Showing 54001 words to 57000 words out of 58144 words
muna godiya Allah ya saka da alheri, mun gode sosai sai ka dawo ɗin" Malam ya ce "Kar kowa ya tashe shi da kansa zai tashi". Suka ce to. Haka Malam ya fita ya bar su tsaye a ɗakin sun zuba masa ido. Gashi anyi aihuwa amma tsabar tashin hankali babu wanda aka sanarwa. Haka sukayi cirko-cirko kowa na ta saƙa da warwara a zuciyarsa.
Bayan kamar minti arba'in Malam ya dawo, kuma har lokacin bai farka ba sai barci yake yi yana ta sauke ajiyar zuciya. Malam ya shiga har cikin ɗakin ya kunce gorar maganin da yazo da shi ya shiga yayyafa masa ruwan. Ai kuwa da ƙarfi ya zabura ya miƙe tsaye yana riƙe ƙansa. Malam ya shiga tofa masa addu'a na tsawon minti biyu kafin ya dawo hankalinsa. Ya fara bin ƴan ɗakin da kallo. Ya sauke ido akan Mama sai ya nufeta da sauri ya na daɗin "Mama lafiya dai ko? Me ya faru mai kuke yi anan? Ina nadiya? Ya faɗa yana haɗa ido da ita ta take ta kuka. Da sauri ya ƙarasa gurin da take ta rungumeta yana daɗin "Wai me ke faruwa ne? Ina cikin jikinki ya shiga?" Haka ya dinga maganganu amma duk sun kasa amsa masa sai kuka da kuma tausayin sa suke ji. Malam ne ya masa magana wanda sai lokacin ya kula da shi. Ya ce "Ka ce "Alhamdu lillhi?" Habib ya kalli malamin ya kalli Mama, sai ta ɗaga masa kai. Nan ya ce "Alhamdu lillhi" ya na faɗa ya fashe da kuka. Sai da Malam ya bari yayi mai isar sa kafin ya fara bashi labarin abun da ya faru da shi ya ɗora musu da tunatarwa. Ya ce "A matsayin ka na musulmi da Allah ya baka takobin kariya daga mugayen sheɗanu da aljannu har mutane, amma kayi sakaci har aka ci galaba a kan ka, kunyi sakaci na barin gidajen ku babu kariya, sannan kuna barin kawunanku babu kariya, ku daina raina addu'a duk yadda take, idan zaku kwanta kuyi, idan kun tashi kuyi, idan zaku fita kuyi, idan kun dawo ma haka. Sannan ko da kuna aiki ne ku dinga kunna karatun Alkur'ani ku ajiye in sha Allahu sheɗanu ba zasu iya shigowa cikin gidanjenku ba. Wannan azkar ɗin na safe da yamma ku daure ku riƙa yi domin shine takwabin mumini. Sosai Malam ya tunatar dasu wanda suka yi alƙawarin daga yau zasu cigaba, shi kansa Habib ɗin kuka yake yana sake yin na damar abun da ya aikata. Ya taka Malam har waje sannan ya ce da Malam ɗin zai zo har gida ya same shi domin zasu yi magana. Haka ya koma gidan ya samu Zainab ta kunna ƙira'a ta ajiyar wayar a Palo. Lokacin da Habib ya ga jinjirar da aka nuna masa a matsayin tasa sai kawai ya fashe da kuka yana rungumeta. Ya sunkuya har ƙasa yana kuka yana daɗin ta yafe masa. Itama ta sunkuya suka saka yarinyar a tsakiya suna kuka. Ya ce "Ba'ayi mata huɗuba ba" Ya ɗago da sauri yayi mata kiran Sallah sannan yayi mata huɗuba. Ta ce "Sunan Mama ko?" Ya girgiza kai ya ce "Nadiya" Jin haka yasa ta sake fashewa da sabon kuka tana girgiza kai shima ya shiga girgiza nasa kan, ta kasa magana sai kuka shima ya kasa cewa komai kuma. Ita kanta Mama da take bayansu hawaye ne ke mata zirya.
