Showing 9001 words to 12000 words out of 58144 words
ita, haka take yin rayuwarta ita ɗaya bata son shiga mutune, kuma hakan ya samo asali ne tun daga farkon rayuwarta da inda ta taso da kuma irin mutanen da tayi rayuwa dasu a baya, har wannan lokacin bata iya sakewa da mutane sosai, kana ganinta zaka mata kallon mara wayo kuma yarinya, sai dai hakan bai sa ta zauna babu ƙawaye ba. Ta na da ƙawaye kusan uku amma wacce kusan kullum suna tare itace Maryam Kabir. Babbar kawarta kenan wacce har gida ta na zuwa, Adam da Amera duk sun san da Maryam, kuma sun yarda da ƙawancen su. Ita kanta Maryam ba sanin cikin Haura take yi ba, domin haka take bata yawan magana sannan tana da wahalar yin fushi. Bata iya faɗin abun da ya dame ta, amma idan kai ka faɗa mata naka zata tayaka neman mafita harda shawara mai kyau. Wani guda ɗaya kuma shine bata da tsoro a rayuwar ta, sam-sam bata tsoron komai ciki harda mutane, zata iya kallon cikin idonka ko idonki ta faɗa miki duk abin da kikai mata wanda bata ji daɗi ba, kuma daga lokacin ya wuce kenan.
A rana ta biyu da Habib ya fara zuwa class ɗin su a matsayin sabon malami ne tazo a makare, hakan yasa koda tazo zata shiga ya tsayar da ita, kuma gashi ita ɗaya ce kawai ta makara duk class ɗin, haka wannan ranar ta rasa wannan text ɗin nasa, kuma abun yayi mata ciwo sosai. Abun ya ɓata mata rai domin koda ta koma gida saida Amera ta tambaye ta abin da ke damunta ta ce babu komai, a ranar haka ta uni abun nata dawo mata a rai. Haka washegari ma tazo school ɗin wanda sai ta tsinci kanta da son ganinsa ko hararsa tayi ko zata huce, amma ranar bai zo ba. Washegari ma haka bai zo ba, haka har kwana biyu bata sake ganin sa, gashi ta kasa tambayar kowa ko an sauya masa class, Kuma ko sunansa bata sani ba, amma ba zata iya tambaya ba, duk sai ta damu da hakan, ta kasa sakuni. Abun da bata sani ba kuwa shine, kullum yana zuwa kawai dai suna yin katari ne na rashin haɗuwa. Rana ta uku ce take da class karfe takwas na safe hakan yasa ta fito da wuri lokacin Maryam ta mata kira ya kai uku. Tana ganinta ta ce "Ni Wallhi Haura duk lokacin da zamu fara exam sai dai mu raba hanya, haka kawai bayan kin san idan muka makara ba ƙyalemu za'ayi mu shiga ba sai ki zauna a gida kamar wata mai aure, ko uwar me kike yi oho!" Ta ƙarasa ranta a ɓace domin har lokaci ya kusa yi. Haura bata ce komai ba sai murmushi da tayi kawai suka tare mai keke suka shiga. Daidai sun nufi class ɗin nasu ne Maryam ta hango Habib ɗin shima ya nufi class ɗin, kuma ga wasu ɗaliban suma suna gudu domin kar ya riga su shiga. Hakan yasa ta ce "Haura ga shi cen wallhi zai shiga" ta faɗa tana kama hannun Haura domin su yi gudu. Sai haura ta kalli gurin da ta nuna mata sai ta kwace hannunta ita kuma Maryam taci gaba da gudun ba tare da tabi ta kanta ba kar tayi mata a sarar wannan karatun nasa da zai taimaka mata a exam ɗin ta.
