Showing 15001 words to 18000 words out of 63585 words
Chapter 6 - FEERYAL Part 2 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.txt
amshi jikin ta.
ta fito ta wuce dinning ta tarar da Aunty a gun ta tanadar mata abin kaunar ta wato cake da yogurt.
ta bayan kujerar Aunty ta zo ta kwantar da kanta gefen kafad'ar ta cikin siririyar muryarta ta ce
"Ina kwana Ammie na."
Aunty ta shafa gefen fuskarta ta ce
"Lafiya lau 'yammatan Ammie antashi lafiya ya lalaci,
a rage lalacin nan gobe ke zakiyi mana breakfast idan Allah ya kaimu, yau ma tare zamu shiga kitchen anjima."
"To Ammie."
ta fad'a tana mikewa a jikin ta taja kujera ta zauna.
Kamar yadda Aunty ta ce da rana tare suka shiga kitchen da Feeryal.
Sosai Aunty ta dage wajen koyawa Feeryal nau'ikan girki kala-kala, bata yadda ta barta kara zube kamar yadda wasu masu kud'in suke yi wa 'ya'yan su ba,
komai sai dai masu aiki suyi ba dai 'ya'yan su ba, suna ganin wai hakan gata ne da yawa sai sunyi aure suke had'uwa da kalu bale daban-daban a gidan auren.
duk da Aunty d'iyar masu kud'i ce bata taso cikin tarbiyyar irin wad'an can 'ya'yan masu kud'in ba.
shiyasa ta zage damtse wajen koyawa Feeryal abubuwa da dama da suka shafi cikin gida.
yawan zama da Miemie takeyi a sashin itama ta karu da wasu abubuwa da dama.
Aunty ce zaune a parlour tana video call da Hajja Umma.
jiya aka sami nasarar zakulo mutum biyu daga cikin tawagar 'yan d'aukar amarya, da hukuma suke ta kan bincike a kansu har yanzu.
Aunty tace
"Amma dai Hajja Umma babu wata matsala ko?
ni fa tun da naji ance an kuma kama wasu 'yan gidan sa duk a tsoro nake,
kar sauran da suke a b'oye suce zasu fito d'aukar fansa."
Hajja Umma ta ce
"A'a babu komai insha'allah, wannan yaro Sadam Abokin Nasir Allah dai ya saka miki, yaron akwai kokari jiyan nan kusan da shi muka wuni a gidan nan da jami'an su, da daddare ya turo jami'an su biyu da folisawa biyu da Nasir ya turo
har muka waye gari yau da su,
har yanzu ma suna nan,
amma naji Alhaji yana cewa anan zasu cigaba da zama har zuwa a kare bincike."
Aunty ta sauke numfashi tare da cewa
"To Allah ya dad'a tsarewa."
"Amin ya Allah, wai ni kam ina kishiya take ne banji d'uriyar ta ba."
"Tana d'aki ai bata san muna waya da ke ba da kin ganta."
Aunty ta d'aga murya ta wala mata kira,
ta fito da sauri tana amsa kiran
"Taho ga Hajja Umma tana niman ki."
da sassarfa ta karaso inda Aunty take ta zauna gefen ta tare da kwantar da kanta a jikin ta, ido ta waro ta ce
"La Hajja Umma shine tun d'azu baki neme ni ba ko."
"A'a nunar gwanda bagashi na nemo ki ba yanzu,
kwana biyu da ban gankiba sai naga kin dad'a kumbura, kazar turai jikin nan ya dad'a komawa tumatur sharaf."
baki Feeryal ta turo ta ce
"Ba Abba ya ce ya ce ki dai na fad'a min ba, ke da shi,
Ammie na kashe ki kira min mijin ta muyi hira."
"A waya kawai zaki ganshi ni kuma ina tare da shi a nan."
"Ai baki sani ba Hajja Umma kullum sai yabi jirgi yazo gurina,
ke kina can kina ta kan cewa masu aiki,
kuyi kaza kuyi kaza, kar ku saka gishiri da yawa a abincin almajiran nan fa ku sa musu magi ya ji."
dariya duk suka fashe da shi.
Aunty ta ce
"Au haka Hajja Umman take fad'a."
kai ta gyad'a tana dariya ta ce
"Kullum sai Abba ya shigo yace ta zauna ta huta ta barsu su suyi aikin, yana fita zata tashi taje bata zama tarika kai kawo ke nan, bata ko gajiya,
ai shiyasa Abba ya ce yafi so na ma, ita kullum bata hutu gata da masu aiki."
dariya Aunty tayi tana dungurin kanta.
