunwa Ammie yunwa nake ji."
a tsakir parlour ta tsaya tayi wani dogon mika mai had'e da hamma ta saki hannayen ta sharaf tana b'ata fuska ta cuno d'an karamin bakinta gaba cikin muryar shagwab'a tashiga bubbuga kafa a kasa wan da ilahirin jikin ta matsawa suke tana fad'in
"Ammieeeee ina cake d'ina."
ta nufi dinnin tana cigaba da kiran Ammien nata.
Aunty ta fito daga kichin da sauri ganin ta nufi dinning tana mussuke ido da hannayen ta bata ma kallon gaban ta.
Aunty ta ce
"Ke Feeryal."
cak ta tsaya bata kai ga karasawa dinning d'in ba.
ta juyo tana tura baki da fad'in
"Ammie yunwa nake ji."
"Maza je ki canza kayan jikin ki sai kiyi wanka kizo."
ta juya tana yarfe hannu cike da shagwab'a ta koma d'aki.

A hankali ya tura plt d'in abincin ya mike, Aunty da ta fito daga kichin rike da wani had'ad'd'en kula, perpesun naman kaza ne dayaji kayan had'i na musamman acikin kular.
ta ce "Har ka gama ne Abdurrahim?."
ya ce
"Eh nagama Aunty."
"Dama na karo maka wannan ne to gashi ka tafi da shi."
ta mika masa kular ya amsa tare da fad'in
"Nagode."
tayi murmushi, shiko ya juya ya fita.....!


Mommyn Twins ce


Da sauri Miemie ta shigo d'akin Feeryal ta isketa kwance tana aikin ta na buga game a waya.
ta hayo gadon tana fad'in
"Yanzu dama wayar nan tana hannun ki nake ta kira baki d'aga ba."
fuska ta marairaice ta ce
"Ayya Miemie wayar a nan na barta yanzu na shigo na d'auka."
"Shine kin ga kira bazaki bi kiran ba."
"Ai missed call d'in da yawa shine kawai ni ban duba ba."
"To Allah ya shirye ki watarana sai arziki ya kira ki kin ki d'agawa ya wuce ki."
dariya Feeryal ta yi ta ce
"Yi hakuri to, ya akayi?."
"Tun d'azu nake ta kiran ki nace miki ki shirya anjima zamuje, dinner yayar kawar mu, Safeenat Sa'id."
"Ke da su wa da su Ameerah wai? ni kam bazanje ba kuje abin ku, kitaho min da tsaraba."
Miemie ta harare ta ta ce
"Ke kenan idan akace aje guri kice bazakije ba, kullum kina kunshe a gida a d'aki,
ina ruwan ki da su Ameerah a kansu zaki zauna,
yarinya tayi miki ne nagaya miki karki kuskura ki kyale ta,
barina naje na fad'awa Aunty mun tabayi Daddy ya ce muje, idan ta ce kije kuma sai kin je."
ta zamo a gadon da sauri tayi d'akin Aunty.

Jim kad'an ta dawo ta ce
"To wlh Aunty ta ce muje, bari ma na ciro miki kayan da zaki sa kifara shiri kafin nima naje na shirya,
8 za'a fara a tashi 11 bikine na kowa da kowa bawai zallan 'yammata ba har da iyaye."
ido Feeryal ta ware ta ce
"Wai da ma da daddre ne bikin ma?."
"E mana kin ga yanzu za'ayi magariba ki tashi ki fara shiri, wannan kayan zaki saka."
ta aje mata wani dogon rigan dokakkiyar les, had'e da gyale da takalmin da zasu hau da kayan.
Miemie bata tafi ba sai da ta ga ta shige wanka.

