Showing 21001 words to 24000 words out of 63585 words

Chapter 8 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

suna masallaci ta yi waje da sauri.

Abdurrahim ta hango yana shigowa da alama daga masallaci ya fito, da sauri ta tare shi tana cewa
"Dan Allah Abdurrahim ka taimake ni Feeryal ba lafiya kaje ka duba ta, kwana tayi bata rumtse ba, jikin ta ya yi zafi sosai,
ina ta kiran Dr tun jiya har yanzu bai zoba, ka tai maka dan Allah."
d'an jim ya yi ganin irin magiyar da take masa ya ginjina kai alamar zai je. da sauri ta juya ta koma ciki,
shi kuma ya wuce side d'in sa yana shiga ya haye gado ya kwanta......!




Mommyn Twins ce



10
Ganin shiru-shiru bai zoba Aunty ta kira sa a waya.
kiran wayar ne ya tashe sa daga baccin da ya fara.
gajeren tsaki yaja, kana ya mike zaune ya yi mika tare da yin salati.
ya zura takalmansa ya mike tsaye ya ja bedside ya d'ibi abubuwan da zai bukata ya zura cikin aljuhun jallabiyar jikin sa, kana ya fita ya nufi sashin Aunty.
a bakin kofar parlour suka had'u ta fita zuwa da kanta ta kira shi.
da sauri Aunty ta juya tana cewa
"Yauwa Abdurrahim dan Allah ka duba min ita."
baiyi magana ba yabi bayanta dan yana mugun jin nauyin ta.

Feeryal na kwance cikin bargo.
Aunty ta hayo gadon tana cewa
"Feeryal ta shi ga shi za'a duba ki,
karaso dan Allah Abdurrahim."
ta janye bargon, idanun ta a lumshe bawai ko dun tana bacci ba sai dan jirin da take ji.
a sannu ya toko d'akin hannayen sa suna nad'e a kirjin sa.
ya karaso bakin gadon,
kallo d'aya ya yi mata ya d'auke idanun sa. a hankali ya sauke hannayen sa da suke nad'e a kirjin sa.
kana a sannu yakai yatsun sa biyu kan goshin ta.
patt!. haka taji kirjinta ya buga san da yatsar sa ya sauka kan goshinta,
da kyarfi ta rumtse idanunta tare da jan numfashi.

Ya janye hannunsa tare da zurashi cikin aljuhu ya zaro allura ya fasa ya zuko shi cikin Syringe.
"Gyara Feeryal ayi miki allura ba sai kin tashi ba a kwancen ma za'a iya yi ko Abdurrahim."
Aunty ta fad'a tana duban shi.
kai ya gyad'a batare da ya yi magana ba.
wani irin zabura tayi jin an ambaci sunan allura.
murya na rawa ta ce
"Aa Ammie ni dai bana so kar ayi min."
had'iye ragowar maganar tayi ganin shi tsaye a gaban ta.
hannu takai ta mussuke idanunta zaton ta gizo ne.
jin Aunty tana cewa
"Ke ki tsaya da'alla abin da ba zafi Abdurrahim yi mata kaji."
huf ta mike tsaye ta tsaya da kafafunta a kan gadon, ta matsa can karshen gado tana yarfe hannu da fad'in
"Wayyo Allah Ammie naji sauki kar a min."
"Ke dalla bana son shiririta kina b'ata masa lokaci fa."
ta janyo ta ta zille tare da fashewa da kuka tana yarfe hannu
"Ammie dan Allah dan Allah Ammie kar a yi min naji sauki ma."
ta rika yarfe hannu tana buga kafa kan katifa.
Aunty ta ruko ta da karfi, ihu ta fasa tana tirjewa.
gajeren tsaki ya ja cike da kosawa ya mika hanu ya fisgo ta ta fad'o kan kafar Aunty, ta rirtike ta, itama ta kankame ta gamgam tare da b'oye fuskarta jikin Aunty.
tsaki ya kuma ja badun nauyin Aunty da yake ji ba da babu abin da zai sa yazo bare har a tsaya ana masa wannan haukar.
kwafa ya yi afili Aunty ta fahimci ransa ya b'aci, ta bugawa Feeryal tsawa
"Idan baki tsaya ba za'a barki da ciwon ki kiyi ta fama, kina hauka ne allura kawai kamar cire ran ki za'ayi haba dan Allah,
yi hakuri Abdurrahim kayi mata."
ta d'an ja sket d'in ta kasa

