Showing 45001 words to 48000 words out of 58144 words
Salim suka fita bayan sun ɗauki wayar ta. Marmarin ganinsa take yi, tayi kewarsa, ta matsu ta sake ganin sa. Wanka ta shiga bayan ta fito ta saka ƙananan kaya da hula ta fito ta shafe jikinta da mai, ta aiyana banbancin dake tsakanin garin Garuk da kuma nan inda take. Kallon makeken gadon ta tayi, da irin kayan da ke cikin ɗakin, ga A.C ga fanka, ga toilet mai kyau harda mashin ɗin wanke kaya, ga sabulai masu ƙamshi da gyara fata. Dariya kawai tayi tana jin gaskiya ba zata ma iya zama a garin Garuk ba kwata-kwata ko mai zai faru, gara ma ta dage ammi ta dawo nan da zama. Palo ta fito ta samu yaran ne kawai suna ta wasa abun su. Ta amshi wayarta ta samu guri ta zauna ta fara kiran Maryam. Ta na ɗagawa Maryam ta fara mata masifa da tambayoyi, Haura ta ce "Kizo gida ina gida" ta na faɗa ta kashe wayar ta na dariya. Bata dade da zama ba sai ga Adam ya fito. Yayi nufin yayi mata magana amma ya share kaman yadda Amera ta ce masa zata ji da komai. Haka tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita. Ta na zaune Maryam ta shigo gidan. Sosai suka sha hira, anan ne Maryam ke sanar mata da cewar ta godewa Allah ma an ɗaga exam ɗin yau kwana uku da farawa, badan haka ba da yanzu an gama. Babu yadda ba tayi da ita ba amma ta ce mata wani guri ta ce, ta shiga faɗa mata yadda Adam ya dinga sintirin zuwa gidan su da kuma makarantar su, harda tambayar ta gidan Malam Habib. Haura ta ce "Kin kai shi?" "To na san gidan ne da zan kai shi?" Ta faɗa da afusace. Haura ta ɗan yi dariya, ta tashi ta shiga kichin. Ganin babu komai yasa lokaci kaɗan ta haɗa lafiyayyar taliya da wake ta sha kifi, ta zubo musu ta haɗo da abun sha. Ta zo zata fita suka ci karo da Amera. Haura ta ce "Anty Maryam ce ta zo, shine nayi mana girki, ga sauran chen a ciki. Ta faɗa kamar a ɗan firgice. Amera ta ce "Ok tom, kin kyauta" ta faɗa ta shige kichin ɗin.
Washegari ta shirya ta tafi school bayan ta gama musu girki. Lokacin babu wanda ya fito a gidan, basu ma yi tunanin zata je school ɗin ba, sai da suka fito suka ga komai ta jera a dainintebul. Cike da wani mamakin Amera ke kallon abubuwan da aka dafa. Bata ce komai ba suka fara ci, amma dai tabbas ta shiga kokwanton, domin wani abun ma basu da shi a gidan, kuma ita bata ji motsin ta a kichin ɗin ba. Sai tayi tunanin ko ita ce ta sayo domin tana so. Koda Adam zai fita sai da ya ƙara tuna mata da maganar Haura. Ai kuwa ya na fita ta gyaran gidan ta hau karatun sabon littafin da ta saya jiya a gurin S Reza mai suna Tsinuwar uwa. Sosai labarin ke mata dadi, wanda bata san lokaci ya ja ba, sai da taga Haura ta shigo gidan. Haura ta zauna ta na kallon yadda Amera ke ta dariya. Ta ce "Anty wannan dariyar fa?" Ta tambaya. Amera ta ce "Please zo ki karanta min wannan littafin" Haura ta amshi wayar tana duba labarin. Ta ce "Anty kina son littafin wannan S Reza ɗin" Amera ta yi