Showing 18001 words to 21000 words out of 63585 words

Chapter 7 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

wlh na mance kina jirana kiyi hakuri dan Allah."
Feeryal ta maida hawayen da suka ciko mata ido sannan ta ce
"Ya Ajmal ne ya ce naje na kira Ameerah wai wannan na kiran ta, shine fa na je."
"Waye wannan kuma Feeryal?."
"Um wai waye sunan shi ma wannan babban yayannan naku mana wai waye ma sunan shi, am Sahab."
"Sahab kuma bamu da wani yaya mai suna Sahab, Ya Abdurrahim ke nan ."
"Eh shi, mamansa ta ce kar na sake ce masa yaya shi ba yayana bane,
dama nima ban san shi ba."
da sauri Miemie ta ruko hannun ta ta ce
"Kibar maganar taho muje kiyi hakuri kinji."
ta janyo ta suka yi gaba.


Shirye shiryen bikin Abdurrahim da Kuraiba yana dad'a kankama, musamman a gurin iyayen su mata Mommy da kuma Hajiya Luba, a d'ya gefen har da Alhaji Jibiril wato mahaifin Kuraiba,
dan yana matukar farin cikin had'a zuri'a da baban family sanannen family irin family'n A.A FIYA.

Daddy ya ba Mommy isasshan kud'en da zai isa yin lefe,
a b'angaren sa baya nuna farin ciki ko akasin sa game da auren.
da farko shima yaso d'an nasa yaje gida can Yelwan Shendam ya nimi mata, amma da Mommy ta buga kasa ta kekashe ita tayi masa mata sai ya kyale ta, tun da ita uwa ce ita ma tana da hakki a kan sa,
sannan kuma ya d'an yaba da gidan da matar ta fito.

Dubai Mommy ta tafi suka had'e da Hajiyan Dubai bayan sun had'a akwatuna set biyu suka wuce Egypt suka had'a set uku kafin ta biyo girgi da kayan ta dawo.
sashin Hajiya aka jibge kayan, 'yan'uwa da abokan arziki ana ta zuwa gani, anata yaba kyau da tarin yawa da tsada irin na kayan.


Feeryal da ta fito daga bathroom d'aure da towel, ta isa gaban wardrobe da sauri ta bud'e gefen da su pant da pat d'in ta suke.
ido ta d'an waro tuno da pat d'in ta ya kare ga period d'in ta ya zo.
dafe goshi tayi tana fad'in
"Wayyo na mance ashe ya kare."
sai kuma ta rufe wardrobe d'in tayi waje tana fad'in
"Ammie Ammie."
a sakiyar parlour suka had'e da Aunty da kiran nata yasata fitowa daga kitchen.
"Ya akayi ne Feeryal mene ne da irin wannan kiran?."
baki ta turo tare da langwab'ar da kai cikin muryar shagwab'a ta ce
"Ammie pat d'ina ya kare."
ido Aunty ta waro gaba d'aya ta mance da tame d'in period d'in ta ya yi, dan ko wani tame tana zuwa duba pant da pat nata,
tagama mancewa da wancan watan pat d'in zai kare bazai kai wannan watan ba.
ta ce
"Subhanallah na gama mantawa ne amma bari Baba Rabi yanzu ta fita taje ta siyo miki, jira yanzu za'a kawo miki."
Aunty ta juya da sauri ta koma kitchen in da suke aiki da Baba Rabi.
ita kuma ta juya ta koma d'aki.

Ta kasa zama sai sintirin shiga bayi take tana wanke shi da ruwa,
sam bata son jini ya b'ata mata jiki ko kad'an,
a rana takanyi amfani da pat kusan goma dan duk san da zataje fisari to fa sai ta canza pat.
gaba d'aya ta damu tana jin ta kamar a kan kaya take,
da sauri ta d'au hijabi ta zura kan towel d'in jikin ta,
ta fita da sauri ta nufi sashin su Miemie.
A parlour ta tadda Ammah ita da Faisal.
ta gaishesu tare da tambayar Ammah Miemie,
Ammah ta ce
"Tana sashin Hajiya."
"Wayyo Allah."
ta fad'a a kasan ranta a fili kuwa cewa ta yi
"Ammah bari na d'auki abu a d'akin Miemie."
Ammah ta yi murmushi tana cewa
"Ke da d'akin ku har sai kin fad'a zaki shige shi."
itama murmushi tayi.
Faisal kuwa cewa ya yi
"Kar dai Miemie ta koya miki halin gulmar nan nata."
nan ma murmushi tayi ta wuce d'akin.
wardrobe d'in ta ta bud'e ta bincika ko zataga pat tagama dube-duben ta bata gani ba,
abin haushin ma ga wayar ta a kan gado bata tafi da shi ba bare ta karb'i wayar Ammah ta kirata da shi tun da itama bata fito da wayar ta ba.
kamar zatayi kuka ta fito.