Baki ya tab'e ya d'an matso ya nitsa allurar ta saman pant d'in ta.
kara ta kurma ta kai hannu ta rike nashi da ke rike da allurar ya bige hannuta bayan ya matse ruwan allurar ya zare shi a jikin ta, yana mai dad'a gimtse fuskarsa, ya cika har wuya.
da kyar ta tsaya a ka kara mata d'aya,
"A sa mata ruwan sanyi a jikin ta."
ya fad'a a takaice.
Aunty ta d'ago ta a jikin ta ta sauka ta shige bayi da sauri.
Feeryal kukan allura har da majina.
ganin Aunty ta shige bayi itama ta mike da sauri ta duro a gadon.
tana d'aga kafa taji abu ya cake ta a bayan hanu.
kara ta kwalla tare da d'ago hannun tana yarfe shi.
wani kallo ya wurga mata sannan ya saki allurar dake hannunsa kasa,
"Stupid girl." ya fad'a kana ya juya ya fice a d'akin

Aunty ta fito da sauri tana fad'in
"Feeryal lafiyar ki tun da an gama ina shike nan ko sai kin tsaya shiririta,
me ya sami hannun naki kike tallafe shi sai kace a hannun aka yi miki allurar."
Aunty ta ruko hannun nata tana cigaba da cewa
"Um kin gani karin gardamar ki har kin ji ciwo a hannu gashi har ya d'an fidda jini, sannu zauna na sa miki towel zaki dad'a jin dad'i, jikin naki ya yi zafi sosai baki ji ya ce asa miki ruwan sanyi ba."

Feeryal bata iya magana ba sai matsar kwalla take.
Aunty ta taimaka mata ta cire kayan jikin ta, ta d'auko mata wani riga bes da wandon sa iya guiwa ta saka, kana ta rika jika towel tana shafa mata a jikin ta.
har sai da taji jikin ya yi sanyi kafin zuwa lokacin kuwa bacci ya d'auke ta.


Aunty ta fita taje ta kama aiki akai-akai take shigowa dubata, sosai jikin ta ya yi sanyi ta jima sosai tana bacci..


"Ya shugaba na akwai tsoron wani mai tsanani a tare da ita, gata a kwance cikin jinya sakamakon tsoron nashi."
waziri Kutup ya yi maganar yana zubewa gaban sarki Aljani Matip tare da d'aura ruwan madubin ganin zahiri daga rayuwar ta bisa kafar sarki Aljani Matip.
kura mata ido ya yi sosai sannan ya ce
"Aje a wanke mata fuskarta da ruwan zuzirr, akwai bak'in yana da magauta masu neman ta sukayi jifa ya fad'o fuskarta,
shi yasa idan tayi duba a gareshi firgici yake dirar mata,
a wancan lokacin malam Buba Mani bai san da ragowa a goshin ta ba, wan da ya gani kawai ya iya cirewa."
kasa waziri Kutup ya yi da kansa yana cewa
"A gafarce ni ya shugaba na amma me yasa sai a kansa take shiga wannan yanayin, ga sauran bil'adam kuma ba haka ba."
murmushi sarki Matip ya yi sannan ya ce

"Magauta bincike suke babu dare babu rana sun watsa taurarin su ta ko ina domin cikar burin su,
tauraru ya fad'a a kansa duk da hasken shi ya disashe taurarun su amma yana tasiri a jikin sa,
shi yasa take jin hakan game da shi,
a wanke mata fuska da ruwan zuzirr na karkashin teku,
ganin da zata kuma yi masa zai kona taurarun su dake razanar da ita,
wanda yake a matsayin tarko gare ta, za'a shafe sammanin su da suke jin sun kusa gado inda take, duk da taurarun nasu baya da kaifin tasiri a kanshi,
har yanzu lalub'e suke cikin duhu."
"Na d'auki umurni ya shugaba na."

Waziri Kutup ya mike domin isar da umurnin da aka masa..