Tana fita ta gabatar da sallar magariba da aka rigada aka kira.
kana ta zauna zaman shafa mai.
Aunty ta turo kofa ta shigo, ta karaso cikin d'akin tana fad'in
"Har yanzu baki gama shirin ba."
fuska ta marairai ce ta ce
"Nayi wanka fa Ammie kaya zan sa."
Aunty ta d'aga kayan da Miemie ta ciro mata dasu aje a bakin gado ta dube ta ta ce
"Ya banga bra a cikin kayan ba."
"Ammieee jiya fa nasa."
"Dan jiya ansa sai yau kuma baza a sa ba, oh ni naga ikon Allah,
laifin Maryam ce."
wayarta ta d'aga ta lalub'o lambar Maryam tana d'agawa ta ce
"Ya miki kyau Maryam da kika kasa gwada mata aibun rashin sa bra."
"Ayya Aunty Faty wai kullum sai an d'aura laifin a kaina, kullum fa laifi na kike gani."
"Ai bazan fasa ganin laifin ki ba har sai randa ta koyi sawa da kanta batare da an ce tasa ba."
Aunty ta kashe wayar tana cewa
"Kullum bra ya kasan ce a jikin ki kwanciya ce kawai zaki cire sa."
baki ta turo tana marairaice fuska cike da shagwab'a.
Aunty ta ciro mata underwear da pant da bra.
ta ce
"Taso maza ki saka."
tana tsaye ta saka ta tayata ta karasa shirin.
da kanta tayi mata d'aurin d'an kwalli,
Feeryal na zaune gaban mirror Aunty tad'au sarkar da 'yan kunne na gold ta saka mata,
man lips kad'ai ta saka ko pauda babu a fuskarta.
amma kyawunta ya dad'a bayyana a gareta ya d'are wacce akayi awa 3 ana mata makeup.
Aunty ta tsaya tana kare mata kallo sai fad'in
"Tabarakallah masha'allah."
ta ke.
ta mika mata gyale ta yafa, ta gyara mata zaman gyalen, kana ta miko mata takalmin da Miemie ta d'auko mata, baya da tudu sosai ta zura a kyawawan fararen kafafunta.
ta fesa mata turare masu sanyin kamshi.
Aunty ta dubeta cike da farinciki ta ce
"Miqe na ganki d'iyar albarka."
ta miqe tsaye tana dariya.
Aunty tayi mata hoto da wayarta tana ta yaba kyawun ta.
Miemie ta shigo da sauri tana fad'in
"Allah dai yasa kin gama Feeryal."
ido Miemie ta waro ta ja ta tsaya tana kare mata kallo baki bud'e.
ta ce
"Kin ganki kuwa kamar ke ce amaryar."
Feeryal ta saki sassanyar murmurshi.
Miemie ta janyo hannunta ta ce
"Taho mu tafi mu ake jira.
"Miemie kada ku wuce karfe 10, ko ba'a tashiba ku dawo gida, kuma ku kula sosai dan Allah kada ku biyewa samaruka marasa d'a'an nan,
wai tukun na ma da gaske Daddy shi ya ce kuje."
cewar Aunty tana tsare Miemie da ido.
Miemie ta ce
"Allah Aunty shi ya ce muje tun da safe muka tambaye shi, ai ya ce ma zai je gurin d'aurin auren d'azu bayan sallar azahar wai Abba'n Feenat ya gayyace sa."
Aunty ta jijjiga kai dan tasan Alhaji Sa'id mahaifin Safeenat, da suke kira da Feenat suna d'an huld'a da Daddy.
ta ce "To shike nan sai kun dawo ku kula sosai dan Allah a fita kuma da addu'a."
suka ce to.

Suna fita suka hangi su Ameerah a jikin mota, da wasu kawayen su biyo.
Sahla ta tab'a Ameerah ta ce
"Kalli can ki ga wacce Miemie ta d'au ko."
Nabila ta ce
"Kan uba wa zata bi, lallai ma Miemie nan shine har da wani gayyato ta."
Ameerah ko tun kafin su karasu take aika musu harara.
kawayen nasu kuwa baki suka bud'e suna kallon Feeryal tare da fad'in
"Wow."
Ameerah ta dad'a b'ata rai har suka karaso in da suke.
ta ja dogon tsaki ta harari Feeryal sama da kasa sannan ta ce
"Ke Miemie wai ya za'ayi ki d'auko wannan kice zata bimu."
"Ina ruwan ki akan ki zata tafi."
cewar Miemie tana yi mata kallon sama da kasa.
Ameerah ta wani dalla musu harara ta ce
"To wlh ba a motar mu ba, ki dai san motar da zaki sata."
Nabila ta ce
"Gaya mata dai dan wannan motar ubanmu ne ya siya ba uban wata ba."
Miemie ta ce
"Ina dai babu wacce ta siyi motar a cikin ku,
to ai alhamdulillahi sai ku bari sai ko wacce acikin ku ta siya da kud'in ta kafin tayi gadara da shi,
na rantse dan dai kawai motar nan bazata d'auke mu bane dukan mu da wlh in mutuwa zakuyi sai ta shiga,
mttss zo muje Feeryal direban Ammah ya kaimu, daga nan ku had'iye motar a cikin ku,
in kuma ba haka ba to wlh duk randa fita ta kama mu sai ta shiga, in zaku mutu sai dai ku mutu."
taja Feeryal sukayi sashin Ammah.

