Showing 48001 words to 51000 words out of 63585 words

Chapter 17 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

kusanci mace ba.
ta tako ta haye gadon ta shige jikin sa gaba d'aya ta narke, dan a mugun hanu take.
tashiga shafashi tana kokarin tura hannu cikin wandon shi.
ya yi saurin ruko hannunta ya ture ta a jikin sa.
tare da buga mata tsawa
"Ta shi ki fice min anan!."
kamar zata fasa kuka ta koma tana fad'in
"Mijin Kuraiba please and please kar ka koreni ajikin ka, I really love you dan Allah."
a haukace takuma rungumo shi tanajin yadda kasanta ke motsawa yana niman mai agazama masa.
ido ya kura mata ganin yadda ta birkice gaba d'aya yana hango tsantsan bukata tare da ita.
gani ya yi shiru bai kuma tureta jikinsa ba.
gaba d'aya ta birkice masa tana safashi da kissing d'in sa.
sai da ya tabbatar da ta kai kololuwa pant d'in jikin ta ya gama jikewa.
ya mike ya bata guri, ya yi mata alama da hanu ta tashi ta fita.
gaba d'aya idanunta ya rufe ta mike takuma fad'o wa jikin sa tana sakin wani numfashi da kyar ta iya furta
"Dan Allah kar kayi min haka Abdurrahim,
hakkina dake kanka idan ka danne bazan yafe ba."
buga mata tsawa ya yi fuska ba wasa ya ce
"I say get out!."
jikin ta ya kama rawa dan ba tsawan wasa ya yi mata ba.
ta fashe da kuka ta kuma fad'awa jikin sa dan wlh tana jin sha'awar da zai iya hallaka rayuwar ta.
rigar jikin ta ta yaga nonuwanta da suka fara zubewa suka bayyana dan ma suna samin gyara dad'an fasalin su.
ta manna su a jikin sa
cikin muryar kuka a rikece ta ke fad'in
"Saboda son da nake maka yasa na kawo kaina gareka shine kake min wulakanci,
duk wani wulakancin da kake min sai na kira Mommy na gaya mata."
Kamar ya yi mata d'na banzan duka haka yake ji, badun gudun abun da Mommy ta fad'a ya kama sa ba da yau sai ya tattakata.
ya fincike ta a jikin sa ya tureta har sai da ta garu da jikin gado, ya ce
"Oya je ki gaya mata."
jan kafa ta shiga yi da kyar ta fice a d'akin tana ji kamar zatayi hauka sabar wutar jarabar dake azalzalarta ta kasa.
tsaki yaja ya koma ya kwanta...
duk yadda taso gusar da sha'awan ta da kanta ta kasa haka ta kwana birgima.


Washegari da safe ya yi shirin tafiya asibiyi, yaje ya duba jikin Daddy bayan ya gama duba jikin nasa ya basa magani ya yi masa allurai.
jiki a d'an sanyaye ya fita dan lamarin jikin Daddy'n kullum dad'a kara gaba yake.
a parlour'n Daddy ya had'u da Mommy data shigo yanzu.
ya gaisheta batare da ta amsaba ta bishi da wani kallo,
cikin kasa da murya dan da mutane cikin parlour'n ta ce
"Idan bakaji tsoron Allah ka sauke hakkin da yake kan ka ba, wlh bazakaga dai-dai ba, kuma wlh ban yafe maka ba,
baka isa ka kunyata ni ba."
ta wuce bedroom d'in Daddy.
har ya ja mota yabar gidan yana mamakin yarinyar wato da gaske karan nasa takai akan yaki kusan tarta, lallai wannan yarinyar tacacciyar mara kunya ce.
a daren ranar kuwa sai da ta maitance da naciya da kafiya ta samu abin da take so,
ba dan son ransa ba...



Wasa-wasa ciwon Daddy sai gaba yake, kullum ba sauki, gaba d'aya ya rame yafita hayyacin sa.
kullum dare kamar sotse soka da jinin jikin sa ake.

Aunty ce ta fito da ga bedroom d'in ta da sauri, zataje duba in da Daddy ya kwana da jiki.
Feeryal ta ce "Ammie ki jirani muje na gaida Daddy."
Aunty ta nufi kofa da sauri tana fad'in
"Feeryal ki same ni acan."
tayi waje da sauri dan jiya da shi ta kwana aranta.
ganin Aunty tayi gaba sai ta koma ciki, da ma batayi wanka ba.
sai da tayi wanka ta shirya cikin riga da sket na atamfa ta d'au bakin gyale ta yafa kana ta fito.
can ta hangi Miemie daf da side d'in Daddy suna tsaye ita da Sumayya.