*°ADAM*
Jin shuru-shuru har bayan sallar la'asar babu masu zuwa neman auren ne yasa ya kira amera ya tambaye ta ina Haura. Ta ce "Gata a baya na a goye" Adam ya ɗan yi murmushi ya ce "Haura fa amanar mu ce kin sani, bana son ki sauya mata da ga yadda kike Please?" Amera ta ce "Ban sauya mata ba, kuma ba zan sauya ba, amma dole nayi nesa da ita domin ban yarda da ita ba, nifa har ga Allah da zaka ji shawara da gida ka kama mata ta koma da nafi sakewa wallahi" Adam ya dawo bakin gadon ya zauna ya ce "Duk akan tace bata son mijinki ko?" Ya faɗa da sigar wasa. Ta ce "Allah na roƙa da ya zaɓa mana alkairi, kuma ya zaɓa mana rashin amincewar tata" Adam ya miƙe tsaye suka fito palo tare. Ya ce "Kira min ita?" Haka dole ta shiga dakin ta sameta a yashe a ƙasa. Ai da sauri ta kira Adam ya shigo yana kallonta. Ruwa ya ɗebo ya watsaa mata. Ai kuwa yana taɓa jikinta ta miƙe zaune. Sai ta fara raba ido. Ta ce "Guber ina Ammita?" Ta faɗa ta na fashewa da kuka. Sai kuma ta ce "Daddy suzo, an ɗaura ko?" Adam da amera dai sai binta da kallo suke yi jin wai Amminta da kuma wani Guber. Take tayi yunkurin yin wani abu amma taji jikinta ya sake, nan take ta gane ba lafiya ba. Ta na kallon tafin hannunta taga babu komai hakan ya tabbatar mata da cewar mafarkin da tayi gaskiya ne. Ta ce "Daddy sir yazo ko?" Adam da tausayinta ya cika sa, kamar ya rungumeta ya rarrasheta. Ya ce "Basu zo ba" ya faɗa a hankali. Amera ta kama hannunsa suka bar cikin ɗakin domin gaf take da wanke fuskar Haura da mari. Sai kuwa ta ɗauko wayarta ta biyo su palon. Ta ce "Daddy dan Allah muje gidan su, Please Daddy help me, yanzu haka ba lafiya ba tunda ai ya ce zai zo?" Ta faɗa tana jin wani tashin hankali domin gaba ɗaya shi take son gani, tsoro da kuma wani madaran san ganinsa ne ya taso mata, babu abun da take hangowa sai yadda Habib ya tsaneta kafin taje Garuk, kenan yanzu ma zai tsaneta, wannan dalilin yasa duk ta fita a haiyacinta. Adam ya ce "Honey please bari na Kaita?" ya faɗa yana jin wani mugun tausayinta. Amera ta ce "Babu inda zaka je wallahi, yau kwananka nawa baka fita, kuma waye sila, sai yanzu daga fara tashin ka, to babu inda zaka je" Haura ta kalli amera ta ce "Anty Please dan Allah ki..." Amera ta ɗaga mata hannu. Ta ce "Daddy to bani aron motar ka Please?" Da sauri ya ɗauki makullin ya bata, ai kuwa ta fita da gudu kamar zararriya. Adam ya ce "Da gaske tana son wannan gayan, Allah ya dawo da ita lafiya, kuma Allah yasa dai lafiya shima yaron, domin naga yana sonta shima" Amera dai bata ce komai ba, domin bata ma so ya bata motar ba, duk da tasan ta iya. Jikinta har rawa yake mata lokacin da ta shiga cikin motar, ta yi mata kii ta bar gidan a guje. Tana barin titin unguwar tasu taje hawa babban Titi bata tsaya duba komai ba ta shiga a guje, hakan yayi daidai da ɗaga wani mai mashin da goyo a bayansa zai karyo kwana ya shiga unguwar ta yi sama da shi ta buga. Lokaci ɗaya jama'ar gurin suka ranƙayo gurin suna salati, domin ta daki mashin ɗin da ƙarfi, kuma sai da yayi sama kafin suka zubo a kan titin, kuma cikin ikon Allah Mai tuƙawar ne ya iya miƙewa wanda aka goye ɗin kuma ko shurawa bai yi ba jine ya malale gurin...📝
S Reza.....
