Showing 33001 words to 36000 words out of 58144 words
kallo irin na tsana ya ce "Ina ne unguwar?" Ta juya ta bar palon ba tare da ta bashi amsa ba. Nadiya ta ce "Please Bebb babu ruwanka da ita dan Allah?" Yana shiga motar ya sameta zaune ta ɗaga kai sama hawaye na zubo mata. Yana shigowa ta dawo da kallonta ga reshe ta ma rasa mai zata ce. Sai da ya bar gidan ta iya yin ƙarfin halin faɗin "Kayi blocking dina, kaƙi zuwa gidan mu, kabar school, baka nemana, yanzu nazo gidan ka kana faɗa min wannan maganar mai kake nufi da ni ne sir?" Ta faɗa da muryar kuka.
Da Karfi ya gangara cen gefen titi ya buɗe motar ya fita, itama ta fita ya zagayo yana zuwa ya ɗauke ta da mari ya ƙara mata a ɗaya jumatun, shi kansa yaji yadda marin ya shigeta sosai. Ya ce "Ga abun da yasa nan dan uwarki! Wai ke wacce irin jakar mace ne, ana soyayya dole ne, me nene dalilin da zai sa ki biyo ni har gida, tun ba yau ba na faɗa miki ina da mata, kuma ni ba aure zanyi ba, ko ma aure zanyi sai na rasa wacce zan aura sai ke mara kamun kai mai bin maza har gida". Ya ƙarasa ya na jin kamar ya shaƙeta ma ta mutu kowa ya huta. Babu abun da take yi sai kuka, ta riƙe gurin da ya mareta. Ta ce "Kenan saboda baka son haduwa da ni yasa kabar aiki kuma kayi blocking dina? Sannan saida ka lalata min raruwa shine kake cewar na fita a sabgarka, kenan dama abun da kake so daga gareni kenan kuma ka samu, shine ka guje ni?" Ta karasa tana fashewa da wani kuka mai karfi, wanda ke fita daga cikin zuciyarta. Ya ce "Wallhi ban taɓa sonki ba ko sau ɗaya, kuma ba zan taɓa ba, ko abin da ya faru tsakanin mu tsautsayi ne da sha'awar ki da kuma ke da kike ta chusa min kanki, kuma nayi nadama, daga yau karki ƙara nuna kin sanni, babu ni babu ke har a bada, idan kuma ba haka ba, wallhi zan baki mamaki na faɗa miki". Lokaci ɗaya Haura ta ɗan saki wani irin murmushi mai ciwo a zuciyar wacce irin wannan abun ya taɓa faruwa da ita ne kawai zata ji irinsa. Ta ce "Kalalat min rayu, ka zageni, ka kuma mareni, ka kirani da jaka ƙazama mara kamun kai mai bin Maza, kuma kace na rabu da kai, sai dai kasan me Wallhi ba zan iya rabuwa da kai ba, ko mai zaka ce min ka faɗa zan jure, kuma zan sake faɗa maka cewar ina sonka Sir?" Ta ƙarasa tana fashewa da wani sabon kuka sannan ta faɗa a jikinsa. Sonsa ne ke ƙaruwa duk zagi ɗaya da zai mata, ba zai gane ba ne, ita da rai take sonsa, zata iya haukacewa muddin yayi mata haka. Da karfi ya cireta daga jikinsa ya sake falla mata mari, ya ƙara mata. Ya ce "Ba dai ke mahaukaciya ba, yar isa karuwa ba, ina daidai da ke, Allah sai nayi ajalinki anan, kowa ya huta, kin bata min rayuwa kin sa na aikata abun da ban taɓa yi ba, nayi Wa mata na da iysyena karya, na rabu da aiki na, na kasa samun kwanciyar hankali. Ta sake fashewa da kuka ta ce "Ka kirani da komai ma amma ina sonka kuma ba zan daina sonka ba har abada, kuma dole sai ka aureni wallhi". Habib ya ce "Sai na aureki ko, zan kuwa babi mamaki, sannan ma a ina kika san mata na?" Ya faɗa yana matse mata baki, domin shifa har ga Allah ya tsaneta wanda bai san dalilai ba. Haura ta kwace da kyra ta sake fashewa da kuka. Sai da tayi mai isar ta Kafin ta ce "Saboda ina sonka yasa na nemo number ta, kuma karka manta kai da kanka kafin na yarda na baka kaina kamin alƙawarin zaka aure ni, Sir wallhi ina sonka sosai, zan iya mutuwa idan na rasa ka, raina ne ke barazanar fita