A hankali take takowa cikin yanayin ta mai sanyi.
Zaraddin da abokin sa Ziyad suna tsaye a bakin get d'in side d'in su, a jikin motar Ziyad d'in.
Ziyad na hango ta ya kafe ta da ido yana fad'in
"Wow See beautifully, kai kaga wata 'yar shila kuwa,
irin wannan kayan marmari haka, kai Deen wai wannan kayan alatun a gidan nan kuke rayuwa da ita,
kai narantse har naji abin na na motsi."
Zaraddin da shima idanun sa a kan ta ya yi wani murmushi mai kama da dariya yana shafa gefen fuskarsa ya ce
"Zazzafa yarinyar mai zafi ce, mallaki na ce ita d'auke idanunka a kanta,
matar da zan aura ce."
"Kai wai da gaske kake ko wasa."
Zaraddin ya ce
"Da gaske nake auren ta zanyi,
idan na aje wannan a gida ta ishe ni komai, babu wata macen da zan kuma kulawa, idan wannan tana gefe na zan koshi har wuya."
"Amma kam taji kayan had'i, to kafin ka d'auke ta zaka bani aron ta na kwana d'aya kawai, ba'a hana mabada rago fata ka sani."
harararsa ya yi yana jijjiga kai idanunsu duk a kanta..


Ta karaso gurin su Miemie.
Miemie ta rike baki ta ce
"Iyee kinga kyan da kikayi cikin atamfa kuwa."
murmushi tayi mata, Sumayya ma ba yabo ba fallasa ta ce
"Sannu Feerya."
itama ta ce "Sannun ki."
ido Sumayya ta waro ta ce
"Nashige su gashi can shigowa, jiya yace na kunce kitson attach d'in nan, ban tsefe ba bari naje na tsefe yanzu kafin mu had'u."
Miemie da Feeryal duk suka juya in da take kallo.
ya shigo a kan keke yana sanye da wando da rigar Jecy yellow,
kafarsa d'aure da farin takalmi sau ciki, da dogon safa.
Miemie ta ce "Ya Abdurrahim nefa ya fito motsa jiki ke nan, Allah yasa ya zo ya tare ki a nan."
"Ai bazan ma tsaya ba d'akin Hajiya zanje na tsefe acan."
ta juya tayi gudu ta tafi sashin Hajiya.
suma suka shige sashin Daddy.

Ziyad ya shige motarsa ya na fad'in
"Deen kar ka mance dai 1 za'a tafi club d'in nan, ka taho mana da wancan zazzafar zata kayata gurin."
kafin Abdurrahim ya karaso gurin Ziyad ya tada mota ya nufi get.
yana karasowa yabi Zaraddin da wani kallo.
Zaraddin ya d'an sosa keya yana cewa
"Bros an dawo."
fuska a suke babu damshin annuri ya ce
"Kar ka sake shigo da shi gidan nan, kar na sake ganin sa a cikin gidan nan......!




23
"Nayi maka magana kan harka da yaron nan baka dai na ba ko."
ya yi maganar yana dad'a tamke fuskarsa. Zaraddin yakuma sosa keya yana fad'in
"I'm sorry bro."
kai ya jinjina
ya wuce kan keken sa zuwa b'angarensa.

