Showing 3001 words to 6000 words out of 58144 words
na tunanin tsawon lokacin da Haura take manne masa akan tana sonsa, kullum idan har tana da class ɗin sa haka zata dinga masa abubuwan da dole hankalinsa ya kai gareta, wasu lokutan har ofis ɗin sa take binsa, tun baya biye mata har ya fara yarda yana ɗan taɓa ta idan sun keɓe ko ya shafa ta. Daga fara mata haka kuma ta sake samun dama sosai domin ita har zuciyarta sonsa takeyi, shi kuma hakan da take masa yasa sheɗan ƙawata masa ita har yake aiyana yadda zai ji daɗi Idan ya samu burin ransa a kanta, gata yarinya ƙarana mai kyau ga tsafta, kuma daga gani yar manyan mutane ce, domin kullum cikin shigar kaya masu ɗan banzan kyau da nauyin kuɗi take.
Saida Habib yayi doguwar tafiya kafin ya tare mai ɗan sahu ya ƙarasa da shi gida. Yana shiga gidan yaga wutar palon a kashe hakan yasa yaji daɗi domin yasan Nadiya tayi barci kenan. Yana zuwa tsakiyar palon yaga haske ya karaɗe palon hakan yasa ya tsaya ya na juyowa ya sauke idonsa akan nata da tayi tsaye tana binsa da wani irin kallon tuhuma. Duk yadda Habib ya kai da ya ɓoye halin da yake ciki sai ya ƙasa domin ba zai taɓa iya samun kwanciyar hankali ba muddin bai san halin da Haura ke ciki ba. Yana tsaye yana kallon Nadiya amma ya fara tunanin yanzu idan ta mutu za'a zarge shi ne ko yaya, to an sanshi da ita ne ko wani yaga lokacin da suka rage a school ɗin, lokaci ɗaya ya tuno da Emeka yasan dole ne sai an zarge shi, hakan yasa bai san lokacin da ya furta "Innalillahi wa inna'ilaihi rajiun ba" Nadiya da fitar sautin salatin nasa ya sake haifar mata da wani irin tsoro da fargaba ta ce "Beb daga ina kake? Wai me yake faruwa da kaine?" Ta ƙarasa tana sakin kuka domin iya abun da tasan zata iya yi kenan a halin yanzu, gashi ba yaro ba bare ta zane shi ya faɗa mata wacce irin masifa ya tabo musu haka da ya kasa samun natsuwa. Sai a lokacin ya kula da cewar ashe fa a gida yake kuma a gaban Nadiya. Jin kukan da take yi ne yasa ya ƙaraso kusa da ita ya rungumeta da karfi yana jin ina ma shima zai iya yin kukan kaman yadda takeyi, sai yake jin ita ai kuka mara dalili takeyi shine ya dace yayi kuka mai dalili. Ta na jiran taji ya fara lallashinta kuma ya faɗa mata matsalar sa amma sai ta lura kamar ma hankalinsa baya tare da ita, sai ma wani irin matsa da yake mata kamar ya manta da cewar mutum ce kuma mace a jikinsa, macen ma mai juna biyu. Ƙarar da tayi ce tasa yayi saurin sakinta yana ja da baya yana kuma kafeta da ido. Sosai tsoro ya sake baiyana a fuskarta ta na furta Innalillahi a ƙasan maƙoshin ta domin lamarin nasa ya fi ƙarfin tunaninta. Juyawa yayi ya nufi cikin daki sai idonta ya sauka akan bayan wandonsa da ya faɗi ɗazu ya kwashi jar ƙasa. Binsa tayi da kallo har ya ɓacewa ganinta. Gaba ɗaya ta rikice to ko dai faɗa yaje yayi ne. Bata san lokacin da ta zauna daɓas a tsakiyar palon ba tana sake rushewa da kuka. Kusan minti ashirin tana kuka amma kamar babu kowa a gidan, haka dole ta tashi ta shiga cikin dakin da yake ta sameshi kwance, yana jin shigarta ya yi saurin lumshe ido