dariya kawai bata ce komai ba. Haura ta fara mata karatun, sai ga haura itama ta fara dariya, sosai suke dariya idan an zo gurin dariya. Duk abun da suke yi Haura an ankara da lokaci domin ta na lura. Hakan yasa sha ɗaya na yi ta ce ta gaji. Amera sai taji kamar da isa tayi maganar hakan yasa taji wani abu kamar na raini dai haka. Ta ce "Ina so zamu yi magana?" Haura ta ce "Tom Anty amma idan na dawo ko?" Amera ta ji ranta ya ƙara ɓaci ta ce "Yanzu" Ta faɗa a dake. Haura ta ce "Tom ina jinki anty?" Amera ta ce "Mai yasa kika ce ba kya son Daddy?" Haura ta ɗago da sauri ta kalle ta, sai kawai ta ɗan yi murmushi ta ce "Anty ke kin yarda ya aure Ni?" Ga ban Amera ya fadi, amma ta dake ta ce "Eh zan so domin yana sonki" ta faɗa a hankali. Haura ta ce "Anty Ni kuma bana sonsa da aure amma ina sonsa a matsayin Daddy" ta faɗa tana dariya domin ita har ranta bata son Adam da aure sai Habib. Lokaci ɗaya Amera ta ji wani abu ya tsurkuleta a zuciya, taji kaman ita kaman ba ita ba. Eh tabbas abun ya mata dadi, amma idan ta tuno da irin son da Adam ke mata sai abun ya bata tsoro. Amma kuma ta kasa samun natsuwa, ita ai ba tayi zaton Haura zata ƙi yarda ba, amma yanzu meye abun yi.
Adam kuwa ya na fita gidan su Amera ya fara zuwa kasancewar sunyi da Abba cewar idan har ta dawo shi zai zama wakilin haura wajen ɗaura auran, hakan yasa yaje har gida ya samesa. Sai da ya fara masu albishir da cikin Amera kafin ya sanar da abun da ya kawo shi. Abba ya shiga hamdala da Allah ya dawo da ita, sannan ya tambaye shi yaushe nei za'a ɗaura. Adam ya ce ya ɗan bashi zuwa nan da gobe za suyi magana da yarinyar. Haka ya bar gidan ya nufi gidan Najib, shima dai sai da ya fara faɗa masa maganar cikin kafin ya sanar da su dawowar Haura. Najib ya ce "Yanzu dai dole sai ka aureta ko?" Adam ya ce "Please bana son kana dawo da abun da ya wuce, Please ban ce ka min komai ba dan haka babu ruwanka. Najib ya ce "To batun cikin Amera fa, Kasan dai yadda take yi idan ta na da ciki ko?" Adam yayi saurin fadin "Aniyar ka ta bika, in sha Allahu ba zamuga wannan ɗabi'ar ba". Ya na faɗa ya bar gidan. Itama dai Khadijah abun da tace kenan amma dole suka zuba masa na mujiya. Koda ya koma gida ya samu Amera ita ɗaya a gida, kuma gata duk a sanyaye, nan dai ta faɗa masa yadda suka yi da Haura, amma bata ce masa bata so ba, ta ce dai sun fara maganar da ita. Ai kuwa sai Gashi yana fsrinciki harda godiya ga Allah. Nan ya shiga yi mata alƙawarin ba zai bata kunya ba, kuma tasa a ranta ita ce ta farko kuma ita ce ita ce itace. Haka dai ita sai duk maganganun nasa ma suka fara ɓata mata rai. Jin yaƙi yin shura ne yasa ta kasa daurawa ta ce "Dan Allah naji, haba ni ka ishe ne, ai naji duk abun da kake cewa" ta na faɗa ta bar masa palon. Ya bita da kallo bai ce komai ba. Ta shiga daki ta fashe da kuka tana jin zuciyarta na zafi ga wani irin ɓaci da ranta yayi da abun da tayi, wai ita da kanta.
