Showing 3001 words to 6000 words out of 63585 words

Chapter 2 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt

Shamsuddin shi dai kamar nashi da sauki,
lallai kunji jiki kunji ta maza."
ganin hararar da suke mata tamike ta gudu tayi waje.
ko da taje sashin Mommy bata sami Ajmal ba, Ameerah ta ce mata yafita a mota.


Satin Feeryal guda bata fita ko nan da can kullum Miemie na hanyar zuwa dubata.
suna zaune a d'akin Feeryal suna hira Miemie ta ce
"Uhm bari natashi naje Ammah ta ce naje nakira Ya
Faisal,
takira wayansa bai d'agaba yazo yashafa maganinsa."
Feeryal ta ce "Ya Faisal d'in bashida lafiya ne?."
dariya Miemie tafashe dashi ta ce
"Ai bashi kad'aiba harda Ya Ajmal Ya Zaraddin da Ya Shamsuddin,
ammafa sun warke kawai Ammah ce wai sai an yi ta binshi yazo ya shafa magani,
kaman wani karamin yaro,
targad'e yayi a hannu."
Feeryal tawani waro ido ta ce
"kai Miemie kefa muguwa ce shine kike dariya Accident sukayine?."
Miemie takuma kwashewa da dariya ta ce "Karo sukayi da Aljani."

Feeryal takuma ware ido tana fad'in
"Aljani kuma a'ina suka sami aljani kuma?."
Miemie ta ce
"Ke dalla duk kin wani tsorata aljanin kanki mana."
ta ce "Ni kuma!."
Feeryal ta fad'a tana buga kirji.
Miemie ta ce
"Sati guda kenan da sukayi karo da aljanun kanki dukkansu sai da sukaji ajikinsu."
nan da nan Feeryal tashiga wani yanayi tana fadin
"Aljani kuma ni d'in harkuma sukaji rauni?
ina na fitama Miemie nida banida lafiya,
ina kwance kemafa kinsani,
ko ke ma kin yadda ni aljanar ce."
nan da nan idanunta ya kawo kwalla.
Miemie ta ce
"Ke dalla karki d'aga hankalinki na tunasune abin ya bani dariya."
Feeryal ta ce
"Dan Allah kibasu haquri ni bansani ba."
ganin kamar hankalin Feeryal d'in ya tashi ta ce
"Ke dalla wasa nake miki, bashida lafiya ne kawai."
Miemie hartafita tana dariyar mugunta.

Washegari

Feeryal tafita taje sashin Ammah dan taji sauki
sosai.
bata sami Miemie ba sai Ammah ita kad'ai,
Ammah take Fad'a mata Miemie tana sashin Hajiya.
Feeryal ta fita.
harzata koma sashinsu sai tajuya tanason ganin Miemie.
a hankali nufi sashin Hajiya tashige ciki tana waige-waige dan tasan sashi Hajiya akwai mage.
ahankali take takowa har ta iso bakin kofar falo,
d'an tsayuwa tayi.
tuno da kashedin Hajiya akan karta kuskura tashigo sashinta.
d'an jim tayi da tunanin ko ta koma ne,
sai kuma ta dan leko kanta, tana fatan ta hango Miemie ta kirata da hanu.
karaf suka hada ido da hajiya.

Hajiya ta saki tana fad'in
"Au har nan kika biyo shi, kinzo ki karasa shiga jikin nasa ke nan?
jikan nawa kika biyomin jika kina lekensa ki samu ki karasa shiga jikin sa,
shigo munafuka zo nan aljanar banza."
Hajiya ta yafato ta da hannu.
Abdurrahim yana zaune idonsa yana kan wayar dake hannunsa yana dannawa.
gefen sa abokin sa ne Dr Imran yana cin abinchi.

