Showing 9001 words to 12000 words out of 63585 words
Chapter 4 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
suka bi motar da ido, su Nabila kirjinsu na dukan uku-uku Ameerah tayi karya ta janyo musu.
ya yi shiru idanunsa akan laptop yana tuka maganar cikin ransa.
Kasancewar motar Ammah ce direban ya yi kokarin wucewa sashin ta da su.
da sauri Miemie data hango su Sahla durkushe a gaban yayan nasu ta ce
"Tsaya-tsaya mu sauka anan sai ka wuce,
Feeryal sauko muje ga su Ameerah can gurin Ya Abdurrahim."
suka sauko jiki a sanyaye kar Feeryal uwar 'yan tsoro taji labari.
a hankali suka karaso suka sunkuya kamar yadda su Ameerah sukayi.
a fusace ya d'ago ya ce
"Miemie har kinyi girman da zakibi samari a mota!."
ido ta waro murya na rawa ta ce
"Wlh Ya Abdurrahim babu wanda muka bi direban Ammah ne ya kaimu kuma shi ya dawo da mu."
da sauri Ameerah ta ce
"Bayan muna ganin ku da su har wani ya yi wa Feeryal kiss, daga nan kuma kuka bisu kuka tafi."
da sauri ya kuma d'ago kansa karaf suka had'a ido da Feeryal da tsoro ke kukarin tafiya da numfashin ta.
maganar Ameerah ce ya sashi mai da dubansa gareta
"Na rantse ya mata kiss a gaban jama'a ma kuwa, ai gasu nan."
ta mika masa wayar ta,
hoton Feeryal karara wani yana mata kiss, ga d'ayan fuskarsu daf da juna har suna gogar fuskar juna.
Miemie ta marairaice murya ta ce
"Kai Ameerah kiji tsoron Allah a'ina akayi hakan."
a fusace yad'a go wayar ya nuno musu fuskar wayar.
Feeryal tayi wani irin zabura, jiki na kyarma.........!
Mommyn Twins ce
Wani irin sarawa kanta ya yi da sai da ta kai hannu ta dafe kan, tana girgiza kan cike da matukar tsoro.
hanjin cikin Miemie ya kad'a.
cikin fusatacciyar murya ya nuna Feeryal da hanu ya ce
"Ke tashi kibar nan!."
ya fad'a cikin tsawar da sai da ta zabura ta zube kasa kana ta mike da gudu ta yi hanyar sashin Aunty.
b'acin rai karara ake hangowa kan fuskarsa, ya mike a zafafe tare da d'aukar belt dake ajiye a gefensa.
yashiga nad'e shi a hannunsa yana fad'in
"Wato kun zama 'yan'iska kamar ku d'in nan har kun iya biyewa sa maruka, yaushe ne aka haifeku!."
Ameerah ya damko yana cewa
"Wato ke har kin iya d'aukar hoto ana bad'a la, ga kinan 'yar iska ko."
yashiga shinfid'a mata belt tana ihu sai da ya mata taya-taya kafin ya sake ta, ya bita da naushi,
tana tsalle tana sosa in da aka zuzzuba mata bulala.
su Sahla kam tuni suka fashe da kuka tun kafin a zo kansu.
ya cafko Nabila itama ya birkita ta da duka, yana sakin ta ta zube kasa tana kuka.
haka Sahla ma.
Miemie ce dukan karshe yadda taga yake huci yana dad'a kyara rukon betl d'in tasan yau kam zataci uban ta,
ai kuwa dukanta yafi na kowa, sai da ya mata bulala ashirin da biyar kafin ya kyaleta.
sannan ya nuna su ya ce
"Daga yau wata ta sake sa kafa ta fita a gidan nan ta gani, ku tashi ku bani guri a nan!."
da gudu ko wannen su ya yi hanyar sashinsu.
