Showing 60001 words to 63000 words out of 63585 words
Chapter 21 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
to ki shiryawa goyon 'ya'yan gaba da fatiha,
ni da FEERYAL kainuwa ne dashen Allah."
Aunty na kaiwa nan ta mike ta nufi kofar fita.
Umma Karima ta mulmulo ashar ta auna tana fad'in
"Karya kike Hajiya Fatima malamin ki ya yi karya, bai isa ya baki sa'an da zaki shigo min har b'angare na ki nimi ki gaya min magana ba,
ni Karima wlh zaki san da ni kikayi, munafukar banza munafukar hofi,
ciki kuwa sai dai ki ganshi akan wancan tsintacciyar aljanar ruwan badai akan 'ya'ya na,
itama Saddiqa'n ma fyad'e aka mata 'yan gulma 'yan bakin ciki, ba cikin shege taje tayi ba,
cikin shege a kanku zai kare."
Aunty tayi waje abinta.
Umma Karima bata fasa kumfar baki ba.
kira ta shiga kwad'awa Saddiqa.
Saddiqa ta fito ta ce
"D'auko mayafinki kizo muje a burge d'an banza, baza'a haifo shi ya zame min masifa alakakai ba,
dama hauka nake na bari a haifo shi."
Saddiqa ta koma ta fito da mayafi.
sukayi waje Umma Karima bata fasa bala'i ba.
Asibitin Dr L'cana suka je ta tura masa kud'i masu yawa, shi kuma ya sunkuya aikin sa.
yayi-yayi cikin ya fita abin mamaki ciki yaki fita,
shi kansa abin ya bashi mamaki duk kwarewa a iya cire ciki irin nashi, sai ga wannan yana son gagarar sa.
kwaya ya cusa mata a gaban ta ya ce suje gida kwayar zaisa cikin yafita dan dole.
tun daga hanya Saddiqa ta fara wash-wash,
Umma Karima ta ce
"Ai dama nakuda zakiyi sai ki daure har ya fita."
abu sai gaba-gaba yake har suka iso gida, Saddiqa ta shige d'aki tayi ta birgima.
kan kace me tafara fita hayyacin ta,
ihun Bilkisu ne yasa Umma Karima tasowa da sauri ta shige d'akin su.
ta tadda Saddiqa a sume, tayi ta yayyafa mata ruwa wai ko dan ta farka ina.
ba sai ga Umma Karima tana salati da kai kawo cikin d'aki.
tayi ta kiran Daddy a waya Daddy bayama gidan yana gun meeting.
ta fita a haukace tayi sashin Hajiya tana ihun fad'in
Saddiqa zata mutu.
suka dawo da Hajiya da ta rud'e ta birkice jikarta zata mutu.
Rahma ce tayi ta kiran Daddy da layin ta kafin ya d'aga ta sa kuka tana fad'in
"Saddiqa zata mutu."
ya ce
"Rahma idan lokacin ta ne ya yi Allah ya yafe mata, dama ai shi mutuwa wajibi ne ga kowa."
ya kashe wayarsa.
Hajiya ta ce wa Nabila da ke kusa da ita
"Kira abokin turawa yazo yanzu kar yarinyar nan ta mutu fa."
Nabila tayi masa missed call biyar ana shida ya d'aga, ta mikawa Hajiya.
a rud'e Hajiya ke fad'in
"Abokin tuwa kazo ka ceci ran kanwarka Saddiqa zata mu."
d'ip ya kashe wayar sa.
Hajiya jin shiru ta ciro wayar baki bud'e.
Bilkisu ce tayi tunanin kiran Family Dr su Allah ya yi taimako ba'a dad'e ba kuwa ya iso."
da kyar ya samo kanta ta farfad'o tana farkawa kuwa sai ga jini ya b'allo mata.
Umma Karima ta sauke wani uban numfashi.
Hajiya ta bud'e baki tana fad'in
"Yoo cikin ne zai b'are dama yake son tafiya da ita, gara ai da ka b'are da ka zauna ka zame mana abin kwatance cikin dangi."
bayan likitan yayi mata duk abin da ya kamata ya tafi, sukuma suka sunkuya gyaran in da jinin ya malala.
Bayan dawowar Daddy da daddare Hajiya ta je da kanta ta sanar masa, cikin ya b'are.
kai ya girgiza kawai dan yasan Umma Karima ce tayi kalan nata, bawai fita ya yi na Allah ba.
Saddiqa wata guda tayi tana jinya zuwa lokacin ta ware ta sami sauki sosai...