[09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*
*FCWA*
*22*
Da wani irin gudu Haura ta fito daga cikin motar ganin kamar Amminta ce a kwance cikin jini. Ai kuwa ta na ƙarasowa taga ita ɗin ce. Hakan yasa ta kurma ihu tana ja da baya tana kallonta, sai kuma take mata gizo kamar ita kamar ba ita ba. Sai Kuma ta dawo da gudu ta faɗa kanta tana kiran sunanta tana jijjigata. Mutane suka rirriƙeta ganin dai kamar ta na da alaƙa da gawar da ta buge ɗin. Duk yadda suka kai da tayi shiru taƙi sai ihu take yi tana kiran sunan Amminta. Wani ne ɗan unguwar taso da ya gane ta ya nuna har gidan Adam cewar yarinyar ƴar gidan ce. Hakan yasa aka ɗauki gawar aka yi gidan da ita. Ita kuma ta zabura da sauri kamar wacce ta tuna da wani abu,ta hau motar ta sake ɗaukar hanyar gidan Habib. Tana tafiya tana kuka. Lokaci ɗaya ta tuno da abun da Guber ya faɗa mata kafin ya bata wannan tsafin. Ya tabbatar mata da cewar muddin wani daga cikin garin Garuk yasan tana ɗauke da wannan tsafin halhalin kuma ta musulunta to tabbas daga shi har ita sai aljanun sun dawo kansu, yayi mata misali da wani da irin haka ya faru da shi har yanzu ba'a san inda yake ba. Hakan yasa gabanta ya fadi take tunanin Allah yasa Amminta bata ganta, ko kuma Allah yasa ba wani abu ne ya samu Guber ba.
A ƙofar gidan ta faka tana tura ƙaramar ƙofar ta buɗe ta shiga. Ƙofar palon ma a buɗe take, hakan yasa ta tura labulen ta shiga ta na kiran sunan sa a karon farko. "Habib!" Ta faɗa da karfi murya ta har wani diri take yi tsabar tsoron da ya cika ta. Lokacin kuma Habib ya fita, daga Zainab sai Nadiya sai wasu daga cikin masu zuwa barka ƙawayen Nadiya ɗin. Ai kuwa suna ganinta kowa ya miƙe jin yadda ta kira sunan da ƙarfi, Nadiya kuwa sai da gabanta ya fadi lokacin da ta haɗa ido da ita, ta shiga karanto addu'o'in neman tsari. Ta ce "Ina Habib?" Ta faɗa ta na kallon Nadiya da take shayar da jinjirar ta. Kafin Nadiya tayi magana Zainab ta wanka mata mari, Haura ta riƙe kumatu tana kallonta zuciya na ɗibanta. Sauran matan suka riƙe baki suna kallon ikon Allah. Zainab ta ce "Itace wannan sheɗaniyar mai bin bokayen da na baku labari" ai kuwa suka ce "Ita ce?" Ta ce "ita ce shegiya" take suka hau jibgarta kamar an aikosu, duka suke mata kamar zasu kashe ta. Ita dai Nadiya bata sa su ba kuma bata hana su ba, domin itama da lafiyar gareta da ta taya su, domin irin su Haura basu da amfani a cikin al'umma. Sai da suka mata shegen duka kafin suka turota har wajen get suka rufe gidan. Ta dinga kuka tana bubbuga get ɗin tana kuma zargin su. Anan ma babu yadda batayi ba domin tayi tsafin saboda ta rama amma babu komai. Nadiya ta kira Habib ta faɗa masa abun da ke faruwa, wanda a lokacin yana gurin Malam ya faɗa masa asalin laifin da yayi tun farko. Malam ya bashi shawara akan ya dage da tuba, kuma babu ruwansa da ita, kar ya sake dukanta koda tazo inda yake kawai dai ya naimi tsari da ita, idan SO samu ne yaje har gidan iyayenta ya faɗa musu abun da ya faru.
