Showing 6001 words to 9000 words out of 58144 words

Chapter 3 - A Bar Wa Rai Complete Books By S Reza.txt

S Reza   

12 Mar 2026

18

mata, hakan yasa take ƙara alfahari da shi a ko ina. Tana iya bakin kokarin ta wajen rufa masa asirin gidan sa, domin tunda suka yi aure ba'a taɓa jin kansu ba, bata taɓa cewar yayi mata abu, tana da hakuri sosai wanda ya haɗu da son da take masa. Duk abun da yace ta bari to babu shakka ta bar wannan abun kenan, haka idan ya saka ta. Yanzu haka zuwan nan da tayi tazo ne domin ta bigi cikin Mama ko taji abun da yake damun sa saboda ta kasa natsuwa kuma gashi yaƙi ya sanar da ita, domin tabbas ta lura akwai abun da yake ɓoye mata kuma ko menene ba karamin abu bane. Mama ta ce "Yanzu kuwa nake tambayarsa cewar haka yake barinki ke ɗaya a cikin gidan?" Nadiya ta ɗan yi murmushi ta ce "Ai kusan muna tare dashi a gida, yanzu ma ban san nan zai zo bane yasa bamu zo tare ba. Mama ta ce "To ma sha Allah, Allah dai ya raba lafiya Kinga kema kya samu abokiyar hira ko abokin taya hira. Habib ya ɗan saci kallonta suka haɗa ido yayi saurin kawar da idonsa yana jin gabansa na faduwa da zuwan nata.

Dukda yasan bata saba kawo ƙararsa sa ba, amma yana jin kaman sauyin da ta gani ne yasa taxo ta sanarwa da Mama. Tashi Mama tayi ta barsu a palon. Ya dawo kusa da ita ya ce "Wa kika tambaya kika fito? Kuma me kika zo yi a wannan lokacin kamar an koroki?" Ta ce "Ai koroni ɗin kayi, kuma ba zan koma ba har sai ka faɗa min abun da yake damun ka, na gaji, gaba ɗaya ka sauya min, baka zama kaci abinci, jiya ina kula da kai ko barci ba kayi ba, yau da safe ka fita babu ko magana, ko ka gaji dani ne, idan ka gaji ka faɗa min sai na bar maka gida?" Ta ƙarasa da kamar faɗa. Habib sai rufe mata baki yake tana ture shi. Ya ce "Haba Beb ina ce na faɗa miki cewar wani sharri ake son ƙulla min a makaranta kuma Allah ya ƙwace ni komai ya wuce"

ta ce "To mai yasa baka koma gida ba?"

Ya ce "Ai daga nan gidan zan koma"

ta ce "Ka min alƙawarin cewar komai ya wuce ba zaka sake yimin irin abun da ka min ba?"

Ya ce "Nayi alƙawarin komai ya wuce" 

Ta ce "To kayi dariya kuma kace beb ba zan sake ba harda riƙe kunne?" Ya ce "Idan kuma Mama ta shigo fa, kizo muje gida har doki sai nayi miki?" Ta ce "No ni yanzu nake so kuma anan" Habib ya sunkuya ya kama kunne ya ce "Beb ba zan sake ba" ya faɗa yana miƙewa.
Ta yi dariya tana jin daɗin hakan. Ta kalleshi ta ce "Ya Allah duk masu son ganin sun tonawa Beb asiri Allah ka tona musu?" Ya amsa da amin. Ta ce "Mu dage da addu'a Allah na tare da mai gaskiya, duk yadda suke son ganin bayanka Allah ya fisu.