Wanka tayi mai ɗaukar hankali da irin kayan da ta saba sakawa wato doguwar riga. Ita kanta tasan tayi kyau, ko waya bata ɗauka ba. Sannan ko jaka babu a hannunta. Ta saka wani ƙaton glas a idon ta. Lokacin da ta ƙaraso ƙofar gidan Habib sai ta dinga bin gidan da kallo, ta na tuno irin ƙorar da aka yi mata a gidan. Kanta tsaye ta buɗe get ɗin gidan ta shiga cikin gidan ta na sallama. Jin babu kowa ne yasa ta shiga palon ta zauna. Minti ɗaya, biyu,uku, huɗu, biyar. Ganin babu motsin kowa ne yasa ta miƙe tsaye ta shiga duba gidan. Ganin babu kowa yasa ta shiga kichin ta samu babu komai na abinci wanda yake a dafe. Sai kuwa tayi musu girki, ta shiga ɗakin sa ta gyara ta koma na Nadiya shima ta gyara. Sannan ta zubo abincin da tayi ta zauna ta na ci tana kallo, a ranta tana jin koma ina suka tafi zasu dawo.
*°Habib*
Ganin get ɗin gidan a buɗe ne yasa ya ɗan yi mamaki domin koda zasu tafi asibitin shi da kansa ya rufe, sai kuma yayi tunanin ko dai Zainab ta dawo daga school ne, amma idan ita ce ai ya mata faɗa akan rashin rufe masa gida. Da haka ya shigo da motar ya zagayo ya budewa Nadiya ta fito da ƙyar domin cikin ya tsufa sosai da ƙyar take tafiya ga kasala kullum ciwo, hakan ne ma yasa kusan kullum suna hanyar asibiti. Sai da ya rufe get ɗin kafin yazo ya kamata suka nufi gidan. Ganin palon a buɗe yasa ya tabbatar da cewar Zainab ce ta dawo, ai kuwa zai saɓa mata tunda bata jin magana. Haka ya shiga lallaɓata har suka shigo cikin palon ya na mata sannu, ita kuma tana taku da ƙyar tana yatsinewa. "Innalillahi wa'inna'ilai rajiun! Ya faɗa da ƙarfi har yana sakin Nadiya tsaɓar tsoro, ita kanta Nadiyar ta tsorata sosai domin sai da ta fadi a tsakiyar palon. Haura kuwa sai murmushi take yi tana kallonsu ganin yadda tsoron ganinta ya rikita su. Ganin sun kasa magana ne yasa ta ce "Sannunku da dawowa?" Habib ya kasa magana, Nadiya kuma ta samu guri ta zauna domin ba ƙaramin jin jiki take yi ba, kuma yaɗuwar da tayi ma taji shi amma ta daure tana ta kallon haura ɗin. Sai lokacin ma suka kula da abinci take ci, ga gidan duk a gyrare har yana tashin ƙamshi. Habib dai ya kasa zama kuma ya kasa ko motawa. Da ƙyar ya nufi gurin Nadiya ya na son kamata domin ya Kaita ɗaki amma ta ɗaga masa hannu alamun ya barta. Haura ta ce "Sir nayi kewarka sosai, ina fatan kaima kayi kewata ko?" Ta faɗa tana nufar gurinsa. Suna haɗa ido ya ji kamar an zare masa lakkar jikinsa, yaji wani sanyi ya shigesa. Ta zo har kusa da shi ta ce "Sir Mai yasa baka sona bayan kuma ka koya min sonka, bayan ka min alƙawarin zaka aure ni, ko matarka bata yarda ba ne?" Ta faɗa tana sha masa fuska. Habib ya ce "Wa ya faɗa miki bana sonki, ina sonki sosai har cikin zuciyata" ya ƙarasa yana sakin fuska. Ta ce "Sir Aure nake so zamu yi na dawo gidan ka da zama" ya ce "Nima zan so hakan baby" yana faɗa yana ta sakin murmushi. Nadiya ta yunƙura da nufin tashi ta bar gurin amma ta sami mistake ta zame. Har Habib ya tashi da sauri zai je gurin ta amma Haura ta riƙe masa hannu ta ce "Sir wannan