Amma ta ce
"Kin sami abin ko ta canza masa gurin ajiya, kin san halin ta da iya b'oye abu kamar me."
d'an jim tayi tana jin nauyin ta ce ga abin da take nima ga Faisal a gurin, sai kuma ta girgiza kai ta ce
"Zanje na dawo kafin ta dawo."
Ammah ta ce
"Ko zakije ki kirata acan tazo ta baki, Miemie idan ta sami hira ba dawowan yanzu ba, bare anje ganin kayan lefe."
Feeryal tayi shiru bata isa taje sashin Hajiya ba kam.
maganar Amma ta kuma ji
"Kije ki kirata Miemie fa bazata dawo yanzu ba."
a hankali ta juya ta fita, kamar kwai ya fashe mata a ciki a haka ta isa kofar Hajiya.
ganin tsayuwa bazai ficceta ba tayi jahadi tasa kai ciki.

Mutane da yawa cikin parlour'n da wanda ta tab'a gani da wanda bata tab'a ganin su ba.
an baje kaya cikin parlour' kamar masu shirin bud'e ShopRite.
gaba d'aya mutane tun shagala da kallon kayan sai santi suke.
har ta karaso ciki babu wanda ya lura da ita, tana ta baza ido dan ta ga ta ina Hajiya take, amma bata ga ko walkiyan ta a parlour'n ba.
da sauri ta isa in da Miemie take tsaye tana ta d'aga kaya tana aikin zuba surutu.
ta tab'a ta ta baya,
bige hannunta tayi tana cewa
"Dalla barni kai gawani arnen sarka wayyo Allah na."
Feeryal ta kuma tab'ata, sai sannan ta juyo baki ta washe ta ce
"La Feeryal ke ce dama na d'auka Nabila ce take tab'ani ta nuna min wani abin,
ke zokiga kaya dan Allah wai duk wa mutum d'aya za'a kai."
hannu Feeryal ta yarfe ta ce
"Dan Allah Miemie ba wannan ba taho muje ki bani pat nawa ya kare Baba Rabi taje siyo min bata dawo ba."
"To naji zauna bari na gama ganin wannan akwatin."
ta turata kan kujerar bayan ta, ta zauna tab'as a kan kujerar.
tana kokarin ta shi ta kuma mai data
"Dan Allah ki tsaya na gama gani muje na baki."
Miemie ta zauna kan hanun kujerar tayi banga banga da kafafunta ga mutane ata gefen ta babu ta yadda zatayi ta mike.
"Miemie muje ki bani dan Allah sai ki dawo."
bata ko jinta hankalin ta nakan magana da kallon kaya.


Ya kosa da jin maganar Hajiya da Mommy ta kawo karar sa gurin ta,
kan yaki zuwa su tattauna yadda shagalin bikin nasu zai kasance da amaryar tasa.
ya mike daga kan kujerar da yake zaune cikin d'akin Hajiya da ta gama zuban ta baya ma jinta idanun sa yana kan waya, ya mike yana d'an jan gajeren tsaki ya zura takalmansa.
ganin tafiya zaiyi Hajiya ta ce
"Kai abokin turawa maza kaje gidan su yarinyar nan kar ka sake baka je ba na gaya maka ke nan,
in banda abin ka ana son yi maka gata ma dube ka fa gabjeje da kai ace baka da iyali,
sa'anninka duk sunyi aure da 'ya'ya uku hud'u,
dubi d'an nan Isa d'an gidan bappanku Jibo matansa biyu da 'ya'ya shida, gasu nan dugui-dugui tafe da kafafunsu,
tafiya na Yelwan nan na ganshi cikin 'ya'yan sa gwanin sha'awa, kuma sa'anka ne,
sai yaushe ne zakayi auren kai idan aka barka haka zakayi ta zama babu aure, ina kuwa uwarka zata so,
itama zataso ganin 'yan jikokin ta kamar yadda nake ganin ku nake jin dad'i."