Tana tsaye a gurin tana ta kuka sai gashi ya ƙaraso. Tana ganinsa ta tsayar da kukan ta nufo shi da sauri tana ka sa ko yin magana tsabar farin ciki. Wannan wani irin so ne take masa, anya kuwa zata moru idan bai aureta abu, take duk wannan zafin jibgar da tashi suka tafi saboda da murnar ganinsa. Tana zuwa kusa da shi ya tare ta hannu ganin tana son rungumeshi. Ta ce "Sir ina ta jiranka, dan Allah kaxo muje a ɗaura wallahi na yiwa Daddy magana ya ce ko kai ne kawai kazo za'a ɗaura, kuma na shiga gidan ka matarka da wasu sun min duka duk saboda da kai" ta faɗa tana ta ƙoƙarin ganin sun hada jiki ga kuma wani sabon hawaye na gangaro daga ido guda ɗaya. Shi kuwa sai addu'a yake yana ta fatan Allah yayi masa tsari da ita, a ransa yana mamakin wai har wannan ya iya zuwa gidan boka. Ya ce "Haura na dawo hankalina, yanzu na san mai nake yi, kuma zan sake faɗa miki, bana son ki, bana son ki, dan haka ki fita daga sabgata dan Allah, wallahi ko mata sun ƙare a duniya ba zan taɓa auranki ba?" Ya faɗa kamar zai yi kuka domin ko maganar da yake yi da ita ji yake kamar dole, ya tsaneta tsana mai yawa. Ta ce "Sir ba zan iya ba, wallahi ina sonka kuma duk abun da nayi saboda kaine Please Sir, kar ka manta kaine ka fara sanina a matsayin Mace, kuma kamin alƙawarin zaka aureni, amma Sir sai yanzu kace ka fasa? Ka manta irin sadaukarwa da nayi maka, na baka komai harda rai na? Wallahi sai da rai nake sonka, idan ba'a bawa raina abun da yake so ban iya mutuwa sir please?" Lokaci ɗaya yayi wani tunani, tausayinta ya tsargu masa idan ya tuno da cewar tabbas shine mutum na farko da ya sameta a budurwa. Ya ce "Shiga motar taki muje gidan naku yanzu" ya faɗa a ɗan sakewar fuska. ta ce "Sai dai kaima ka shiga tawa motar mu tafi tare?" Ya ce "Sai na fasa zuwa" ai da sauri ta shiga, tana tuƙi tana kallon sa har suka iso ƙofar gidan Adam. Yayinda Habib ke cigaba da addu'a da kuma tattauna abun da ya kawo shi. Sai yanzu ma ta tuno da abun da ya faru ɗazu na Amminta, amma lokaci ɗaya sai taga abun kamar fa a mafarki ne ya faru, kawar da wannan batun tayi, ta bari idan na da gaske ne ai zata ga gawar Amminta ɗin a gidan idan ta shiga. Hakan yasa ta sauƙa ta buɗe get ɗin da kanta ta shiga da motar shima haka. Ganin bata ga kowa bane yasa ta fara tunanin to ina aka kai Amminta ɗin, ko har an binne ta. Tana gaba yana baya har cikin palon. Habib ya samu guri ya zauna, haura ta shiga ciki ta kira Adam wanda tare suke da amera suna hira akan fitar Haura ɗin da mota. Bayan sun gaisa Adam ya ce "Sai kuma muka jiku shiru Allah dai yasa lafiya?" Habib ya ce "Lafiya Alhamdu lillhi" ya gyara zama ya kalli Adam da Amera da ita kanta Haura ɗin da take zaune ta zuba masa ido birninta kawai taji anyi zancen aure. Ya ce "Zan so sanin shin kune kuka haifi Haura?" Suka kalli juna. Itama ta lalle su da mamaki. Amera ta ce "A'a ba mu bane gaskiya?" Habib ya ce "Su waye iyayenta?" Adam ya ce "Lafiya dai ko?" Habib yayi murmushi ya ce "Gata nan ta faɗa muku komai da bakinta?" Suka kalleta sai ta ce "Sir dan Allah a ɗaura auran yanzu daga baya sai ayi maganar?" Tayi maganar kamar mai shirin fashewa da kuka. Habib ya ce "Idan kin faɗa musu gaskiya zan yarda a ɗaura mana aure" ta ce "Kayi alƙawari?" Ya daga mata kai.
