Showing 48001 words to 51000 words out of 58144 words
haka ne za'a ɗaura miki kwananan" Haura ta yi dariyar ƙarfin hali ta ce "Daddy nifa bana sonka da aure, ga wanda nake so, kuma ni shi kaɗai nake jin zan iya aura, saboda haka kawai a bar maganar wani aure ga wanda nake so shi kadai". Ta ƙarasa tana zama kusa da shi. Adam ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya ji ƙirjinsa yayi masa nauyi kamar an tara masa abu a gurin, ya sunkuyar da kansa ƙasa ya dafe kan. Amera ta taso tana masa sannu, itama Haura ta fara masa sannu. Ya ɗago kai har idanunsa sunyi jaa sosai. Ya kalli Habib ya ce "Tashi ka zauna" Habib ya zauna yana kallon Adam da gaba ɗaya yanayinsa ya sauya.
Anan palon aka tsayar da magana akan Habib ya turo magabatansa nan da juma'a mai zuwa. Amma Haura tayi caraf ta ce ina sai dai su zo gobe. Shima Habib ɗin ya ce goben yayi masa zasu zo. Haka aka bari akan gobe zasu so ɗin. Haura ta rakashi har mota ya shiga suka yi sallama akan yana zuwa gida zai kirata. Suna fita Adam ya kwantar da kansa a kan kujerar da yake zaune yayi shuru. Amera ta zo kusa da shi ta ce "Honey ya kamata musan ina wannan yarinyar taje tsawon wannan lokacin, domin ni ina tunanin tana tare da shi ne fa, sun shirya komai ne, ku..." Adam ya ɗaga mata hannu ya na tashi ya bar palon.
Habib kuwa gidan Mama ya wuce darigt, yana zuwa suka gaisa ta tambayi Nadiya da jiki ya amsa. Ta ce "Sai kuma naga Zainab ta dawo wai kace ta dawo gida, bayan kuma a kasan jikin Nadiyar dole sai da wani a kusa da ita, domin ta shiga watan ta?" Habib da har ya manta da cewar ya koreta ya ce "Ni ɗin Mama, ƙarya take min ni bamuyi haka da ita ba. Mama ta ƙwadawa Zainab kira tana zuwa ta ce "Kika ce shine ya ce Ki tafi gida ashe ƙarya kike masa, wai mai yasa Zainab ba kya son zaman lafiya ne?" Zainab ta kalli yayan nata suka haɗa ido ta ce "Allah Mama shi ne ya ce na dawo gida, ko ciki bai bari na shiga ba" Adam ya ce "To naji yanzu kizo mutafi" ya na faɗa ya miƙe domin bai so a cigaba da maganar, kuma maganar ma da yazo da ita ya fasa. Haka suka tafi da Zainab ya sauketa a ƙofar gidan, shi kuma ya koma da matarsa baya. Gidan kawunsa ya je ya faɗa masa abun da ya ke so yayi masa na zuwa gidan su Haura gobe. Kawun ya kalle shi da kyau ya ce "Tambaya ko dai ɗaura aure?" Habib ya ce "Kawu gaba ɗaya ma duk wanda a kayi?" Ya ce "To ai ita mamar taku bata min maganar ba, ko ita ce ta aikoka, domin yau ma naje gidan, Sannan kuma har yaushe ma kayi auran na ka, shekara ɗaya ne fa gaba ɗaya habibu, kuma gashi yarinyar nan ciki ne gare ta, da ka bari ta sauƙa lafiya ko?" Habib ya dage shi dai kawai aje. Hakan yasa ya ce zai yi magana da Mama amma Habib ya ce baya so ya ta sani. Jin hakan yasa kawun nasa gane cewar a kwai iskanci a lamarin. Sai kawai ya ce "Allah ya kaimu goben". Da haka ya koma gida. Ya na shiga ya samu babu kowa a palo, hakan yasa ya shige ɗakinsa ya cire manyan kayan da ya saka ya sa kanana ya fito palo yana nemo number Haura. Dama welcome back yayi nan take ya cireta daga blocking ɗin da yayi mata ya kirata. Zainab ta fito daga ɗaki ta ce "Yaya Nadiya fa har yanzu jikin ne, ni sai nake jin kamar aihuwa ce". Ya ce "To kije ki taimaka mata mana, ko ni kike so naje gurin aihuwar?" Ta ce "To bani waya na kira Mama, ni na manta tawa a gida?" Habib ya mike tsaye kaman zai mareta ya ce "To ke meye amfanin ki da ba zaki taimaka mata ba har sai kin kira Mama a cikin daren nan, to ba zan bada wayar ba, kuma karki kuskura ki kira Mama a daran nan na faɗa miki?" Zainab ta ce "Wai yaya lafiya kuwa kake, ko ma me Nadiya tayi maka ai ciwo ba wasa ba, kuma ma na ce maka aihuwa ce fa, Dan Allah yaya ka zo ko..." Marin da ya kai mata ne yasa ta bar gurin da gudu ta koma ɗakin da Nadiya take kwance.