Daddy ne yafito daga bedroom d'in Aunty da shirin tayiya office,
Aunty na biye da shi rike da hular sa.
sai da suka zo tsakiyar parlour ya tsaya tare da duban ta.
murmushi tayi masa cikin zolaya ta ce
"Daddy wai kai bazaka tsufa bane kullum fa a haka kake baka kara gaba."
janyo ta ya yi yana kokarin rungume ta tayi saurin gocewa tana dariya da fad'in
"Aa Daddy a nan kuma idan Feeryal ta fito fa."
murmushi ya yi mata ya kalli kofar Feeryal ya ce
"Wannan 'yanmatan taki da alama bacci take har yanzu, a taso ta tayi breakfast."
har ya juya zai tafi sai kuma ya kuma juyo wa murya da alamar shiga yanayin sanyin jiki ya ce
"Fad'imatu idan na dawo akwai wata maganar da nake so muyi da ke,
amma kafin nan zan tinkari Hajiya duk da zuciyana yana bugu da sauri-sauri,
har ina jin yana min zafi, amma zan tinkare ta ahakan duk da bani da tabbacin samin nasara."
Aunty ta dubeshi cikin rauni ta ce
"Daddy mene ne kuma."
murmushi ya yi mata ganin nan da nan ta shiga damuwa ya ce
"Babu ko mai sai na dawo ai nace zamuyi magana ko, kiyi min addu'ar samin nasara, a gurin Hajiya."
kai ta jinjina.
har gurin mota tarakashi sannan ta mika masa hularsa, direba yaja shi zuwa sashin Hajiya......!
Mommyn Twins ce
Daddy na zaune a parlour'n Hajiya bayan sun gaisa, Hajiya tayi ta kawo masa hirarraki, yana amsata amma gaba d'aya hankalin sa na ga maganar da take cikin ransa, wanda yake tunanin tinkarar Hajiyar da shi.
Daddy ya gyara zama ya fuskanci ta da kyau ya yi karfin halin soma magana.
r"Hajiya dama wata magana nake tafe da shi, amma bansan da wace fuska zaki fiskanci lamarin ba,
amma Hajiya dan Allah ina so ki fahimce ni, a matsayin ki na uwa a gare ni, nasan kinfi kowa son ganin farinciki na,
yin tawassali da Allah babu abin da yafishi dad'i da samin nasara a rayuwa,
ka yadda Allah shike da ikon yin komai a duniyar nan, duk abin da ya sami bawa da sanin ubangiji duk kuma abun da kaga ya faru da kai dama rubucacce ne cikin kaddarar ka sai dai wani yazamo sila,
shirka haramun ce babu laifin da Allah baya yafewa bawa har idan yamutu yana aikatashi face shirka,
haramun ne shaidar zur abin da baka da tabbaci akan sa ka tabbatar da cewa hakan ne."
da sauri Hajiya ta ce
"To Abubakar ni ban gane in da wanna batun naka ya dosa ba,
wai wa'azi kake yi min ko me?
tun kafin kazo duniya nake jin wa'azi,
ai naga kamar shirin fita kayi katashi ka tafi Allah ya bada sa'a, wa'azi kam ai andad'e ana jin sa."
Daddy ya d'an yi shiru da wasi-wasi tap cikin ransa ya gyara zama yana son dai-dai nutsuwar sa, kai tsaye yasoma fad'in
"Hajiya ba haka ba,
abin da nake tafe da shi nake son sanar miki shine,
ina so na bawa Abdulrahim auren FEERYAL, saboda wasu dalilai idan da zaki fahimceni da zan zayyano miki dalilan nawa, kuma nasan zaki bani goyon baya..."
wani irin zabura Hajiya tayi tamkar taga wani muhimmin mugun abin tsoratarwa.
wani irin bugawa kirjin Ajmal daya sako kai zai shigo parlour'n ya yi har sai da ya kai hannu ya dafe kirjin nasa, dake bugu dum-dum-dum!.
wani irin bakin abu yaga ya gilma masa a ido, ya juya da sauri ya koma side d'in su.
a parlour'n kuwa Hajiya
ta mike tsaye a zabure take fad'in
"Abubakar kasan me kake fad'a kuwa! ko kunne na ne yajiyo min ba dai-dai ba?
aljanar kake son aurawa abokin turawa!
to bari kaji wlh ko bayan ba raina banyarda ka aura masa ita ba,
bama shi ba ko wani d'a a gidan nan kai koma waye har idan da dangantaka sakani na da shi, wlh ban yarda ba ban yafe maka ba Abubakar idan ka aurawa wa wani jikana,
wannan mayyar aljanar ruwan bare jikana na fari abokin turawa!."