Haka taci gaba da tafiya har yanzu kusa da ita, bai ko nu na ya san da ita ba zai wuce sai ta tsinci kanta ta faɗin "Good morning Sir?" Ta faɗa ta na ɗan sauri ta kamo shi domin su jere tare. Sosai taji daɗin ganinsa, gashi kuma tayi niyyar idan ta gansa ta haharesa ko tayi masa rashin kunya amma sai ta kasa, sai ma wani irin daɗi da taji, ga ƙamshin sa da yakeyi ya tafi da ita. Habib ya ɗan juya ya kalleta sai kawai ya ɗaga mata hannu alamun amsawa yaci gaba da tafiya. Ita ma bata ce komai ba ta ce gaba da jerawa dashi ta na jin yadda saurin nasa ke son fin ƙarfinta. Shi kuwa da mamaki yake ta satar kallon ta, shi bai ma kawo cewar class ɗin sa zata shiga ba, har saida yaga ta biyo bayansa. Da Karfi ya daga mata tsawa sannan ya nuna mata hanyar fita daga class ɗin yana jin wani irin ɓacin rai da rainin wayon yarinyar. Kowa dake class ɗin saida ya tsarota balle amma banda ita da ta kafe shi da ido. Kallonsa ta yi ganin yadda har wani ɗaga jijiyoyin wuya yake kamar wata uwar a kayi masa. Juyawa ta yi kaman zata fita ɗin sai da ta tabbatar ya juya ya shiga sai ta shigo da gudu, kasancewar gurin zamanta a gaba yake yasa har ta zauna bai kula ba. Saida ya ajiye abubuwan hannunsa sannan ya juyo ya fara musu jawabi cike da ƙwarewa da iya koyarwa. Rubutu yayi sannan yayi tambaya sai Haura ta ɗaga hannu yace ta tashi. Nan ta bada amsa sai ya bita da kallo. Yana so ya tabbatar da cewar kamar itace wannan yarinyar da ya kora fa yanzu amma ya kasa gano wa, hakan yasa ya fito ya leƙa waje amma baiga kowa ba. Dawawo yayi ya sake kallonta da mamaki a fuskarsa ita kuma tana tsaye har lokacin domin bai bata izinin zama ba. Ganin dai ya rasa mai zai ce ne yasa yace ta zauna, yana ta satar kallon ta da kuma mamaki. Sai dai duk lokacin da ya leƙo sai ya tarar tana kwallonsa harda murmushi. Haka duk lokacin da yazo haka zata dinga masa dariya ko murmushi harda ɗaga masa gira. Tun ya na kawar da kai, abun na basa mamaki har ya fara ankara da abun. Watarana bayan an tashi ne ya kirata ofis ɗin sa yana so ya kankara mata worning akan idan bata daina masa wannan shirmen ba zai zane ta...
S Reza...✍️
[09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️*
*°S-Reza✍️*
_First class writers association_
_My Whatsapp chanel_
*Chapter 5️⃣*
Bayan ta zauna ya ce "Ke baki da hankali ne? Baki san nan school bane da zaki dinga mana wasa da shirme, to daga yau idan na ƙara shiga class naga kina dariya saina zane ki a gaban mutane, wawiya mara kamun kai kawai" Ya na faɗa bai bata damar yin magana ba ya koreta daga ofis ɗin ya na mamakin yadda take iya kafe shi da ido. Tun daga lokacin Haura ta gane son Habib take yi, kuma daga ranar kullum idan tazo sai ta dinga jin kamar ta je ta faɗa masa cewar ta na sonsa, ita dama a yanayin rayuwarta babu kunya bata ma san cewar abun kunya ne mace tace wa saurayi ta na sonsa ba, haka ita a irin rayuwar ta bata jin zata ji kunyar abun da take so, kuma a yanayin yadda take jin Habib ranta ko kanta ne zata iya bashi. Hakan yasa yanzu take yin duk mai yiwuwa domin taga ta jawo hankalin sa, ana haka Maryam ta gane halin da take ciki, babu irin maganganun da bata faɗa mata ba tace babu ruwanta ita dai tana sonsa. Tun Habib baya yana ɗaure fuska har ya fara damuwa da ita. Haka zata ja sket ɗinta har cinya tana kuma kanne masa ido. Ta na sonsa sosai domin shine mutum na farko da take jin tana so har haka a rayuwarta. Haka watara ma ya sake kiranta ofishin sa domin yaga abun nata ya fara wuce gona da iri. Saida lokacin tana shiga