A hankali ta tako cikin parlour'n jiki a sanyaye,
tazo gaban ta ta tsaya kanta a kasa tana murza 'yan yatsunta.
Imran ya d'ago yana duban wanda Hajiya take wa fad'a.
da d'an mamaki yake kallonta, yaga kaman yasan yarinyar da Hajiyan take wa fad'a.
Hajiya ta zazzare mata ido
"Na ce kin biyoshi harnan kikarasa shiga jikinsa ne,
munafuka bance kada ki kuskura ki tako min cikin sashi ba,
kuma nayi miki kashedi kan jikoki na, bance kads ki shiga tsafgar wani daga cikin su ba,
shine kika biyo shi dan ki karasa shiga jikin sa ko."
kai ta girgiza da sauri idanunta suka kawo kwalla,
muryarta na rawa ta ce
"Gurin Miemie na zo."
ta ce
"Fita ki bani guri munafukar baza aljana kawai."
ai da gudu
Feeryal ta fita,
bata tsaya ba sai da ta fice daga sashin nata gaba d'aya.
Miemie ta b'ata rai taji haushin abin da Hajiya ta mata, sai dai bata da bakin magana yanzu duba da wanda yake gurin.
har ta fice Abdurrahim bai d'ago ba idanunsa yana kan waya.

Tana fita Imran ya aje jokali da sauri ya dubi Hajiya ya ce
"Hajiya da gaske aljana ce wannan?."
Hajiya ta nimi guri tazauna tana cewa
"kwarai kuwa Imrana yarinyar nan Aljanace na gaske,
kar kaga abin da ta mana a lokacin auren Farida, da manyan zakuna ta zo ta wargaza taron jama'a, in ba aljana ba ta ya za'ayi ta d'auko zakuna tana yawo da su."

Imran ya gwalalo ido cike da tsoro ya ce
"Innalillahi amma Hajiya karfa ta fita ta dawo mana da damisai, A.A ana magana kana shiru,
yarinyar da kayi jinyarta a Abuja ce fa,
wai ma ya akayi tazo gidan nan, dama wancan karon naga Daddy a asibitin da ma tana da dangi da gidan nan ne?."
Hajiya ta ce
"Dangi da wa? tsintacciyar tsintarta Fatima tayi a cikin ruwa, d'iyar aljanu ce fa,
kai tunda kake katab'a ganin kyakkyawa irin ta ai sai aljanun ruwan."
Imran ya kama baki yana saurarar Hajiya.

Abdurrahim yaja gajeren tsaki ya mike yanufi kofa.
Imran ya biyo bayan sa,
Hajiya tana fad'in
"Kai abokin turawa ina zaka je, ka tsaya naje na duba kar ta tsaya a hanya tayi maka wani abin,
kai Imrana kasashi kuyi addu'a wasayyawu ya tsaya a kanta."
Imran ya ce
"To Hajiya A.A ka tsaya kadai ji abin da Hajiya ta fad'a."
ganin ba tsaya wa zaiyi ba ya biyo sa da sauri.

Feeryal da Miemie suna tsaye a d'an gaban sashin Hajiya.
Miemie nata bata hakuri sai share hawaue take.
Feeryal na d'agowa sukayi ido biyu da Imran.
da sauri ta ce
"Miemie mu tafi."
Imran kuwa suna had'a ido da sauri ya makale bayan Abdurrahim cikin yin kasa da murya ya ce
"A.A gata nan fa mu canza hanya."
Abdurrahim baiyi magana ba yaci gaba da tafiyar sa.
sai da suka zo daf da su sannan yaja ya tsaya,
ya d'an dubeta a dakile ya ce
"Wai ke aljana ko......!