Kusan karfe sha ɗaya suka koma gida bayan ya biya sunyi siyayya na kayan kwalliya harda abubuwan sha da take so. Suna komawa gida suka shiga kichin tare yayi kokarin kawar da komai ya tayata sukayi girkin rana, kuma suka zauna suka ci. Suna ci suna hira amma hankalinsa naga agogo domin baya so ya makara, so yake biyar tayi masa yana cikin class ɗin yadda zai kori duk wanda ya shigo daga baya. Kamar daga sama yaji Nadiya ta watso masa tambayar da sai da ta hautsuna masa kayan cikinsa, har abincin da yaci na yunkurin dawowa tsabar tsoro. Ta ce "Na kira number ka ɗazu naji an ɗaga ina ta magana naji shiru, hakan ne yasa hankalina ya tashi, kuma ina ta kira ba'a ɗagawa, lafiya dai ko?" Ta faɗa tana zama kusa da shi. Tsabar firgita bai san lokacin da ya furta cewar "Ta ɗaga?" Nadiya ta kalleshi cike da rashin fahimta ta ce "Ita wa ɗin, number ka fa nake magana?" Sai lokacin ya kula da abun da yayi. Gaba ɗaya abun ne yayi masa biyu, farincikin bata mutu ba, da kuma tsoron abun zatayi da wayar gashi babu security a wayar. Ya ce "Eh ita wayar nake nufi, yanzu haka take min sai ta ɗaga kanta da kanta ko tana aljihu ne" ya faɗa ba tare da yasan lokacin da ya shirya karyar ba, kawai dai yaji tana fitowa ne daga bakinsa. Ganin kamar ta yarda sai ya ɗora da cewar "Faɗuwar da nayi jiya ne na zauna a kanta, to shine ɗazu da na fita na kaita gurin gyara, to ko tana gurin ne kika kira, yanzu ma haka zan biya ne na amsota idan zan tafi makaranta". Ya faɗa yana kuma jin ko shi ya gamsu da wannan batun. Ta ce "To Allah ya ƙara kiyaye wa beb. Ya amsa da amin. ƙarfe huɗu ya baro gida ya tsaya a wani masallaci yayi sallar la'asar. Yana fitowa ya nufi school ɗin. Bai shiga ajin ba sai biyar yana ta mamakin yadda Nadiya tace an ɗaga wayar to kenan ita ce ko yaya. Koda ya shiga class ɗin ya tarar an zo da yawa, amma ga guraren wasu nan da yawa basu zo ba. Nan take ya fara yin abun da ya kawo shi, duk wanda yazo sai ya kora shi waje. Sosai ya ya haɗe ransa Kamar kullum baya ko bada fuskar raini ga kwanni ɗalibi. Ya gama bayani kenan ya juyo yana neman ƙarin bayani a gurin ƴan ajin yaji ana shigowa, yana ɗaga kai ya ganta tana tafiya kamar mara lafiya, sanye da wani sket ɗan ƙarami ya ɗangale mata, fuskar nan tata babu ko kwalliya sai ma wani ɗan haske da tayi, jakar school ɗin ta rataye a kafaɗarta ta dama. Tsayawa tayi tana kwallonsa shima ya shagala da kallonta har ya manta da cewar a gaban dalibai yaƙe. Bai san lokacin da yace mata "Get in" ya faɗa har lokacin yana jin yanayin nata har cikin ransa. Lokaci ɗaya dalibai suka fara kallon-kallon, bayan kowa yasan halinsa na hana kowa shiga idan har ya shigo class. Ganin haka yasa ya yi saurin yiwa na waje alama da hannu akan suma su shigo. Haka suka shigo yaci gaba da jawabi amma hankalinsa na gareta. Ita kanta shi take kallo domin ko rubutu ɗaya batayi ba, yana ɗago kai sai ya samu shi take kallo. Dogayan ƙafafuwanta dake waje masu haske suna daga cikin abun da suke ɗauke masa hankali idan ya kalleta. Idan bai yi ƙarya ba har kanne masa ido yaga tana yi tana murmushi, zuciyar sa ce ke harbawa da karfi yana ta ƙoƙarin ganin ya natsu sosai. Haka ya gama koyarwar ya fita ya ya nufi ofis ya yi mata alama da ido akan ta same shi a cen. Yana shiga ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai zagaye yake yi yana ta alla-alla ta shigo ya amshi wayarsa ta ƙara gaba shima yasan inda dare yayi masa, tunda Allah yasa bata mutu ɗin ba. In sha Allahu ya ɗauki darasi daga wannan abun, ko kallonta bai zai ƙara ba. Yana cikin haka yaji ta turo ƙofar a hankali kuma ta rufe tana kwallonsa, shima kallonta yayi har yana haɗiye yawu ba tare da ya sani ba. Jakar hannunta ta jefar gefe ta nufo gurin da yake tana masa wani irin kallo mai tafiya da imanin mutum. Habib sai ya tsinci kansa da kasa daina kallonta. Ta tsaya a gabansa ta ce "Sir" sai kuma tayi shiru ta dafa girjinsa sai kuwa gashi ya zauna a kan kujerar dake kusa da shi...📝