Kofa ya nufa yana fad'in
"Ko naje ko banje ba aure ai bazai fasu ba, to kuyi mana kawai, me zai sa sai naje."
yayi waje yana d'aga kiran da ya shigo wayarsa."
Hajiya ta d'aga murya tana cewa
"Ai aure kamma kamar anyi an gama baza'a cigaba da zuba maka ido ka cigaba da zama tuzuru ba."

Da sauri ta waiga jin ana jan abu akan kujerar da take kai.
caraf idanunta ya sauka cikin nashi.
wani irin mugun fad'uwar gaba ne ya ziyarce ta zuciyarta ya yi wani irin tsalle kamar zai faso kirkinta ya fito.
da d'a gimtse fuska ya yi yana gyara rukon wayar da ke kunnensa,
ya yin da hannunsa guda ke rike da rigarsa da ke kan kujerar da Miemie ta turata kai.........!




9

Da karfi ta janye idanunta daga cikin nashi wanda kad'an yarage ta kwalla ihu tsabar tsoro ga wani irin mashahuriyar kwarjinin dake cike cikin idanun nasa.
da sauri ta kalli inda hannunsa yake yana kokarin jan rigarsa a kan kujerar da take zaune a kai.
da sauri ta wani irin zabura ta mike tsaye jiki na kyarma.
ya d'ago rigar yana mai ware idanunsa a kansa, ya yin da fuskarsa ya dad'a sauyawa izuwa na b'acinrai karara.
ido Feeryal ta ware kan rigar da sauri ta dafe kirjinta dake ta tsalle yana niman hanyar fita, numfashin ta na sarkewa tagama sadakarwa fita zaiyi ya bar gangar jikin ta.
bata ankara ba taji ya jefo mata rigar kan fuskarta tare da jan dogon tsaki
"Mssttt stupid wawuyar kazama."
kana ya juya ya fice a parlour'n.
hanu na rawa ta ciro farin rigar daga kan fuskarta,
wanda jini ya yi makeken shati a jiki.
tana rarraba ido cikin parlour'n sai dai babu wanda ya lura da abin da ya faru kowa hankalin sa na kan kallon kayan da suke kallo.

Da sauri ta bubbuga Miemie ta juyo.
tuni hawaye yasoma sauka a idon ta,
Miemie ta ce
"Feeryal mene ne kuma?."
rigar ta d'ago ta nuna mata murya na rawa ta ce
"Ina ta ce miki kizo mu je gashi kinsa na b'ata masa riga."
ido Miemie ta waro ta ce
"Wannan kamar rigar da Ya Abdurrahim da ya shigo da shi a hannunsa, dan singlet ne kad'ai a jikin sa sai wannan rigar dake rike a hanun sa ya shigo, ya wuce d'akin Hajiya kafin shigowar ki."
kai ta gyad'a hawaye ya zubo sharr.
Miemie ta ce
"Munshige su yi sauri muje mu wanke kafin ya fito ya gani."
cikin Feeryal ya dad'a d'ura ruwa cikin muryar da kuka ke son kwace mata ta ce
"Ai ya gani."
kirji Miemie ta dafe da sauri ta jata sukayi waje, sai da suka fita kafin ta ce
"Da gaske yafito ya gani?."
kai ta gyad'a hawaye na zuba.
Miemie ta rike kugu tare da sauke numfashi sannan ta ce
"Muje mu wanke masa da sauri."
Feeryal ta gyad'a kai jiki na rawa suka wuce sashin Ammah.

Suna shiga d'aki Miemie ta ce taje bayi ta gyara jikin ta, tad'u pat da sabon pant ta bata da kaya ta saka.
tafito ta rab'e bakin gado tana ciccire ido, ganin yadda ta tsorata da yawa Miemie ta shiga bata baki tana fad'in
bazai mata komai ba ta saki ranta ai ba da gangan tayi ba, kuma ma ai ita ce da laifi, ita ta sata zama kan kujerar da rigarsa ya ke kai.
ta shiga bayi ta wanke masa rigarsa tas da ruwan kumfa mai kamshi, kana ta sarkakeshi da ruwa mai kyau,
yafita kwal babu ko d'igon jini, kana ta wanke towel da hijabin da Feeryal d'in ta cire.
ta matse a inji ya boshe ta fito da su.
ganin yadda rigar ya yi haske bazaka tab'a ce wani abu ya same shi, nan Feeryal tad'an ji sanyi cikin ranta.
Miemie ta kuma fesa turare har kala uku a jikin rigar sannan ta jona ayon ta goge shi ba rigar ba hatta cikin d'akin gaba d'aya ya garwaye da kamshi.
Miemie ta d'ago ta dubi Feeryal da ta d'an fara dawowa hayyacin ta ta ce
"Yauwa to muje a kai masa."
Feeryal tayi raurau da ido
"Miemie bazai duke ni ba?."
"Babu abin da zai miki muje to ni zan kai masa imma dukan ne ni ya duke ni."