Sai bayan sallar la'asar ta farka.
tana bud'e ido ta saki murmushi ganin Chuchu da Chulu a kusa da ita.
Chuchu na rike da hannunta tana share mata d'an guntun jinin da ya fito kan bayan hannunta.
mikewa ta yi ta zauna tana fad'in
"Laa Chuchu Chulu kunzo ne har kun dawo daga tafiyar?."
suma murmushin suka mayar mata, Chulu ta ce
"Dawowar mu ke nan, muka biyo nan,
baki da lafiya kinji sauki ko mu baki magani."
"Naji sauki kaina ke min ciwo kad'an kad'an yanzu."
wani d'an karamin tandu mai murfi ta ciro, ta kwance marfin ta ce
"Kawo hannun ki na zuba miki ki wanke fuskarki zaki ji kan ya dai na miki ciwo."
ta mika hannu ta tsiya ya mata har sau uku tana wanke fuskarta da shi..
fuska ta yamutsa tana
kallon hannunta dake rike a hannun Chuchu sannan ta ce
"Wannan Sahab d'in nan ne ya caka min allura a gurin."
Chuchu ta ce
"Kina so ki rama?."
ido ta d'an waro ta ce
"Tsoro yake bani kuma duka ya ke yi fa, baku ga yadda ya yi wa su Miemie ba."
"Ki dai na tsoron shi ba ga munan ba zamu taya ki,
idan ya ce zai duke ki zamuyi mishi irin na Mommyn shi,
kin mance tun da data tab'a dukan ki muka rike mata kafa ta kasa iya tafiya, to haka zamuyi masa shima."

Dariya ta fashe da shi tuno da abin da suka tab'a yi wa Mommy tun tana karama.
sai da dariyar ta yi tare da cewa
"To amma ai kunce shi kun kasa iya yi masa komai, shifa mugu ne baku ga yadda ya caka min allura ba."
"Ina abin da muka baki ki sa masa a jikin san nan?."
"Yana can cikin wardrobe nifa tsoro nake ji, a ina ma zan ganshi na saka masan."
"Duk in da kika ganshi ki san yadda zakiyi ya tab'a jikin sa, ta nan ne kad'ai zamu sami damar iya yi masa wani abu,
idan ba haka ba to mu ba zamu iya yi masa ko mai ba ba zamu iya zuwa jikin sa ba,
mun d'au ki wancan a in da kika ajiye,
amma zamu baki wani."
d'an shiru tayi tana tunani ta ya za a yi ta iya hakan.
"Babu abin da zai miki ki daina tsoron sa mu zamu taya ki kinji."
kai ta gyad'a.
Chulu ta mika mata wani jan ganye guda d'aya ta ce
"Idan wannan ya tab'a jikin sa zamu iya zuwa jikin sa, bai isa ya yi miki wani abu ba zamu rama miki."
ta karb'a tana murmushi nan take ta kudiri aniyar saka masa a jiki, duk da bata san ta in da zata fara ba.

Har kusan magariba suna tare sai da Aunty ta shigo tashinta ta tashi magariba yayi tayi wanka,
kafin su Chuchu suka tafi.

Kasancewar tana fashin sallah,
tana fita daga wanka ta saka kaya ta fito parlour.
Aunty taji dad'in ganin yadda ta warware sosai, kamar ba ita ce jiya da d'azu abin tausayin nan ba.

Suna parlour da Aunty na sallar magriba ita kuma tana kwance tana buga game a wayarta.
Miemie ta shigo, ta zauna gefen ta tana fad'in
"Mara lafiyar ke nan d'azu na shigo ai kina bacci Aunty ke ce min baki da lafiya."
murmushi ta yi
"Eh amma naji sauki."
"Ba dai tsoro ne ya saki ciwo ba,ma tsoraciya kawai."
dariya kawai ta yi.
Miemie ta zauna sukayi ta hira har bayan sallar ishe kafin ta koma sashin su.


Siyama ce ta fad'o cikin d'akin Umma Karima, ta cire takalmi mai tsinin da ke kafarta tayi wurgi da shi.
"Ya ya mene ne hakan Siyama?."
"Aunty Karima kiyi wani abu dan Allah, ki duba fa ki gani lokaci kurewa ya ke dad'a yi,
auren nan fa da gaske za'ayi,
gashi duk wata hanyar da zanbi wai dan hankalin sa ya dawo kai na duk a banza,
dubeni ki gani dubi shiga ta ki gani ki ga irin had'ewa ta fa,
a haka yazo ya iske ni a sashin Mommy amma ko kallo ban isheshi ba,
duk yadda zanbi na janyo hankalin sa na bi amma babu wata nasara."

Umma Karima ta mike ta dafa kafad'ar ta ta ce
"Ina so ki kwantar da hankalin ki,
kar ki damu zaki mallaki Abdurrahim zaki same shi a tafin hannunki, boka yabani tabbaci kuma yana kan aiki a kan haka,
na yadda da boka Mali nasan bazai wasa mana kasa a ido ba,
auren nan da ke za'ayi in har ina numfashi."
"Aunty Karima in har abin nan bazai yuwuba kawai ni zan tinkare sa, na fad'a masa ina son sa."
"Dalla matsa can mashirmaciya kawai shi zai zo da kansa yace yana son ki, kuma zaki sha mamaki ki zuba ido kawai ki gani."

