Showing 24001 words to 27000 words out of 58144 words
ciro wayarta ta shiga kiransa. Amma number a kashe, kira uku ta yi bata shiga sai ta kunna data ta shiga online. Sakon Bebb ta fara cin ƙaro da shi har guda uku. Da sauri ta shiga ta na karantawa, gashi minti biyar da sauƙar ta a online ɗin. Ganin bata kai ne yasa itama ta fara mayar mata da amsa, Dama tambayar ta tayi akan ya karatu, yau bata ganta ba lafiya dai ko. Bayan ta gama ta kamo number Habib shima ta ajiye masa saƙo da yawa. Har zata sauƙa taga sakon Maryam, ta na dubawa taga ta na online, hakan yasa suka fara hira.
*°Habib*
Lokacin da ya iso get ɗin gidan sa, ya kai minti uku a cikin motar ya kasa shiga cikin gidan, nadama ne fall ransa, hakan yasa yake ta tunanin hanyar da zai bi domin ya goge haɗuwa da ita, domin haushinta yake ji da hasken gaske. Wayarsa ya ɗauko, yayi blocking din number ta har ta whasop. Sannan ya cire layin ya karya shi ya yar. Ya ja motar sa ya ƙarasa cikin gidan. Budewa yayi ya fito daga cikin motar ya na jin wani irin fargaba na haɗa ido da Nadiya. Matarsa ta Sunnah gashi ta na ɗauke da juna biyu, mai kula da shi, mai masa biyayya, bata rage shi da komai ba amma ya tsallake ta ya je ya aikata zina! Abun da baiyi tun ya na saurayi ba sai da yayi aure. Sai yanzu ya fara tunanin ma a yadda ya baro gida, ya ce mata bashi da lafiya ta bashi magana ya sha, sannan ta shiga kichin domin ta haɗa masa farfeso duk saboda ta damu dashi. Sauke ajiyar zuciya yayi ya na jin kaman kar ya shiga gidan. Haka ya tura ƙofar palon ya shiga da wata siririyar sallama. Kasancewar hankalinta naga ƙofar domin taji shigowar sa gidan, hakan ne ma yasa taji sallamar tasa. Ajiye wayar tayi ta amsa sallamar ta na kwallonsa yadda ya ke a sanyaye sai itama jikinta yayi sanyi, kuma fargabar da take ciki ya ragu dalilin ganinsa. Miƙewa tayi da sauri ta na tambayar ina kuma ya je shida bashi da lafiya kuma bai faɗa mata ba, ta kira shi kuma bai daga ba. Zama yayi a kan kujera ya dafe kansa. Itama tazo kusa dashi ta zauna ta kama kan nasa ta ce "Bebb jikin ne dai? Nayi mamakin da na fito na samu baka nan, kuma baka faɗa min zaka fita ba?" Ya ce "Sorry na je kemis ne an min allura domin sosai zazzaɓi ya sake kamani". Cikin Muryar tausaya wa ta shiga masa sannu, ta na faɗin "Bari na kawo maka abinci?". Haka ta shiga kichin ya bita da kallon so da tausayawa. Har ta kawo masa abincin tunani ya keyi. Shinkafa ce da wake da miya, sai kuma farfeson da tayi masa, sai apul da kankana da ta yanka tun ɗazu. Sai abun sha. Haka yake ta kallonta har ta gama haɗawa. Dama tasan baya iya cin abinci idan baida lafiya, haka take kasawa ta tsare sai ya ɗan ci ko babu yawa. Hannunsa ta kama ta saƙƙo da shi ƙasa ta na masa sannu. Ta fara zuba masa shinkafar ta mika masa. Sannan ta zubo naman shima a wani plet ɗin ta miƙa masa. Baya jin yunwa ko kaɗan, amma saboda taji daɗi yasa babu musu ya ƙarɓa ya na godiya ya fara ci. Shi shida ne ta bangaren iya girkin Nadiya, amma na yau sai yaji shi salam, babu ɗanɗano ko kaɗan a bakin shi. A zuciyarsa ya ce "To dama bakin mazunaci ai baya gane ɗan ɗano mai daɗi da mara daɗi kaman yadda farjinsa baya iya banbance haram da halak. Tsayawa yayi da cin abincin yayi shiru ya na jin kamar ya fara kuka. Nadiya ta ce "Please Bebb Dan Allah ka