Showing 54001 words to 57000 words out of 63585 words
Chapter 19 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
shi yafi miki rufin asiri ke kan ki sai kin fi samin kwanciyar hankali,
imma baza'a had'a bikin dana Maryam ba bayan bikin ayi natan kawai ya wuce,
tun da bikin Maryam d'in yazo daf, taje ta cigaba da karatun ta tana da aure ai yafi."
Aunty ta sauke numfashi tabbas idan ta aurar da ita zatafi samin nutsuwa da kwanciyar hankali.
kullum tana cikin fargabar yawan kai mata hari da maza keyi.
ta ce
"To shike nan Hajja Umma zan fara samin Daddy da batun kafin Abban ya kirashi in yaso daga baya iyayen Sadam d'in suzo."
sukayi sallama ta kashe wayar.
Siyama bata dawo gidan ba sai da yamma lis saurayin nata ya dawo da ita.
yana sauke ta a mota Saddiqa na fito wa.
ya zuge glass d'in motar suka had'a ido ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa.
ya leko yana fad'in
"Wannan fa naga kunyi kama da ita."
ya yi maganar yana maida kallon sa kan Siyama.
Siyama tawani narke murya tana yauki ta ce
"Saddiqa wai d'iyar Aunty ta ce, ai dole muyi kama."
Saddiqa ta karaso gurin ta dube shi da murmushi ta na cewa
"Inayini Uncle."
ido d'aya ya kashe mata sannan ya amsa gaisuwar nata.
Siyama ta dube shi tana fad'in
"Baby sai yaushe?."
"In kin so ko anjima da daddare sai na dawo."
"Ah ka bari sai gobe."
"To Allah ya kai mu."
ya dubi Saddiqa ya ce
"To sai anjima 'yanmata."
hannu ta d'aga masa ta ce "Mu kwana lafiya."
ya ja motar sa ya yi gaba, su kuma suka shige ciki Saddiqa tana cewa
"Aunty Simaya a ina kika samo wannan amma fa ya had'u."
Siyama ta washe baki ta ce
"Ba kad'an ba fa bamu jima da had'uwa da shi ba, kinga har maganar aure yake min,
amma duk had'uwar shi ai bai kai yayan ku ba, badun ina da sammanin samun Abdurrahim ba da wannan zan aura."
Saddiqa tayi dariya suna shigewa parlour'n su.
Da daddare Siyama na kwance suna waya da saurayin nata, cikin hirar tasu yake tambayar ta ina mai kama da ita.
ta ce "Tana can d'akin ta."
ya ce "Allah kuna kama fa sosai kyakkyawa kamar ki."
Siyama ta washe baki dajin dad'in an yabe ta an ce mata tana da kyau.
ta ce
"Ai haka kowa yake fad'a muna kama da ita, d'azu ai itama sai da ta tambaye ni wai a ina na samo had'ad'd'en gayen nan."
dariya ya sake yana fad'in
"Au ki ce ita ma ta tambaye ni kamar yadda na tambaye ta yanzu."
"Eh wlh tayi maganar ka d'azu ma, ko na kaimata ku gaisa ne?."
"Aa ki barta dare ya yi kidai bani number ta ma gaisa ko ta Whatsapp ne, mai kama da baby na kyakkyawa."
Siyama tayi dariyar jin dad'i, ta ce
"Tom zan turo maka."
suna gama wayar ta tura mishi lambar Saddiqa.
Koda Aunty ta sami Daddy da batun da Hajja Umma tayi mata kan Major Sadam, yanzu ya matsa yana so inda so shine samu a had'a bikin su dana abokin sa Inspector Nasir.
Daddy ya yi shuru sannan ya ce ace
su dakata tukun ba yanzu ba...
Kullum Umma Karima a cikin tunani take na yadda zata bi ta idda samin nasara a karo na gaba ta ke.
har in tana bukatar samin nasara kuwa ya zama dole Feeryal tabar gidan,
ta nan ne kad'ai idan tayi jifan ta zai fad'o kan wanda take so batare da an tsare shi ba.
sai dai wannan karo tana bukatar taimako dan ta lura a yanzu dole sai ta sami mai tallafa mata kafin ta idda kudirin ta.
da sauri ta mike ta d'au mayafi tayi sashin Mommy.
a parlour ta tadda Mommy ita da su Ameerah.
Mommy na ganin ta tasan wani labarin ta kawo mata, ta jata sukayi cikin d'aki.
a bakin gado duk suka zauna, Mommy ta dubeta ta ce
"Ya dai Hajiya Karima akwai labari ke nan."