Da sauri Umma Karima ta d'aga hannu a kafad'ar ta tana cewa
"Tsaya ma tukun wai nikam kamar naga sonshi da gaske kika fara."
a dibirbirce Siyama ta ce
"Kamar ya Aunty Karima ai ni so nake ayi-ayi musamu abun da muke bukata, naga jinkirin zuwan lokacin ne kawai."
"Ai ho yanzu naji batu
je ki ki cire kayan nan ki huta, ki kwantar da hankalin ki kamar tsumma a randa, kamar yanzu lokaci zaiyi ayi a wuce gurin."
Siyama ta sauke b'oyayyen numfashi kana ta tattari takalmarta ta yi d'akin su.


Feeryal ce kwance a parlour saman doguear kujera rike da waya tana buga game.
Miemie ta shigo ta zauna gefen ta tad'a mata buka acinya tana fad'in
"Yanzu dama wayar tana hannunki nake ta kira kika ki d'aga wa."
"Wash Allah Miemie ta zafi fa."
"Ai dama so nake kiji zafin, ayi ta kiran ki a waya kike d'agawa, tun d'azu na tura miki abu ta Whatsapp baki ma hau online d'in ba bare ki gani,
ke kam ma ba amfanin wayar ki,
kalli kiga ni ashoben da muka cire na kannen ango kala biyar ne, Unaisa da Umaima'n Hajiyan Dubai ne zasu taho mana dashi daga can,
duk kalolin nan ba karamin kyau zasu miki ba."
ta karb'i wayar tana duba wa
"Gaskiya sun yi kyau kam."
ta fad'a tana mika mata wayar.
Miemie ta ce
"Ai sosai ma kuwa idan muka yi waya da su zance a siyo har da ke."
"Da ni kuma to ai ni ba kanwar ango ba ce me zai sa nayi ashoben."
Miemie ta tsare ta da ido.
kai ta gyad'a tana cewa
"Eh ai Mommy ta ce shi ba yaya na ba ne kinga kuwa ni ma ba kanwar sa bace."
"Dan ta fad'a shine me dalla kiyi abin ki, kowa zai sa ke ne bazaki saba."
Feeryal ta d'au wayar ta ta cigaba da buga game d'in ta tana cewa
"Meye a ciki tun da ba tsirara zanyi yawo ba, nifa bazanyi ba karma ki sa su kawo."
Aunty da ta fito daga kitchen tayi shiru tana sauraran su.
Miemie ta mike tana cewa
"To idan an kawo an d'in ka kar ki sa."
"Ki sa a kawo da ita zata saka ma."
cewar Aunty tana karaso wa cikin parlour'n,
Miemie ta ce tom kana ta dubi Feeryal da
ta tab'e fuska.
Tana cewa
"Goben zamuje gyaran gashin kuwa ni fa so nake ma ayi min kitso gashina sai karyewa yake gara naki shi baya komai,
kar gashin yagama gwaguyewa."
"Eh zamuje."
"To Allah ya kaimu."
ta fice ta koma sashin su.



Washegari da wuri Miemie ta gama shiri ta biyo wa Feeryal suka fito bayan Aunty ta gama yi musu kashe din su dawo da wuri.
suna hanyar su na zuwa parking lot Ameerah ta hange su.
murya ta d'aga
"Ke Miemie tsaya-tsaya-tsaya."
Miemie ta juyo tana dalla mata harara dan tasan bai wuci halin nata na rashin mutunci zatayi mata ba.
Ameerah ta karaso in da suke ta harare su sama da kasa sannan ta ce
"Da kika cewa su Unaisa su karo ashobe na mutum d'aya, ke zaki sa kala goma iri d'aya da naki da wanda za'a karon."
"Ina ruwan ki meye damuwar ki idan zan sa duka, idan kuma ma wata zan bawa kina da matsala ne,
ko akwai sisin ki a cikin kud'in siyan kayan,
Daddy ne me bada kud'in ko ke da kika titsiye ni kina tambaya ta."
"Ai nasan bai wuce ma wannan Aljanar kika sa ba, to tunda kud'in bana uban ta bane baza a kawo da ita ba,
ta had'a dangi da Ya Abdurrahim d'in ne da zatayi ashoben bikin sa,
to bama son gayyan sod'i, ta tsaya a matsayin ta dangin sa ne zasuyi ashoben bikin sa ba bare 'ya'yan tsintuwa ba."