Zainab na barin gurin Haura ta ɗaga kiran suka fara hira. Bangaren Nadiya kuwa sosai ta fita a haiyacinta, ita kanta Zainab ta tsorata kaman wacce zata mutu irin wannan shure-shure, hakan yasa itama ta fashe da kuka domin bata san me zata iya mata ba. Ganin dai abun ba na ƙare bane yasa ta sake zuwa palon ta same shi yana waya harda dariya abunsa. Ta na kuka ta ce "Yaya asibiti Nadiya zata mutu wallahi!" Ta faɗa da wani irin kukan da sai da gaban Habib ya fadi, ya danyi jim kaɗan kamar zai fahimce ta, sai kuma ya ce "Na rantse da Allah Zainab idan baki bar nan ba zan mugun saɓa miki, wai ina wasa dake ne, dan ubanki ke ba zaki iya taimaka mata ba, ba zaki tsaya tare da ita ba kina mace wawiya kawai". Zainab ta juya izuwa cikin dakin ta na tafiya tana waigawa tana kallonsa, ita dai bata ga laifin da mace za tayi har a shareta a irin wannan halin ba. Shi kuwa ta cikin wayar take tambayar sa cewar ya yi wa iyayen nasa magana, ya ce ai gobe suna hanya. Ta ce "Sir ko nazo na taya ka hira ne?" Ya ce "Da kuwa naji dad'i wallahi?" Ya faɗa ya na ce ko wasa take yi. Ta ce "Tom bani minti ɗaya?" Yayi dariya ya na cewa ya bata. Minti ɗaya kuwa ta ce ya shigo ɗaki tana ciki ta na jiransa. Yayi dariya har yana riƙe ciki. Ya ce "To ai ko aljana ce ba zata iso yanzu ba, bare kuma ke" Haura ta ce "Wai kana ce da wasa nake ne, ka shigo ina ciki a kwance?" Habib ya ce "Ni ba wannan ba, wai dama Daddy ba shi ne ya haife ki ba, kuma dama shima sonki yake yi shi zai aureki?" Ya tambaya domin shi tun ɗazu abun ya tsaya masa a rai. Haura tayi shiru tsoro na son kamata, har yaushe ya samu damar yin wannan maganar. Jin shiru yasa ya ce "Hello" har zai sake cewa wani abu yaga an bude ƙofar ɗakin nasa an fito. Duk da a zaune yake amma sai da yayi tsalle sama ya dawo kan kujerar yana yin wurgi da wayar hannunsa. Ta ce "Meye haka? Tun ɗazu fa nazo ina ciki ne fa" ta faɗa ta ƙarasowa kusa da shi. Habib dai har lokacin a tsorace yake gabansa na faɗuwa, haka yana ji ta zauna a kusa da shi sai kuma ta kama hannunsa. Ɗaki suka koma suka cigaba da hira, ta sake yin amfani da wannan damar ta rufe masa baki. Sai kusan karfe sha biyu kafin ta bar gidan.