Daddy da yaji kamar ciwon sa zai tashi sabar tashin hankalin da ya shiga agurin,
dama yasan da kamar wuya Hajiya ta yadda.
ya dafe kirjinsa da ya soma yi masa zugi ya ce
"Hajiya da zaki fahimce ni ki bani dama na kawo miki dalilai na."
"Rufamin baki dalilan banza da lilan hofi,
ai baka da wani dalilin da zaka gayamin akan auren mutum da aljana,
ai in zaka mutu babu abin da zai sa ayi auren nan, ko mutuwa zakayi sai dai ka mutu Abubakar."
Hajiya ta juya ta shige d'aki tana falle zane tana gyara d'aurawa sabar masifa.
bata karasa ciki ba takuma juyowa ta dawo
"Ni za'a kawowa zancen banza zancen iska,
to maza-maza kaje ka fita da yarinyar nan a gidan nan yanzu, idan kuma ba haka ba ni nafita na bar maka gidan ka,
baka zab'eta a kaina ba ai dama shi yasa ka masa kan ta zauna wai ana bincike,
ai ita yakamata ayi bincike a kanta ba wasu ba,
to wlh idan baka kori yarinyar nan ba saina sassab'a maka."
Hajiya takama jan hanci tana cigaba da fad'in
"Dama ashe abin da yasa kaki rabata da gidan nan ke nan, Abubakar nasake fad'a maka in zaka mutu abokin turawa bazai auri yarinyar nan ba,
yaushene ma yayi aure da za'a sake masa wani auren, kai wlh ko shekara goma ya yi da yin auren fari idan wannan aljanar yarinyar ce bazaiyi na biyu da ita ba,
tashi maza ka fita min anan ni zaka kawo wa tsiya."
Daddy ya mike jiki ba kwari ya fita.
A b'angare Ajmal kuwa d'akin sa ya shige ya kulle kansa ciki.
ya kafa kansa jikin garu-bango yana jin wani irin azaba cikin ransa.
yarika dukan jikin garu-bango yana fad'in
"Why Why why! ya akayi nayi nauyin baki ne, ni nake son FEERYAL Daddy ba Ya Abdulrahim ba."
ido ya rumtse da karfi tare da buga kanta a jikin bongo, sai kuma ya zame kasa ya zauna ya mike kafafunsa, ya jingina bayansa da jikin garu yana juya kai hannunsa na dafe da gefen zuciyar sa, ya yin da idanunsa ke a rumtse.
Daddy kuwa yana fita ya shiga mota direba yakai shi office sai dai me yakasa zama office d'in ya fito yasa direba ya maida shi gida.
Aunty ta mike tsaye da sauri ganin Daddy ya ya shigo bedroom d'in ta.
ta ce
"Daddy ba dai mantuwa kayi ba, naga ka dawo da wuri."
zama ya yi yana cewa
"Zauna Fad'imatu muyi magana."
Aunty ta zauna tana kallon shi da alamun soma shiga fargaba.
"Fad'imatu."
Daddy ya kira sunanta.
"Na'am Daddy."
ta amsa zuciyar ta na d'an harbawa.
"Jiya magabatan wannan yaro mai son Feeryal Major Sadam sunzo, nasa akayi musu masauki a masaukin ba'i na cikin company;
sunzo nima masa auren ta sannan sun taho da shirin su sunaso a yanka musu sadaki, da sa rana duk a jiyan, dan suna tafe da kud'i idan aka yanka sadaki subiya nan take, a samusu ranar da bazai wuce wata guda ba.
sai dai ni na ce musu nayi mata miji tuntuni,
kuma a halin da ake ciki zan aurar da ita wa mijin da nayi mata nan da kwanaki kad'an,
Fad'imatu na sami Hajiya da ma nasan ba lallai ne ta aminta da abun da naje mata da shi ba,
ina da yakinin bani kad'ai ba kowa zai amfana da abinda nake son aiwatar wa."
Aunty ta jinjina kai kamar ko da yaushe acikin yadda da maigidan nata take ta ce
"Insha'allahu duk abin da kake son aiwatarwa alkhairi ne,
amma mene ne shi d'in Daddy?."
numfashi ya sauke sannan ya ce
"Zan aurawa Abdulrahim Feeryal hakan ne kawai zai kaini ga tsira daga farmakin da ake kawo min cikin bacci, wanda bansan ta ina ne yake zuwa ba."
zumbur Aunty ta mike tana girgiza kai da fad'in
"Aa Daddy dan Allah kar ka soma, dan Allah kar kabar maganar nan ta fita na roke ka, kaje ka sami Hajiya ka ce mata dama fad'a kawai kayi ba zartarwa zakayi ba;
Daddy ka rufa min asiri ya zanyi da rayuwa ta a cikin gidan nan idan wannan maganar ta fita,
ya zanyi da Hajiya da Hajiya Halima da sauran 'yan gidan nan, Daddy so kake na tattara na tafi ko, dani da Feeryal d'in duka,
dan Allah Daddy kar ka sake wannan maganar, Feeryal kam ma tana da wanda zata aura Major Sadam, ka bashi auren ta kawai."