Umma Karima ta gyara zama cikin dabara da kwarewa a iya makirci take fad'in
"Yanzu Hajiya Halima haka zamu zuba ido mucigaba da kallon matar nan,
da wannan aljanar ruwan da ta kawo mana ita gida, ta zame mana fitina alakakai,
to bari kiji ina mai maganin da na kawo shi rannan ya duba Alhajin nan,
ya ce yarinyar ba karamar matsafiya bace, aiki tayi da tsafin ta har ta kore shi a gidan,
yanzu haka ya ce idan bamusan yadda mukayi muka fitar da ita a cikin gidan nan ba,to wlh mu sai ta fidda mu kaf a kan 'ya'yan mu."
Mommy ta dafe kirji ta ce
"To yanzu meye mafita Hajiya Karima, wannan hasabibiyar yarinyar ya zamuyi da ita?."
"Mafita d'aya mud'agawa Alhaji hankali mu tada bori cikin gidan nan, mu zuga Hajiya musa ta tasa shi ya kore ta,
in ba haka ba fa ina mai tabbatar miki muzata kora cikin gidan nan,
kuma duk shirin Hajiya Fatima ce makirarriya ta kwantar da kai ta had'a mu da gamasheka, tana sarar mu ta kasa."
Mommy ta ce
"Amma fa Hajiya Karima idan muka ce zamu d'aga hankali da yawa kinsan halin Alhaji karshe ya ce, zamuyi a bakin auren mu,
ni kinsan fa saura biyu ne sakanin mu ya guntule d'ayan tuntuni,
gara ke ma bai tab'a yi mi ko d'aya ba,
ni ina ganin kawai mubi a sannu mu sami Hajiya mu tuna mata ai dama ya ce,
idan aka gama bincike ne akan wanda suka sace ta mai tawagar d'aukar amaryar nan,
zata koma can Abuja, mu tuna mata da wannan batun dan naga kwana biyu tayi shiru, kuma nasan har da ciwon Alhajin ne ma yasa tayin shiru,
tun da ya sami sauki zance ya kare tasashi ya koreta ta koma can in da akayi gayyar ta."
Umma Karima ta d'anyi shiru bataso haka ba, taso Mommy ta d'auki zugarta kamar yanda kullum take sata akan keken b'era.
ta ce "To shikenan hakan ma za'a sami nasara, bari zan sami Hajiyar nasan yadda za'ayi."
nan ta cigaba da kisawa Mommy yadda zasuyi kafin ta koma sashin ta...
Shirye-shiryen bikin Maryam da Inspector Nasir yana ta matsowa,
duk abun da aka sawa rana komi daren dad'ewa zai iso.
ana saura sati d'aya bikin Aunty da Feeryal suna zaune a parlour kiran Maryam video call ya shigo wayar Aunty.
Aunty na d'agawa Maryam ta turo baki tana fad'in
"Aunty Faty wai sai yaushe ne zaku zo ne kam, biki saura sati d'aya ai yau ya kamata kuzo."
Aunty ta ce
"To mara kunyar amarya mai kiran a zo bikin ta."
dariya duk sukayi Feeryal na dariya ta ce
"Aunty Maryam an gama d'inkamin ashobe na kuwa?."
"Ke da Sadam yazo ya karb'i naki wai zai kai da kansa a d'inka miki,
jiya ma suna nan yayi ta kiran wayar ki baki d'aga ba."
shiru Feeryal tayi sarai taga kiran shi jiya, bata d'auka ba, yau da safe ma sai da ya mata missed call yakai biyar bata d'aga ba.
maganar Maryam taji tana fad'in
"Ai bakiga d'inkin da yasa akayi miki ba ya nuna min hoton su a waya."
murmushi kawai tayi tana kwantar da kanta a kafad'ar Aunty.
Aunty ta bita da ido tana son karantar yanayin ta.
"Aunty Faty dan Allah ku taso gobe."
Maryam tayi maganar tana marairaice murya.
Aunty ta ce
"Sai ana gobe d'aurin aure zan shigo, ni kad'ai Daddy ya ce zan zo banda Feeryal,
ya ce har yanzu ba'a gama bincike ba,
shigowarta Abuja yana da hasari yanzu."
da sauri Feeryal ta d'ago murya kamar zatayi kuka ta ce
"Ayya Ammie ni dai zanje."
"Aa Feeryal ki bari tukun komai yagama dai-dai ta, idan natafi ana gobe kwana biyu kawai zanyi na dawo."
