Showing 1 words to 3000 words out of 58144 words
[09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️*
*°S-Reza✍️*
_First class writers association_
_My Whatsapp chanel_
*JAN HANKALI!*
Abarwa rai abun da take so shine daidai a gareta koda kuwa wannan abun bashi da inganci a tare da ita. Shin kun taɓa ganin yadda ake yin soyayya da rai bada zuciya ba? Shin da gaske idan aka hana rai abun da take so ana iya samun matsala!?. Labarin Abarwa rai labarin soyayya ne mai ɗauke da abun mamaki da kuma kuskuren so. Ina wanda suka karanta littafin Amera da Adam? Ina fatan dai baku manta da wacece Haura ba, wacce take zaune a gidan su Adam da Amera bayan ta musulunta kuma ta rasa gaba ɗaya iyayenta. To ina muku albishir cewar labarin ta ne da wani malamin makarantar su. Shin yaya zaman Haura a gidan su Amera da Adam? Shin Adam na sonta da gaske? Idan haka ne Amera zata yarda? Muje zuwa cikin labarin domin jin yadda zata kasance!.
*GARGAƊI⚠️*
Kuskure ne yin amfani da wani sashe daga cikin wannan labarin ba tare da neman izini ba. Wannan littafin ƙirƙirarran labari ne, ban yi domin cin zarafin wani ko wata ba, idan yayi daidai da labarin ka/ki to arashi ne.
_Bismilahi rahamanun Rahim!_
*ABARWA RAI!*
*Chapter 1️⃣*
Da hanzari ya fito daga cikin ɗakin nasu yana gyara zaman hular kansa alamun dai sauri yake yi sosai. Yana ƙarasowa cikin palon ya saki murmushi ya nufo gurin da matar tasa take zaune tana jiran fitowar tasa. Ya na zuwa kusa da ita ya ce "Yauma na makara baki tashe ni da wuri ba, sauri nake yi sai na dawo" Ya manna mata kiss a koshi bai jira komai ba ya nufi hanyar barin gidan. Binsa tayi da kallo har ya kama ƙofar palon zai buɗe tayi ƙarfin halin faɗin "Yauma ba zaka ci abinci ba kenan ko?" Ta faɗa da wata murya mai nuni da rashin jin daɗin hakan. Juyowa yayi ya kalleta ya ce "Abinci kuma, kin duba lokaci kuwa, kiyi hakuri idan na dawo zanci nayi alƙawari" ya ƙarasa yane buɗewa ya sa kai. Ya buɗe kenan zai fita ta sake cewa "Ga wayarka ka manta da ita" ta faɗa tana miƙewa ta nufo gurin da yake riƙe da wayar fuskar tata a haɗe na rashin jin daɗin abincin da ta sha wahalar girkawa domin sa amma a banza. Da sauri ya fara shafa jikinsa yana mamakin yaushe har wayar tasa tazo palo shida yasan a ɗaki ya ajiye abarsa. Hannu yasa ya amsa bai tsaya cewa komai ba ya bar gidan harda haɗawa da gudu. Yana zuwa ya buɗe motar ya shiga ya bar gidan da gudu domin kuwa yayi latti. Saida taga tafiyarsa kafin ta shafa ɗan ƙaramin cikin jikinta sannan ta dawo tana addu'ar Allah ya ƙara tsare mata mijinta, idan akwai abun da yake ɗauke masa hankali akan komai Allah yayi masu maganin ko menene. Gaba ɗaya ta kasa gane masa a cikin wannan sati ɗayan. Ba haka ya saba mata ba, a kwai abun dake damunsa, kuma ta dubu wayarsa bata ga komai ba. Zama ta yi a palon ta kunna kallo tana yi tana danna waya. Habib na isa school ɗin har dalibansa sun gama cika class ɗin nasa, shida yake zuwa da wuri domin kawai duk ɗalibin da ya ƙara ko minti ɗaya ne sai dai ya koma gidan babansa amma yau shine ya makara. Hakan yasa bai ko bi ta ofishin sa ba ya shiga cikin ajin da zai koyar ɗin. Yana shiga suka tashi suna gaida shi ya ɗaga musu hannu yana raba idonsa a cikin ajin. Yana satar kallon yadda ɗaliban