Suka fito Feeryal na jan kafa da ka ganta kasan a mugun tsorace ta ke.
can suka hango sa bakin get na side d'in sa yana tsaye jikin motar da alama fita zaiyi dan ya sauya shiga,
wani riga da wandon yadi ne skai blue d'inkin haf jamfa a jikin sa, ya yi matukar kyau cikin shigar,
murjajjen fatarsa Chocolate colour sai d'aukar ido ya ke.

Miemie ta tsaya da sauri ta dubi ta ce
"Feeryal dole fa ke zaki kai masa, karb'a ki kai masa ki bashi hakuri, nasan idan nakai masa zaice kin rainashi me yasa ke baki kai masa da kanki ba."
nan da nan Feeryal ta dad'a birkicewa har sai da taji wani jiri ya gilma mata.
"Yi sauri ki kai masa kinga zai shiga mota."
Miemie ta damka mata rigar a hannunta.
"Je ki mana Feeryal kar ya tafi."
numfashi ta fizga da kyar kana ta soma d'aga kafarta, jikinta na rawa ta kankame rigar gam-gam kamar mai shirin b'uya jikin rigar, jikin ta na b'ari da kyar take iya d'aga kafarta tana tafiyar sand'a,
gaba d'aya jikinta kyarma yake,
yanayin tsoron da take ciki bazai misaltuba.
da kyar ta isa in da yake, kasan cewar fuskarsa na ta jikin mota ne ya bata baya.
nan ta sami damar iya tsayuwa ta bayansa, da kyar ta iya bud'e baki murya na rawa had'e da sarkewa ta miko masa rigar tana fad'in
"Ka.ka..kayi hakuri ga.ga..rigarka."

Da d'an sauri ya waigo da alama baisan da mutum a gurin ba ga yadda ya juyo d'in,
wani irin dibirbircewa tayi kamar ta kurma ihu ko ta ruga aguje.
sanda idanunta ya sauka cikin nashi.
sabar tsoro sai da rigar ya sub'uce a hannunta ya fad'i kasa.

Ido ta waro tare da kai hannun ta duka biyu ta toshe bakin ta,
sai kuma tayi saurin sunkuyawa ta d'au rigar ta rungume shi a jikinta gam-gam.
ido ya bita da shi fuskarsa babu annuri.
kai ta shiga girgizawa tayi baya da kafarta ta shiga ja da baya murya na rawa ta ke fad'in
"Dan Allah kayi hakuri."
wani kallo ya wurga mata tare da cewa
"Move here!."
ya juya ya shige motar sa yayi wa motar ki ya nufi babban get.

Da sauri Miemie ta fito daga mab'uyarta ta zo in da take da sauri ta ruko ta tana cewa
"Feeryal bai karb'a bane?."
kai ta gyad'a mata hawaye sharr.
Miemie ta ce
"Ai dama da wuya ya karb'a taho muje kawo rigar bazai kuma sawa ba zan baiwa Isa direba"

Ganin yadda Feeryal d'in ta birkice gaba d'aya, Miemie ta rakata sashin su, suna shiga Miemie ta juya,
ita kuma ta shige bedroom d'in ta ta haye can kuryar gado ta dunkule guri guda ta cusa fuskarta cikin blanket.

Miemie na fita tayi gurin Isa direba ta kai masa.
Isa direba ya yi ta murna ganin riga mai kyau da tsada.
kasancewar war yau asabar ne su Ajmal suna gida,
akan idon su tayiwa Isa direba kyautar rigar.
zata koma Faisal ya kira ta, ya ce ta zo ta kaiwa Ammah kulan ta.
ta karaso gurin su.
Faisal ya mika mata kular yana fad'in
"Ke a ina kika sami rigar can da kika bashi."
"La ai bansan kuna nan bama da kai na kawo mawa, ko kuma ba kai bama Ya Ajmal ko Ya Shamsuddin."