A parlour su Feeryal suka tsaya sabo da wasu 'yan'uwan Daddy dake tare da shi a bedroom d'in shi.
sun b'ata lokaci kafin suka fito, nan suka sami damar shiga duba shi.
jiki a sanyaye Feeryal take gaida Daddy ganin jikin nashi sosai ne.
murmushi ya yi mata yana amsawa da kai.
Aunty na d'akin tana ta faman gyara in da aka b'ata, Umma Karima ta shigo tabi Feeryal da kallon banzan.
tana cewa
"Tun da anyi gaisuwar sai a tashi aje ba zama ake yi ba, ya kamata ma fa a hana masu shigowa gaisuwar nan haka bamusan da me ake shigowa ba,
ba 'yan waje kad'ai za'a hana su shiga ba har da wanda suke gidan,
ana jinya amma kullum ciwo gaba ya ke,
waya sani ma ko ana tufka wasu na warwara ne."
Aunty ta ce
"Idan ma tufkar ake daga gefe ana warwara insha'allah Daddy zai sami lafiya, kullum fatan sauki muke nima masa."
Umma Karima tabi Aunty da kallon banza tana cika tana batsewa ta isa ta hakimce kan kujera.
tana fad'in
"Magana nake kan b'aren da suke cikin gida masu shigowa kan sa, bamu yadda ba idan ba na jikin sa jinin sa ba babu mai kuma zuwa duba shi, za kuma ayi Meeting akan haka."
Aunty tayi kamar bata jita ba dan tasan niman magana take ita kuma bazata biye mata ba damuwar ciwon Daddy ma kad'ai ya ishe ta.
Miemie ta janyo hannun Feeryal sukayi waje.
a bakin kofar parlour'n Daddy ta tsaya tana fad'in
"Wlh matar nan nakusa na tsaya na wanke ta daga sama har kasa,
rashin mutuncinta karuwa yake dad'ayi."
Feeryal tayi murmushi bata ce komai ba dan tasan da ita Umma Karima take.
Kuraiba suka hango tana zuwa, wasu masassun kaya ne a jikin ta, sai wani d'an misitsin gyale data rataye shi a gefen kafad'ar ta.
da wani takalmi mai tsinin gaske a kafarta,
ta toshe ido da bakin glass tana taunar cingam.
"Um kaga amarya ansha gayu wane za'aje club, kuma wai an zo gaida siriki ke nan."
cewar Miemie tana mara baki.
Feeryal ta kalli Kuraiba sannan ta maida kallonta ga Miemie ta ce
"Ai kuwa tayi kyau."
da sauri Miemie ta ce
"Dalla ina wani kyau anan tana tafiya kamar agwagwa, ni har tama ban haushi."
"Ke Miemie Allah ba ruwana taho mu tafi."
Feeryal ta ruko hannun Miemie tana kokarin janta dai-dai san Kuraiba take karasowa kofar parlour'n.
yatsa ta saka ta d'an ture glass d'in idon ta sama, tana wani taunar cingam yana kas-kas.
ta bisu da wani kallon rashin daraja sannan ta ce
"Ku ta ina kukaga mijin Kuraiba ya shige?."
Miemie ta mayar mata da irin kallon da ta musu sannan ta ce
"Waye kenan me irin wannan sunan sai dai ki shiga ciki ki tambaya."
mai da gilashin tayi ta gyara zaman sa a idon ta, ta buga cingam d'in ya bada kara kass.
har sai da hankalin mutanen dake cikin parlour'n ya dawo gurin su, kana tayi musu kallon sama da kasa tacikin glass, sannan ta sa kai ta shige ciki.
da sauri Feeryal ta ce
"Miemie ba sunan ta ba ke nan Kuraiba? to ai mijin ta ke nan ta ke nufi."
"Na gane sarai 'yar rainin hankali mu zata gwadawa iyayi, wai wani mijin Kuraiba to ai ko bata fad'a ba ai ansan mijin ta ne, ni bana son mutum mai iyayi irin haka, ita gatanan me miji,
ai sarai naga shigowar Ya Abdurrahim d'in ta can kofar ba gashi can ba tsaye da uncle Bashir,
dubi yadda ta nufe su ni fa haushi ma tafara bani, ni na tsani macen da batasan kanta ba,
dan kayi karatu a kasar waje sai ka zamo mara jan aji a matsayin ka na mace, komai ka nuna wayewa kawai,
ai badun ciwon Daddy ba muma da last year zamu bar kasar, amma wlh sai dai ma na rike kaina narika jin kaina a big girl,
ni zo mu tafi ma dan Allah naje naji muryar Murad d'ina zuciya ta tayi sanyi."
ta janyo feeryal suka fice.