ta ƙarasa gabansa ta rungume shi ta ce "Sir me kake so nayi maka?" Ta faɗa da wata shegiyar muryarta mai laushi. Habib ya kasa cewa komai sai ma biyeta da yayi har sukayi shafe-shafe. Tun daga lokacin yake ta kokarin ganin ya gujewa abubuwan da take masa amma ya kasa, har ta kai ta kawo shima yana damuwa da rashin ta, idan yazo school bata nan ya dinga damuwa kenan. A haka ne ranar suka so aikata wa amma ta suma. Lokacin da ya bar class ɗin a daren itama ta farka da tari, amma taga duhu amma ko a jikinta. Miƙewa tayi ta na mayar da kanta ta fara neman hanya zata fita sai ta taka wayarsa. Hakan yasa ta sunkuya ta ɗauka. Hotonsa ne shida Nadiya a gaban wayar, hakan yasa gabanta ya faɗi ganin yana da mata. Dafe wayar tayi a ƙirjinta ta na jin wani irin haushi da kishin ganin su a tare. Zama tayi a class ɗin domin ita dama ko kaɗan bata san tsoro ba, domin ita ko magana ce bata jin tsoron yiwa mutum bare kuma zama a cikin duhu ko kuma yin tafiya cikin dare. Ta kai minti uku ta na danna wayar sannan ta kama hanyar fita daga class ɗin. Haka tazo bakin get Emeka ya taso ya na tambayar waye. Tace masa itace. Ba tare da doguwar tambaya ba ya buɗe mata ƙaramar ƙofar ta fita ganinta da ƙaramar jaga ga shi kamar barci tayi. Dukda haka bai tsaya ba saida ya koma ya sake duddubawa.
Koda ta isa gida lokacin hankalin Adam da Amera harda suna Salim duk a tashe yake sun kasa zama, gashi kuma bata tafiya da waya school, kuma Adam yaje har school ɗin ance babu kowa. Amera ta ce "Ina kika je haura?" Ta faɗa da ɗan ɓacin rai ganin lafiyar ta lau. Haura ta ce "Anty babu ko ina fa, na tsaya yin rubutu ne har dare yayi" ta faɗa ta na zama a kujera mai cin mutum Uku. Salima ta karasa kusa da ita tace "Anty Daddy ya na ta faɗa harda mommy ki daina dadewa haka kinji?" Haura ta ce "To ba zan sake ba, amma kunyi sallah?" Ta ce "A'a yanzu zamuyi" ta ce "To kuzo muje muyi?" Ta faɗa ta na kamowa harda Salim ɗin da shima yake zaune kusa da ita. Amera ta kalli Adam ta ce "A kwai matsla fa, tun ba yanzu ba na fara lura da yarinyar, anya kuwa ba soyayya ta fara ba, nifa ina tsoron kar wani ɗan iskan saurayin ya yaudareta kasan ba wayo gareta ba. Ta ƙarasa ta na jin tsoron har zuciyarta. Adam ya ce "Soyayya kuma, a'a kawai dai zuwa gobe sai mu zauna da ita muji meye ya faru. Haura na shiga ɗakin suka yi alaula kowa yayi Sallah sannan suka fito palo domin cin abinci. Haka suna cin abincin suna ta satar kallonta, ita kuma ganin haka yasa ta mayar da hankalinta ga cin abinci da kuma wasa da sukeyi da su Salim. Suna gamawa ta kwashe kwanunkan ta kai kichin ta fito ta raka su Salim ɗaki bata fito ba sai da sukayi barci. Ta na fitowa ta samu adam da Amera a palon suna kallo. Har zata wuce Amera ta kira sunanta. Ta dawo ta zauna kusa da ita tana kallonta. Har zatayi magana Adam ya ce "Ba nace ki bari sai da safe bane, Kinga Haura je ki kwanta sai gobe kinji" ya ƙarasa yana bata umarni. Haura ta mike ta shige ɗaki. Kwance tayi ta na kwallon saman ɗakin. Abun da ya faru dasu yaune keta dawo mata, kenan guduwa yayi, to ko ya na tunanin mutuwa tayi shi yasa ya gudu. Ta na sonsa zata iya masa komai, amma sai ta tabbatar da cewar zai aureta, lokaci ɗaya kuma ta tuno da cewar yana da mata fa. Da sauri ta mike ta dauko wayar tasa ta na kallon hoton nasu. Gwada jan wayar sama tayi sai taga babu password. Da sauri ta gyara zama ta shiga gurin hotuna, babu hotonansu da yawa domin daga shi har ita ba masu son yin hoto bane. Jin kamar motsin mutum yasa ta kashe wayar ta kwanta.