Bangaren su Nadiya kuwa sai kusan sha biyun suma ciwon ya lafa, hakan yasa Zainab dole ta kwanta a ɗaki, ashe ba aihuwa ba ce, kawai abun da ta gani ne ya furgitar da ita. Cikin dare ta miƙe ta shiga toilet da ƙyar domin sai da ta dafa bango. Kuma har lokacin jiri na kamata, amma kaman yadda ta sabarwa da kanta haka ta ɗauro alaula ta fara Sallah a zaune. Sosai take ta yin Sallah tana kaiwa Allah kukanta, domin tabbas ta yarda cewar Haura ba haka ta bar Habib, bayan ta idar taji kamar ta je ɗakinsa ta duba shi amma ba zata iya ba. Maganin da aka basu a asibiti ma yana cikin motar basu kwaso ba. Haka ta kwanta tana ta tunani, tana tuna to kenan gurin boka taje aka yi masa a siri ko me, kenan dai da gaske ne abun da ya faɗa akan ta. Dama ace mutuniyar kirki ce, da ita da kanta zata bari Habib ya aureta saboda irin son da yake mata, amma irin waɗannan matan masu zuwa gidajen bokaye ba'a taɓa yarda da su. Kuka take yi sosai, wai yau itace bata da lafiya aka haɗa Bebb zuwa kusa da ita.
Washegari Zainab bata da class sai na yamma, hakan yasa ta tashi da wuri ta ɗora musu abin kari. Bata gama ba sai kusan takwas da wani abu. Ta jera musu a gurin cin abincin tannan ta shiga ɗaki ta kira Nadiya. Haka ta fito daga ɗakin sai da Zainab ta kama ta domin da ƙyar take tafiya, cikin yayi ƙato yau ko gobe. Ta ce "Ina Habib ɗin?" Tana rufe baki sai Gashi ya fito waya a kare kuma cikin shirin fita saboda haura ta ce masa yazo ya Kaita school karfe tara take da takarda, ya ce zai ci abinci ta ce yazo zata girka masa, hakan yasa ya shirya da sauri ya tito. Zainab ta ce "Yaya ina kwana?" Ya ɗaga mata hannu alamar amsawa. Nadiya ta ce "Bebb!" ta faɗa a hankali, itama ya ɗaga mata hannu ya nufi hanyar fita. Zai buɗe ƙofar kenan yaji an turo an shigo. Da sauri ya cire wayar a kunnensa yana kallon mai shigowar. Itama Nadiya kallon ƙofar palon tayi, Zainab ma gurin take kallo domin da ƙarfi aka turo ƙofar. Mama ce ta shigo sai kawunsa biye da ita a baya. Da sauri ya ce "Mama ina kwana?" Ya faɗa a rikice. Ta ce "Ban kwana ba, koma ka zauna?" Ya ce "Mama bari na dawo sauri nake yi ana jira na nane, wallahi yanzu zan dawo?" Mama ta ce "Wallahi idan baka koma ba sai na ɗauke ka da mari wawa kawai mara hankali". Habib ya riƙe Kamatu yana kallon Mama jin batun mari. Ta ce "Ko Ba zaka zauna bane?" Ta faɗa da tsawa. Ya koma ya zauna. Ta kalli Nadiya da hawaye suka wanke mata fuska. Ta ce "Wai me ke faruwa a gidan nan ne? Ke Nadiya dake nake, nasan ke ba zaki min karya ba, me kika masa?" Nadiya ta fashe da kukan da tun ɗazu take son yi, tana jin kamar ta haɗiye zuciya ta mutu zaɓar zafin da take ji. Ganin dai kukan nata yaƙi tsayawa ne yasa ta dawo da kallonta ga Habib ta ce "Ne ke faruwa a cikin gidan ka? Wacce yarinya ce kace aje tambaya maka auranta yau?" Gaban Nadiya ya faɗi jin batun aure, take kukan nata ya tsaya ta ƙurawa Habib ido da yake ta cika yana batsewa. Mama ta daga masa tsawa. Ya ce "Eh Aurenta zanyi Saboda ina sonta...📝
S-Reza...