ci, ko abincin ne baiyi daɗi ba?, yanzu fa ka ce allura a kayi maka, kuma ko da rana ba wani abincin kirki kaci ba, dan Allah ka daure ka cinye wannan abincin sai ka haɗa da kayan cikin nan kasha wannan sai ka kwanta. Ta ƙarasa ta na jin a ranta inama ya iya cinyewa. Ya ce "Amm Bebb cikina a cunkushe ya ke ba zan iya ƙara cin komai ba". Ya faɗa da muryar rashin lafiya. Ta ce "To ka ƙara ko kaɗan ne ka daure" Ganin yana girgiza kai yasa ta taso ta ɗauki kwanon abincin ta ɗebo ta kai masa baki. Tsayawa tayi ta na kwallonsa jin wani ƙamshin turare mai daɗin ƙamshi dake fita daga jikinsa. Bata zargin mijinta hakan yasa ta sa masa abincin a baki, ta na mamakin a ina ya samo wannan turaren shi da ya je yin allura, jin zuciyarta na kasa haƙura ne ya sa ta ce "Bebb ka sake samo wani kalan turaren ne?" Ta faɗa tana kuma sake ɗebo abincin ta nufi bakinsa. Da sauri ya buɗe bakin ta saka masa yana zare ido kamar munafuki. Haka ba tare da yayi magana ba saida ya cinye wannan abincin tass harda naman da ta zubo masa. Ya na gamawa ta shiga ta haɗa masa ruwan wanka ya shiga ya watsa ya fito ya saka kayan barci, ya kwanta ya na addu'ar Allah yasa kar Nadiya ta sake masa tambayar. Ya na cikin tunanin ta shigo ɗakin ta kashe wutar ta kwanta a bayansa ba tare da ta ce masa komai ba, yana jin yadda ɗan cikin nata ya tokareshi ta baya. Haka Habib ya ta juye-juye ya na ta tunani akan hukuncin da yake son yanke wa, babu mafita dole ne yayi hakan muddin ya na so ya manta da wannan yarinyar. Haka sai wajajen asuba barci yayi gaba da shi, kuma ana kiran sallah ya tashi.
Haka ya wayi gari wasai kansa ya daina ciwo, zazzaɓin ma babu, sai kawai rashin natsuwar zuciya. Ya na zaune a palo sai tunani ya keyi, yau ko zuwa ya taya ta aiki ma ba ta samu ba. Ita kuma tayi tunanin ko ciwon kan ne har yanzu. Bayan so yaje ya aika abun da zai lalata masa rayuwa, shi yasa yake ta shawara da zuciyar sa akan wannan hukuncin. Sai ya saƙa ya kwance hardai ya yarda da shawarar zuciyarsa duk da cewar gabansa na faɗuwa da abun da zai biyo baya. Sosai yayi ƙoƙarin sakin jikinsa suka karya ya nuna mata ya warke, harda wasa da dariya. Bai bar gidan ba sai sha biyun ra na, ya je ya sayi sabon layi ya sa aka yi masa welcome back, ya saka a wayarsa. Yaje yayi aski ya aske kansa gaba ɗaya yayi malolo ya bar iya gemun nasa shima yasa aka rage masa shi. Gaba ɗaya ya sauya kama kamar ba shi ba. Ya nufi makaranta duk yau Lahadi ne kuma bashi da class. Kai tsaye ofis ɗin shugaban makarantar ya nufa ya mika masa takardar barin aiki gaba ɗaya. Shugaban makarantar ya kalleshi bayan ya gama karanta takardar. Ya ce "Malam Habib wani irin ciwo ne ke damun ka da har zaka bar aikinka saboda shi?". Habib ya ce "Shine kawai mafita domin kar ya taba aiki na". Malam ya sake kwallonsa ganin yadda ya sauya kama, sai ya fara tunanin ko dai ciwon taɓin hankali ne yake son kama shi shine ya bar aiki. Tunanin hakan yasa ya ce "Tom Malam Habib Allah ya sawaƙe, kuma za'a tura maka albashin ka na wannan watan harda wani tallafi daga hukumar makaranta domin kula da lafiyar ka. Kuma duk lokacin da ka samu lafiya muna maraba da kai a kowani lokaci. Nan take ya sa hannu na barin aiki, ya na yi zuciyar sa na faduwa idan ya tuna irin wahalar da suka sha shida Mama kafin su samu wannan aikin.