S Reza...
[09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI!❣️*


°*S-Reza✍️*

_First class writers association_

_My whasop chanel_

*Chapter 4️⃣*
Cikin wata siririyar murya ta ce "Sir i miss you, ina ta tunaninka ko barci na kasa yi ina ta son nazo school kawai saboda na ganka, shin kaima ka yi kewa ta?" Ta ƙarasa ta na zama a kan cinyarsa. Kasa magana Habib ya yi sai binta da kallo kawai ya ke yi, ga shi duk ta cika masa ofis ɗin da wani almurin turare mai shegen ƙamshi. Tambayoyi ne da ya wa a bakinsa da yake so yayi mata amma ya kasa samun damar yin ko guda ɗaya. Bai san mai ya sa idan baya tare da ita yake jin zai iya rabuwa da ita ba, amma daga lokacin da suka yi ido biyu sai komai ya kama gabansa, sai ya ra sa wannan ƙwarin gwuiwar da yake tunanin yana da ita na rabuwa da ita. Jin ya yi shiru ta sake faɗin "Sir baka yi kewar tawa ba ko?" Ta faɗa ta na tura hannunta cikin rigarsa kan ƙirjinsa. Wani irin ajiyar numfashi ya sauke ya na lumshe ido. Iska ta hura masa a fuskar sa hakan yasa ya buɗe idon da sauri ya sauke a kan nata. Sai ta sakar masa murmushin nan na ta mai narkar da shi. Shi kuwa idanunta ya kalla masu ɗan girma sai yaga yadda suka bada wani irin kala kaman jaa kaman kuma fari. Gabansa ne ya faɗi, domin sai yanayin idanunta suka yi kaman ba na mutane ba. Sai lokacin ya samu damar yin magana kamar mara lafiya ya furta "Ina waya ta?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye bayan ya ture ta ta sauƙa daga jikinsa. Kawar da kai gefe ya yi ganin ƙirjinta a waje lokacin da ta tashi, har tsoron haɗa ido da ita yake yi. Ita kuwa sai ta tsinci kanta da son rungume shi domin da gaske tayi kewarsa, hakan yasa bata tsaya yin tunani na biyu ba ta rungume shi na kusan minti ɗaya kafin ta sake shi jin bai hanata ba kuma bai taɓa ta ba, ya dai tsaya kamar gungume a tsaye ƙiƙam. Ya sake ce wa "We're is my phone?" Ta ce "Sir wayarka na mantota a gida saboda saurin da nakeyi, amma idan ka na so yau kazo gida anjima sai na baka, ko ka bari ranar Monday na kawo maka school" Da sauri ya ce "What akan me zan zo gidan ku, saboda me?" Haura ta ce "Sir baka sona kenan?" Ta faɗa kamar tayi kuka da wannan malalaciyar muryar tata. Habib ya kalleta da mamaki a zuciyarsa ya furta so kuma dani!. A fili kuma ya ce "Soyayya kuma?" Ya faɗa da mamaki. Domin shi dai bai jin sonta, amma yana jin tana burgeshi, yana son ya ganta, kuma yana jin daɗin magana da ita, muryarta na masa daɗi sosai. Ya na faɗa ta juya da sauri ta ɗauki jakarta ta gyra rigarta, ta ɗauki biron gabansa tayi rubutu a wata karamar takarda ta ajiye masa ta juya har zata fita sai kuma ta juyo ta ce "Idan kana son wayarka kazo ka amsa ko ka kira wannan number". Ta na faɗa ta bar ofis ɗin ya bita da kallo. Da sauri ya ɗauki takardar yana dubawa. Sunan unguwarsu ne da number gidan su, kuma ga number waya nan da alama tata ce. kaman ya yayyaga takardar amma ya fasa ya saka a aljihu ya shirya ya fito daga ofis ɗin yana kallon yadda har aka kusan watsewa daga school ɗin. Yazo zai buɗe motar ya shiga yaga anyi rubutu a murfin motar da farin abu. Ya tsaya yana karantawa kamar haka. Sir I'm waiting for u in my dream, Sir don't forget about your phone, Sir I'm in love with you, Sir i love You to moch Bay". Yana gama karantawa ya shiga waige-waige ko zai hangonta, amma ko mai kama da ita bai hango ba. Da sauri ya shiga goge wa da hannu, ganin yana goguwa ne yasa ya buɗe motar ya ɗauko sauran ruwa ya shiga wanke wa. Yana gamawa ya buɗe matar ya shiga, ya ɗwuke ki zai kunne kenan yaga rubutu akan sitiyarin motar da wata farar takarda ƴar ƙarama. Gabansa ne ya bada wani rass, zuciyar sa tayi wani irin tsalle kamar zata fito, waro ido waje yayi yana dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya, sannan ya shiga duba takardar da kyau. "Sir I love you" Shine abun dake jikin takardar, sosai ya shiga duba cikin motar, to ta ina ta shigo, shida kansa ya buɗe motar da zai shigo fa. Sosai hankalinsa ya tashi ya rasa ma to wani tunani zaiyi domin wannan lamarin a kwai ɗaurewar kai sosai.