Mommy Twins ce



Da sauri ta d'ago idanunsu ya sarkafu da juna,
cikin hanzari ta janye idanun ta, ya yin da
taji wani irin mummunar fad'uwar gaba.
kwarjinin sa ya mata mugun girma ta iya jona idanun ta cikin nasa.
a hankali tayi kasa da kanta jikin ta,
a matukar sanyaye.
tsintar kanta tayi da jan d'an gajeren tsaki a kan lab'b'anta, wan da batayi sammanin fitowarsa ba.
ta gyad'a masa kai ta ce
"Eh."
har lau kanta a sunkuye.
kai ya jinjina idanunsa a kanta.
sai kuma ya soma tafiya batare da ya kuma cewa komai ba.
Miemie tayi saurin janyo hannunta suka nufi sashin Aunty.
da sauri Imran da yagama tsorata ya biyo sa.
ya sha gaban sa murya a marairaice ya ce
"A.A kasan me kayi kuwa? dan Allah dan annabi ka rufa mana asiri, dan nasan idan ta tashi ba iya kanka zata tsaya ba, har da ni da ta ganmu tare,
meyasa kayi mata irin wannan tambayar,
haba A.A,
meye na tambayar ta ita aljana ce,
kagafa ranta ya b'aci;
wlh babu ruwana ni zanje na bata hakuri tun kafin ranta ya dad'a b'aci."
"Kai dalla ka dame ni bani hanya na wuce."
"Wai kai A.A kayi abu ma bakasan kayi ba, wani iri ne kai da baka da tsoro ne haka,
to wlh ni kam babu ruwana bazaka jamin fitina ba ina zaman zama ta."
ko oho ya yi masa har suka shige side d'in sa.
Imran kuwa gaba d'aya ya rud'e bai fasa masa
magana ba.


Sai da su Feeryal suka shige sashin Aunty kafin
Miemie ta tsayar da ita a farfajiyar side d'in.
Miemie ta wawwaro ido ta ce
"Feeryal me yasa zaki ce masa haka ki amsa masa ke aljana ce,
kinsan waye shi a gidan nan kuwa?
dan Allah ki rufa mana asiri, tsaki fa kika yi masa kin san kuwa Ya Abdurrahim baya son tsaki."
"Ya zanyi Miemie shike nan tun da Allah ya halicceni haka laifina ne,
idan ban amsa masa cewa ni d'in aljanar bace me kike so na ce masa,
bayan kowa da hakan yake kira na,
mayyar aljana annoba."
hawaye suka fara zuba a idon ta, ta rike hannun Miemie gam cikin muryar da kuka ke son kwace mata ta ce
"Miemie duk wanda ya kuma tambaya ta ni aljana ce haka zan amsa masa,
illa iyaka ina suce na bar musu gidan su."
Miemie ta ce
"Feeryal kinyi ganganci masa tsaki kuma yaji fa."
"Nasan yaji ai ni ma haushi tambayar tasa ta bani."
Miemie tasa hanu a kai ta ce
"Nashiga uku bansan ya zan yi ba yau dole zamuje ki bashi hakuri, Feeryal ni ina son jiki na bana son abinda zai tab'a min lafiyar jiki,
Feeryal yaushe kika iya maida magana haka?
ina zuwa."
ta fad'a da sauri ta juya ta fita.

Feeryal ko mai da hawayen idanun tayi,
taja kafa ta shige ciki.
Aunty na ganin yanayin ta ta ruko hannunta tana tambayar ta me ke faruwa.
raurau tayi da idanun sai kuma ta cuno baki gaba ta ce
"Ba wani ne ya tambayene wai ni aljana ce ko."
tayi kwafa
"Ai na rantse idan ya sake ce min bazan kyale shi ba."
Aunty ta kura mata ido ta ce
"Wani waye a ina kika ganshi?."
"Daga sashin Hajiya ya fito Miemie ta ce min wai shima yayan su ne."
Aunty ta buga kirji ta ce
"Ba dai Abdurrahim ba kirufamin asiri Feeryal
kira bani da Hajiya,
daki tab'ashi gara ki tab'a kowa a gidanan nan,
dan wallahi akansa Hajiya bata kyale kowaba babu ruwanki dashi."
Feeryal tawuce d'aki tana shagwab'e fuska.
babu wanda yatab'a tareta haka gaba da gaba yana yimata irin tambayar da ya yi mata.