Washegari bata da class sai na yamma hakan yasa bata fita ko ina ba, ta ɗauki wayarta ta' shiga Whatsapp tana chatting sai taga ana kiransa. Dubawa tayi taga an rubuta Beb da Hoton zuciya. Kaman ta ɗaga sai ta fasa, ganin an sake kira ne yasa ta ɗaga amma tayi shiru. Haka Nadiya ta gama hello hello amma babu amsa. Number Nadiyar ta saka a wayar ta tayi seving bayan ta kira itama ta masa seving. Ajiye wayoyin tayi jin Amera na kiranta. Ta ce "Me kike yi a ɗaki ne tun ɗazu, kin duba lokaci kuwa?" Haura ta ce "Aunty yanzu fa dama zan fito" Amera ta bita da kallo sai kuma tayi shiru ta ce "Mai zamu dafa da rana?" Ta tambaye ta domin dama wasu lokutan ita ce ke zaɓar musu abun da zasu girka. Haura ta buɗe baki zata yi magana suka ji sallama. Juyawa sukayi a tare suna amsawa. Nana ce tare da mijinta Nasiru suka shigo. Amera ta ce "Ai da gida ma kika wuce nima yanzu nake son tafiya" Haura ta ce "Anty Nana maraba" ta samu guri ta zauna ta na faɗin "Idan baki son zuwan nawa ai sai na koma ina da gurin zuwa. Kafin tayi magana Nasiru ya shiga gaida Amera cikin girmamawa, ta amsa ta na masa maraba. Da sauri Haura ta buɗe friji ta kawo masa ruwa. Sannan ta koma kichin. Bata fito ba sai kusan biyu na rana lokacin ta gama komai. Har lokacin kuma Nana ta na nan, hakan yasa ta zobo mata abincin ta kawo mata. Itama Amera ta ce ta zubo mata. Bayan ta ajiye musu ne ta koma ɗaki domin ta shirya. Amma sai ta dauki waya ta shiga dube-dube, daga haka ta shiga whasop sai taga number beb ɗin nan tayi magana. Hakan yasa ta mayar mata. Daga haka kuma ta shiga toilet domin yin wanka. Koda ta fito ta shirya da sauri lokacin taji muryar yaran sun dawo. Fita tayi ta cire musu inifon ta zuba musu abinci suka ci tare sannan ta ƙarasa shiri ta nufi school ɗin tana ta addu'ar Allah yasa yazo.