"Ayya yanzu Aunty Faty banda ita ke nan a zuwa, wlh ni har naji auren ma yafita min a rai."
Maryam ta fad'a kamar itama zatayi kuka.
Aunty ta kashe wayar ganin duk suna son caza mata kwakwalwa.
Feeryal har da kuka ita ala dole sai ta bita.
da kyar Aunty tayi ta rarrashi har sai da Daddy ya shigo ya taya ta.
ya ce tayi hakuri itama zataje saura kiris a kammala bincike...
Ana goge d'aurin auren kuwa, Aunty ta gama shirinta tsaf zatabi jirgin karfe 9 na safiya.
yau Feeryal ko baccin safiya bata koma ba, tana nan tana bori ita sai tabi Ammie'n ta.
tun a daren jiya Miemie tazo ta kwashi wasu kayan ta tana ta murna dan a sashin su zata zauna kafin Aunty ta dawo.
ai kuwa da sassafe ta zo side d'in Aunty.
karfe 8 dai-dai Daddy ya ce Aunty ta fita direba ya kai ta saboda karfe 9 jirginsu zata d'aga.
a tare suka fito Feeryal kayan bacci ne a jikinta ta d'aura hijabi iya gwuiwa a kan kayan baccin, tana tafiya tana sharar kwalla.
Miemie na d'auke da d'an madaidaicin akwatin Aunty.
a can tsakiyar farfajiyar gidan mota ke jiran ta.
Daddy na zaune a bayan motar Abdurrahim na tsaye a jikin kofar gefen da Daddy yake.
tun kafin su karaso direba ya yi saurin bud'e wa Aunty d'aya gefen, suka karaso Aunty na kokarin shiga motar Feeryal ta saki kukan shagwab'a tana bubbuga kafa kasa tare da yarfe hannayen ta,
cikin muryar ta mai sanyi take fad'in
"Ammie ni dai zan biki."
Daddy ya ce
"Aa Feeryal ina mun gama wannan maganar tun jiya,
kiyi hakuri idan komai ya dai-dai zakije ai,
yanzu kam babu halin ki shiga Abuja gaskiya,
kiyi hakuri kinji."
bayan hannun ta takai tana share hawaye tana jan shashsheka, wasu hawayen suna zuba.
Ammah da ta karaso gurin yanzu tayi karamar dariya tana fad'in
"Aa Feeryal wai duk kukan rabuwa da Ammie'n naki ne haka, to ayi hakuri."
Ammah ta dubi Aunty ta ce
"Har kun fito ashe to Allah ya kiyaye hanya, a dawo lafiya."
Aunty ta amsa da amin-amin.
kana Ammah ta d'an rusuna ta gaida Daddy cikin girmamawa.
Aunty ta shige mota tana fad'in
"Yanmatan Ammie kwana uku fa kawai zanyi na dawo, a daina wannan kukan dan Allah."
Feeryal hanci takuma ja tana goge ido da bayan hannu.
direba ya yi wa motar ke Daddy ya dubi Abdurrahim yana cewa
"Ka duba yuwuwar dacewar sayar masa da duka gonakin audugar 30 wad'an da ba'a sasu a jadawalin kai su company ba, na gaya masa kai ba manomi bane likita ne bansan me yasa yake son sako ka cikin lamarin ba,
ko da yake ya ce min wai kafini sanin harkar noma, na ce wane kai tun kan a haife ka nake noma, in ya ce fed'e mutane a d'inke to na yadda."
murmushin gefen baki ya yi tare da rufe masa murfin gefen sa.
Aunty ta gyara zama tana fad'in
"Daddy ka had'a kanka da shi shifa d'an zamani ne."
cikin yin kasa da murya Daddy ya ce
"To bayan ina da ke 'yar zamani ai nima nazama d'an zamanin ke nan."
murmushi ta yi shima ya mayar mata.
kana yacewa direba yaja su tafi, dan shi zai rakata airport d'in da kansa.
Feeryal takuma yin rau-rau da ido sai ga hawaye sharr san da taga motar su Aunty yana shirin fita daga gidan.
Amma ta ce
"Taho muje Feeryal yi hakuri mana kinji, kin san matsalar da yasa baza'aje da ke ba, badun son kare ki daga 'yan ta'addan can ba ai da dake za'aje."
Ammah ta yi gaba.