Ya na hanyar gida ya na ta mamakin yarinyar, amma ta ɓangare ɗaya kuma ya na jin sanyi da Allah yasa ta na nan da ranta kuma babu abun da ya sameta. Gaba ɗaya ma ya manta bai iya tanbayarta yaya aka yi ta fita daga cikin school ɗin ba bayan an rufe get, to ko dai a cikin school ɗin ta kwana. Shi kadai dai yake ta tunani har ya iso gida. Bayan ya faka motar ya koma ya rufe get ɗin ya nufi cikin gidan da sallama. Jin ba'a amsa bane yasa ya nufi ɗakin sa domin ya ɗauro alaula jin an ta Sallah. Lokacin da ya fito ya samu Nadiya ta na salla a palon hakan yasa ya wuce ta izuwa masallaci, har lokacin tunanin abun ya ƙi barin kansa. Koda ya dawo bata palon hakan yasa ya nufi cikin ɗakin na ta. Ya na shiga ya sameta zaune da waya a hannu. Yana shiga ta ce "Ina wayarka?" Ta faɗa babu wasa a muryarta, kuma ga wani kwantancen rigima da ya hango a kan fuskar tata. Habib ya kalleta da mamaki kuma duk rashin gaskiya sun baiyana a fuskar sa, da gyr yayi ƙarfin halin faɗin "Ta na ta ta na ta gurin gyra ai na faɗa miki"  Sai ta miƙe tsaye wanda hakan yasa saida ya ɗan ja baya domin ya tsorata da yanayinta. Ta ce "Beb ina wayarka, bana son ƙarya wacce shegiyar ce ka bawa da har take turo min sako ta whasop, kuma har take kirana sai na ɗaga taƙi yin magana ?" Daram dararam! Gaban Habib ya bada wannan sautin. Da Karfi ya fisge wayar yana kallo kamar zai shiga cikin ta. Gashi nan har yanzu ana online a wayar, ga saƙo nan kusan guda biyar ana turowa harda kira da akayi. Sai kawai ya tura kira shima ta whasop ɗin yana jin wani sabon tashin hankali da wannan yarinyar ke son jefa shi, shi ina zai iya da rikincin Nadiya gata da ciki dama ya ya aka ƙare. Ya gama karantawa amma ya kasa ɗagowa su haɗa ido, gashi har kiran ya yanke ba'a ɗaga ba. Fizge wayar ta yi ta ce "Baka faɗa min ba wacce?" Ta faɗa cikin tsawa wannan karan ma. Habib ya auro dauriya ta mazaje ya ce "Wai mata suna gyaran waya ne, nace niki gurin gyara na kaita, kuma ɗazu naje bai fito ba, shi yasa da kika ce an kira ki abun ya bani mamaki. Tayi masa wani irin kallon rainin hankali ta ce "Tun fa ɗazu nace maka an kira ni, Ok ita wayar sai ta zaɓi iya numbar na ta kira, kuma sai ta hau whasop nan ma ta zaɓi iya numbar na ta turawa message irin wannan ko? Shin Habib wai ka fara kula-kulan mata ne ban sani ba, na rantse da Allah idan har na sameka da cin amana ta zaka sha mamaki, kasan wacece ni, kasan abun da zan iya da wanda ba zan iya ba. Ta na faɗa ta bar masa dakin ya bita da kallon mamakin jin yadda ta ambaci sunansa ɓaro-ɓaro a bakinta wanda rabon da yaji ta faɗa tun da suka fara soyayya.