idan na rasa ka, ban taɓa son kowa ba sai kai, Sir ka taimake ni ka Aure ni domin kar Na shiga wani hali pls Sir?" Habib ya tofa mata yawi tsaɓar takaici sannan ya shiga motarsa ya ja ya bar ta a duke tana kuka. Ta daɗe a haka kafin ta share hawayen ta tare mai mashin ta faɗa masa inda zai kaita. Tana hanya tana ta kuka tana tunani, zuciyarta tayi mata zafi sai take jin kamar mutuwa zatayi. Suna ƙarasawa ta sauka kenan sai ta kasa tsayuwa da ƙafafunta ta zube a gurin sumammiya. Tana buɗe ido ta ganta a Palo Amera tsaye a kanta. Ta sake fasa wani irin ihu tana kiran sunan Anty? Ta ce "Waiyoo Anty zuciyata na min zafi, please kira min shi yazo kar Na mutu?" Amera ta ce "Waye ne, me ke faruwa ne, ina kika je mai ya faru da ke?" Ta jera mata tambayoyin cikin tashin hankali. Ai da sauri ta ɗaga waya ta kira Adam ta sanar da shi halin dake faruwa. Haura ta ce "Anty zan mutu, zuba min ruwa anan please Anty?" Ta faɗa tana nuna mata zuciyarta. Amera ta ce "Bari Daddy yazo muje asibiti ko?" Haura ta kafe Amera da ido ta ce "Aunty ya yaudare ni, wai she ba sona yake ba, wai baya sona Anty wai bai taɓa sona ba Anty dan Allah ki taimaka min ki kira min shi dan Allah Anty?" Ta karasa tana sakin wani tari sai ga gudan jini ya faɗo ɗan ƙarami. Amera ta fasa uban ihu tana rike ta, lokaci ɗaya ta fara wani irin jijjiga tana juya wuya da cikinta, ana haka Adam ya shigo gidan a rikice. Yana ganin halin da take ciki ya saɓe ta izuwa asibiti. Itama ta biyo bayan su...✍️
S Reza...
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI❣️*
*FCWA*
*Chapter 14*
Har suka isa asibitin ihu take yi ta na faɗin zata mutu, waiyoo ƙirjinta zafi, ya cuceta, ya ce baya sonta. Sannan har lokacin jini na fitowa daga bakinta, gaba ɗaya ta fita a haiyacinta shi kansa Adam a tsorace yake ganin yadda take yi kaman zata mutu.
*°Adam*
Zaune yake a gaban likitan yana sauraron bayanin da yake masa. Sai da ya gama gaba ɗaya kafin yayi ƙarfin halin faɗin "Ciwon zuciya fa likita? wannan ƙaramar yarinyar ita ce ciwon zuciya zai kama? To a garin yaya?" Yayi tambayar da tsoro da mamaki. Likitan ya ce "Wannan ba ƙaramar yarinya bace allaji, kuma nima tambayar da nake son na maka kenan a matsayin ka na mahaifinta, me nene yake damunta har haka da zai lalata mata rayuwa?" Adam ya ce "Babu abun da ke damunta likita, hasali ma ita bata yin rashin lafiya, bamu taɓa kawota asibiti ba, bana tunanin da gaske ne wannan ciwon da ka faɗa ne yake damunta". "To akwai abun da yake damunta domin tabbas zuciyar ta ta kamu da ciwo wanda daf take da bugawa, yanzu munyi mata allura an saka mata ruwa, zuwa anjima zata farka, mun mata wannan ne domin ta samu hutu da ƙarfin jiki, idan ta farka zaku iya tafiya domin maganin ciwon ƴarku yana tare da ku muddin kuna son rayuwarta, dole wai abu ne tasa a ranta kuma yake ƙoƙarin gagararta shine ya haifar mata da hakan, ina mai sake jaddada maka cewar idan har baku zaunar da ita kun ji damuwarta ba, zaku iya rasa ta". Likitan na gama faɗa ya miƙa masa hannu alamun ya gama dashi. Adam ya fito daga ofis ɗin duk ya na rasa tunanin mai zaiyi. Kenan dai Haura Soyayya ce ta saka mata ciwon zuciya ko dai wani abu ne daban. Lokaci ɗaya wani irin mahaukacin kishi ya ɗarsu a zuciyarsa, sai kawai ya dinga nazarin abun da ya dace yayi a wannan gaɓar, a garin yaya har ya bari Haura ta fara Soyayya har tayi irin wannan nisan a ciki.