Ganin yadda Feeryal tashigo a firgice Aunty da tun d'azu hankalinta yake tashe ganin karfe goma yayi basu dawoba.
har 11 tarinka kiran wayar Feeryal d'in saijin ringing d'in sa a d'akinta tayi.
wayar Miemie kuwa yana shiga ba'a dagawa.
tajawota dasauri tana dad'in
"Ke Feeryal lafiya meyasa baku dawo akan lokaci ba sai yanzu, meyasa kuka zauna meyafaru naganki Hak?."
Aunty tana maganan cikin tashin hankali.
Feeryal ta kankameta tana kuka bata b'oyemata komai ba tafad'a mata duk abin da ya faru.
Aunty taja Numfashi cike da fargaba tace
"Yanzu ina su Miemien suke, suna gurin yayansu kenan?."
Feeryal tace Eh.
Aunty tatsaya shiru kana taja hannunta suka shiga d'aki.
Tana fad'in
"Shiyasa tunfarko banso tafiyan nan nakuba,
samari 'yan bana d'ayan nan basu da tabbas,
shiyasa kullum magana ta baiwuce ki kula ba,
Feeryal Allah ya yi miki baiwar zubin halittar da ba kasake za'a barki ki rika yawo ba,
fitar nan sam bana son shi sai ya zama dole."
Aunty ta rika fad'a Feeryal da har lokacin tsoro bai gama sake ta ba,
sai sharar kwalla take.
sai kuma Aunty ta shiga rarrashin ta,
kana ta taimaka mata ta cire kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka tafito.
tagabarta da sallahn isha tasa kayan bacci ta haye gado takwanta,
tare da sunkulewa guri guda tana rarraba ido cikin tsoro.
har lokacin Aunty nacikin d'a kin tasata tayi addu'ar bacci kafinnan tafita .
Takai zamani guda batayi bacci ba tana sake-sake a ranta sai chan bacci barawo ya sami damar yin awon gaba da ita.
Nabila ta shige sashin su a guje tana mussuke jikin ta inda ta sha bulalu.
Umma Karima ta zabura da sauri tana fad'in
"Ke lafiya yaya haka?."
Nabila ta zube gefen ta tana cewa
"Ya Abdurrahim ne ya bige mu."
"Duka kuma a laifin me?."
Umma Karima tayi tambayar tana yamutsa fuska.
Nabila ta gyara zama ta shiga fesa mata labarin abin da ya faru karya da gaskiya.
Umma Karima ta ware ido tare da buga kirji ta ce
"Ita da laifi ku da duka! jar'uba har ta iya tsotsar bakin namiji a cikin bainin nasi,
baiyi kasa-kasa da ita ya farfasawa shegiya baki, muga bakin da zata tsotsi bakin wani namijin da shi ba,
ai wannan yarinyar tajima tana iskanci tun tana kankanuwar, tafiyarta Abujan da taje ma iskanci take acan ai munsan komai,
gashinan asirinta na kan tonuwa kad'an ma ke nan, in Allah ya yarda asirinta yarika tonuwa ke nan,
sai tabar gidan nan,
ai abin da yasa Abdurrahim ya koreta ba zai iya yiwa kazanta hukunci ba,
ai sai dai ku tsaftatattun kannen sa,
ta ya zaiyi yayiwa 'yar'iska hukunci, hukuncin ta ke nan kora gidan ma gaba d'aya zata bari,
yanzu kam alkadarin ki Fatima ya karye daga zaran Abdurrahim ya ce ta bar gidan nan dole zata bari,
hahahaha."
ta karasa maganar da shekewa da dariya tana tafa cinya.
Washegari kuwa Umma karima har da kiran Ameerah ta zo ta nuna mata hoton.
Umma Karima ta rike baki ta ware ido kan wayar tana fad'in
"Tabd'i jam lallai yarinyar nan cikakkiyar 'yar'iska ce asirinta yarika tonuwa ke nan."