Ameerah ta ce da kawayen nasu
"Dalla kuzo mu tafi muna b'ata lokacin mu anan."
Hafsat d'aya daga cikin kawayen nasu ta ce
"Haba da kun bari ta shiga nan ai, ni wlh tagama tafiya da ni kamar na kwana ina kallon ta,
sai kace ba 'yar'uwar ku ba kuke hantarar ta haka."
Ameerah ta yamutsa fuska ta ce
"Wa wannan aljanar babu abin da ya had'a mu da ita, 'yar tsintuwa ce ba dangin mu ba."
"Ko ni ma tayi min kyau bari mu isa muyi musanyar number na sata a friend list d'ina, wannan ka shiga da ita cikin kawaye ai girmanka sai ya karu."
cewar d'aya kawar tasu Laila.
bakin ciki kamar ya kashe Ameerah anyi abin da ta tsana wato yabon wata bayan ita,
sai taji ta dad'a tsanar Feeryal.
har suka isa tana jan tsaki da yin kwafa.

Motar su ta riga nasu Miemie isowa.
Feenat ta tare su da murna tana mu su oyoyo, ta jasu ta kai su gurin zaman da ta tanadarmu su.
ta cike su da kayan motsa baki

Zaman su da kamar 20min motar su Miemie ya iso. suna shigowa Hall d'in kallo ya dawo kansu.
Feenat ta mike da gudu tazo ta rungume su,
Feenat dama ita tasan Feeryal sau biyu suna had'uwa da ita idan tazo gurin su Miemie.
ta ce
"Kai Feeryal gaskiya naji dad'i ganin ki taho muje ku gaisa da su Mommy da ango da amarya.
taja hannun Feeryal Miemie ta biyo su tana cewa
"Au ita kad'ai ma kakaji dad'in zuwan ta to mu bari mu koma."
sukayi dariya.
dai dai sanda suka karaso zasu ratsa ta tsakiyar filin.
MC ya canza wata zazzafar waka,
bai sai kaji gurin ya amsa da hele ba.
ya yin da camara ya saito su yana ta kashe musu hotuna masu d'aukar video suma suna yi.
Feeryal kunya kamar ta nitse kasa, Miemie da Feenat kuwa sai wani fankama sukeyi.
suka janyota cikin takama, ita ko da kyar take iya d'aga kafarta har suka iso gurin zaman ango da amarya.

Feenat cikin rawar kafa ta ke fad'in
"Feeryal Miemie ga ango Ya Mujahid ga amaryar tamu Aunty Nuwaira,
Ya Mujahid kawaye na ne wannan Feeryal wannan Miemie."
ta nuna ko wannen su.
Mujahid ya fad'ad'a murmushin sa ya ce
"Mun gode da ziyartar taya mu murna."
"Bayan naku sai namu da ita wlh ni naga mata."
maganar abokin ango ke nan Ibrahim daya taso daga gurin zaman sa.
yana d'aya daga cikin mazajen da suka kasa control d'in kansu da ganin ta har sai da ya iso gare ta.
Mujahid ya yi dariya ya ce
"Allah aboki na."
"Insha'allahu kuwa akwai Mom d'ina anan bari na kirata tazo shaida ga surukarta nan."
Feeryal dai kasa tayi da kanta.
suna kokarin barin gurin suka jiyo magana a bayan su.
"Ina surukar tawa take, wacece haka ta birkita min lissafin my son?."
Feeryal takuma yin kasa da kai.
Mom in Ibrahim ta leko fuskarta tana fad'in
"Ah lallai ba shakka dole ka rud'e insha'allahu kuwa ka samo mata, Feenat kawarki ce ko daga ina ta taho?."
kai Feenat ta gyad'a tana murmushi, ta ce
"Daga gidan Alhaji Abubakar Fiya."
"Masha'allah zamu dangana da gidan kuwa domin a bamu ita."
Ibrahim ya kankame hannun Mom d'in sa ya ce
"Mom dan Allah yau aje."
ta dunguri goshin sa ta ce
"Ba yau ba kam sai gobe."
Feeryal kam takasa cewa komai kanta na kasa tana wasa da 'yan yatsunta su Miemie nata dariya.
Feenat ta ja su zuwa gurin su Mommyn ta
tagabatar da su, a gurin Mommy'n ta da kawayen ta.
atake a gurin wata hajiya ta ce tayi wa d'anta kamun Feeryal.