suke kus-kus kuma yasan akan makarar da yayi ne. Yau sau biyu zaiyi koyarwa na karfe takwas ɗin safe zuwa tara da rabi da kuma na yamma karfe huɗu. Hakan yasa yake ta addu'a a ransa cewar Allah yasa duk tana cikin wannan lokutan na sa. Saidai haka ya gama koyarwar safe bai ganta ba, hakan yasa ya gane bata da ajin safe sai na yamma. Bayan ya kammala ya koma ofishin nasa ya dafe kai yana ta tunani. Bai san yaya zanyi da wannan yarinyar ba, karfi da yaji ta saka masa tunaninta na dole, gashi yau bata zo ba duk yabi ya damu, sai ya tsinci kansa da addu'ar Allah dai yasa lafiya lafiya take. Ada idan yana da koyarwar sau biyu a rana to idan ya gama na safe gida yake komawa sai kuma yamma ya dawo, amma yau tsabar zumudi sai ya ke jin idan ya bar school ɗin yaje gida zai iya ɓata lokaci, hakan yasa ya fita ya sayo abinci ya dawo ofis ɗin ya zauna yaci, sannan ya miƙe ya ɗan shiga zagawa a cikin school ɗin yana kallon yadda dalibai wasu na fita wasu na shigowa, wasu kuma a zaune. Kusan duk inda ya wuce sai sun bishi da kallo domin kowa yasan wulaƙancin Malam Habib.
Misalin ƙarfe huɗu ya shiga cikin ajin ya ɗaure fuska babu alamar annuri ko kaɗan. Idonsa ne ya sauƙa a kanta tana sakar masa murmushin nan nata mai tafiya da imaninsa, bai san lokacin da tari ya sarƙe shi ba. Yan aji dai sun zuba masa ido ganin ya tsaya shi bai shigo ba kuma bai fita ba. Tana zaune a inda ta saba zama wato kujerar gaba. Bayan sun gaida shi ya amsa ya ƙarasa gaban allun karatun ya fara rubutu yana yi yana satar kallonta ita kuwa sai murmushi takeyi. Yauma sanye take da doguwar riga baƙa samfarin abaya, kanta babu kitso tana yafa ɗan kwalin a kanta ba tare da ta ɗaure ba. Juyowa yayi zai fara jawabi sai dai abun da ya gani ne yasa ya shiga wani jawabin da bashi yayi nufin yi ba. Hakan yasa ajin ya cika da surutu suna tambayar lafiya kuwa Malam yake yau. Kaman yadda ta saba masa ƙafafuwanta ta shiga ware masa dukda cewar akwai dogon wando a jikinta amma hakan da tayi yasa ya rasa control ɗin sa. Gyaran murya yayi ya ce musu yana zuwa. Ofis ya koma ya ɗauki ruwa yasha ya dafe kirji yana jin wani irin abu na jansa game da yarinyar. Babu abun da yake buƙata kaman ya jita a jikinsa kaman yadda ta sabar masa, bai taɓa yin zina ba amma yana jin tabbas zai iya yi akan wannan yarinya domin yana jin hakan a duk lokacin da ya haɗa ido da ita. Komawa ajin yayi yaci gaba da bayani har lokacin tashi yayi yanayinsa bai sauya ba. Ofis ɗin ya sake komawa yana addu'ar Allah yasa yau ma ta biyo shi ciki, da tabbas yadda yake ji ɗin nan akanta komai ma zai iya faruwa. Ya kai minti biyar amma bata shigo ba hakan yasa ya fito ya nufi cikin ajin nasu yana tafiya a hankali domin yasan ba zata iya tafiya ba har sai ganshi. Yana shiga class ɗin kuwa ya sameta zaune ita ɗaya da alamar itama shi take jira. Tana ganinsa ta mike tsaye tana kwallonsa cikin ido. Da Karfi ya haɗiye yawun bakinsa yana ƙarasa kusa da ita. A hankali ta ce Sir" yayi saurin ɗora hannunsa akan leɓenta ya ce "Shiiit" yana jin wani irin abu na na jansa zuwa gareta. Sai ta lumshe ido ta buɗe a hankali, hakan yasa bai san lokacin da ya haɗe bakinsu ba. Izuwa lokacin babu kowa a makarantar har duhu ya fara yi. Haka ya shiga kissing dinta har ya rabata da