Miemie ta ruko hannunta ta ce
"Muje Feeryal."
a hankali ta soma d'aga kafarta tana waigen baya in da take hango fitar motar su Aunty.
gajeren tsaki yaja idanunsa a kan waya.
zura wayar dake rike a hannun nasa ya yi cikin aljuhun jallabiyar jikin sa.
kana ya zura hannayensa duka cikin aljuhun,
har suka zo daf da shi zasu gotashi Feeryal bata fasa waigen ba.
ya saka mata kafa ta fad'i tim a kasa.
kara ta sake tare da fad'in
"Wayyo Ammie na, wayyo kafata."
ta rike gwuiwa tana yarfe hannu kwalla na zuba.
da sauri Miemie ta sunkuya tana yi mata sannu dan bata lura da abin da ke faruwa ba.
Ammah ta juyo da sauri ta dawo in da suke tana fad'in
"Sannu Feeryal fad'uwa kikayi ne garin yaya?."
shiko gefe yabi ya wuce cikin garden ya yi zamansa.
Ammah da Miemie suka tallafo ta suwa sashin su tana tafiya tana yarfe hannu...
Kwanan Aunty biyu a ran na uku ta juyo dan hankalin ta na gida gun Feeryal, duk da tasan Ammah zata kula mata da ita.
Siyama ce ta fito daga d'aki ta wuce dinning ta bud'e kular abinci zata d'iba.
da sauri ta toshe hancinta ta juya da gudu ta koma d'aki, ta wuce bayi tashiga kela amai.
Umma Karima da ke zaune a parlour ta bi bayanta da kallo.
zuwa can ta fito tana yamutsa fuska.
Umma Karima ta ce
"Ya dai Siyama me ya faru kamar amai naji kike yi?."
fuska ta dad'a yamusawa ta ce
"Wannan matar Sukai na ce ta dai na cika wad'an na Spices d'in cikin abinci amma bataji ba, wari suke min da zaran na zo ci sai naji zuciya ta na shi."
ido Umma Karima ta ware ta ce
"Siyama kar dai zargina ya kasance gaskiya, gaba d'aya yanayin ki ya koma irin na masu ciki,kwana biyun nan."
kame-kame ta shiga yi tana fad'in
"Ci..ci...ciki kuma Aunty Karima a'a kam ni kam bani da komai."
Umma Karima ta mike zumbur ta ce
"Haba Siyama nasan jiya fa nasan yau, to me zaki b'oye min ma tukun,
wani irin hauka ne ya kaiki barin ciki ya shige ki, wannan d'an iskan dake zuwa babu dare babu narar nan shine ya miki ko?,
na shiga uku ni Karima zaki lika mana abun fad'a."
da sauri ta d'au wayarta ta kira lambar Family Dr su, yana d'agawa ta ce
"Duk abin da kake kabari ka zo, ina niman ka."
ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya wlh bana ma garin nayi tafi sai jibi zan dawo."
Umma Karima ta kashe wayar da sauri bata jira ya gama maganar nashi ba.
ta ce
"D'auko mayafin ki da sauri kizo muje, yau cikin nan bazai kwana a jikin ki ba,
kafin wani ya ankara an cire d'an banza,
ina zan iya ina fama da wani damuwar wani damuwar ya kuma kunno kai,
akwai wani arnen likita gurin shi yanzu zamuje yanzu ba sai anjima ba."
ta shige d'aki da sauri itama ta d'au mayafin ta suka fito.
tun kafin su karaso parking lot take kwad'awa direba kira, ta ce ya taho da makullin mota da sauri.
suka shige mota tayi masa kwatancen asibitin da zai kaisu,
wani private hospital ne.
suna isa ta janyo ta da sauri sukayi cikin asibitin.
bayan an bud'e musu Folder aka turasu ofishin likita.
suna zama Umma Karima ta soma kora masa bayani jiki na rawa, ta ce ko nawa ne ita zata biya bata so cikin ya kwana a jikin ta. ya caja su 500k batare da b'ata lokaci ba tayi masa transfer zuwa account d'in sa.
kud'in suna shigo masa ya mike ya ce yana zuwa.
ya fita.
Abdurrahim na zaune cikin office d'in sa sako ya shigo wayar sa.
ko da ya d'auka ya bud'e, hoton Umma Karima da Siyama ya gani.
yana kokarin aje wayar kira ya shigo.
sunan Dr L-cana ya bayyan a screen d'in wayarsa.
kamar bazai d'aga ba har wayar takusa yankewa kafin ya d'aga.
daga cikin wayar Dr L-cana ya ce
"Hello AA How far, how you are there."
ya ce "Fine."