kamar mai barci. Toilet ta shiga ta wanke fuskarta sannan ta dawo ɗakin ta hau kan gadon ta kwanta ta juyo tana kwallonsa. Kasancewar a kwai hasken wuta yasa ta kafe shi da ita, tana kallon yadda yake buɗe idon yana rufe wa kamar munafuki. Ta ce "Beb nasam ba barci kake ba, dan Allah ka faɗa min me yake faruwa, me ya kawo ƙasa a bayan wandonka a cikin wannan daren?" Ai da sauri ya mike tsaye ya duba wandon nasa sai ga nan alamun kasan. Hakan yasa ya cire wandon ya na faɗin "Faduwa nayi, kuma ki kwantar da hankalinki komai lafiya" ya faɗa yana shigewa Toilet ba tare da yasan mai zaiyi a ciki ba sai dan kawai ya gujewa tambayoyin wannan ƴar jaridar da ya samu yau. Yana shiga toilet ya sake haɗe kansa da bango yana ta tunanin yanzu gobe haka za'a je school a samu gawarta. Sai lokacin ma ya tuna bai duba gobe karfe nawa yake da class ba. Tuno da haka yasa ya fito da sauri kamar ma harda gudu ya hada a ganin Nadiya. Sai lokacin ya tuna da cewar ya bar wayar tasa a cikin ofis ɗin sa, sai ma lokacin wani tinani ya fado masa, anya kuwa a ofis ɗin ya bar wayar tasa. Take gabansa ya bada wani rass da ya tuna cewar tabbas da wayar a jikinsa ya zame wandonsa lokacin da yake ƙoƙarin yin abun. Da karfi ya furta "Na shiga uku na lalace" ya furta yana dafe koshi. Nadiya ta tashi zaune tana kwallonsa. Da sauri ya karasa gurin da laptop dinsa take June a jikin chaji. Ya buɗe ta hannunsa na rawa ya kunna. Tana daga gurin da take tana kallon yadda hannayensa ke rawa sun kasa bashi haɗin kai akan abun da zaiyi. Yana dubawa yaga yau class ɗin sa na yamma ne kawai babu na safe. Sai ya rufe laptop ɗin yana kuma jin ai dole ne ma gobe yaje school da wuri kafin kowa yaje, to amma idan kuma aka kama shi fa, to amma idan bai je ya ɗauke wayarsa daga gurin bafa har aka zo aka gani. Sai kawai ya bari akan gobe yaje da wuri ko iya wayar ya dauke koda kuwa mutuwa tayi. Yana kashe laptop ɗin ya juyo sai ya ga Nadiya zaune tana kwallonsa tana hawaye. Shi wallahi har mantawa ma yake yi da tana dakin.
Danne abun da yakeyi yayi ya hau kan gadon ya rumgumota jikinsa ya ce "Please I'm sorry, matsala ce ake so sai an dora min ita a makaranta wacce ban san da ita ba, hakan yasa gaba ɗaya na kasa natsuwa" ya ƙarasa yana jin shi da kansa ƙaryar bata samu gurin zama a bakinsa ba bare kuma zuciyar Nadiya da ya sani da saurin gane gaskiya ko ƙaryar da zai mata. Yana ji tace "Hum" daga haka kuma bata sake cewa kuma bai, kuma hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba domin bai son yin wata maganar kuma. Daga haka ta kwanta sai dai ta kasa barci tana ta hasaso abubuwan da zasu iya firgita mata miji kamar haka, amma duk tunanin da tayi sai ta kasa yarda, harda tunanin ko dai ciki yayiwa wata amma tasan ba halinsa bane. Sai kusan ɗaya yaji alamun barci ya ɗauketa hakan yasa ya ɗan leƙa fuskarta yaga da gaske barci takeyi. Sai ya tashi zaune yaci gaba da zaman jiran wayewar gobe. A kunnensa a kayi kiran sallah sai a lokacin ya tuna da ko magriba da isha bai samu yayi ba. Ya shiga toilet ya ɗauro alaula ya tada sallar