Tana shiga ta saki murmushi ganin wad'anda suke cikin dakin.
ta ce "Lah chuchu chulu yaushe kukazo"
sukace mata tund'azu muke jiranki.
ta ce
"Dana sani da tundazu nadawo gurin Miemie naje."
sukace kinason mudaumiki mataki akanshi ne?.
kai ta gyad'a ta ce
"Eh amma fa karkuyi Ammie'nah ta sani dan ta ce babu ruwa na da shi."
sukace to.
zama tayi suka soma hira sosai daga bisani,
ta ce zatayi wanka.
tashige bayi sukuma suka tafi.
bayan tagama wanka tafito ta gansu a tsaye kowannesu rike da hannunsa.
murmushi tayi musu ta ce
"Kunje kun same shi?."
sukace mata
"Eh kai ina wannan fa bazai tab'uba,
munkasa iya masa komai,
sai dai mubaki wani abu ke kimasa da kanki,
mun mun kasa iya matsowa kusa da shi bare har mu tab'a shi."
Chuchu tasa hannunta abaya taciro wani abu ta mika mata ta ce
"Kisan yadda za'ayi yataba jikinsa."

Feeryal taware ido ta ce
"Zan iya kuwa abarshi kawai."
sukace zaki iya mana jikinshi kawai zai tab'a shikenan kin rama abunda yayi miki.
takarba tabude drower tasaka tadawo suka cigaba da hirar su.


Da sauri Umma Karima ta nufi sashin Mommy.
ta jata suka shige can kuryar d'aki.
Mommy ta dube ta tana zama bakin gado ta ce
"Allah dai yasa lafiya Hajiya Karima, irin wannan shigowa a bujajan haka."
"Inako lafiya Hajiya Halima, kwana uku boka Mali ya bani zai turo bakin aljani ya gama da waccan matsiyaciyar juyar,
kusan kwana goma ke nan nake zuba ido naji shiru,
ba na fad'a miki yadda mukayi da shi ba."
Mommy ta ce
"To ni ma dai har yanzu ban ga alamun hauka a jikin ta ba,
to ko watakila bai gama aikin bane,
amma kinsan maganar boka Mali baya fad'u kasa."
Umma Karima ta ce
"To ai nima shine na gani watakila bai gama aikin bane dan ya ce min aikin yana da wuya, sai anyiwa aljanin shiri,
kai nifa kinsan bana son jira da yawa, nafi son komai cikin gaggawa;
yau zan koma gurinsa kawai, naje naji mekefaruwa, in kina da aike ki kawo."
Mommy ta ce
"Ai kuwa ina da sako, batun auren yaron nan Abdurrahim da Kuraiba,
jiya na tsare shi da batun tun da ya dawo ayi-ayi-ayi auren nan,
mahaifiyar yarinyar nan kusan kullum sai ta kira ni,
'yar nan bata tab'a ganin sa ba sai a hoto amma ta ce taji ta gani sai shi,
Hajiya Luba ta ce kullum sai ta taso ta gaba itafa shi take so a aura mata shi kawai har kuka take a kansa;
amma yaron nan nayi ta binsa yaje gidan su yaki kin san sa da masifaffen taurin kai,
ki fad'awa boka Mali ya karkatar da hankalinsa yaje su dai-dai ta ayi auren nan."


Umma Karima taji wani dum a kirjinta amma sai ta waske ta yab'o murmushin yake a fuskarta ta ce
"Ai kuwa in banda Abdurrahim me yake jira da bazai yi aure ba, to amma fa kinsan sai kin kawo kafin alkalami kafin a fara aiki."
"Ah ai dama dole bari na baki wani abu ki bashi."
ta mike taja drower ta d'au dubu d'ari biyar ta mika mata ta ce
"A kai masa wannan idan ya ce da kari ba matsala za'a kara masa."
Umma Karima ta karb'a ta mike tana fad'in
"To bari naje duk yadda ake ciki zakiji."
ta fice ta koma sashinta ta shirya ta garzaya dajin boka Mali.