Maryam da ta shigo ta tadda suna wayan ta leko cikin wayar Feeryal ta washe baki
"Aunty Maryam ina kika je ne?."
"Gidan su Haulat yanzu kuwa muke hiran ki da ita, tana tambaya ta yaushe zaki dawo."
"Ai nakusa dawowa, sai dai bana so na rabu da Ammie na ne."
tayi maganar tana dad'a kwanciya jikin Aunty.
"To ai sai ku dawo tare da Ammie'n naki."
cewar Maryam tana mata hararar wasa.
Wayar ta da ke rike a hannunta ne ya yi kara,
ganin Miemie ce ke kiran nata yasata d'agawa.
"Hello Miemie."
daga cikin wayar Miemie ta ce
"Feeryal yi sauri kizo kiji wani magana."
"Wacce magar Miemie?."
jin shiru yasata ciro wayar a kunne taga har ma ta kashe kiran.
ganin Aunty sun kama wani hirar da Hajja Umma sai ta fice zuwa sashin su Miemie.
Har ta kusa rabin isa sashin nasu kiran Miemie ya kuma shigowa wayar ta.
"Yauwa Feeryal tsaya ma kawai bazan zo."
"Ai gashi na fito ma bari na karaso."
"To tsaya-tsaya ma kawai bari ni na fito."
Miemie ta fad'a tare da katse kiran.
Feeryal ta sauke numfashi tana fad'in
"Oh Miemie."
Gefe ta matsa ta jikin wasu dogayen bishiyoyin fula da suke jere a gurin, tana jiran fitowar ta.
maganar da taji ta cikin bishoyoyin ne yasata juyawa da sauri ta d'an leko ta sakankanin flaws d'in.
karaf suka had'a ido da Ameerah da ke zaune da saurayin ta suna hira kan kujerun da suke cikin gurin.
saurayin ya mike da alama sun gama hirar zai tafi.
da sauri ta d'an matsa baya.
Tana tsaye har motar saurayin ya fita a gidan.
a razane ta waigo jin an buga kafad'ar ta ta baya.
Ameerah ta bita da kallon sama da kasa ta ce
"To sannu bakar munafuka, wacce munafurcin ne yakawo ki nan kika zo kina leka min saurayi,
Allah ya toni asirin ki saurayi na kike lekawa."
murya a sanyaye Feeryal ta ce
"Kiyi hakuri wlh bansan kuna nan ba, kuma ni ba lekensa nake yi ba."
"Karya kike yi leka shi kike yi ai ina kallon ki,
sai kin fad'a min uban da yasa kike lekashi, ko naci uban ki da duka anan, dama ina da cikin ki."
"Allah Ameerah ni ba leken sa nake ba, ban ma san kune a gurin ba."
Miemie da ke tahoto ta bud'e baki tana kallon yadda Ameerah ke d'agawa Feeryal murya ita ko sai magiya da kwantar da kai take kamar zatayi kuka.
da sauri ta karaso gurin ta na fad'in
"Ya ya akayi wai mene ne?."
da sauri cikin tsiwa Ameerah ta ce
"Kamata nayi tana leka min saurayi."
Feeryal tayi narai-narai da ido ta ce
"Allah ba leken sa nake ba magana naji na leka bansa su bane."
Miemie ta ce
"To lallai saboda Feeryal d'in ta rasa aikin yi sai ta tsaya leken saurayi kamar wacce ta rasa samari,
ta ce ba leka miki saurayi tayi ba ai sai kiyi hakuri ki rabu da ita."
"Karya take lekashi take yi ai na ganta da ido na."
Ameerah tayi maganar cikin hayagaga.
Miemie ta ce
"To meye a jikin saurayin naki da za'a leka shi,
ana ta ce miki kiyi hakuri kina ta wani d'agawa mutane murya to ta kalla kiyi abin da zakiyi,
dalla wuce mu tafi, Feeryal tayi abin da zatayi."
"To idan zan mata abun da zan matan zaki hana ne,
kema bakifi karfin na had'a da ke ba bana son shishigi."
Miemie ta dalla mata harara ta ce
"Kar ki yadda kice zakiyi min ehe ni ba Feeryal bace kul in gaya miki,
kisan wad'an da kike wa rainin wayon ki, kar ki yadda kice zakiyi min,
dalla wuce mu tafi kin tsa tana gaya miki magana har kina bata hakuri."
taja nannu Feeryal fuuu suka kara gaba bata fasa mitar ba.