Sai da rana kafin Miemie tashigo sashin su Feeryal.
a falo ta tadda Aunty da Feeryal d'in zaune,
ta zauna tare da gaida Aunty,
ta amsa tana cewa
"Kunyi rashin hankali Miemie da kukakai goma awajen taron nan,
watakilama shiyasa maza suka bibiyeku,
da kundawo kan lokaci da duk hakan bai faruba,
Allah dai yatsare yasa yayanku baimuku komai ba dai?."
Miemie taja rigarta tagwada wa Aunty shatin bulala Aunty tawaro ido tace
"Subhanallah abin da ake guje muku ke nan Miemie yanzu ina amfanin sa, sam fitar dare ba na d'iya mace bace, Allah shikyauta gaskiya ku rika kiyayewa."
Feeryal kaman zatayi kuka ganin shatin bulala a jikin Miemie.
ta ce "Wayyo sannu Miemie dan Allah kiyi hakuri ."
Miemie tayi kwafa ta ce
"Wallahi bazan kyale Ameerah ba,
ba ita ta iya munafurciba dukda tare aka bige mu."
Aunty ta ce
"Kiyi hakuri kar kice zakuyi fad'a da ita tunda itama anbigeta, ki rabu da ita kawai, ku dai kurika kiyaye abin da zai janyo muku laifi."
Miemie sai kwafa take tana cize lips.
Aunty tayi kitchen tana saka lamarin aranta sam bataji dad'i ba da Abdurrahim bai hadasu da Feeryal ya musu hukunci dukan su ba,
tun da in laifin ne tare sukayi,
ya ware kannensa kenan yamusu hukunci?.
ta girgiza kai kawai tana shigewa kitchen.
"Ke Ameerah kada kiyi gigin cewa zaki yad'a hoton nan a Media dan wlh idan kika kuskura Ya Abdurrahim ya ci karo da shi sunan ki sorry, sai ya yi miki kabarin da ba sallah,
jiya ma ke nan ya yi miki dukan d'aukar hoton bare kuma kin yad'a shi wa duniya,
zai ce dama kin saba yad'a hotunan batsa wlh mukam babu ruwan mu."
cewar Sahla da suke tare da su Ameerah a parlour'n Mommy.
Nabila ta ce
"Gaskiya nima dai ban bada goyon baya ba, kibari Ameerah mu aje hoton nan zai zame mana makami nan gaba, ai shegiya banso Ya Abdurrahim ya barta ta ba, da ya mata shegin duka 'yar iska yanzu kam mun gama da ita babu wanda zai zo gurin ta,
in yazo kuwa sai ya gani."
Sumayya ta rike hab'a ta ce
"Hm wlh Ameerah kibi ahankali ku rabu lafiya da Ya Abdurrahim,
ina dukan da ya miki akan d'aukar hoton ne shine zaki ce zaki yad'ashi wa duniya, idan fa kika kuma shiga hannunsa bazaki ga da kyau ba."
Ameerah ta ja tsaki
"Mttss ai na rantse da Allah yadda aka bige ni sai an bige ta, wulakantaccen duka ma kuwa,
da wayarta zanyi sending hoton wa duniya kowa ma yagani ta yadda kowa zai d'auka ita d'in ce ke tallen kanta wa duniya."
Sumayya ta gorgiza kai ta ce
"Ameerah nadai gaya miki kibi a sannu, idan ta kwab'e miki bazakiga da kyau ba."
Ameerah ta mike tana hararar Sumayya ta wuce d'aki,
cike da shan alwashin sai ta aikata.
Bayan kwana uku da faruwar haka da sauri Miemie ta shigo sashin Auny.
A parlour ta tadda Feeryal ita kad'ai tana zaune tana kallo a TV.
Miemie ta zauna kusa da ita tabuge cinyar
ta tana fad'in
"ke Ibrahim yakirani fa tund'azu,
ya d'agamin hankali shiyasa ma nazo amma tun d'azu ina kwance ne banyi niyyar zuwa gurin ki ba,
tun da ke tsoro ya hanaki fitowa kizo in da nake, matsoraciya kawai,
sai aka ce miki kuma shi Ya Abdurrahim d'in duka yake haka kawai babu dalili,
kuma ma ai dukan da ya min ni nasan har da naki ya had'a dan duka na yafi na kowa tun da tare muke da ke,
tare Ameerah ta kulla mana sharri."