Daga can in da su Ameerah ke zaune suna kallon duk abin da ke faruwa,
sun cika sunyi tab kar Ameerah taji labari.
har sai da ta gaza b'oye kishin ta ta ce
"Lallai ma Feenat mu da muka zo kan lokaci ma bata gabatar da mu ga kowa ba, sai masu zuwan kurarren lokaci su ake wani gabatar da su kamar wasu kwamishinoni, mttsss aikin banza,
ni yanzu ma zan tafi."

A d'an gefe da su Ameerah Feenat ta sama wa su Miemie gurin zama.
suna zama wasu maza guda biyu suka dumfaro in da suke.
cikin kasa da murya Miemie ta ce
"Feeryal ga wasu gayu fa suna zuwa nan, kalli can yadda wasu gungun gayun ma ke kallonki,
gaskiya ke me sa'a ce,
dalla ki ware jiki kiyi abu kamar wayayyiya, sai wani shan jiki kike."
"Miemie nikam mu tafi."
tafad'a tana sunkuyar dan tana d'agowa taga idon mutane a kanta.
"Sannunku 'yammata ko zaki samin number ki?."
d'aya daga cikin samarukan da suka iso gurin su ya fad'a yana mikawa Feeryal wayarsa.
Feeryal tayi shiru batayi magana ba.
Miemie ce ta karb'a ta saka masa lambar ta mika masa.
ya amsa tare da fad'in "Thanks."
kana suka koma gurin zaman su.

Feenat ta kawo musu drinks da d'an abin motsa baki.
Miemie ce ta ci Feeryal kam ko drink bata iya sha ba, dan gaba d'aya a takure take idon jama'a ya takura mata.
anata gudanar da shagalin biki.
MC ya gayyato kannen ango zuwa fili.
Feenat ta ja su Miemie, Feeryal ta make kafad'a tace suje ita kam bazata iya ba.
duk yadda Miemie tayi ta tashi fir taki.
haka suka kyaleta suka je gurin su Ameerah.
Feenat ta ce
"Ameerah Sahla Nabila Hafsat Lailat ku zo mu shiga fili ga MC na kiran mu."
duk suka mike ban da Ameerah da ta b'ata rai.
"Ameerah ta so mana."
cewar Feenat.
ta ce
"Kuje kawai bazan shiga ba."
bata kuma mata magana ba jin MC na ta nanata kannen ango su fito, suka garzaya cikin fili aka sakar musu kid'a suka sunkuya tika rawa.

Feeryal sai murmushi take sakewa idanunta akan su Miemie da suke ta cashewa.
bata yi aune ba taji saukar lips d'in mutum kan kumatun ta.
dai-dai lokacin kuma hasken camara ya haske su.
a razane ta juyo wanda jin hakan ya bada dama wajen dai-dai tar fuskarta da tashi, nan ma hasken camara takuma haska su.
a razane ta mike tsaye tana binsa da kallon tsoro.
shigo gayan murmushi ya mata tare da kashe mata ido ya ce
"Hi baby haupa."
yaja kujerar ya zauna yana fad'in
"Zauna mana muyi hira, nifa sonki nake ko zamuje mu sha ice cream."
da sauri tayi baya dan ba karamin tsorata da shi tayi ba.

Ameerah ta mike tsaye tare da jefa wayar ta cikin jaka, da sauri ta shige cikin filin ta ja hannunsu Sahla da Nabila, suka fito.
suka ce yaya dai Ameerah?.
ta ce
"Ku taho mu tafi gida yanzu fa karfe goma da rabi, kafin mu isa 11 ta wuce."
tayi gaba suka biyo ta a baya suka shige mota dama direba na zaune a ciki yana jiran su sukayi gida.