Umma Karima na zube a gaban boka
bayan ta gama sanar masa da rashin nasarar su,
har yanzu dai Hajiya Fatima na nan daram babu abin da ya same ta.
tana zaune ta kasa kunne tana jin jawaban boka Mali cikin b'acin rai yake fad'in
"Mun tura bakin aljani sai dai anyi rashin sa'a,
basuyi ido da ido da ita ba;
alamu na nuna mana wani ya haukace a madadin ta,
sai dai abin bakinciki tun ranar nake zuba idon ganin bakin aljani da kyakkyawan labari,
amma har yau bai waiwayo ni ba,
wannan yarinyar da take rukonta hatsabibiya ce nayi tason ganin ta cikin duban tsafi na kasa,
wannan yarinyar tana da had'ari dole sai ta kauce a gareta kafin a sami biyan bukata."
ta ce
"Boka babu yadda za'ayi a kawar da yarinyar ita?."
ya ce "Ke zakiyi hakan idan kikayi mukuma zamu karasa sauran aikin,
dan bama iya ganin ta a cikin duban tsafin mu."
Umma Karima ta jinjina kai da tunani iri-iri a ranta.



Umma Karima ce zaune a d'akinta ita da kanwarta Siyama,
washegarin da ta je gurin boka Mali.
ta sa Siyama tayi wanka ta shirya cikin wasu,
d'amammun kaya wanda ya bayyana surar jikinta gaba d'aya.
ta mikawa Siyama wani kwalli a cikin d'an tandu da kwalbar turare wanda boka Mali yabasu ta ce
"Saka wannan kwallin a idon ki, ki shafa turaren a fuskarki, kud'in aikin da ta bayar ayiwa d'an ta a kan wata shi na bada ayi a kanki zuwa kan d'anta,
Hajiya Halima ke nan har yanzu da sauran ki kar nake ganin ki,
kin haifi 'ya'ya maza, a yau Alhaji ya fad'i ya mutu kin mallake gidan,
tun da nayi-nayi ban samo d'a na miji ba,
to ki sani akan d'anki zan samo d'a na miji, daga nan kuma zance ya kare."
Siyama ta karb'i kwalbar turaren tana dariya ta shafa.
tana fad'in
"Sai dake Aunty na."
Umma Karima ta ce
"Yauwa to yanzu komai yayi dai-dai Abdurrahim yana ido biyu dake,
shikenan burinmu yacika yanzu iwar haka yananan a sashin Hajiya Halima;
jeki can in baki sameshiba ki garzaya sashinsa basaina gayamikiba ko me zakiyi kinsa meyakamata kiyi,
d'an ta zai shigo hannun mu reshe zai juya da mujiya."


Siyama tashige sashin mummy da sallama tana wani kararraya tazauna akan kujera inda ta taddasu Ameerah da Sumayya tagaida,
mummy data fito daga bedroom d'in ta.
Sumayya ta bita da kallo tana fad'in
"Irin wannan kwalliya haka Aunty Siyama, ina zuwa haka?."
"Kai Sumayya sai kace bana kwalli, babu inda zani."
Sumayya ta yi dariya ta ce
"Ai kwalliyar tayi kama da ta zuwa party ce."
Ameerah ta kallete ta da wutsiyar ido,
ta yamutsa fuska ta cigaba da dannan wayarta.
Siyama ta ce
"Wai Ameerah ba magana ne?."
Ameerah ta d'an d'ago ta ce
"Sorry hankali na na wani wajen."
Siyama tayi shiru da bakin ta dan ta san halin Ameerah sarai bata kyale kowa ba.
ta gyara zaman ta
tana d'an satan kallon gun bata dai ganshiba.
zuwa can ta mike ta fita.