Feeryal ta marairaice fuska batayi magana ba sai narai-narai da ido take suna kokarin kawo kwalla.
Miemie ta ce
"Bari na kirashi dan ya ce yayi ta kiran ki baki d'aga wayan sa, nace kad'an daga aikin ki."
tana kokarin kiranshi Feeryal ta ce
"Ni dai Miemie da kin barshi to mezanmishi."
Miemie ta ce
"Ke dallah wannan had'add'an gayen,
kuma yace zai zo na ce wallahi yazo."
Feeryal taware ido ta ce
"Wallahi babu ruwana Miemie yazo ina baburuwana."
Miemie ta ce
"Ke wlh dad'ina dake tsoro, da har dake aka buga
ranar da ban san ya zakiyi ba nasan har fitsari sai kinyi tsabar tsoro,
ke wallahi Ibrahim dagaske yakeyi ya ce aure yake son yi babu wani bata lokaci,
ya ce yana zuwa yau gobe babansa zaizo."
kafin Feeryal tabata amsa Aunty tafito.
Miemie ta ce
"Yauwa Aunty dama wanine sunansa Ibrahim muka had'u da shi agun bikinan ya ce yana son Feeryal,
abokin yayan Feenat ne ya ce zaizo yau gobe kuma yaturo magabatansa anemamasa izini gurin daddy."
Aunty taware ido ta ce
"Badai shine kuka hadu da shi ya yi mata rashin d'a'ar nan ba?."
Miemie ta ce
"A'a wlh Aunty bashi bane wannan mutumin kirkine kuma yana sonta,
abokin yayan Feenat ne ma har Mom d'in sa ya nuna mata Feeryal."
Aunty tad'anyi shiru sannan ta ce
"Amma dai yafara neman Daddy'n tukunna, in ya amince sai ya zo."
Miemie ta ce
"Ya ce zai turo babansa gobe yau zaizone kawai ya tambaye ta da kansa idan ta ce ya tura sai ya tura."
Aunty tace Allah yakaimu.
Dayamma wajen karfe 4:40 saiga kiran Ibrahim awayan miemie yazo yana bakin gate.
Miemie tazo tasa security suka bud'e masa gate takaishi bakin sashin Aunty.
ita tashiga ta kirawo Feeryal, dakyar Feeryal tafita sai da Aunty ta ce mata taje tadawo karta dad'e.
tafito da babban hijabi tunkafin takaraso inda yake,
ya kafe ta da ido yana fadin
"Masha'allah wallahi kamar da hijab d'inma kinfi kyau."
Feeryal takaraso a hankali ta d'an tsaya gefe da shi ta ce masa
"Inayini."
wani murmushi ya sake idanunsa a kanta.
Miemie ta ce bari tad'an basu guri tayi falon Aunty tazauna.
Feeryal natsaye Ibrahim nata zayyane mata kalan son da yake mata shifa nan da wata d'aya yakeso ya aureta.
Feeryal dai batace kalaba sai hijabin dataja tarufe gefen fuskarta.
yaleko fuskarta yana fadin
"Bud'e mana inata magana bakice komiba,
kitsaramana yadda zamu gudanar da shagalin bikinmu."
jan hijabin tadayi tana murmushi tarufe fuskarta sosai.
salati sukaji abayansu ana tafa hannu.
"Innalillahi wa innailaihirraji'un! lallai kun shahara wato iskancin naki harcikin gida,
abin naki ya girmama har maza kika fara kawo mana su cikin gida kuna sheke ayarku,
iskancin naku har gida!."
Umma karima tayi maganar cike da hayagaga takawo hannu tad'aura abaki tana tana fad'in
"Yihuhu jama'a kuzo nakamasu, na kamasa da idona."