Da sauri ya bi bayanta ya samu bata palon. Sai ya bita kichin ɗin ya samu tana juye abinci a kula sai turiri abincin yake yi. Da saurinsa ya nufo gurin ta zaiyi magana tayi saurin nuna shi da chokalin hannunta ta ce "Karka ce min komai Wallhi idan kamin magana zan kwaɗa maka wannan chokalin. Ta faɗa tana kawar da kai tana cigaba da abun da takeyi. Juyawa yayi bai ce komai ba ya bar gidan gaba ɗaya da motar sa yana jin wani irin ɓacin rai, mai yasa zata dinga kiran matarsa, bata da hankali ne, sai kawai ya nufi unguwar da ta rubuta masa yana jin yau sai ya wanke mata fuska da mari sau babu adadi, kuma yayi mata ƙargaɗi akan ta fita daga sabgarsa.

*°HAURA*
Aisha Adam sunanta kaman yadda ku ka sani, amma ta na amfani da sunanta na asali a school. Ta na zaman ruƙu ni a gurin Amera da Adam wanda suka ɗauketa kamar ƴar su. Su biyar ne a gidan Adam sai Amera sai ƴan biyunta da ta haifa Salim da Salma sai ita Aisha ɗin Wato Haura. Tun lokacin da ta zama ƴar gida basu taɓa nuna mata wani banbanci tsakanin ta da Salim ko Salma ba, hatta su kansu basu taɓa sanin cewar ba Amera ce ta haifi Haura ɗin ba. (Duk mai son jin asalin labarin Haura yaje ya naimi littafin Amera da Adam) Sun tashi cikin soyayyar juna sosai, domin babu laifi Adam na da rufin asiri sosai, dukkanin bukatunsu ya na ƙoƙarin sauƙe musu. Anan hannunsa ta yi secondary har izuwa yanzu da take matakin diploma shekara ta karshe. Bata da matsla dasu haka suma suna jin daɗin zama da ita. Ta na musu biyya daidai gwargwado haka kuma ta na jan ƴan ƙannen nata a jiki sosai domin duk inda take suna nan. A wannan shekarar zata kammala karatun ta daga nan kuma zata cigaba kaman yadda tace musu kuma suka bata goyan baya, dukda cewar su ɗin suna son yi mata maganar aure amma suna tsoron kar taga ko da wata manufa ne, kar tayi tunanin ko sun gaji da ita ne. Haura yarinya ce karama sosai kuma a kwai rashin wayo sosai a tare da ita, sannan hausarta bata fita daidai har wannan lokacin. Bata tsayawa da samari kwata-kwata duk da yadda suke yawan tsayar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login