[09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*
*FCWA*
*20*
Mama ta ce "Saboda kana sonta?" Habib ya ce "Eh Mama ina sonta kuma yau muka yi da iyayenta akan zan tura aje gidan su a tsayar da magana" Mama ta kafe Habib da ido ta rasa me ma zata ce masa, sai ta dawo da kallonta ga Nadiya da itama shi take kallo. Ta ce "Habibu Lafiya kuwa kake?" Ya amsa da cewa "Mama lafiya nake mana, me kika gani?" Kawunsa ne ya ce "A ina yarinyar take, kuma yaushe kuka haɗu da ita da har za kai nema maka aure ba tare da anyi bincike kanta ba?" Habib ya ce "A makarantar da nake koyarwa muka haɗu da ita, kuma har gidan su na sani zan raka ku idan zaku tafi sai muje tarw". Mama ta ce "To ba zaka aureta ba, na ce ba zaka aureta ɗin ba, muddin nice na haife ka to wallahi ba zaka ƙara aure yanzu ba, saboda baka da hankali kalli halin da matarka ke ciki, amma kai tunanin ƙara aure kake yi, ko wani abun ta yi maka wanda bai dace ba shine za ka yi aure domin ka rama, to ban yarda ba na faɗa maka". Habib ya ce "Nifa ina sonta, kawai kiyi hakuri amma dai sai na aureta wallahi, zuciyata ta kamu da sonta gaskiya ayi hakuri a bar wa rai abun da yake so?" Ya faɗa ya na mikewa tsaye dalilin kiransa da take ta yi. Daga Mama har kawun da Nadiya da Zainab sake baki sukai suna kallon sa har ya bar palon. Zainab ta ce "Mama Allah yaya tsoro yake bani yanzu, haka fa jiya ya dinga min ihu kamar zai mareni". Nadiya kuwa marar ta ce ta ƙulle tun ɗazu da taji batun aure, hakan yasa ta kasa cewa komai sai fama da take yi da marar. Zuciyarta na raya mata yanzu kuma auranta zai yi, har yake iya faɗin irin wannan maganar a gaban mama, tabbas wannan abun azumin ne, ta ƙara yarda da cewar Haura asiri tayiwa mijinta, hakan yasa ta ƙara jin irin radade na ratsa ta. Ganin abun yafi ƙarfinta ne yasa ta kurma ihu tana durƙushewa a gurin. Wani irin azaba ne ya fara ratsata wanda bata ma san cewar ihu take yi ba. Sunan Allah kawai take kira tana kuma dafe bayanta ta na fadin "Innalillahi Mama baya na, zai tsage mama, mara ta, cikina, Mama ki taimaka min Zainab, mara ta mama Waiyoo Allah innalillahi wa inna'ilaihi rajiun". Lokaci ɗaya palon ya rikice da salati suna kama ta. Mama ta ce "Zainab je ki duba ko bai tafi ba ya kaimu asibiti da motar tasa kaman aihuwar ce ta zo". Zainab ta fita da gudu amma tana zuwa har ya bar gidan, haka ta dawo ta sanar musu. Dole Kawu ya fita ya samo musu mai dan sahu suka nufi asibiti.