Bayan ya gama ya je ofishin sa ya kwashe komai nasa sannan ya bar school ɗin. Duk inda ya wuce sai an sake kwallonsa domin ba'a gane shi ba. Haka ya ja motar sa ya bar school ɗin ya na jin hawaye na son zubo masa. Dole yayi nesa da ita, ya tsaneta baya son ko jin muryarta. Haka ya dawo gida ya samu Nadiya ta sake wanka ta haɗa kayan wankin su tana jira yazo ya kai musu gurin wanki. Ya na shiga kuwa tai masa magana sai ya kira mai wankin akan yazo ya kwasa ba zai iya zuwa ba. Zama yayi palon ya na son ya sanar mata da cewar ya bar aiki amma amma ya kasa. Yana kallon yadda take chatting ta na dariya abunta. A ransa ya ce "Yanzu ita babu abin da yake damunta saboda ita ba mazinaciya ba ce, gashi dai hankalinta a kwance. Haka ya uni a gida, dama shi ba wasu a bokai ne gareshi ba, haka yake rayuwarsa daga gurin aiki sai gida sai gidan Mama. A bokai sai irin na school ko wanda suke koyarwa tare. Ya ce "Wai ni me kike kallo ne haka da kika ta dariya tun ɗazu?" Habib ya faɗa ganin dariyar Nadiya ɗin kaman da gaiyya takeyi yi, kaman tasan halin da ya ke ciki ne ta ke masa dariya. Ta ce "Wallhi Bebb wata friend ce da muka haɗu ta na bani labarin matar babanta lokacin da take da ciki, shine fa abun yake bani dariya, taji nace mata ina da ciki shine take tambayar wai ni cikin baya sani masifa irin na matar ne, shine da nake tambayar ta ita matar meye ta ke yi haka na masifa, shine take bani labari, wai masifaffiya ce ta bugawa a jarida a lokacin da take cikin, wai hatta mijin nata bata barshi ba, kowa ya shigo gidan nan ba'a wanyewa lafiya da shi, ko waje ta fita bata dawowa sai anyi faɗa da ita, mijinta kuwa ya sha duka da kashe kuɗi duk saboda ita. Habib ya ce "Wannan kam iskanci ne, duk a kan tana da cikin sai kace mai ɗauke da cikin aljannu?" Nadiya ta sake fashewa da dariya ta ce "Wa ya ga nima na fara yiwa Bebb haka, sai kawai na kalleka na ce bana son ganinka a cikin gidan" Habib ya ce "Sai na tashi na fita ai wannan ba komai ba ne, ta fifiyata zanyi rabda kika neme ni sai na dawo" Nadiya ta ce "Shima wai mijin nata da yaji bala'in yayi yawa sai ya tattara kayansa ya bar mata gidan ya tafi chan wani guri. Habib ya ce "Lallai ya na da hakuri wannan mijin" ta ce "Idan kai ne ba zaka iya ba?" Ya kalleta sai ya ce "Anya kuwa, amma zan iya ai ina sonki". Sosai take bashi labarin rikicin cikin Amera wanda shima tsabar nishadi sai da ya samu kansa da jin dadi. Har ya na manta wa da batun gaya mata barin aikin nasa. Ita kuwa Nadiya har video call suka koma da Haura ana ta hira.