Feeryal tayi murmushin takaici taja hannun Miemie ta ce
"Muje Miemie."
Miemie ta fisge hanun tana cewa
"Ke kam kin yi asara Ameerah haka zaki kare da gori, idan kikace zakiyi min ni wlh farfasa miki baki zanyi 'yar rainin wayo."
"Miemie muje dan Allah, ki rabu da ita."
Feeryal ta fad'a tana kuma ruko ta.
Ameerah ta waiga gefe da sauri ta isa bayan mota ta sunkuya ta d'auko magen Hajiya da ke kwance a gindin mota, ta jefawa Feeryal a jiki tana gad'in
"Munafuka idan bata rabu da ni ba ya zatayi da ni."

Wani irin uban ihu Feeryal ta kurma tare da kankame jikinta dake cirawa,
nan da nan kwayar idanunta suka sauya, tayi wani irin yanke jiki ta rid'u a kasa, tare da kuma kwalla kara ta zare gyale da d'ankwalin kanta ta yamusa gashin kanta.
tayi wani irin mikewa ta shako wuyan Ameerah.........!



11

Wani irin damka tayi wa wuyan Ameerah, tana wani irin gurnani.
idon Ameerah ya firfito, ta d'aga hanu kafafaka kamar kaza a cikin ruwa ta rike hanun Feeryal tana ja tayi-tayi ta iya b'anb'are hannunta a wuyan ta ta gagara.
ganin yadda Ameerah ta ke fafutukan niman numfashi, da sauri Miemie ta ce
"Sake ta Feeryal yau kin nuna mata shiru shiru ba tsoro bane gudun magana ne, kyale ta mu tafi wannan ya zame mata darasi in ita mai gane wa ce,
in kuma bata gane ba gaba a kuma ankarar da ita."
da sauri Miemie ta shiga kokarin janye ta, sai ji tayi kamar dusi take tab'awa.
"Feeryal kyale ta sake ta haka."
tafad'a tana jan hannunta dake wuyan Ameerah, amma ko gizau hannun ta baiyi ba.
da sauri ta dube ta cike da mamakin yadda taji takasa iya b'anb'are hannunta dake wuyan Ameerah.
da karfe ta d'ago kanta dake sunkuye gashin kanta ya rufe fuskarta.
a razane Miemie tayi baya ganin kwayar idanunta da suka sauya izuwa na ban tsoro.

Da gudu ta juya tana fad'in
"Me gadi security Feeryal Ameerah kuzo dan Allah wlh ba ita ba ce ba Feeryal ba ce!."
gaba d'aya ta kid'ime, tayi bakin get a guje tana kiran security.
Nabila da Sahla da komai ya faru a kan idon su dan tare suke da Ameerah dama, su suka tsaya jiranta ita kuma ta karaso ciwa su Miemie mutunci.
suka juya da gudu sukayi sashin Mommy suna fad'in
"Wayyo Allah Mommy Feeryal zata kashe Ameerah."
Mommy ta fito a hargitse dai-dai sanda Security suma suke karasowa gurin.
Aunty ma ta iso a bujajan Baba Rabi ta sanar mata da abin da ke faruwa.

Security suka bugawa Feeryal tsawa sukace
ta sake ta.
ganin bata da niyyar sakin ta,
ga yadda numfashin Ameerah ke yi kamar zai bar jikin ta, suka shiga kokarin jan Feeryal da jan hannunta a wuyan ta.
amma ko gizau basu iya ko da jijjigata ba.
Mommy ta ce
"Wayyo Allah shegiya mayya zata kashe min yarinya."
tayi kukan kura
tashiga dukan Feeryal da hanu bibbiyu ta baya tana fad'in
"Mayya sake ta kashe ta zakiyi."
wani irin sa kafa tayi ta baya ta angiza Mommy sai ga Mommy a kasa shirim, ta kawo ihu ta saka, tana dafe bayanta.
security hud'u sukayi kan Feeryal sukayi sukayi su iya kwace Ameerah a hannunta suka kasa.
Aunty da hankalin ta yayi mummunar tashi
ta zo ta gaban Feeryal tana fad'in
"Kuyi hakuri dan girman Allah ku sake ta na gama ku da Allah, kar ku ja mana masifa."

"Ai ita ce masifar babban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login