Ai kuwa nan take ta fara basu labarin abun da ya faru, daga lokacin da ta tabbatar da cewar Habib ya gujeta sai ta tafi garinsu. Shi kansa Habib sai yanzu yasan ita ɗin wacece. Amera kuwa tsabar tsoro yasa ta miƙe tsaye tana mata kallon mamaki. Shi kansa Adam bai taɓa kawo cewar zata iya komawa garinsu har ta karɓi tsafi ba. Habib ya ce "Dama ita arnan daji ce?" Amera ta ce "Kaman yadda kaji ta faɗa da bakin ta" Ya ce "Innalillahi wainnailaihi rajiun! astagfurulla! Take ya shiga salati yana tuba har da kuka. Shi kasan Adam hawaye yake yi domin Haura ta goge masa hadda. Amera ta ce "Tsintanciyar mage kenan, akan soyayya, kin bar Musulunci, sannan kin cutar da bawan Allah da matarsa harda mu gaba ɗaya, wallahi kinyi asara Haura, Allah ya wadaran ki, ai dama ni tunda kika dawo naƙi yarda dake, na faɗa masa ya ce wai ba komai saboda shi Man of God ne! Yafi kowa son kyautatawa, ai gashi yanzu kaji da bakinka". Adam ya rasa ma me zai ce. Ta ce "Dan Allah Daddy ka ba shi hakuri, wallahi yanzu bana tare da komai please a ɗaura auran ina sonsa har raina" Amera ta ce "Waye zai ƙara yarda dake Haura, yanzu haka dole ki bar mana gida domin ba zamu taɓa zama dake ba kina mushirika kafura sheɗaniya. Habib ya miƙe zai fita ta yi saurin kama masa Kafa, ya kalleta, sai kawai yaji wani irin ƙyamar kansa da tsanar kansa da jin haushin kansa na kusantarta da yayi, dole ne ma yaje asibiti a duba shi. Ya rasa mai zai ce mata. Sai kawai ya shiga kwace ƙafarsa ya ture ta ya fita. Tabi bayansa tana kuka tana faɗin zuciyarta zata mutu. Wani irin mari ya sauke mata wanda ke cike da ɓacin rai da zuciya da haushi da tuƙuƙin ɓakin ciki, bai ko bi ta kanta ba ya shiga mota ya nufi gida. Yana shiga gida yasa Nadiya ta haɗa duk abun da take bukata su koma gidan Mama. Haka a wannan yammacin ya haɗa komai nasa suka koma. Ya karya layinsa, ya toashe duk wata ƙofar da zata iya samunsa.
Sai da ya bar gidan kafin ta iya dawowa cikin haiyacinta. Ta fita waje ta bishi da gudu har bakin babban titi. Daidai gurin da ta bige Amminta ta tsaya tana dube-dube. Ta ƙarasa gurin mutanen da ta gani ta tambaye su ina aka kai matar da aka bige ana. Suka ce "yaushe?", ta ce "ɗa zu". Suka ce ai ba'a bige Kowa anan ba. Haka ta dawo gida duk ta rasa me zata yi. Ta na shiga gidan taga Amera ta na watso mata kayan ta harabar gidan akan ba zasu zauna da ita ba ta tafi garinsu taci gaba da tsafin ta. Adam ya fito da sauri ya kwashe kayan ya shigo dasu yana kamo hannun Haura ɗin suka koma ciki. Ya zaunar da ita a palo har zai yi magana ta miƙa masa makullin motar sa ta na jin kanta ya fara sarawa ga har yanzu ana kiranta. Ta ce "Daddy kayi hakuri ina son Habib zan iya mutuwa idan na rasa shi, ka taimaka min ka kira shi ya dawo?" Duk yadda yaso yayi mata magana ya kasa. Ya kalli