Zaraddin ya shigo parkour'n Mom
tana zaune ita da Shamsuddin.
Mom ta bishi da kallo har
ya zauna.
ya kalle ta yana shirin yin magana Mom ta ce
"Ya akayi ne Zaraddin?."
ya ce "Mom aure nake so."
cikin farinciki da jin dad'in fitar kalmar aure daga bakin sa ta ce
"Kai nagode Allah shike nan kayi auren ma ka huta da bakin mutane, sai su karaci mugun bakin su ta wani gurin, ka sami matar auren ce, wace yarinya ce wane ne uban ta a garin nan? ai kuwa ko wata baza'a kai ba zayi auren nan."
Mom gaba d'aya farinciki ya lullub'e ta Zaraddin d'an gaban goshin ta da kansa ya ce yana son aure yau, wan da tuntuni Dad ya ce ya fidda mata ya yi aure maganganun mutane sun dame sa a kan halinsa.
ya ce shi bai ga matar aure ba. ya ce
"Mom a cikin gidan nan take kuyi-kuyi magana kawai ku aura min ita,
yanzu nake son a aure min ita,
idan ba'a aura min ita bafa za'a sami matsala."
Shamsuddi ya dube sa yana fad'in
"Yanzu kai Daddy na kwance ba lafiya kake maganar kana son aure yanzu-yanzu da wurwuri,
ta ya za'ayi aure a gidan nan yanzu Daddy yana kwance ba yi da lafiya,
ka daiyi tunani ka bari idan ya sami sauki koma meye sai ayi."
Zaraddin ya harare sa ya na cewa
"Sai me ciwon nasa zai hana a d'aura aure ne, abun da za'a tara mutane kawai a shaida shine me."
Shamsuddin ya girgiza kai tare da fad'in
"Allah ya baka sa'a."
Mom ta ce
"Uhum yanzu kayi magana dan wani ba lafiya in dai ba ango ko amaryar bace ai ba wani abin tashin hankali bane,
bari Dad d'in ku ya shigo muyi maganar, a saida rana karshen wata ayi biki,
wace ce cikin su Bilkisu Saddiqa Nabila Sumayya Miemie ko Ameerah?."
Zaraddin ya ce
"Ina duk ba su ba wancan kyakkyawar Feeryal dai."
wani irin d'agowa Shamsuddin ya yi.
Mom ko korji ta dafe a tare suka furta
"FEERYAL!."
Zaraddin ya ce
"Eh ita ita nake so idan ba ita ba babu wata macen da zan aura, kawai a bani ita idan ba haka ba."
ya wani girgiza kai.
da karfi Shamsuddin ya mike ya nuna shi da yatsa ya ce
"Karya kake Feeryal bata dace da kai ba."
Zaraddin ya mike yana cewa
"Idan bata dace dani ba da wa ta dace, ita nake so kuma sai na aure ta."
"Dani ta dace ba da kai d'an kwaya ba, Feeryal tawa ce."
da karfi Zaraddin ya shako wuyan Shamsuddin ya ce
"Idan ban kashe kaba na nuna maka halin kwaya anan,
idan ka sake cewa Feeryal taka ce idan ban bubburma maka wuka ba."
Shamsuddin shima ya cukime shi yana fad'in
"Mu burmawa juna wuka dai, duk iskancin ka ka isa kayi min na kyale ka ne,
na fad'a baza a aura maka ita ba,
kayi abin da zakayi."
da sauri Mom ta shiga turesu tana fad'in
"Bakuda hankali ne yanzu akan mace kuke fad'a, macen ma aljanar ruwa,
to duk cikin ku babu shegen da ya isa ya aure ta,
baku isa ku auro min wancan bakar mayyyar aljanar ba."
Shamsuddin ya sake shi ya juya da sauri ya nufi kichin yana fad'in
"Zakaga abunda zan yi a kan ta kuwa."
Mom ta sa hanu a kai ta yi kiruru tana fad'in
"Wayyo Allah tambad'ad'd'iyar yarinyar can ta had'a min yara fad'a zasu kashe kansu."
Zaraddin ya fito da wuka ya yi kan
Shamsuddin.
Dad da shigowar sa ke nan ya buga masa sawa.
"Zaraddin! kar ka soma."
da sauri Mom ta shiga sakanin su hannun ta akai bata fasa kururuwa ba.
da d'ebewa Feeryal albarka ba.
Zaraddin ya saki wukan kasa yana huci ya ce
"Wallahi da na nuna maka halin kwaya Feeryal kuma ni zan aureta ba kai ba."
Dad yakuma buga musu tsaya
"Banzaye shashshun yara, yan zu akan mace kuka shirin kashe kanku,
ina ta son ganin rayuwar ku yaci gaba ina son ganin komai ya juya ya dawo karkashin mu,
amma kun tsaya shashanci, barsu su kashe kansu."
Zaraddin ya juya fuu ya yi waje yana huci.
Miemie dake tsaye bakin kofa rike da kula Ammah ta aiko ta ta kawo wa Mom ta tsaya tana kallon ikom Allah.
ai tana bata kular ta juya.
in da tabar Ammah da Faisal nan ta same su, ta karaso baki na kaikayi na son bada labari.
ta zauna tana rike hab'a da fad'in.
"Cafd'i jam da yau anyi kisa agidan nan."
Ammah ta waro ido ta ce
"Kisa kuma?."
Faisal ya ce
"Ji wannan makaryaciyan ai ke narantse Miemie kin shiga uku da baki."
ya yi maganar yana kai mata bugu a baki, ta kauce tana fad'in
"Wallahi da gaske ne Ya Zaraddin da Ya Shamsuddin suke fad'a,
Ya Zaraddin har da d'aukan wuka wai zai kashe Ya Shamsuddin, wai kuma kasan akan wa suke fad'an? akan Feeryal jifa wai duk suna sonta."
Ammah ta ce
"Ikon Allah lallai yarannan basu da hankali shine har da d'aukan wuka."
Faisal ya yi shiru kamar ruwa yaci kansa.
Miemie ta kalleshi ganin yadda jikin sa ya yi sanyi ta ce
"Ai kaima Ya Faisal tuntuni na gama gano ka kaima sonta kake,
Feeryal dukkanin ku baku da ce da ita ba."
hararar ta ya yi ya ce
"Ke ina ruwan so da wani dacewa ko rashin sa,
da Ammah zataje ta sami Aunty nasan da za'a bani ita."
"Babu in da zani ma duk kuje ku nimi matanku a wani wajen."
cewar Ammah.
Miemie ta fashe da dariyar ganin yadda ya wani narke murya kamar maraya.
ya bita da hanu ta mike da gudu ta shige d'aki tana dariya.



