Showing 63001 words to 63585 words out of 63585 words

Chapter 22 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

bata ciki, ta wuce har cikin bayi, nan ma bata nan.
ta fito tana fad'in
"Ina kika b'oye ta fito da ita yau bazata kuma kwana gidan nan ba."
Aunty bata ce kala ba suka karaci masifarsu suka gama bincikota basu ganta ba suka tafi.
sai da suka tafi tukun Feeryal dake kichin suna aiki da Baba Rabi ta fito.
dan tajiyo hayaniyar su kuma tasan a kanta ne bai wuce ace tabar musu gida ba, dan Aunty bata sanar mata da abun da ke faruwa ba.

Mommy bil hakki ta d'aga bori babu wanda ya isa ya aurawa d'an ta Feeryal.
a gefe guda ma Hajiya na nata,
a d'aya gefen kuwa labari daya isarwa Umma Karima kaukane kawai batayi.
Bappa Salihu baiyi kasa a gwuiwa ba ya diro Lagos bayan maganar su da Daddy da kwana biyu, ya iso da daddare.
bai bari sai gari ya waye ba ya iso sashin Hajiya.
Hajiya tayi mamakin ganin sa a irin wannan lokacin.
Hajiya ta cewa Kulu ta kawo masa abinci
Bappa Salihu ya ce
"Bar abincin ki Hajiya Hanne bacin abincinki bane ya kawo ni."
Hajiya ta d'aga hanci sama tana cewa
"Yoo wata maganar aka gaya maka ke nan, nifa in akan batun auren abokin turawa ne da aljanar yarinyar nan ne,
bafa zan zuba ido ina gani a kakabawa jikana damuwa ba."
"Yanzu fisabilillahi Hajiya Hanne, ya kyautu ke nan kirika jifan d'anki da irin wad'an nan munanan kalamai,
mutumin da ba wani cikakken lafiya yake da shi ba, kike son ki rika d'aga masa hankali,
haba Hajiya Hanne har duniyar tayi miki dad'i irin haka, yau idan ya fad'i ya mutu wayake da asara,
ni bazan yadda nasa iso akan wani dalilinki mara ma'ana ki salwantar min da rayuwar d'a ba,
sabo da Yaya Shitu Fiya bashi da rai shike nan kike so ke ki baje kafa kizamo kece uwar kece uban,
to kar ki manta muna nan mu rai uku masu rai, ba kuma zamu sa miki ido ki nima yiwa 'ya'yan mu baki akarin banza ba,
musamman shi jigon mu Abubakar,
wani irin shirme ne wannan,
kiyi gaggawar janye furucinki a kanshi in ba so kike ki zamo ajalinsa ba,
daga ya so had'a sunnar annabi shike nan kibi ki tada hankalin ki,
bakin ciki kike da sunnar annabin?."
Hajiya ta ce
"Ni dama ai ban masa baki ba na gaya masa ne kawai bai isa ya aurawa jikana aljana ba."
Bappa Salihu ya ce
"To ai ba jikan ki bane ke kad'ai, kin san munfiki iko da Abubakar."
Hajiya ta ce
"To kuzo ku zauna da 'ya'yan ku ai dama tun ba yauba kuke nuna min bushashshen iko da gadara, nifa gara na koma gun dangina ma, dana zauna ana gwada min wani gadara,
in dai aure ne da wannan aljanar ko bani gidan nan baza'ayi sa ba."
Hajiya ta mike ta shige d'aki ta soma tattare-tattaren kaya, tana mita.
Bappa Salihu ya mike ya fita yana girgiza kai da fad'in
"Hajiya Hanne ikon Allah."

Washegari da safe bayan sallar asuba Daddy ya shigo sashin Aunty, tana kan sallaya yazuba mata goro da minti a gaban ta.
da sauri ta d'ago ta ce
"Daddy wannan fa?."
zama ya yi a bakin gado sannan ya ce
"Na auren Abdulrahim da Feeryal ne da aka d'aura yanzu.......!



*Masha'allah anan wannan littafi na biyu ya kawo karshe sai mun had'u a littafi na na uku*🤗



*FEERYAL littafin kud'i ne ki biya domin karantawa cikin aminci 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank.
ki tura shaidar biya ta Whatsapp number ta 08034690723 ina maraba da ku masoya na ni ma ina kaunar ku*🤗


Bari muzo mu raka FEERYAL d'akin ABDULRAHIM kowa ya tafi cikin shiri fa dan bamusan ya zamu tarar uwargida Kuraiba ba😂🤸⛹️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login