Tana sako kanta zata fice daga parlour Mommy sukayi kicub'us da shi yana kokarin shigowa.
ta wani sake jiki tana wani yauki, ta narke murya
"Barka da warhaka yallab'oi, ina yini."
"Lafiya."
ya amsa a takaice
ko in da take bai kallaba ya rab'a gefen ta ya shige cikin parlour.
wani irin lumshe idanu tayi tare da jan numfashi ta na shakar daddad'an kamshin sa.
da sauri ta bud'e idanunta, ta taune baki tana dana sanin da ta fito da ta cigaba da zama har ya shigo.
da sauri ta juyo ta koma ciki a zaune ta ganshi gefen Mommy.
ta zo ta gaban shi ta wuce tans kad'a mazaunan ta,
ta zauna kusa da Sumayya kujeran da ke fuskantar sa,
Sumayya ta ce
"Aunty Siyama baki tafi ba ashe."
ta d'an saci kallon in da yake fatanta ya d'ago su had'a ido,
shiko baima san tana yi ba idonsa akan waya.
ta ce
"Am Sumayya dama aron wayarki zaki bani nakira tawa bansan ina na jefa ta."
Ameerah ta kalleta tana mara baki ta lura da satar kallon da take wa yayan nasu.
"Yar wahala."
ta fad'a a kasan ranta.

Sumayya ta ce
"Ina ma wayar tawa take."
ta waiga gefe da gefen ta
"Yauwa ga shi can."
ta nuna kujerar da Abdurrahim ke zaune gefen sa wayar take,
shigowar sa Sumayya ta tashi a kujerar ta bashi gurin zama kusa da Mommy.
Sumayya na kokarin mikewa ta d'auko mata, tarigata mikewa.
ta isa gurin ta kai hannu kamar zata d'au ka sai ta tura wayar ya da d'a matswa jikin sa.
ta saka hanu ta gogi jikin sa.
da sauri ya d'ago suka had'a ido, tawani narke murya
"Oh yihakuri waya zan d'auka."
gajeren tsaki yaja ya maida idanunsa kan waya.
da sauri ta juya cike da farincin burin ta ya cika, tad'an lallasa wayar kana ta mikawa Sumayyar wayarta ta ce
"Naji muryar Nabila wayar tana hannunta."
ta juya da sauri ta fita cike da farin ciki.

Tana komawa sashin su ta rungume Umma Karima tana fad'in
"Aunty Karima ya ganni na ganshi."
Umma Karima tayi makirin dariya ta ce
"An gama 'yar gari, kwantar da hankalin ki kin sami Abdurrahim a tafin hannunki."
suka wani kwashe da dariya suka tafa.


Mommy ta dubi Abdurrahim da tun shigowar sa daya gaisheta bai kuma magana ba, sai aikin danna wayarsa ya ke.
ta ce
"Kaje kun gaisa da Kuraiba'n kuwa?."
"Mommy abani breakfast."
ido ta bisa da shi sarai tasan so yake ya kawar da maganar nata.
ta ce "Ameerah je kice Shatu ta had'o masa breakfast."
"No ki barshi."
yafad'a tare da mike wa tsaye.
Mommy ta ce
"Ai nasan dama ba ci zakayi ba shiyasa ma ban sa an kaimaka ba,
ina tayi maka magar yarinyar nan baka cewa komai."
"Banje ba."
ya fad'a a takaice
Mommy ta ce
"Amma ai yakamata ace kaje, ko da sau d'aya ne ku gana, kafin akai sadaki."
ya zura takalman sa baiyi magana ba yafice.

Sashin Aunty ya nufa dan yasan can ne kawai zai sami abincin da zaici cikin kwanciyar hankali.
da sallama ya shigo Aunty na kokarin shiga kichin.
ta dakata ya karaso suka gaisa,
yanayin sa ya tabbatar mata da abinda ya kawo shi,
dan tasan gadon Daddy ne ajikin sa,
shima baya cin abincin masu aiki.
Aunty tayi murmushi ta ce
"Abdurrahim ka isa dinnin bari na kawo maka breakfast."
ta wuce kichin shi kuma ya kara dinnin ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in.
ta had'o masa breakfast mai rai da lafiya ta kawo masa.
kana ta koma kichin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login