"Ki ci gaba da tsayu kowa yarika cin tuwo a kanki yana wanke kwanon, idan Ameerah ta gane kina tsoron ta to kin shiga uku bakisan wannan shegiyar bace, kin tsaya kina wani bata hakuri baki gaggaya mata magana ba, ita da saurayin nata."
"To me zan ce mata Miemie jiran ki fa nake wlh ni ba leken saurayin ta nake ba."
"Dalla ni ki daina min wannan maganar kayan haushin, kar kiyi baki ki iya rama waba, Ameerah da kike gani rashin mutuncinta ya wuce duk in da kike zato."
shuru tayi bata ce komai ba.
Kamar ko da yaushe Umma Karima ce zaune gaban bokanta, babu d'ankwali babu takalmi.
a gaban su wata tukunyar kasko ce tana tafarfasa ita kad'ai tamkar yana kan garwashin wuta.
boka Mali ya leka cikin tukunyar
cikin kazamyacciyar muryarsa ya kece da dariya
"Hahaha aiki na kan wakana sai dai har yanzu kin kasa samo cikon na uku har yanzu aikin ki bai cika ba,
bazaki tab'a samun yadda kike so ba har sai kin jefa duka ukun cikin tukunyar nan."
cikin damuwa Umma Karima ta ce
"Boka duk yadda zanyi nayi na kasa samu babu wata hanyar da za'a bi a cikita min aiki na in yaso sai na biya kawai."
Sandar tsafin sa ya buga kasa yayi wasu surkullensa kana ya zaro wata laya ya ce ya jefata cikin tukunyar nan,
wani irin kumfa had'e da bakin hayaki fuuu ya taso cikin tukunyar.
ya ce
"Duk sanda layar nan ta gama narkewa har idan baki samo cikon na ukun ba to aikin ki ya lalace, sai dai a fara daga farko."
da sauri ta ce
"A'a boka hakan bazama ta faruba ko ta halin kaka zan nemo bazan bari aikin shekara da shekaru ya tashi a banza ba."
"Hahaha kin yi tunani mai kyau maza ki tashi ki bazama nima."
Umma Karima ta mike a bujajan tayi waje bayan ta zazzage masa bakin jaka.......!
8
Mommy ne zaune a bedroom d'in ta rike da waya a kunnen ta, tana fad'in
"Ki bata hakuri Hajiya Luba halin Abdurrahim sai a hankali, ko ni nan hakuri da shi nake dole sai tayi hakuri,
har zuwa san da zata shigo gidan sa bazata tab'a samin yadda take so da shi ba, dan shi wani irin mutum ne baud'ad'd'e,
san da suka kasance a tare ai ita mace ce tasan yadda zata bi ta karkato da hankalin sa gare ta."
Hajiya Luba ta ce
"Amma dai babu dad'i haka ace an bada sadakin ka ko sau d'aya saurayin bai tab'a zuwa ba,
kullum a cikin karya take wa kawayenta baya kasar ne, har wasu sun fara gane wa."
"Karki damu Hajiya Luba ke dai a saka bikin nan kawai daga zaran anyi ba shike nan ba,
bari alhaji ya dawo zan masa maganar ya turo aje a sa rana, ayi bikin nan da wuri kawai, kudai kuci gaba da shiri nima ina kai za'a kawo muku lefe satin aure."
"To yanzu naji batu Hajiya Halima ga d'iyar taki ma wai na bata ku gaisa."
Mommy ta washe baki
"Ah bawa surukar tawa mu gaisa."
Hajiya Luba ta mikawa Kuraiba da ke kwance a jikinta waya tana fad'in
"Ga Mommy'n naku kullum in muna waya kiyi ta ce nabata ku gaisa kamar baki da wayar kiran ta ku gaisa."
Mommy ta yi dariya
"Yar albarka ya kike ya shirye-shirye."
"Lafiya lau Mommy muna kai."
"Yauwa madalla kiyi ta hakuri da Abdurrahim lokaci na zuwa."
"Mommy ko na kirashi baya d'aga wayar."
"Kar ki damu Kuraiba daga zaran kunyi aure duk wannan matsalolin sun kare, kinji ko."
ta ce to.
"Yauwa to sai anjima."
Mommy ta kashe wayar.
Kuraiba ta gyara kwanciyar ta jikin uwar tata.
Hajiya Luba ta ce
"To kinji da kunnen ki Hajiya Halima ba karamin kaunarki take ba,
zaki kuma sami d'anta yadda kike so cikin ruwan sanyi."
"Momma ina son Abdurrahim burina kawai na mallake shi, nadad'e ina mafarkin samin miji kamarshi,
kyakkyawa kakkarfan namiji a tsaye mai kud'i."