Ibrahim yatsaya yanamata kallon mamaki,
Feeryal ko gaba d'aya jikin ta ya d'au kyarma........!
KUYI HAKURI DAN ALLAH BANI DA BAKIN DA ZAN IYA BAKU HAKURI WLH SAM BANSO HAKAN TA FARU BA AKASI AKE TA SAMU KWANA BIYU,
DA DAREN NAN NASAMU NAYI WANNAN KUYI HAKURI DA SHI DAN ALLAH
*Assalamualaikum barkanmu da wannan lokaci barkanmu da dawowa hutun Ramadan anyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana ya karbi ibadun mu*
Ibrahim ya bita da kallo ganin kiri-kiri da gaske sharri take son gina musu,
ya ce
"Me kike nufi ne wai? muna tsaye muna hira ki ce kin kama mu, kin kamamu muna me?."
da karfi ta ce
"Iskanci iskanci na kama ku da idanun nan nawa kiri-kiri ka shige cikin hijabi kana kwakularta,
munafukan Allah ta'ala asirinku ya tonu.
jama'a kuzo na kama 'yan'iska."
kan kace me ma'aikatan da suke aiki a babban kichin sun taho gurin.
Umma Karima bata fasa kwalala ba fad'i ta ke
"Na kamasu wlh na gansu da ido na, ya makale cikin hijabin ta suna aikata masha'ar su.
Mommy da Mom akusan tare suka iso gurin 'ya'yan su sun kaimusu rahoto.
sai tafa hannu suke da sallalami.
Ammah da mai aikin ta ta sanar mata da abin da ke faruwa ta fito abujajan.
Ibrahim na tsaye ya cika da mamaki matuka.
Mom ta rike hab'a tana sallalami, da fad'in
"Ai dama akwan a tashi in dai halin mutum ne sai asirinsa ya tonu,
a had'asu da karnuka da security su rakasu da duka 'yan'iska tambad'ad'd'u, zaku kawo mana iskanci har cikin gida."
cewar Mom tana aika wa Ibrahim da Feeryal banzan kallo.
Ammah data karaso gurin tayi saurin cewa
"A'a baza'ayi haka ba zo ka wuce katafi abinka kaji bawan Allah."
Mommy ta ce
"Kamar ya zakice ya tafi Hajiya Safiyyah ai yazama dole su karb'i hukun ci dukkan su shi da wacce ta jajub'o sa."
Ammah ta girgiza kai ta ce
"Ashsha ai ni banga shaidar da ke nuni da abin da ake zargi ba,
mutum d'aya bai wadatar da bada shaida kan zina ba,
a cikin ku akwai wannda ta gani da idon ta bayan Hajiya Karima?."
Ammah tayi tambayar tana tsaresu da ido.
duk ma'aikatan suka girgiza kai, Ammah ta ce
"To kaje abin ka kaji,
dan kuma Hajiya Halima da Hajiya Nafisat kusan a tare muka iso nan da su,
babu wanda acinin mu zai bada shaidar abin da ake zargi, dan ita zargin zina sai ana da kwararan shaidu guda uku wad'an da suka gani da ido."
Ibrahim yaja kafarsa yana girgiza kai yama kasa iya cewa komai, tsabar mamakin matar,
ya shige motarsa ya bar gidan baya ko ganin gabansa.
Gaba d'aya gurin ya kacame da hayani Mommy da Umma Karima da Mom, sai bala'i suke suna fad'in
yarinyar da kowa yasan ita 'yar'iska ce a filin Allah cikin bainin jama'a take iskanci, har ana d'aukarta hoto da video waye bai san 'yar iska bace.
Aciki kuwa TV da yake a kunne ne ya hana Aunty da Miemie jin abinda yake faruwa da wuri,
sai da hayaniyar ya kara yawa kafin suka jiyo hayaniyar sosai.
da sauri suka nufo waje.