Lokacin da ta bar ofis ɗin sa bayan tace masa wayarsa na gida kuma alhalin tazo da wayar kawai bata so ta bashi ne, kuma yau bata so tayi dare ne yasa ta fita. Tun a hanya ta sake fito da wayar ta kunna data ta sake ganin number Bebb tayi magana, hakan yasa suka fara chatting ta nayi tana dariya. Kafin magriba ta isa gida lokacin adam ya dawo. Ta na shiga suka mata barka da dawowa ta faɗa wanka ta saka kayan gida ta fito palo ta samu har an gama abincin daren. Homework ɗin yaran ta fara nuna musu, sannan tayi musu wanka suka zauna suna cin abinci. Bayan sun gama suka zauna a palon ana hira Adam na basu labarin rashin jin yaran Khadijah ƙanwarsa da yaje gidan yau. Haura ta ce "Ai kawai Daddy wannan yaron a kaishi aikin soja domin zai fi bada gudunmawa acen. Amera ta ce Salim da ya girme shi amma duka yake wa Salim harda kuka. Adam ya ce "Ai dama ko zubin halittar su ai ba ɗaya ba ne, ai wannan yaron idan ya girma ba ƙaramin mai zuciya za'ayi ba. Adam ya buɗe baki kenan suka ji ana buga ƙofar palon. Adam ya ƙarasa gurin yana tambayar waye bayan ya buɗe. Yaron ya ce "Wai wani ne a waje mai Mota yace a kira masa Aisha Adam Haura" yaron ya ƙarasa yana juyawa. Adam yabi yaron da kallo yana tuna maganar Amera da tace ko dai Haura Soyayya ta fara. Kaman ya fita yaga waye amma kuma ya bari sai ya fara jin ta bakin ita Haura ɗin. Amera ta ce "Waye ke sallama?" Adam ya ce "Wai wani ne a mota yazo gurin Haura" ya faɗa yana kallon ta. Da sauri ta ɗago tana kallon daddyn nata. Ta ce "Daddy ni?" Ya ce "Wacece Aisha Adam Haura?" Cike da fara'a da kuma addu'ar Allah yasa shine ta ce "Daddy waye shi ɗin?" Amera ta ce "Ban gane wani yazo gurinta ba, ka fita kaji waye, kuma me yazo yi ne?" Adam ya ce "To kin san ko tasan da zuwan nasa ne?" Amera ta kalli Haura ta ce "Kunyi da wani zai zo gurinki ne?" Haura ta ce "Eh Anty" Da sauri Adam ya ce "Waye shi?" Amera ma ta ce "A ina kika sanshi, kuma me yazo yi?" Suka jera mata tambayoyin a lokaci ɗaya. Haura da gaba ɗaya hankalinta ya tafi da son ganin ko shi ɗin ne ko ba shi ba ne ta ce "Anty bari na fara dubawa na gani ko shine ko bashi bane?" Ta faɗa tana tashi ta nufi ɗakin ta, sai gata da hijabi bayan ta sake fesa turare, suna zaune ta wuce su suka bita da kallo.
Tun daga nesa ya hangota hakan yasa ya kafe ta da ido har ta ƙaraso. Buɗe motar yayi ya fito yana cigaba da kallonta. Kafin tayi magana ya ce "Bani waya ta yanzu ko na kwakƙwaɗa miki mari?" Ya faɗa ransa a haɗe. Haura ta ɗan saki murmushi ta ce "Sir naji daɗin zuwanka gidan mu, bari na kawo maka ruwa kaji?" Ta ƙarasa tana komawa cikin gidan. Tana ji yana kiranta amma bata ko juyowa ba. Tana shiga palon Adam da Amera suka tsayar da maganar da suke yi suna binta da kallo ganin tana ta murmushi abunta. Haura ta ce "Anty shine yazo hira" ta ƙarasa da dariya. Amera ta ɗan yi dariya itama ta ce "Shine wanda ya hana ki sakewa kwana biyu kenan ko?" Haura ta shiga kichin ta haɗo masa ruwa da ɗan abun taɓa wa. Ta fito ta sake wucewa waje. Gaba ɗaya Habib mamakin yarinyar ya keyi,ita wai ma murmushi yake yi abun ta. Bata nufi gurin da yake tsaye ba, sai ta ƙarasa gefe da gurin motocin Daddy ta ajiye tren sannan ta kawo kujeru guda biyu ta zauna a ɗaya ta na kwallonsa. Haka ya nufo gurin ya zauna ya ce "Bani waya ta? Mai yasa aka kirani kika daga? Kuma kika buɗe min whasop harda chatting da matata, wai baki da hankali ne ko menene?" Ya ƙarasa ransa