rigar jikinta ya kwantar da ita a ƙasar gurin duk hankalinsa naga abun da ransa ke so. Ita kanta ranta na son abun hakan yasa take ta bashi haɗin kai, babu abun da ke fita sai nishin su. Dogon wandon nata ya zame shima ya cire nasa ya mata rumfa ya fara ƙoƙarin cika umarnin ziciyoyinsu. Har ya kusa cimma burin ran nasa ya jiyo muryar mai gadin makarantar yana tambayar waye a ana. Hakan yasa ya tsaya daga yunkurin da yake yi, jin alamar ana zuwa ne yasa ya rufe mata baki da hanci kuma ya danneta domin ya tsayar da wannan nishin da take yi. Sosai take murƙususu domin bata samun damar shaƙar numfashi kasancewar har da hanci ya toshe mata, shi kuma yaƙi sakar mata hanci domin kar tayi magana akama su. Daidai lokacin mai gadin ya turo kofar ajin yana hassakawa da fitilar sa mai hasken gaske. A wannan lokacin ne kuma take shura ƙofa hakan yasa ya haɗe ƙafafun nata da nasa ya danne yana ƙara matseta a ƙasan. Idanunsa suyi jaa sai addu'a yake a ransa akan kar a kama shi. Haka mai gadin ya gama duba ko'ina kafin ya jawo ƙofar ajin ya fita. Yana fita Habib ya ɗaga Haura yana mayar da wandonsa da ya zame duk ya rikice. Sai dai me ganin batayi motsi bane yasa ya shiga kiran sunanta "Aisha Adam" ya kira sunan a hankali. Jin shiru yasa ya sunkuyo da sauri yana ɗagota jikinsa yana taɓa ta. Amma ko alamar numfashi babu a jikinta, sai ma wani langwaɓewa da take yi alamun bata numfashi. Cikin tashin hankali ya sake jijjigata yana kiran ta, lokaci ɗaya wani irin tsoro ya shigeshi da ya aiyana ko dai mutuwa tayi. Sai lokacin yake tuna yadda take ta murƙususu tana shure-shure amma yake ƙara danneta. Rigarta ya fara ƙoƙarin mayar mata, sai wandon da ya zame mata, gaba ɗaya ya fita a cikin haiyacinsa ya rasa me zaiyi. Fuskanta ya sake kalla ya ganta fayau sai ya tashi da sauri domin yaje ofis ɗin sa ya ɗauko ruwa ya watsa mata ko suma tayi. Haka ya shiga ofis ɗin ya ɗauko sauran ruwa a gora ya fito. Saidai yana fitowa daga ofis ɗin nasa mai gadin nan ya haske shi da fitilarsa yana tambayar waye anan. Lokaci ɗaya Habib ya saki robar ruwan tsabar tsoro ya rasa mai zai ce , kamar ya kwaɗa ihu ya fita a guje. Amma haka ya daure ya ce "Emeka nine, barci ne ya ɗaukeni a ofis sai yanzu na tashi" ya karasa maganar a rarabe wanda kana ji kasan ba'a cikin natsuwarsa yake ba. Emeka mai gadi ya ce "A a Malam Habib ne kika daɗe har wannan lokacin baki tafi gida ba?" Habib ya ce "Barci ne ya ɗauke ni" yana faɗa yana bin Emeka ɗin izuwa waje. Emeka ya ce "Ina ta jin motsi ne ta cikin wancen ajin yasa take ta dubawa kasan yaran nan wasu sai su ƙi tafiya ɗakunansu sai zauna anan har safe. Habib ya ce "Um um haka ne" haka Emeka keta zuba masa surutu har suka zo bakin get. Shi dai sai leƙe ta ya keyi har ya shiga motar ya kasa kunnawa kusan minti biyu Emeka ya leƙo yana sanar dashi cewar zai rufe get ɗin. Yana tafiya a mota shi ɗaya yana tunani ga wani zufa da yake karyo masa. Jin ana kiran sallar magriba ne yasa ya kalli agogon hannunsa yaga shida da arba'in. Sai lokacin ma ya tuno ya bar wayarsa a ofis ɗin sa ga hularsa da itama ya barota a ciki. Dole ne sai ya koma school ɗin nan to amma ta ina zai bi ya shiga makarantar bayan babu hanya dole sai ta get. Kasa tsayawa yayi ya nufi gida duk a rikice.