Hajiya Luba ta yi dariya tana cewa
"Kud'i kam akwai shi dan kuwa su kud'i gadarsa sukayi, jinin kud'i ne a jikin su yake malala,
kwantar da hankalin ki kamar kin sami Abdurrahim kin gama."
Kuraiba tayi wani murmushi tana hasasho kasantuwar su da shi..
Nan da nan Mommy ta sunduma cikin soma shirin auren Abdurrahim da Kuraiba,
a gefe guda kuwa Umma Karima ma na nata shirin dan kuwa ta lashi takwabi sai kanwarta Siyama ta auri Abdurrahim dan tanan ne kawai zata dad'a samin cikar burin ta.
bokan ta ya bata wasu lakanin suna nan suna ta aikin shaye-shaye da shafe-shafen magani.
Feeryal da Miemie ce zaune a cikin keb'ab'b'en gurin hutawa dake gefe da sashin Ammah, wanda yake a matsayin mallakin sashin,
kamar yadda ko wani sashi na gidan yake da irin gurin.
an zagaye fulawowi kujeru na zagaye a cikin sa gurin hutawa ne na musamman da aka kawata shi da furanni.
Miemie ta bud'e baki da hanci tana kallon Siyama da ta doshi hanyar part d'in Abdurrahim.
ganin yadda tayi da baki Feeryal ta saki murmushi mai sauti tana fad'in
"Meye hakan Miemie?."
Miemie ta yamutsa fuska tare da cewa
"Dubi waccan 'yar wahalar shegiya jibeta ba gaba ba baya ba nono ba d'uwawu,
gatanan tsangargar tana tafiya tana wani karairaya jiki kamar an d'aurawa muciya zane,
me Ya Abdurrahim zaiyi da ita,
shi da ya yi rayuwa cikin turawa da larabawa,
har garama Kuraiba tana da d'an cika ita ma d'in dai ba wani fasalin kirki ne da ita ba,
Mommy ce kawai ta masa dole sai ta had'a shi da 'yar kawar ta,
shiyasa Hajiya ma ta ce yaje can Yelwan Shendam ya nimi mata akwai kyawawan mata a gurin,
Mommy ce ta ki da Yelwa zamuje mu sha biki,
da kinje garin kakanmu kin gani garin fa akwai dad'i."
Da sauri Feeryal ta waiga inda Miemie take nuna mata Siyama,
tana daf da shiga part d'in sa.
hab'a Feeryal ta rike ta ce
"Ke Miemie ki raba ni da niman magana ni dai bani da karfe idan ta jiki sai dai na gudu na barki."
"Wlh wannan had'eta zanye na kalmashe 'yar banza, ai ke kin shiga uku da shegen tsoro ina abin jin tsoro a jikin waccan shamuwar mttss."
taja dogon tsaki.
Feeryal ta girgiza kai tana fad'in
"Ni dai babu ruwa na."
"Dalla ta shi mu je ki rakani na amshi book d'i na gurin Sumayya,
banson kayan haushin nan naki."
Feeryal ta mike tana dariya.
Suka fito daga cikin gurin Miemie tana fad'in
"Book d'in nan shi ke tayani hira da daddare idan bamuyi waya da Murad ba,
Sumayya daga aro ta rike taki bani, kullum sai tace zata kawo min gara naje na amshi kayana,
yau Murad ya yi tafiya book d'in ne zai taya ni hira."
"Wani irin book ne haka, mene ne a cikin sa?."
"Love story ne gobe zan baki ya kwana a gurin ki ko zaki shiga layi, dan naga ke sai an d'auraki a network kafin ki dawo saiti,
jiya ma da wani abokin Ya Faisal ya ganki a sashin Ammah sai da ya tambaye ni ke,
kawai na watsar da lamarin ne dan nasan ke d'in sai a hankali."
baki Feeryal ta tab'e dan tana ganin soyayya duk shirme ne da kuma b'atawa kai lokaci.
Suna shiga cikin side d'in Mommy Feeryal ta tsaya a farfajiya bata yadda ta shiga ciki ba.
ta ce wa Miemie taje ta dawo tana jiran ta dan bata mance gargad'in Mommy kan shigo mata sashin ta ba.
Da sauri Ajmal ya turo karamar kofar da ke jikin get d'in side d'in ya shigo.
Feeryal ta waiga suka had'a ido ya sakar mata murmushi.
itama takaitaccen murmushi ta mayar masa tare da sunkiyar da kanta.
ya karaso in da take yana fad'in
"A'a Feeryal ya kika tsaya a nan baki shiga ba."
