Showing 57001 words to 58144 words out of 58144 words
Amera ya ce "Zaki iya zama da ita a haka a matsayin kishiya Honey?" Adam ya faɗa har cikin ransa. Amera ta tsaya chak tana kallonsa, wani abu mai kama da sarewa da kuma tsoro ya shige ta. Ya ce "Eh idan har zaki yafe mata zan aureta a haka, Amera nasan zuciyarki mai kyau ce, kuma kin san halin Haura ko wannan abun gaddara ce yasa da kuma yarinta, amma nasan ita kanta tayi nadama" Haura ta ce "Daddy ina son Habib shi kawai zuciyata ke so dan Allah ka taimaka min na same shi, Daddy ka taimakawa rai a bashi abun da yake so Daddy please?". Amera ta riƙe kai ta rasa abun cewa, har ga Allah a wannan matakin muddin yace zai auri Haura to tabbas ta haƙura da auransa wallahi wallahi ko shine autan maza ta bar shi kenan, ai so ba hauka bane, me ya rasa, mai ya gani a jikinta, abu kamar dai shima asirin tai masa. Adam ya ce "Haura Habib ba zai aure ki ba, domin baya sonki, abun da kika yi masa ya sake shi ya dawo hankalinsa, Haura Daddynki yana sonki, shima ransa na sonki ki daure ki ba wa ran Daddy dama da lokaci Haura?" Lokaci ɗaya ta sake fashewa da kuka da ƙarfi ta tashi da sauri ta shiga ɗakinta tana ta ihu zuciyarta na mata zafi. Shima sai ga kukan nan ya fara zuwar masa da hawaye.
Ya kalli Amera da itama kukan ya fara biyo kumatunta. Ya ce "Honey zuciyata zafi take min, rai na na sonta ba domin kin gaza a komai ba, haka kawai nake son na taimaka mata. Please ki bani goyon baya na cikawa zuciyata burinta dan Allah ki yarda a bar wa rai abun da yake so please Amera kiyi jahadi?" Amera ta fashe da kuka mai karfi ta ce "A bar wa rai abun da yake so koda mai cutar da shi ne? A bar wa rai abun da zai hallakar da al'ummar da suke tare da shi? A bar wa rai abun da baya sonsa, Honey yarinyar nan ba alkairi bace, wallahi babu alkairi a tare da ita, a hakan zan haɗa miji da ita?" Adam ya ce "Ba halinta bane, nasan wacece haura ta tuba har abada Please Honey?" Amera ta sake rungume shi ta ce "Sai dai ka sauwaƙe min sai ka zauna da ita, wannan shine adalcin da zan iya maka daga kai har ita" Adam ya ce "Ba zan iya ba, kuma ba zan iya ƙin aurenta ba" Amera ta ce "Honey na yarda ka aureta na yarda" Ta faɗa har tana zubo da majina daga hancinta tsabar kuka. Adam ya matseta a jikinsa yana rarrashinta.
A cikin daren bayan sallar ishe Adam ya kira Amera ya kira Haura wacce har lokacin kuka yake yi. Babu abun da take kira sai Habib da cewar zuciyarta na mata zafi. Sai da Adam yayi da gaske kafin tayi shiru, gaba ɗaya ta rame tayi baƙi duk ta sauya kama, kamar ma bata cikin haiyacinta. Ya faɗa mata cewar abun da tayi kuskure ne, kuma shirka ne, saboda haka ta tuba kuma ta sake ƙarɓa Musulunci kuma tayi alƙawarin ba zata sake fita ba, kuma ko garin nasu ba zata sake zuwa ba. Anan taso ta faɗa musu abun da ya faru na Amminta amma taga ba amfani domin ta tabbatar hakan ya faru ba anan bane. Haka tayi alƙawarin aka bata kalmar shahada. Sannan Adam ya ce gobe da safe za'a ɗaura musu aure. Tana jin haka ta fashe da kuka. Daga haka Amera ta tafi ɗakinta bata san yaya suka ƙare ba, tayi alƙawarin ba zata sanarwa kowa ba, ta cigaba da addu'a tana kaiwa Allah kukunta akan idan har ba alkairi bane kar Allah ya tabbatar da wannan auran, idan kuma da alkairi Allah ya sanyaya mata zuciya. Ranar batayi barci ba, haka ta kwana tana Sallah harda kuka da hawaye. Ba ita tayi barci ba sai bayan da tayi sallar asuba.
Ihun su Salim da Salma ne ya farkar da ita. Jin kukan nasu kamar bana lafiya bane yasa ta kwaso da gudu ganin har rana ta fito. Maza ta gani su biyar Najib kawai ta iya ganewa sai Adam da ya zauna ya dafe kai yana hawaye, sauran kuma da baƙaƙen kaya an luluɓe gawa a palon gidan. Hakan yasa zuciyarta ta yi sama da ƙasa. Take taji kanta na juyawa ta kasa fahimtar abun dake faruwa. Ta ƙyr ta iya fadin "Innalillahi wa inna alaihi rajiun tana nufar gawar da ta buɗe da ƙarfi taga Haura kwance fuskarta tayi baƙi kanta babu gashi, gaba ɗaya a harƙitse take.
Abun da ya faru shine... A cikin daren nan shima Adam bai iya barci ba ya tashi ya dinga Sallah yana kaiwa Allah kukansa akan idan Haura alkairi ce ya tabbatar masa. Duk yadda yake jin sonta amma bai manta da zabin Allah ba. Itama Haura haka batayi barci ba, a daren ta fita izuwa gidan Habib wanda zuciyarta ke janta. Duk da nisan gidan haka ta taka a ƙafa a cikin daren. Sai dai koda taje gidan a rufe, anan ta zauna ta dinga rusar kuka tana bubbuga musu ƙofar, ganin kamar a rufe yake ta gaba sai ta kamo hanya tana tafiya tana kuka har gida. Lokacin da ta shiga ɗakin ta ɗauko waya ta shiga kiran sa. Lokaci ɗaya taji an shaƙe mata wuya, take kuma maganar da Guber ya faɗa mata ta dawo mata akan muddin wani abu ya faru zata haukace. Babu abun da take ji a kanta sai sunan Habib hakan yasa itama ta fara kira sunan nata, nan take aka fara abartar da ita, a turata nan a jawota nan. Sanin abun da zai faru da ita ne yasa da hannunta ta ɗauko wuƙa ta daɓa wa kanta. Nan take ta fara shure-shure, duk da haka sai da suka mayar da ita kamar ba ita ba kafin ta mutu. Sosai mutuwar ta taɓa su, musamman ma yaran da suka saba da ita sosai. Shi kuwa Adam sai da yayi jinyar zuciyarsa kafin ya iya saduda. Amera ta ce "Tabbas duk abun da zaka yi ka riƙa saka Allah a ciki domin ya zaɓa maka mafi alkairi" Adam ya ce "Allah ya saka miki Matata ya sauƙeƙi lafiya. Ta amsa da amin. Haka suka cigaba da rayuwa har cikin Amera ya tsufa ta haifi namiji mai kama da babansa.
Alhamdu lillhi, tammad bihamdilla, anan littafin A bar wa rai yazo karshe, kurakuran dake ciki Allah yayi mana abuwa ya yafe mana. Abun da ke na faɗakarwa da ilmantar wa Allah ya bamu ikon yin aiki da shi. Yan uwa ayi min afuwa wannan littafin tunatarwa ne gare mu akan sakaci da addu'a, da kuma illar biyewa zuciya, da rai, son zuciya bakinta inji hausawa. Ina muku fatan alkairi daga S Reza....