magriba bayan ya idar yayi Isha. Ita kanta sallar yana yi ne yana tunani domin bai yi ta a cikin natsuwa ba. Sallar asuba ma a cikin ɗakin yabi jam'i duk da kuwa yasan illar yin hakan, yasan irin asarar da mutum ke yi idan ya rasa jam'i salla musamman salar asuba da Manzon Allah saw yake cewa "Tabbas munafuki baya iya tashi domin yin sallar asuba a jam'i, duk wanda ka ga yana iya tashi ya je masallaci domin yin sallar asuba to tabbas ba munafiki bane. Amma dukda wannan sanin haka ya danne har aka idar da sallar tare da shi. Daidai lokacin Nadiya ta farka tana furta addu'ar tashi daga barci wato "Alhamdu lillahil lazi ayana ba'adama amatana wa'ilaihin nushur. Ta bishi da kallo ganin yana salla a gida domin bata saba ganin haka ba. A cikin wannan satin ne ma yake makara har sai an tada salla zata tashe shi kuma haka zai yi alaula cikin sauri ya tafi, kasancewar taga baya barci da wuri, to idan ya dawo ne kuma zai ta barci har sai tayi da gaske zai tashi ya shirya ya tafi makaranta. Haka take ta fama kwana biyun nan. Ta ce "Beb salla a gida kuma kamar Mace?" Ta faɗa tana sauka daga kan gadon cikin muryar barci. Ya ce "Bana jin dadi ne" ya faɗa yana fita daga dakin ya dawo Palo.
Haka ya kishingiɗa a kan kujera mai ɗaukar mutum uku yana ta alla-alla gari ya ƙarasa wayewa. Yana zaune har shida da rabi lokacin gari yayi haske sai ga Nadiya ta fito bata ce masa komai ba ta shiga kichin. Sai lokacin taga kwanukan abincin sa da baici ta dawo dasu. Na safe ma sai almajirai ta bawa, haka na rana ma da taga bai dawo ba. Wannan kuwa shi zata ɗumama sai ta haɗa musu shayi tunda suna da bredi koda ƙwai huɗu ne sai ta soya musu. Tunda Allah yasa yau ya tashi da wuri itama bari ta haɗa komai da wuri sai ta kai masa kar ya sake fita barci komai ba. Bata fito daga kichin ɗin ba saida ta soya ƙwai guda huɗu ta hado ruwan zafi. Ta kawo dainintebul ta ajiye, sannan ta koma ta zubo jalof ɗin taliyar da waken da ta ɗumama a flet ɗaya ta ajiye. Ta kwaso kayan shayi harda biride ta ajiye duk tana yi tana satar kallon ganin hankalinsa baya gareta. Saida ta haɗa masa shayin kafin ta ƙarsa gurin da yake tana kiran sa. Firgigit ya dawo hankalinsa yana kallonta. Ta ce "Breakfast na gama ka tashi kaci da wuri kafin ka fita" ta ƙarasa tana barin gurin. Ya kalli a gogon palon mai irgen biyar-biyar sai yaga ya bashi karfe bakwai harda minti biyar ga kuma ɗan ƙaramin tsinken ya kusa hawa kan ɗaya number mai nuni da cewar da minti goma ya kusa. Ya kalli Nadiya ya ce "Bari na shirya nazo" ya shige daki yana jin shi har ma ya manta da batun abinci, baya ko iya tunawa da shi bare kuma yaci. Ko minti biyar bata ce yayi ba ya fito cikin shigar ƙananan kaya, yau ko samun damar gyara ma gashin bai samu ba, ta kalleshi ganin ya nufo gurin da take zaune tana jiransa. Tun kallon farko da tayi masa ta gane baya cikin haiyacinsa har yanzu, domin ba haka ya saba fita ba. Ya sunkuya ya ɗauki kofin shayin gabanta ya kurɓa sai ya ajiye. Sai ta kalli wanda ta haɗa masa a kusa da shi, ko bai ga wannan ɗin bane oho. Tayi tunanin zama