ai lokaci na ne, nazo ne fa kawai domin na ganka na samu muyi hira". Sai kuwa ya ce "Haka ne fa, yau ranar ki ce gaba ɗaya". Ganin ya na ta kallon gurin da Nadiya ke kwance ta na ihu ne yasa Haura kama hannunsa ta na fadin "Sir zo mu shiga ciki zan baka labari. Ai kuwa sai ya miƙe yabi bayanta, suka bar Nadiya kwance tana murƙususu a gurin. Sun kai minti biyar da shiga dakin Zainab ta dawo. Daga ɗakin da suke Haura ta hangota, hakan yasa ta tambaye shi wacece ya ce ƙanwarsa ce. Hakan yasa ta ce masa yaje ya hana ta shigowa cikin gidan. Ai kuwa tare suka fita har palon, kuma har lokacin Nadiya na kwance a gurin har ɗankwalinta ya fita. Ganin Habib ya fita Haura ta dawo kusa da ita ta ce "Idan har mutuwarki itace zata bani damar shigowa gidan nan to Allah yaji ƙanki, zan iya miki alfarma ɗaya, ko dai kiyi hakuri na shigo Mu zauna tare ko dai na fitar da ke Ni na shigo. Saboda babu abin da ba zan iya ba akan damuwar burin zuciyata, karki wahalar da kanki akai na, domin wallahi sai Sir ya aureni. Ta na faɗa ta tsalleketa ta koma bakin window tana kallon Habib da Zainab suna ta muhawara. Cen dai sai Gashi ya shigo gidan ya ce "Ta tafi, amma dole zata dawo saboda kayanta suna nan" Cikin wata murya mai kamar ta bankwana Nadiya ta kira sunan Habib wanda yaji sa har cikin zuciyarsa. Ya kalleta sai kuma ya kalli Haura da ta kafe shi da ido. Ai da sauri ya tsallake ta ya dawo gurin Haura yana murmushi. Haura ta ce "Kama ta ka Kaita ɗaki" ai kuwa da sauri ya saɓeta Haura na binsa a baya har ɗaki, yana ajiye ta suka baro ɗakin suka dawo palo...📝
Wai me ke faruwa
S Reza...
[09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*
*FCWA*
*Chapter 19*
Bayan sun zauna a palon Haura ta dube shi ta ce "Ina so yau muje gurin Daddy tare da kai kuma ka tabbatar masa da cewar zaka aure ni, kuma ka bashi hakuri akan abun da ya faru wancen lokacin da baka zo ba?" Ta faɗa ta na shigewa jikinsa. Habib ya amsa da sauri kamar mai tsoro. Ya ce "Zan bashi hakuri kuma ba zan baro gidan ba sai da alƙawarin auren mu" ya faɗa cike da shauƙin jinta a jikinsa. Ta ce "Sir ba kayi kewata ba ko?" Ya ce "Nayi sosai ma, baki san yadda naji bane kwana biyu da bana ganinki" Ta ce "To ba kai ne kake korata ba harda duka na saboda matar ka ba?" Ta faɗa da shagwaɓa a muryar ta, har tana cuno baki gaba. Habib ya ce "Ba laifi na bane, kuma ai na baki hakuri, yanzu dai a fuskanci gaba baya ta wuce. Ta ce "Yanzu ni da matarka wa zaka saɓa idan an ce ka ɗauka?" Habib ya ce "Wacce mata kuma idan gaki, ai ni kin fiye min kowa da komai a duniyar nan, dan Allah ki daina ma haɗa kanki da ita" Ta sake cewa "Da gaske kake Sir?" Ya ce "Da gaske nake ina mutukar sonki" Haura farinciki kamar zai hallaka ta, sai yanzu take jin cewar tana yin soyayya, domin kaso a soka ai shine so, tabbas ko mai zai faru sai ta auri Habib ɗin ta. Sai kuma ta mike tsaye ta kama hannunsa suka shige ɗaki ta na masa kalaman da suke ƙara hargitsa shi. Suna shiga ita kuma ta fito ta nufi ɗakin Nadiya. Ta tura ƙofar ta shiga