Lokacin da ya shiga palon Nadiya ce zaune tayi wankanta sanye da atanfa riga da sket, cikin nan ya ɗan taso kaɗan ɗan wata biyar. Kallo ɗaya tayi masa gabanta ya faɗi, hakan yasa ta mike da sauri ta na faɗin "Beb lafiya dai ko?" Ta faɗa tana kama hannunsa. Habib ya ɗan saki fuska kaɗan ya ce "Kawai bana jin dad'i ne, tun ɗazu kaina ke ciwo barci ma nai tayi a school ɗin" ya ƙarasa yana riƙe kansa. Nadiya ta ce "Aiya sorry, bari na haɗa maka ruwa kayi wanka sai kaci abinci kasha magani, amma ina hularka ko a mota ka barota?" Ta tambaya kuma ta bashi amsar da zai bata, ta ƙasara duk a tsorace domin tun auransu bata taɓa ganin lokacin da ciwon kai ya mayar da shi haka ba. Habib yayi ƙarfin halin faɗin "Eh tana mota" ya ɗora cewar "ki bari kawai idan na kwanta ma zai tafi" ya faɗa yana zama a kan kujerar palon. Da sauri ta sake kamo hannunsa da ta sake ya mike suka nufi ɗakin sa, ta shiga toilet ta haɗa masa ruwa mai zafi. Koda ta fito ta samu ya dafe kai yana tunani har bai ma san ta fito ba, ta ɗan kafe shi da ido na minti ɗaya sannan ta ce "Beb me ke damun ka ne, anya kuwa ciwon kai ne kawai?" Firgigit ya dawo daga tunanin ya miƙe tsaye ya ce "Na'am to zanje ina ne?" Ya haɗa maganar duk a rikice. Nadiya ta ce "Toilet zaka shiga ruwan wankan na ciki" Sai ya nufi toilet ɗin ba tare da ya cire kayan jikinsa ba. Zama tayi a ɗakin ta na ta nazarin yanayinsa, to wai me ke faruwa da shi ne, ina yake yawan zuwa yanzu ne, ko dai ya fara shaye-shaye ne, to amma bata ji warin komai a jikinsa ba. Shekara daya da wata ɗaya kenan da auransu, bata taɓa ganin irin wannan sauyin daga garesa ba, hasali baya ɓoye mata komai nasa, bashi da gurin hira sai gida, amma a cikin wannan satin gaba ɗaya ya sauya mata. Tana zaune shiru bai fito ba, sai ta tashi ta koma ɗakinta ta ɗauko masa maganin ciwon kai ta dawo ɗakin har lokacin bai fito ba. Ta sake fita ta haɗo masa abinci da ruwa ta kawo har lokacin bai fito ba. Sai ta shiga fiddo masa da kayan da zai saka na barci. Har ta gama bata ji alamar zai fito ba domin daga inda take tana jin zubar ruwa. Tashi tayi ta nufi toilet ɗin tana zuwa ta murda murfin ta leƙa. Ƙamewa tayi a tsaye tana kallon sa. Tsaye yake bai ko cire kayan nasa ba ya sakarwa kansa ruwan sanyi bayan ga na zafi da ta haɗa masa a gefe. Mamaki ne ya kamata gami da tsoro ganin bai ma san ta buɗe ba kansa na ƙasa. Da ƙarfi ta ce "Habib" ai kuwa ya ɗago yana sauke ido a kanta. Cikin kuka ta ce "Wai me ke faruwa ne, meye matsalar ka, shin ban kai ka faɗa min abun dake damun ka ba ko, na sani dama tun ba yanzu ba kana ɓoye min abu amma babu komai laifi na ne da nake son naji damuwar ka. Tana faɗa ta juya ta bar ɗakin tana kuka. Habib kuwa kayan jikin nasa ya cire ya ɗaura tawul ya fito ya saka wasu