*°Haura*
Ta na idar da sallar asuba ta sake yin wanka da ruwan zafi, bayan ta fito ta saka doguwar riga da hijjabi haf Sunnah ta shiga kichin. Nan ta fara tunanin abun da zata dafa musu mai ɗan sauƙi domin ta na jin jikinta babu daɗi kaman zazzaɓi ke son kamata, gashi ta na so yau ita ce zatayi musu girki ko dan saboda laifin da tayi musu jiya. Haka ta fere dowa ta dafa, sannan ta fasa ƙwai ta fara soyawa, ta na aikin ta na sauraron waƙar soyayya cike da jin dadin baitocin cikin waƙar kamar da ita a kayi, ta na bin waƙar cikin sauƙi harda ɗan juya kanta Amera ta shigo kichin ɗin ta na binta da kallo. Sai da ta tsaya ta gama ƙare mata kallo sama da ƙasa sannan ta ƙaraso ciki ta na mata magana. Haura ta ce "Aunty good morning?" Amera ta amsa ta ɗora da "Yau da soyayya aka tashi kenan?" Haura ta yi shiru ta na dariya. Ta sake cewa "Kin gama komai ne ko na kama miki?" Haura ta ce "Na gama saura kaɗan, amma naga kamar babu biredi dama ina so a haɗa da ruwan shayi ne" Amera ta ce "Ok bari na faɗa masa sai ya samo mana yanzu kafin ki gama ko?". Tana faɗa ta bar kichin ɗin Haura ta cigaba da bin waƙarta ta na jin daɗi a ranta, barin ma idan ta tuna da cewar yau Habib zai zo a tsayar da magana. Bakwai da minti goma ta gama komai, ta jera musu a gurin cin abinci ta shiga ɗakin su Salim da Salma ta taso su, bata fito ba sai da tai musu wanka ta sawa kowa kayan zaman gida kafin ta fito dasu zuwa gurin karyawa. Suka zauna suna wasa kafin masu gidan su fito. Sai kusan takwas saura suka fito a tare. Da sauri Haura ta miƙa musu gaisuwa suna yaran suka gaida su. Adam ya dafa su gaba ɗaya ya na amsawa. Ya kafe Haura da ita a ɓoye. Nan suka zauna Amera ta zubawa Adam sannan ta zuba nata, itama Haura ta zubawa yaran nasu itama ta zuba nata suka fara. Gurin yayi shiru kowa ya mai da hankalinsa ga cin abincin, yayin da Adam ya ta tauna maganar da zai yi. Ita dai Amera hankalinta na kansa, yayin da haura kanta ya ɗan fara tsananta da ciwo...📝
Habib Zai zo kuwa?