Aunty ta tsaya cike da mamaki tana jin abinda yake faruwa cikin b'acin rai sosai ta dubi Feeryal dake tsaye ta toshe bakin ta da hijabi tana hawaye ta ce
"Ke Feeryal da gaske kin aikata abin da suke fad'a?."
da sauri ta girgiza kai murya na rawa hawaye na zuba ta ce
"A'a Ammie."
hannun Feeryal Aunty ta janyo ta dawo da ita kusa da ita sannan ta dubi Umma Karima ta ce
"Hajiya Karima kin dai ji da kunnen ki ta ce bata aikata ba, to kuwa tabbas bata aikatan ba,
ki tsaya a matsayin ki kada ki sake shiga lamarin ta bai shafe ki ba."
"Iye lallai ma kuwa ba shakka! irin ga waliyyiyar nan wacce bata fad'an karya daga ta fad'i magana gaskiya ce,
tana aikata iskanci kiri-kiri a kamata dan ta ce batayi ba shike nan ya zauna a kan bata yin ba."
Aunty tayi saurin katse ta
"Ni na yarda da d'iyata idan da ta aikata nasan bazata tab'a yi min karya ba zata fad'a min,
dan haka bata aika ta ba,
kowa ya kama gabansa kubar min kofar side!."
Nan da nan ma'aikatan kowa ya kama gabansa.
Umma Karima tayi shewa tare da tafa hanu tana fad'in
"Ahayyeee rass. ke har kina da bakin fad'ar wannan maganar yarinyar da gata nan cikin hoto kiri-kiri tana rungume da wani katoton gardin d'an iska,
a cikin bainin nasi kowa ya gani babu wanda bai sani ba,
an dai ji kunya wlh, an aje katuwar 'yar'iska a gida ana son ta b'ata mana yara"
Aunty ta yi saurin katse ta
"Ki iya bakin ki Hajiya Karima kar ki kuskura ki wuce gona da iri, zakiyi nadamar bakaken kalaman ki."
Mommy ta watsawa Aunty kallon banza tana cewa
"Bafa zai yuwu ba yazama dole ayi zama da Alhaji dan wlh bazamu zauna da 'yar iska ta gurb'ata mana rayuwar 'ya'ya ba, Ameerah Sumayya wuce mujen ku bari Alhajin ya dawo."
Mom ma ta kad'aga keyar Sahla bayan ta gama fad'an miyagun maganganun ta.
Umma Karima ta dubi Aunty tana fad'in
"Hajiya Fatima alkadarin ki na daf da karyewa, dan bazamu bar tsintacciyar agola cikin 'ya'yan gida ta koya musu iskanci ba, na fad'a na kara fad'a,
kiyi abin da zakiyi."
Siyama ta yamutsa fuska ganin kamar tana son yin magana Miemie ta dalla mata harara.
Umma Karima ta kad'a keyar nata iyalan
Bilkisu Rahma Saddiqa Nabila Siyama suna gaba tana bayan su.
Ammah tabi bayan su da kallo kana ta girgiza kai tana fad'in
"Agwagwa ke nan 'ya'yan ki nagaba kina baya, mugun abu yabi dare cikin duhu Allah shi kyauta,
kiyi hakuri Feeryal, Hajiya Fatima sai dai ayi ta hakuri dan wad'an nan mutanen halin su sai su."
Aunty ta ce "Mugun nufin su ya kare a kan su, insha'allah abin da suke son gani kuwa bazasu gani ba,
haka zasu kare da kai kawo."
ta ja hanun Feeryal suka shige ciki Miemie ta biyo bayan su, Ammah kuma ta koma sashinta tana mai mamakin hali irin na Umma Karima da su Mommy masu shaidan zur.
Ibrahim a hargitse ya isa gida, yana dai-dai ta parking ya fita da sauri ya nufi sashin Mom d'in sa.
ganin yadda ya fad'o cikin parlour da sauri ta tare shi tana fad'in
"Son lafiya me ya faru mene ne!?."
a binka da d'an gatan da bai saba shiga damuwa ba ya labarta mata abinda ke faruwa