kananan kaya jinss da ƙaramar riga ya fito falo. A tunaninta hakuri yazo bata kuma ya faɗa mata abun dake damun nasa, hakan yasa ta sake haɗe rai tana juya masa baya. Amma sai taga ya nufi hanyar waje. Ya ce "Ina dawowa yanzu" yana faɗa ya kama ƙofar ya buɗe ya fita. Ta bisa da kallon mamaki, wannan fa abun nasa ya fara wuce tunaninta, ina kuma zaije bayan sallar Isha, gashi ko abincin ma ba lallai yaci ba, bare ma yayi Sallah. Da sauri ta leƙa shi ta window taga ya fita a ƙafa. Ɗakinsa ta koma taga komai a yadda ta kai masa su, ko maganin ma bai samu ya sha ba. Lokacin ne kuma hankalinta ya sake tashi da wannan sabon al'amarin. Shi kuwa Habib gaba ɗaya hankalinsa ne ya kasa kwanciya, yana jin dole ne ko ta kan katanga ya haura yaje ya duba yarinyar nan, idan mutuwa tayi ya san yadda zaiyi da ita, idan kuma suma tayi ya farko da ita ya kaita har ƙofar gidan su. Lokacin da ya ƙaraso bakin makarantar ya sallami mai mashin ɗin da ya kawo shi, sai ya tsaya yana duba ta ina zai iya bi ganin katangar tayi tsayi ga kuma irin wannan wayar wutar nan a zagaye jikinta...✍️
S Reza... Sabon labarin mu kenan, mai taken abarwa rai abun da take so, farko kenan kuma soman taɓi. Kude ku kasance da S Reza domin jin yadda zata kaya.
[09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI❣️*
*°S-Reza ✍️*
_First class writers association_
*Chapter 2️⃣*
Har bakin katangar ya ƙarasa ya na shiga duba wa ko zai iya samun ƙaramar hanyar da zai iya kamawa ya haura amma babu dama. Haka ya dinga zaga wa har ya zagayo ta gaban get ɗin, ya tsaya daga nesa yana jin gabansa na faɗuwa kar Emeka ya hango shi. Haka ya sunkuya ya na tafiya a duƙe kamar ɓarawo har ya ƙaraso bakin get ɗin. Nan ya tsaya ya na sauke ajiyar zuciya. Kama bakin get ɗin yayi ya leƙa sai ya hango ƙofar ɗakin Emeka a buɗe amma baya gurin. Hakan yasa ya kama bakin get ɗin kenan ya ga hasken fitila ta haske masa ido, hakan yasa yayi saurin sakin get ɗin sai gashi a ƙasa tim ya faɗo, kuma bai tsaya ta zafin da yaji ba dalilin jin muryar Emeka ɗin da yayi ya na nufowa gurin da sauri domin ganin waye. Da gudu yasha kwanar makarantar yana jin yadda bayansa ke masa zafi. Bai tsaya a nan kusa ba domin yasa zai iya bin bayansa. Sai da yayi nisa kafin ya samu guri ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya. Bayansa ya dafe ya na haki sai kuma ya riƙe ƙirjinsa ya na jin takaicin kansa. Take zuciyar sa ta shiga aiyano masa suffar Haura da ya gani yau, ya na yin ƙirjinta da yaja hankalinsa yanzu gashi baiyi komai ba yasa kansa a matsla, alhalin yana da matarsa ta Sunnah a gida halak ɗin sa da zai iya yin komai da ita. Take ya shiga tsinewa zuciyarsa da ta raya masa wannan masifar da bai ma kai gayi ba kenan. Haka ya kama hanyar gida a ƙafa yana tafiya ya