*°ADAM*
Zazzaɓi ne mai ƙarfi ya riƙe shi tun jiya, hakan yasa bai ko iya fita ba yana ɗaki yana ta tunani shi kadai. Babu yadda Amera bata yi da shi ba akan yaje asibiti ba amma ya ce babu komai kawai ɗan ciwon kai ne zuwa an jima zai daina. Ganin yadda yake ta rawan sanyi ne yasa ta kira Khadijah ta faɗa mata. Ai kuwa ba'a fi minti goma ba sai gata tare da Najib duk hankalinsu a tashe. Suma babu yadda ba suyi da shi ba amma ya ce ba zai je asibiti ba. Haka dole Najib ya kira masa abokinsa likitan da suke zuwa asibitinsa. Nan take kuwa ya duba shi ya bashi magani ya saka masa ruwa, sannan ya bar sauran maganin da za'a dinga bashi. Da Najib ya tambayi abin dake damunsa sai ya ce kawai damuwa ne da gajiya da kuma yawan tunani, dan Allah kwantar masa da hankali koma me nene ke danun sa. A haka likitan ya tafi. Duk yadda Najib yaso jin abun da ya faru har ya shiga wannan damuwar Amera ta ce bata sani ba. A gidan suka uni har bayan sallar magriba, har ruwan ya gama shiga kuma babu laifi jikin nasa ya ɗan yi kyau amma har lokacin yana jin jiki. Gaba ɗaya a kusa da shi suka uni, daga Amera har Haura da su Khadijah, suna ta jansa da hira yana amsawa sama-sama. Ita dai Khadijah haka kawai bata son wannan haura ɗin, ko yanzu bata cika amsa mata magana, kuma tasan wannan ciwon bai wuce nasaba da ita ba, itama Haura ɗin da ta fahimci haka sai ta manta da ita, bata ko shiga sabgar ta. Washegari Haura ce tayi musu girki wanda ko kichin ɗin ma bata shiga ba, Amera dai yau sai bin ta da kallo take yi lokacin da take jere abincin. Sosai take nazarin yarinyar, tun da ta dawo take yin abubuwan kaman farkon zuwanta, karan farko da Amera ta zargi ko dai har yanzu bata bar yin tsafin bane, wata zuciyar kuma ta ce kodai wannan tafiyar da tayi cen gurin ƴan uwanta taje ne. Take Amera ta miƙe tsaye ta nufi gurin abincin ta buɗe tana kallonsa. Ta ce "Haura yaushe har kika girka wannan abincin?" Haura tayi wannan murmushin nata mai shigawa mutum rai ta ce "Kina barci lokacin da nayi" Sai kawai ta kawar da wannan maganar ta ce "Haura zo?" ta faɗa tana kamo hannunta. Haka ta jata har cikin ɗakin da Adam ke kwance.
Sosai Amera ta tausaya masa, tasan duk saboda yana son ta ne yasa wannan ciwon. Tabbas ta yarda yana son Haura, kuma zata taimaka masa domin dama tayi masa alƙawari. Suna shiga ɗakin Adam ya mike zaune yana binsu da kallon mamaki. Amera ta ce "Gashi nan a gaban ki haura sabo da yana sonki ne kwanta rashin lafiya, mutumin da ya mayar dake mutum lokacin da baki da maraba da dabba, mutumin da ya shiga damuwa da matsaloli duk saboda ke, wanda ya toshe kunne daga maganganun mutane akan ki ya riƙe ki, wanda ya bar..." Adam ya ce "Amera meye haka?" amma ta ɗaga masa hannu ta ce "Barni na faɗa mata ko ita wacece idan ta manta" ta cigaba da fadin "Ke duk duniya kina tunanin akwai wanda ya dace ki aura da ya kai Adam nagarta, yanzu kina da tabbacin masu zuwa auranki idan suka ji ke wacece zasu aura wa ɗansu? Haura wallahi muddin wani abu ya samu mijina zan nuna miki iyakar ki, nafi son mijina fiye da komai, ina baki shawara akan ki rabu da wannan mutumin domin ki rufawa kanki asiri, ba wai ina tallata miki mijina bane domin bana sonsa, ina son abun da yake so ne saboda irin halaccin da yamin a rayuwa" Amera ta ƙarasa ta na kuka mai karfi. Haura kuwa idanunta a ƙeƙashe sai dai tausayi sun baiyana a fuskar ta ganin irin kukan da Amera ke yi. Kaman zata yi kuka ta fara magana kamar ba ita ba da bata wani yin dogon magana a gaban su