Faisal ya harareta "Ke ni sa'anki ne."
Ajmal ya yi dariya ya na fad'in
"A ina kika sami irin wannan rigar haka, ko saurayin ki ne ya kawo miki tsarabar nashi."
"Cap waya bashi kud'in siyan wannan rigar, a ina ma taga saurayin tukun."
cewa Faisal yana hararar ta.
Shamsuddin ya ce
"Wa ya fad'a maka wad'annan yaran ai sai Allah duk suna da samaruka, ranar ma ina jin Sahla wai tana hira da saurayi a waya hmm."
dariya ta yi tana cewa
"Rigar Ya Abdurrahim ne fa dan mun samasa datti a jiki shine wai baya so,
shine nikuma na kawa Isa direba kyautar sa, ban san kuna nan ba da ku na kawo muku."
"Yauwa idan kuka kuma yin datti da wani ya ce baya so ku kawo min, wai ina mutumiyar taki ce yau na ganki ke kad'ai."
cewar Shamsuddin.
ta ce "Yanzu muka rabu tana side d'in su, Ya Shamsuddin kana so Ya Abdurrahim yayi mana kabarin da ba sallah ke nan idan muka kuma sa masa datti a jikin kaya, tap hmm."
ta juya da sauri ta bar gurin..

Tun da Feeryal ta kule d'aki bata fito ba tana nan a dunkule cikin bargo tsabar tsoro har wajen magriba tana kwance, kan kace me jikinta ya had'a zafi rau zazzafan zazzab'i ya saukar mata.

Ganin shiru-shiru Aunty bata ji d'uriyarta ba, nan ta tuna da tun d'azu taga shigowar su da Miemie, Miemie ta fita ita kuma ta shige d'aki,
bata kuma ganin ta ba tun daga lokacin.
Aunty ta nufi bedroom d'in ta na kwad'a mata kira.
ta tura kofar ta leko kanta ciki,
can ta hangota kwance dunkule cikin blanket tana rawan sanyi.

Da sauri Aunty ta iso bakin gadon tana fad'in
"Subhanallah Feeryal lafiya me ya same ki?."
ta hayo gadon tare da zame blanket d'in taji jikin ta zafi rau kamar wuta.
hankalin Aunty ya yi mummunar tashi, nan da nan ta d'aga waya ta kira family doctor su.
ya ce mata ya fita ya yi nisa amma zai dawo zuwa anjima zai zo.
Aunty ta ce
"Dan Allah Dr ka taimake ni kazo yanzu."
"Hajiya kiyi hakuri zan iya kaiwa awa d'aya a hanya ma kafin na iso kinsan yanayin garin akwai gosulo da yawa, kuma na d'anyi nisa wlh amma dai zan iso ko zuwa bayan isha ne in Allah ya yarda,
a bata paracetamol ta sha kafin na iso."
Aunty ta kashe wayar ta mike da sauri ta je d'akin ta ta d'auki paracetamol da ruwa ta dawo ta d'agota ta tallafo ta tana fad'in
"Sannu Feeryal sannu kinji, baki da lafiya shine zaki kwanta kiyi shiru da ciwo na cinki,
sha maganin nan kafin Dr ya zo."

Rau-rau tayi da ido sai ga hawaye masu d'umi sun zuba, cikin galabaitaccen murya ta ce
"Ammie kar yamin Allura dan Allah Ammie kice kar ya min Allura."
"Kiyi hakuri Feeryal kinji jikin ki kuwa, nasan ma dole sai an had'a da allura kafin ya yi sanyi, sannu kin ji, ina ne ke miki ciwo yanzu?
sha maganin maza yanzu kafin ya zo."
Ta saka mata maganin a baki had'e da ruwa ta sha tana matsar kwalla.

Aunty na zaune a gefen ta tayi mata pillow da cinyarta, sai sannu take jera mata.
ko da lokacin sallah ya yi a nan d'akin nata tayi al'wala tayi sallah.
har wajen karfe tara Aunty na zuba idon ganin Dr ganin goma saura ta kuma kiran sa a waya.
ya ce
gashi nan a hanya gosulo ya tare shi.

Aunty tayi salati ta rasa ina zata sa kanta sabar damuwa.
ga shi Daddy baya nan.
a haka suka kwana tare da ita, jikin ya d'anyi sanyi ba sosai ba sakamakon paracetamol d'in da ta sha.
kusan asuba jikin ya kuma yin zafi rau sai rawar sanyi take.
Aunty ta rasa ina zata sa kanta shalelen ta ba lafiya.

Ana idar da sallar asuba ta kira number Dr sai dai akayi rashin sa'a wayar akashe.
tayi ta kiran number har gari yayi haske, ganin hakan ba zai samar mata mafita ba.
tayi waje da sauri tana kwad'awa direba kira.
sanin yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login