sai ta sameta a kwance kamar mai barci duk ta fita a haiyacinta, har lokacin tana numfashi sama-sama. Sunkuyawa tayi kamar mai duba wani abu a bakin kofar, amma ta ɗago bata ga abun da take nema. A hankali Nadiya ta buɗe ido jin an shigo tana kallonta, sai ta fara karanto addu'o'i a zuciyarta, domin dai ita ta tsorata da yarinyar. Duk yadda Haura taso da tayi mata abun da tayi nufi sai ta kasa, taso tayi amfani da cikin jikinta domin ta furgitata har ta haukacewa Habib yayi mata shegen duka ya sake ta amma ta kasa hakan. Daga karshe ma ɗakin ta bari tana jin haushin Nadiya ɗin, tana tunanin kawai ta fita a sabgar Nadiya kawai tayi ta amfani da Habib. Duk yadda taso akan su aikata zina a karo na biyu amma yaƙi yarda ya ce shi auranta zai yi, itama saboda tafi son auran yasa ta haƙura ba tare da tayi masa dole ba. Sai kusan magriba suka bar gidan bayan yayi wanka ya saka manyan kaya. Lokacin da suka iso ƙofar gidan Adam an fito daga sallar magriba. Ya shiga da motar har cikin gidan ya paka. Ta ce "Karka ji tsoron komai kawai kai dai kace masa da gaske kake sona kaji?" Habib ya amsa yana fitowa daga cikin motar. Tana gaba yana binta a baya har bakin palon. Ta buɗe ta shiga da sallama. Lokacin gaba ɗaya suna palon, yaran ne kawai a cikin ɗaki suna Sallah.
Da gudu haura ta kara so gurin Amera ta faɗa jikinta ta na faɗin "Anty gashi na kawo shi, yazo ya bada hakuri akan wancen lokacin, kuma ya tabbatar da aure na zai yi" Amera ta kalli Adam da ya kafe Habib da ido. Amera ta ce "Sannu da zuwa ga guri ka zauna?" Ta nuna masa kujerar dake kusa da shi. Habib ya zauna. Haura ta ce "Daddy ga shi yazo ya baka hakuri?" Kafin Adam yayi magana Habib ya fara miƙo gaisuwa. Amera ta amsa ta na cewa Haura taje ta samo masa ruwa. Haura ta tashi tana kallon fuskar Daddy. Adam ya ce "Me ya kawo ka gidan nan bayan dukan da kayi mata da kuma ƙin zuwa da kayi a lokacin farko da aka nemeka, ka manta sanadiyyar abun da kayi mata har kwanciya a asibiti tayi, shine yanzu ka dawo ka sake karya mata zuciya ko?" Habib ya ce "Duk abun da ya faru kuskure ne shi ne yasa nazo yanzu na bada hakuri, wallahi yanzu a shirya nake domin nayi komai akan ta, saboda ina sonta, kuma auranta zanyi wallahi" Adam ya ce "To ka makara domin an riga ka, yanzu haka auranta ya kusa saboda haka ina so ka fita daga sabgar ta, kar na ƙara ganinka da ita, idan ba haka ba zan baka mamaki?" Habib ya zamo ƙasa ya fara roƙo harda magiya yana cire hular kansa kamar zai yi kuka. Ita dai Amera ta kasa magana, abun ya ɗaure mata kai, ita tunanin ma da ta fara yi shine dole ne fa sun san ina Haura ta je tayi wannan daɗewar, shin suna tare da shi ne ko dai yaya. Ana cikin haka haura ta ƙaraso gurin tana kallon yadda Habib ke ta rikon Daddy kamar zai masa sujjada. Ta na ajiye ruwan Habib ya ce "Ki taya ni bashi hakuri wai an kusa miki aure, dan Allah kice yayi hakuri zan iya shiga wani hali idan ban ganki ba" Haura ta ce "Aure kuma?" Adam ya ce "Eh aure! Kaman yadda na faɗa miki kuma Amera ta faɗa miki to