"Fad'imatu zauna dan Allah."
Daddy ya fad'a yana ruko hannunta.
kai ta girgiza ta ce
"Aa Daddy tsoro nake ji dan Allah ka janye batun nan."
"Ke ma ashe bazaki saurare ni kiji dalilai na ba,
Fad'imatu kaf duniya babu wanda yake fahimtata sama da ke, kin fi kowa sanin damuwa na, zauna dan Allah."
jiki a sanyaye ta koma in da ta tashi.
ya dube ta da kyau kana ya soma magana
"Na jima ina tunanin wanda zan zab'awa Feeryal a matsayin abokin rayuwarta, tun lokacin da ta fara tasowa,
nake yi mata fatan nagartaccen miji, wanda zai kula da ita yaji kan lamuranta,
a daren da aka rasa Feeryal ranar auren Abdulrahim,
yasa kafa yafita nemo ta batare da wani ya sani ba, yaje ya kwato ta a hannun wad'an da suka so b'ata mata rayuwa,
lokacin da ya dawowa da ita gidan nan tun a ranar naji shine ya dace da rayuwarta."
zama Daddy ya gyara kana ya kira sunan ta
"Fad'imatu kinsan wa yake citona cikin munanan mafarkan da nake, kuma me nake ji ake fad'a a kanta,
Feeryal ce;
cemin ake itace hasken kub'uta ta kar na barta tayi nesa daga rayuwa ta."
a hankali yashiga bata labarin abubuwan da yake gani cikin mafarki wanda dama bai tab'a zama ya fad'a mata irin abubuwan da yake gani ba, sai dai idan ya farka ya ce mata, zasu kashe shi.
sannan ya d'aura da fad'in
"Dama ina da shirin aura mishi ita, tun a daren ranar auren shi naga dacewar hakan,
dalilin da yasa na dad'a karfafawa kuwa a shine mafarki na,
Fad'imatu shin kina so na dad'a kasancewa cikin yanayin da na shiga a kwanakin baya ne,
ki karfafa min gwuiwa mana,
ina ji a raina da gaske Feeryal alkhairi ce a rayuwar mu,
zamanta a cikin mu alhaki ne."
Aunty ta sauke numfashi ta ce
"Daddy bana fatan ka sake kasancewa cikin halin da ka shiga a baya,
amma Daddy Hajiya fa bazata tab'a amincewa ba, sannan ita kanta uwar Abdulrahim Hajiya Halima bazata amince ba,
sannan shi kansa Abdulrahim d'in da
'yan'uwan ka da kowa da kowa ma, ba lallai ne su amin ta ba,
me zai hana idan ta auri Major Sadam d'in ace ya zauna da ita a garin nan, ai kaga muna tare da ita ke nan bamuyi nesa da juna ba."
Daddy ya ce
"Amincewar Hajiya kad'ai nake bukata, bayan ita bana bukatar kowa sai ya aminta."
Aunty tayi shiru tana tunanin taya hakan zata kasance, lallai kuwa matsala yanzu ne zata kunno kai.
Da kyar Ajmal ya samu ya rarrashi zuciyarsa, yafito cikin 'yan'uwan sa.
Hajiya abin bai mata ba da daddare tayi tattaki zuwa sashin Daddy,
takuma jaddada masa ko bayan ranta akayi auren nan bata yafe ba.
Hajiya bala'i take tana fad'in
"Sabo da aljanar yarinyar nan ta gama shiga jikin ka, shine kake nima ka kakabawa abokin turawa ita dan shima ta shige jikin nasa ko,
to kai da kayi gayyarta kaje can ka karata badai jikana ba,
wlh takar baki idan ka kuskira sai ka biyani nono na!
kuma gobe-goben nan nake son yarinyar nan tabar gidan nan, idan bata tafi gobe ba ni zan tafi kuma kar ka sake kaje in da nake bani ba kai ke nan."
Hajiya ta juya ta fita tana cigaba da bala'i.