zaiyi sai taji yace "Thank you Beb I'm okay, sai na dawo" yana faɗa kuma ya ja mata hanci ya bar gidan yana sauri. Har ya fita ta ƙaranin get ɗin sai ya tuna da bai ɗauki motar ba. Haka ya dawo ya tada motar ya fita daga gidan. Kamar kar ya dawo ya rufe get ɗin amma haka ya fito ya rufe yana kama hanyar school. Sosai yake gudu yana addu'ar Allah yasa shine mutum na farko da zai fara shiga cikin makarantar duk da kuwa yasan bashi da class ɗin safe. Amma sai me zai faru tun daga nesa ya hango get ɗin makarantar a wangale ga kuma dalibai har sun fara shiga. Ya kalli agogon motar ya bashi karfe bakwai da rabi harda minti ɗaya. Gabansa ne ya shiga bada wani irin sauti mai kamar ana dakan sakwara, dukda safiya ce sai ya ji kamar zufa ce ke ƙoƙarin karyo masa, musamman da yazo kusa da get ɗin yaga kamar mutanene a tsaitsaye ana kallon wani abu, wanda zuciyarsa ta raya masa cewar gawar Aisha Adam ce aka gani shine kowa ya tsaya kallo...📝
Muje zuwa a kwai ƙura a gaba.
S Reza...
[09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️*
*°S-Reza✍️*
_First class writers association_
_My Whasop chanel_
*Chapter 3️⃣*
Tsabar fargaba da saurin da yake na ganin ya shigo cikin makarantar domin ganewa idonsa abin da ke faruwa har ƙoƙarin bi ta kan wasu ɗalibai mata ya yi ba tare da ya ankara ba. Tsakanin get ɗin da cikin makarantar ma a kwai tafiya mai ɗan tsayi, hakan yasa yana shiga ciki da motar tasa sai yaga wani malami ne a gefe yana magana da wasu dalibai shine dalilin da yasa yaga sauran ɗaliban suna leƙawa. Yana gyara pakin ya fito da sauri ya nufi cikin makarantar ba tare da yayi wa kowa magana ba. Ofis ɗin sa ya fara shiga ya duba baiga wayar tasa ba, hakan yasa ya fito da sauri ya nufi class ɗin da abun ya faru. Koda ya shiga ɗalibai uku kawai ya gani a ciki, suka tashi suna gaida shi cike da mamakin ganinsa a irin wannan lokacin da sunsa ba shine zai karantar dasu ba. Bakin allon karatun yaje ya tsaya yana satar kallon gurin da abun ya faru a yammacin jiya. Sai dai bai ganta ba kuma bai ga wayarsa ba. Sake mayar da hankalinsa yayi izuwa gurin nan ma babu ita babu wayar. Duk da haka bai gamsu ba sai ya nufi gurin ya ɗan wayance harda sunkuyawa yana dubawa. Daidai lokacin kuma ɗalibai kusan su goma suka shigo cikin ajin mata da maza ana dariya, wasu ma zancen banza sukeyi. Jin haka yasa ya ɗago da sauri yana mamaki to me ya faru. Yana ji suna gaisuwa amma yasa kai ya fita duk jikinsa yayi sanyi. Ɗaliban suka bisa da kallo suna ta mamakin yanayinsa, ko dan irin wankan da suka saba gani a tare da shi yau babu. Ofis ya koma ya zauna sai ya fara tunanin to ko dai ba mutuwa tayi ba, ai kuwa idan bata mutu ba dole yau zata zo school kenan. Hakan yasa faɗuwar gaban nasa ya ragu yana so sai karfe goma zai koma class ɗin ko zai ganta. Haka yaci gaba da zama a cikin ofis ɗin har karfe goma sannan ya fito ya nufi class ɗin amma yaji an kira sunansa ta baya. Kaman a tsorace ya waigo yana sauke idonsa akan wani malami wanda tun zuwansa school ɗin dashi suke ɗan gaisawa sama-sama. Ya ce "Malam Habib