"Miemie nake jira ta shiga yanzu zata fito mu tafi."
agogon hannunsa ya duba kana ya dube ta ya ce
"Yauwa dan Allah shiga ki cewa Ameerah wai taje in ji Ya Abdurrahim,
sauri nake yi ana jira na a office."
da sauri ta d'ago suka had'a ido sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta,
jiki a sanyaye ta ja kafarta, da fargabar abin da zai biyo baya idan ta shiga, tana kuma jin nauyin ta ce masa bazata iya shiga ba.
Tayi taku d'aya zuwa uku ya kira sunan ta
"Feeryal."
cak ta ja ta tsaya tare da waigawa bata bari sun had'a ido ba kanta a kasa.
numfashi ya furzar kana ya ce
"Ina so muyi wata magana yaushe kike da lokaci, nazo na same ki a side Aunty."
Shiru tayi tana wasa da bakin gyalen ta.
"Jeki sai na dawo."
ya fad'a tare da juyawa da sauri ya tafi.
Takai minti 5 tsaye a bakin kofar tana tunanin shiga daga bisani ta tura kofar ta shiga da sallama a hankali.
Mommy ce zaune ita kad'ai a parlour tana ganin Feeryal ta ware ido.
"Ke me ya kawo ki nan?."
ta fad'a tana dad'a ware ido a kanta.
Feeryal taja ta tsaya jiki na kyarma.
"Ke kutumar uban ki nace uban me ya kawo ki sashin nan, au anturo ki ki barbad'a wani barbad'en naku ne ko,
zo nan."
Mommy ta fad'a cikin tsawa.
Feeryal ta zabura ta shiga takowa in da take ta tsaya gefen ta.
tsawa takuma buga mata
"Miko min maganin da ta turo ki ki barbad'a min, ki koma ki ce mata malamin ta ya fad'i."
kai Feeryal ta girgiza cike da tsoro ta ce
"Ba.ba..babu komai dama um Ya wannan ne um Ya wannan."
gaba d'aya ta mance sunan shi da taji Ajmal ya fad'a da kuma yadda Miemie take kiran sa da shi. sai fad'in Ya wannan ta ke.
Mommy ta ce
"Da kyau mana bakuyi sammanin asirin ku zai tonu ba, dole ki rika kame-kame, hatsabibiya bakar ashana sai naci uwar ki a nan kafin naje na sami wacce ta turo kin."
"Abdurrahim."
taji an rad'a mata a kunnen ta, ido ta rumtse ta had'iye miyau da kyar, muryar Chuchu tajiyo a kunnen ta tana rad'a mata sunan nashi, kana ta bud'e ido da sauri ta ce
"Ya Abdurrahim ne ya ke kiran Ameerah."
kirji Mommy ta buga ta ce
"Waye yayan naki nashiga uku!
to bari kiji in gaya miki kar ki sake nasake jin kin dangana min d'a da yayanki dan shi ba yayun aljanu bane,
kar ki sake nasake jin kin kira min d'a da yaya shi ba yayanki bane,
kije can ki nimi yayan ki, kul nasake jin kin kira shi da yaya sai na dirza bakinki ya yi jini,
wuce ki bani guri shegiya mayyar aljana."
Su Miemie da suke d'aki da su Ameerah har suna rige-rigen fitowa suga wacce Mommy take wa bala'i.
Miemie ta tsaya sororo tagama mancewa tare suke da ita tana jiranta a waje.
jiki na b'ari Feeryal ta nufi kofa sakamakon kuma buga mata tsawa da Mommy tayi, gaba d'aya ta birkice har tana karo.
Sumayya tayi saurin cewa
"Gurin Miemie kika zo gata nan fa."
bata ko waiga ba tuni tayi waje jiki na rawa Feeryal bakaramin tsoron tsawa da fad'a take ba nan da nan yake birkitata ta fice hayyacin ta.
Ameerah ta buga dogon tsaki
"Mssttt na rantse na tsani yarinyar nan bansan me yasa Daddy yaki koran ta ba."
Miemie ta bita da sauri Feeryal bata tsaya ba sai da ta fice a farfajiyar side d'in gaba d'aya.
ta tsaya tana maida numfashi kamar wacce tayi tsere.
Miemie ta karaso da sauri murya a raunace ta na fad'in
"Yi hakuri Feeryal kin gaji da jirana ne kika shigo ko, ai dama tafiya kikayi abinki baki shiga musu side ba bare ayi miki rashin mutunci,