Wad'annan kalaman da Hajiya ta fad'a sunyi mugun tsayawa Daddy a rai, dan kalmace mai girman gaske akan kowani d'a idan uwa ta gaya masa.
kalaman sunyi masa girma har sai da yaji kamar ciwonsa na shirin tashi.
ranar a daddafe ya kwana kirjinsa na zafi.
washegari da safe Daddy ya kira Bappa Salihu na Yelwa mahaifin Mommy kanin mahaifin su, yasanar masa abun da ke faruwa.
Bappa Salihu ya ce
"Hajiya Hanne ke nan, wannan magana bazata yuwu a waya ba zanyi tattaki nazo Lagos d'in, insha'allahu gobe zuwa jibi zan shigo Jos nahayo jirgi na iso nan Lagos d'in."
Daddy ya yi ta masa godiya kana ya katse kiran.
lambar Abdulrahim ya kira ya ce yazo yana niman sa.
batare da b'ata lokaci ba ya shigo parlour'n nasa.
ya nimi guri ya zauna tare da gaida Daddy ya amsa yana kuma duban sa da kyau, sannan ya d'anyi gyaran murya kana ya ce
"Abdulrahim nakiraka ne domin nagaya maka hukuncin dana zartar a kanka,
duk da kakarka ta nuna rashin amincewar ta,
bazanyi kasa a gwuiwa ba zan sanar maka kafin lokacin dana yanke yazo,
Abdulrahim zan aura maka Feeryal bayan ganin dacewar hakan na zartar da hukuncin."
da karfi ya yi wani irin d'agowa ya dubi Daddy.
Daddy ya jijjiga kai tare da fad'in
"Kwarai kuwa hukuncin dana yanke ke nan."
kasa ya yi da kansa batare da ya ce ko mai ba.
Daddy ya ce
"Tashi kaje idan na tsaida rana zan sanar maka."
da sauri ya ce
"Amma Daddy."
"Amma me Abdulrahim musu zakayi min?."
kai yakuma sunkuyar wa, bai kuma magana ba,
a sannu ya mike ya yi waje Daddy yabi bayan sa da kallo.
Abdulrahim na fita Daddy ya kira Mommy a waya ya ce tazo yana son magana da ita.
Mommy ta shigo ta same shi a parlour ta nimi guri ta zauna.
Daddy ya dube ta kana ya ce
"Hajiya Halima nakira ki ne domin na sanar miki abun da na yanke kan d'ana,
bana so ace kinji maganar a gun wani, ki kalli hakan a kan rashin adalci;
ina sanar miki hakan ne dalilin ke ma uwa ce a gare shi, kafin na zartar da hukunci yana da kyau na sanar miki,
zan d'aurawa Abdulrahim aure da Feeryal,
ni mahaifin Abdulrahim ita na zab'a masa a matsayin mata."
Daddy na kaiwa nan ya mike yanufi kofar fita
wani irin daramm damm Mommy taji tamkar saukar aradu aka, sabar tashin hankali da d'inbin mamaki da jin abun tamkar almara kasa iya furta komai tayi.
tabi shi da kallo har ya b'acewa ganin ta.
sai sannan ta sauke wani uban ajiyan zuciya kamar wacce ta suma ta farfad'o.
ta ce
"Tabd'ijan wlh karya ne bazai tab'a yuwuwa ba!."
A haukace Mommy ta mike tabi bayan sa, ta hango har ya shiga mota direba ya ja shi sun nufi get.
sashin Hajiya ta nufa tana zuba ruwan bala'i bata ko ganin gaban ta.
tun daga bakin kofa take fad'in
"Hajiya ciwon nan ya fara tab'awa Alhaji kwakwalwa fa, kinji me yake gaya min yanzu kuwa, wai zai aurawa Abdulrahim wannan aljanar yarinyar."
Hajiya ta ce "Wato bai janye maganar ba ke nan, to ai sai ya yi mugani, ba sai ma ya ganta a gidan ba."
ta fita fuuu Mommy tabi bayan ta.
"Ina aljanar take fito kibar gidan nan, tun da bana uban ki bane."
Hajiya ta fad'a sanda suke shiga parlour'n Aunty.
Aunty ta mike tsaye da sauri.
Mommy ta wurga mata kallon banza sannan ta ce
"Kina tunanin yadda kika sami kan Alhaji haka zaki sami na d'ana, wlh karya kike ba dai d'ana ba kam."
tuni Hajiya ta wuce d'akin Feeryal ta na fad'in
"Ina kike fito kibar gidan nan jikana yafi karfin ki."
Hajiya ta shiga raba ido cikin d'akin ganin