dama class ɗin safe kake dashi yau?" Habib ya ɗan sosai kai ya ce "Amm da kawai na zo gurin wani malami ne zan amshi abu, yanzu zan tafi" ya faɗa kamar a rikice. shi kansa Malam Ali ya fahimci kamar dai wani abu na damun sa. Ya ce "Ok Tom bari na shiga nawa class ɗin lokaci yayi sai na fito zan zo ofis ɗin na same ka" yana faɗa suka sake yin hannu Malam Ali ya tafi, shima Habib ɗin ya kama hanya. Yana zuwa bakin class ɗin shi kuma malamin dake ciki zai fito hakan yasa ya yi saurin mika masa hannu suka gaisa. Ya shiga ɗaliban suka gaida shi. Nan ya fara raba ido ko zai hangonta. Gurin da take zama ya kalla yaga babu kowa a gurin, sannan ga wannan ƙawar tata da suke zuwa makarantar tare. Kaman ya kirata ya tambaye ta amma yana tsoron kar yaje daga yin tambaya ya tono wani abun. Haka ya wayance da tambayarsu wani abun daban sannan ya fita daga class ɗin. Wannan karan kam saida suka buɗe faken hirar Malam Habib, wasu na tambayar me yake damunsa, ko dai yana neman wasu dalibai ne jiya. Duk ya koma wani iri daga jiya zuwa yau, ya kasa sakewa yayi komai. Gashi bai san gidan su ba, shi babu ma abun da ya sani game da ita. Cikin motarsa ya koma ya shiga yana dafe kan motar yayi shiru kusan minti biyar bai ko rintsa ido ba. Sai kuma ya tada motar ya bar cikin school ɗin. Hanyar gida ya nufa sai kuma ya nufi gidan iyayensa domin tun jiya da yau duk bai jeba kuma ko kiransu bai samu yayi ba. Haka kawai zuciyar sa ke raya masa in sha Allahu bata mutu ba, ai kuwa idan haka ta tabbata shida ita kuma har abada, ko kallonta ba zai sake yi ba, bare akai ga yayi yunkurin aikata wani abu da ita. A ƙofar gidan ya ajiye motar tasa ya shiga da sallam. Mahaifiyarsa ta amsa ya ƙarasa ciki da ɗan rashin kuzari. Ita kadai ce a gidan sai ƙanwarsa da yasan tana school yanzu haka. Zama yayi akujera yana ta kokarin ganin ya kawar da komai dake kan fuskar tasa. Ya ce "Mama ina uni ya ƙarfin jiki?" Ya faɗa yana ɗan ƙirƙirar murmushi. Mama ta amsa tana tanbayarsa lafiya dai taga ya ɗan zube ko baiji daɗi ba ne. Ya ce "Eh Mama zazzaɓi ne ya ɗan dameni tun jiya, amma dai yanzu da sauki" ta ce "To Allah ya ƙara afuwa, ya ita Nadiyar da jiki, yanzu haka kake fita ka barta ita ɗaya a gida ga tsohon ciki?" Habib ya ce "Ai ina koma gida idan bani da karatun safe, yauma sai biyar zan shiga class ɗin duk muna tare da ita. Yana rufe baki sallamar Nadiya ta karade palon. Kasa amsawa yayi sai Mama ce ta amsa tana mata maraba. Itama tsaye tayi ganinsa a gidan sai tayi kamar bata gansa ba ta gaida Mama ta samu guri ta zauna fuskar nan a haɗe. Ƙanwarsa ce domin su ɗin ƴan ya ne da ƙanwa. Mama itace tasha nono ta sakarwa mahaifiyar Nadiya ɗin da Allah yayiwa rasuwa shekaru biyar kenan. Hakan yasa Nadiyar ta dawo gidan da zama, kuma dama tun kafin rasuwar a kwai shaƙuwa a tsakaninsu, da ta dawo gidan ne kuma ta koma soyayya har akayi aure. Nadiya na sonsa sosai, domin bata haɗa son da take masa da komai, sannan ita ɗin mace ce mai kishi sosai hakan yasa take godiya ga Allah da ya bata Habib domin shi mutun ne da bashi da lokacin