Da sauri Umma Karima ta shigo sashin Daddy, lokacin ana daf da kiran sallar magriba.
tasan yanzu kowa ya koma sashin sa, Ajmaal da yake kwana tare da shi ma yanzu ya fita shirin zuwa masallaci.
Daddy na kwance kan sallaya yana zaman jiran a shiga sallah ya mike ya gabatar.
ta shigo ta hakimce kan kujera ta ce
"Tashi Alhaji muyi magana."
nan da nan ya aiwatar da abun da ta ce
ya mike ya zauna.
zama ta gyara tana kallon shi sannan ta ce
"Ina takaddun kadarorin ka suke ina so ka tattaro su duka ka bani, yanzun nan."
ya ce "To Hajiya Karima amma basa d'akin nan, ni da Abdurrahim ne kad'ai muka san in da suke, gashi ni bani da lafiyan da zan iya zuwa na d'auko miki."
ta ce "Kira shi Abdurrahim d'in yanzu kace ya taho da su."
ta d'auko wayarsa ta mika masa bayan ta danna kira wa lambar Abdurrahim.
ya yi ta ringing har ya yanke ba'a d'aga ba.
takuma mai da kiran a karo na biyar shima har yakusa yankewa kafin aka d'aga.
da sauri ta saka wayar a amsa kuwa ta mika masa.
daga cikin wayar aka ce
"Ayi hakuri ranka shidad'e Sir yana Operating room yana surgery."
karb'ar wayar tayi ta kashe sannan ta ce
"Yana dawowa kasashi ya kawo maka a daren nan, zan zo na karb'e su da safe."
ya ce To.
ta mike ta fita.

Bayan sallar isha Aunty Ammah Mommy Mom Hajiya, da 'ya'yan su.
duk suna cikin parlour'n Daddy,
in da Abdurrahim da Abbie da Dad suke ciki tare da Daddy dan yau jikin nasa ya tashi fiye dana kullum.
Aunty dake zaune tayi jugum, sai addu'a take cikin ranta.
gaba d'aya hankalin ta baya jikin ta yana gurin Daddy, sai kwalla take ta sharewa a b'oye.
Aunty ta nisa ta ce
"Hajiya nace ko za'a kai Daddy gurin magani ne a d'an tab'a na gida, a had'a jinya biyu ko Allah zai sa aci karfin lamarin."
"Ba ke zaki bada wannan shawarar ba mu zamu yanke."
cewar Umma Karima da ke shigowa parlour'n maganar Aunty ya dira a kunnenta.
ta karaso ciki tana cigaba da fad'in
"Mu masu 'ya'ya da mukasan zafin sa mu zamu yanke hakan, bake da bakisan zafin sa ba,
sabo da kin raina kulawar da Abdurrahim yake bashi, likitan da likitotin kasar waje suka yadda da aikin sa fiye da nasu, yake jinyar sa shine zaki kushe kokarin sa,
to mu masu 'ya'ya mun yadda da aikin sa bamu yarda akai shi wani guri ba,
ke da baki haifi ko d'an hanji da shi ba baki isa ki rika nuna mana yadda zamuyi ba."
Aunty ta girgiza kai tana murmushin takaici ta ce
"Idan ma tunanin ki hakan nake nufi Abdurrahim yakasa kula da shi, to kicigaba da sawa ranki hakan,
sannan baki da ikon hanani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login