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*
*°S-Reza*
_First class writers association_
_My Whatsapp chanel_
*Chapter 1️⃣1️⃣*
Sai da suka gama cin abincin kafin Adam ya kalli Haura da tun ɗazu ta gama cin nata abincin ta na dai zaune ta na kallon Salim. Ya ce "Karfe nawa ne ya ce zai zo?" Haura ta amsa da "Sai dai na sake tambayar sa amma bai faɗa min ba" Adam ya ɗan saci kallon Amera sai suka haɗa ido, ya kawar da kai. Ya ce "Ki ce masa yazo da wuri domin a kwai gurin da nake son zuwa yau" Haura ta amsa masa. Ya tashi ya bar gurin ba tare da ya sake cewa komai ba. Amera ta kalli Haura ta ce "Da gaske kina son wannan mutumin kuwa Haura?" Amera ta tambaya ta na kallon yanayinta. Ta ɗago kai ta na kallon ta ba tare da ta ce komai ba, kanta ne ke sara mata tun ɗazu, wanda izuwa yanzu har da zazzaɓi ne ke son kama ta, sai kuma taji tambayar tayi mata wani iri. Jin bata ce komai bane yasa Amera sa ke faɗin "Yanzu idan Daddynki ya ce miki baya son ki da shi saurayin naki zaki iya hakura da shi?" Ta yi mata tambayar domin sanin ko da gaske take son mutumin. Haura ta ce "Anty nasan ma Daddy ba zai hana ba, domin ina sonsa kuma shima yana sona" ta ƙarasa maganar a hankali. Amera ta saki wani murmushi mai lankwasa harshe. Ta sake cewa "To tsakanin shi da Daddy wa kika fi so?" Kafin tayi magana Salim da Salma suka haɗa baki gurin cewa "Daddy muke so" itama ta ce "Nafi son Daddyna akan kowa ai Anty" Amera ta ce "Kenan idan ya ce karki ƙara kula shi zaki daina?" Ta ce "Anty kaina na ciwo, idan kina da magani ki bani, ko naje na sayo?" Amera ta ce "Sorry ina da shi, bari na zo. Haka ta shiga ɗaki ta ɗauko mata maganin ciwon kai ta bata ta sha. Amera ta ce "Kije daki idan kin gama waya da shi kin faɗa masa cewar yazo da wuri sai ki samu ki kwanta ki ɗan samu barci ko ciwon zai tafi ko?" Haura ta miƙe ta nufi ɗaki Salim da Salma suka bi bayanta amma Amera ta dawo dasu akan su barta ta huta. Ta na shiga ɗakin ta ɗauki wayarta ta kira shi amma bata shiga, sosai ta dinga jera masa kira amma shiru. Jefar da wayar tayi a kan gado ta kifa cikinta ta na tunanin to mai ya samu wayar tasa ne, shi bai san tayi kewarsa bane, tun fa jiya bata sake jin maganar sa ba. Ta na cikin haka Amera ta shigo ɗakin ta ce "Yauwa na manta ban faɗa miki ba, wani irin abinci yafi so sai kawai mu fara shirin kafin lokacin ko?" Haura ta ce "Anty ban san abun da yafi so ba, kawai ayi koma meye zai ci" ta ce "Kin tabbatar?" Ta ɗaga mata kai. Amera ta ce "Kunyi waya ɗin?" Haura ta amsa da "Yanzu zamuyi" Amera na fita haura ta fara rubuta masa saƙo dan gajere ta tura. Sannan ta sake kwantawa tana tura kanta cikin filo ta na tunanin Habib da yadda suka kasance jiya, har yanzu ta na ɗan jin zafi, ta na tunanin ma abun da ya ke ƙoƙarin haifar mata da zazzaɓin kenan. Haka ta dinga tunani har taji wayanta na ƙara. Da sauri ta ɗaga ta na duba sunan mai kiran. Ido ta waro ta na mamaki, ai kuwa da sauri ta ɗaga ta na sallama. Ta cikin wayar Nadiya ta amsa ta na tambayar ta bata hau online ba, ta na ta jiranta. Haura ta ce "Yanzu dama nake shirin hawa" take ta kashe kiran. Ta buɗe Data. Haka suka dinga shan hira har bata san lokacin da ciwon kan ya tafi ba domin hira sosai suka sha ta na bata labari, karshe ma aka koma Vedo call. Babu laifi Nadiya na da kyau daidai gwargwado, kuma bata rasa komai ba, sannan ita Haura bata jin komai game da ita wai na kishi, hasali ma harga Allah ta na son Nadiyar so sosai kuwa, ko dan saboda Habib na sonta ne, haka kawai take jinta rai, kuma take jin dad'i hira da ita. Ta bangaren Nadiya itama haka ne, yarinyar na burgeta, tana son yarintarta da kuma yanayin Hausar ta, ta na son kulawarta, hakan yasa bata gajiya da hira da ita. Suna ta hira har bata san lokaci yaja har haka ba. Hakan yasa ta ce mata tana zuwa zatayi abu ne. Koda suka kashe ta duba shi