Dr L-cana cikin harshen sa da bai gama sayawa ba ya ce
"Wannan kamar matar Daddy'n ka ne na gane fuskarta, d'ayan ce dai ban gane ta ba sai dai naga sunyi kama ko daughter ta ce,
abortion suka zo ayi wa yarinyar,
nayi wani tunani nace bari na sanar maka,
kar azo a sami damuwa, shin nayi mata?."
a zafafe ya ce
"Then, So what! meye nawa da zaka kirani kana gaya min, It is not my.concerned, I don't have problem,
damuwar su ce wannan,
so please Don't call me again;
ko ma meye ku kara ta."
ya kashe wayarsa yana jan dogon tsaki.........!
Mommy'n Twins ce
Ganin ya kashe wayar Dr L-cana ya d'aga kafad'a tun da ya yi ko oho da maganar shiko yana ganin kud'i bazai barsu ba, komai ya faru ma daga baya ne.
ya koma ciki yasata ta tube ta haye gado.
ya had'o kayan aikin sa batare da b'ata lokaci ba ya burge cikin. ya bata magunguna suka nufo gida.
suna isa gida Umma Karima ta jata d'aki ta sunkiya mata bala'i.
"So kike ki samu a bakin mutanen gidan nan, badun na ankara da wuri ba ai da zance ya kwab'e,
idan mutane suka sani har ya shiga kunnen Abdurrahim ai shike nan kuma, sai mun nimi yadda zamuyi mu rufa bakin sa,
kar ki kara irin wannan ganganci;
ki cigaba da shan magani ki warke ko su Bilkisu kar ki bari su gane komai."
tayi waje tana janyo mata kofar.
A b'angaren Abdurrahim bakin cikin kiran da Dr L-cana ya yi masa akan Siyama da Umma Karima,
an danganta shi da su da abun bakin cikin da sukaje yi yaji,
ya tattari abubuwan amfanin sa yazari makullin motar sa yabar asibitin.
yana isa gida ya gyra parking yafito ya nufi side d'in sa.
direct upstairs bedroom d'in sa ya nufa.
yana tura kofar yaja ya tsaya cike da mamaki yaji b'acin ransa ya karo.
masu aiki yagani guda biyu cikin d'akin,
d'aya tana d'ale a kan gadon sa tana gyarawa d'ayan kuma tana cikin bathroom d'in sa
tana wankewa.
wani uban tsaya ya buga musu, a razane duk suka taho gaban sa suka zube.
cikin muryar b'acin rai sosai ya ce
"Waya baku damar shigo min side d'ina har ku wuce ko ina ku shigo min har cikin bedroom!?."
murya na rawa suka ce
"Mai d'akin ka ce Hajiya Kuraiba."
wani b'acin ran yakuma jin ya ziyarce sa.
cikin tsawa ya ce
"Ku fita ku b'ace min da gani! ko da wasa na sake ganin wata ta sako kafarta cikin side d'in nan ba ma d'akin nan ba, wlh sai kun raina kanku."
a zabure sukayi waje jiki na kyarma. a stairs sukayi kiliya da Kuraiba da taji dawowarsa ta shigo gefen sa.
ganin yadda suke sauka kamar ana biyo su ta ce
"Kai wai har kun gama gyaran ko ya?."
basu iya bata amsaba sukayi waje da gudu."
da sauri ta karasa haurawa tana shiga ta gansa yana tsaye yana rage kayan jikin sa, fuskarsa babu annuri.
ta karaso tana kokarin rungume sa ya buga mata tsawa tare da nunata da yatsa
murya cike da b'acin rai ya ce
"Waya baki ikon shigo min da wad'an can abin cikin d'aki, ke kanki albarkacin Mommy kike ci, badun haka ba na rantse baki isa ki taka kafarki cikin bedroom d'in nan ba, gargad'i na karshe,
kada ki sake ki sake gayyato min wasu 'yan'aiki cikin side d'innan ma gaba d'aya."
duk da taji tsoron yadda yake magana cikin fusata sosai, amma sai ta waske cike da salon bariki ta narke murya
"Haba mijin Kuraiba ai yanzu ni nake da ikon sawa ko hanawa a cikin gida na,
wai kullun ina gidan amma wai sai Ajmaal ya shigo ya gyara maka bedroom's zuwa parlour,
shine yau na ce yabari ni zan sa masu aiki su gyara idan sun gama gyaran nawa."
wani irin mari ya d'auke ta dashi tun kan ta kaiga rufe bakin
ta.
cikin karaji ya