Feeryal na tsaye jikin ta na b'ari shiko yana zaune idanunsa a kanta yana latsar lips d'in sa da kanne mata ido.
"Gashi kamar wayayyiya kina abu kamar na marasa waye wa, muje hotel ki tayani kwana duk abin da kike so zanyi miki, zan kuma sallame ki da 2 million,
idan baki aminta da ni ba zan iya using da condoms."

Jikin ta ya d'au b'ari tsoro yadad'a bayyana a gare ta.
maganar Miemie taji a bayan ta
"Feeryal wai rawan ne baki iya ba ko me."
da sauri ta waigo murya na rawa ta ce
"Miemie mu tafi gida."
mikewa ya yi yazaro kati cikin aljuhun sa ya aje sa kan table d'in gaban su ya ce
"Idan kin yanke kuhunci zaki iya nemana ta wannan katina ne, I'm waiting for you, kiyi shawari da kawar taki ina jiran ki ko yaushe."
ya juya ya bar gurin.
Miemie ta bi bayansa da kallo tana fad'in
"Wai mene ne Feeryal?."
Feeryal tayi rau-rau da ido sai ga hawaye sharr, ta d'aura yatsar ta kan kumatun ta sannan ta ce
"Kiss yamin a nan sannan ya ce wai na bishi hotel."
ido Miemie ta waro ta ce
"Shine baki masa kaca-kaca ba kika tsaya kina masa kallon tsoro,
d'an iska ina yashiga na tara masa jama'a anan awa d'an iska dukan tsiya."
"Miemie ki rabu da shi ni kam mu tafi gida kawai."
tayi maganar hawaye na ci gaba da zuba a idon ta.
"Dan Allah share hawayen ki kar kisa mutane su tsaya kallon mu, na gane shi ai wlh sai na nemo shi,
tsaya Feenat ta zo tace mu jira ta."

Feeryal ta share hawayen ta da tafin hannunta.
Miemie sai masifa take tana d'urawa mutumin zagi.
sun b'ata lokaci a zaune kafin Feenat ta dawo gurin su.
lokacin karfe 11 saura minti 15.
suna fita Ibrahim ya biyo su, nan suka kuma b'ata lokaci har 11 ta cika, kafin suka d'auko hanyar gida.



Su Ameerah kuwa karfe 10 da mintuna 50 dai-dai suka ido gida.
direba na gyara parking a babban parking lot suka fito.
suna tafe kowa zai wuce sashin su suka hangi Abdurrahim zaune cikin wani kayataccen zagayayyen gurin da aka zagaye shi da fulawowu masu kyau da kawa,
sama d'an rumfar bukka ce mai zawaye da koyayen wuta, kasan rumfar kujeru ne.
gurin haske ne sosai kamar tsakiyar rana ba dare ba.
yana zaune laptop na gaban sa yana danne-danne a cikin sa.
"Kuzo nan."
yafad'a idanunsa akan laptop.
kallon junan su sukayi, kana suka janyo kafafunsu inda yake.
suka durkusa a gaban sa.
sunkai minti 5 bai ce da su komai ba kuma bai d'ago ya dube su ba, yana ta aikin latsa laptop d'in sa.

Zuwa can ya soma magana
"Ina kuka fito har 11 na dare kuna waje?."
Suka had'a baki wajen fad'in
"Munje dinner yayan kawar mu ce."
sai a lokacin ya tsai da abin da yake ya d'ago ya dube su d'aya bayan d'aya sannan ya ce
"Da daddaren nan sabo da rashin mafad'i ko me, ina Miemie ta ke?."
da sauri Ameerah ta ce
"Samarukansu ne suka d'auke su bamusan ina suka je ba."
"What! samarukansu ita da wa?."
ya furta yana duban su, abin ya bala'in bashi mamaki wai wad'an nan 'yan hanci wai su ke da samaruka.
ta ce
"Ita da Feeryal kuma da ganin su 'yan iska ne,
samarukan, sai da na ce su zo muje gida suka ki."
tana rufa baki motar su Miemie yana shigowa gidan.
duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login