Shiru ne ya ratsa palon gidan nasu na ɗan daƙiƙa kaɗan yayin da kowa ya shiga tattauanawa da zuciyarsa akan wannan lamarin. Babu abun da ya tsayawa Adam arai kaman ciwon zuciyar da likita ya tabbatar masa da cewar ya kamata kuma a kan s, son ma son wani ba shi ba. Yanzu gashi ita da kanta ta sake tabbatar masu duk abun da ya faru tsakanin ta da shi, kuma ta na faɗa tana kuka akan dan Allah Daddy ya taimaka ya kira mata shi, gashi ya mayar musu da yarinya kamar wacce ta samu taɓuwa, yau ɗaya duk ta rame sai kuka. Wani ƙatoton abu ne ya tsayawa Adam a wuya ya kasa tafiya kuma ya kasa dawo da shi. Idan ya kalli Haura sai ya rasa mai zai ce mata. Amera ta ce "Yanzu fa dole ne zaka tashi keje gurin wannan yaron kaji gaskiyar abun da ya faru, idan ma ta kama hakuri zaka bashi to sai ka bashi haƙuri domin dai kana ganin halin da take ciki" Amera ta katse shurun da palon yayi da wannan maganar. Adam ya mata wani kallo ya ce "Kina ji ta ce harda dukanta yayi, harda barin aiki dauk dan baya son ganinta, to ana soyayya dole ne, wani irin zubar da mutunci ne wannan ace wai ni uban yarinya naje ina bawa saurayi haƙuri yazo ya auri ƴata?" Amera ta ce "To ai dole ce tasa, wallahi kamawa tayi, idan ma har fiye da Haƙuri ne ai za'ayi, kaga idan ma kai ba zaka iya zuwa ba ni zan iya takawa har gidan na bashi hakuri, ai risinawa wasa ba gajiyawa bane,meye a cikin bada hakuri dai kawai Allah natuba!. Haura da tun ɗazu take sauraronsu tayi shiru a palon ta na ta tunanin abubuwan da suka faru tsakanin ta da shi. Lokacin da ta fara ganinsa, lokacin da tazo shiga class yayi mata tsawa, lokacin da suka jero tare da shi kawai ta na kallonsa, lokacin da ta sameshi a ofis na farko, lokacin da ya fara shafa jikinta, lokacin da take masa murmushi idan ya shigo class, lokacin da take ware masa ƙafafuwanta, lokacin da suka rage a school daga shi sai ita har komai ya kusa faruwa har ta suma ya gudu, lokacin da suke waya tana masa shagwaɓa, lokacin da yazo gidan su, lokacin da ya zo ya ɗauketa ya kaita wani gida, lokacin da ya rabata da budurcinta, lokacin da taje gidansa yau da abubuwan da suka faru. Hannu tasa ta dafe ƙirjinta hawaye na zubo mata, ba zata iya yin rayuwa babu Sir ba, Wallhi mutuwa zatayi, ƙirjinta zafi ga cikin jikinta da gaba ɗaya shima zafi yake mata. Adam ya ƙaraso gurin da haura take ya dafa ta ya ce "Haura kiyi hakuri ki manta da shi, Wallhi wannan yaron ko auranki yayi wahala zaki sha, sannan ni zan aura miki wand..." Da sauri Amera ta ce "Wai honey wannan wacce irin magama ce fisabillahi!? Kana ganin halin da yarinya ke ciki amma kai ba damuwarka ta samu lafiya ba, ita ga wanda take so, kuma taji ta gani shi take so, kawai hakuri da zaka je ka bayar ka kasa yanzu kana mata zancen wani, yaya kake so tayi da ranta dan Allah?" Ta karasa har tana miƙewa tsaye. Adam ya ce "Wallhi Amera kimin shiru, na rsante da Allah ranki zaiyi mugun ɓaci muddin baki min shiru ba, na san duk take taken ki, kuma wannan abun ba shi zai hana faruwar komai ba idan Allah ya so" ya faɗa da mugun ɓacin rai! Amera ta ce "Take taken na na me? To mai zan taka, ai ko yanzu wallahi ka..." Maganar da Adam ɗin yayi ce yasa ta tsaya da maganar tata. Wani irin shiru ya sake ratsa palon yayi da gaba ɗaya palon kowa ya ɗauke wuta, daga kan Haura zuwa Adam da ita Amera ɗin. Saida Adam gama tattara dukkanin ƙwarin gwuiwar sa kafin ya ce "Haura kina sona zaki aure ni ki zauna tare damu har abada, domin ki manta da wannan yaron?" Sai da ya faɗi maganar kuma kunya da tsoron amsar da zata bashi ya cika masa kirji. Kallon kallo aka fara yi a palon yayin da haura ta tsayar da kukan nata, ta kafe Daddy da ita, Amera ma sai kallon Adam takeyi domin abun ya bata mamaki. Kawai sai fashe da wani sabon kuka ta kasa magana. Adam da yake jin ina ma shima zai iya kukan ta ce "Baya sonki ba zauna dake sa mutunci ba, ba zai..." Da sauri ta ce "Ni ina sonsa a haka Daddy, Please Daddy ka kira min shi, wallhi bana son kowa sai shi. Adam ya ce "Harda ni ba kya so?" Haura ta ce "Eh Daddy Wallhi shi nake so" Adam yaji kaman ta kira sunan uwarsa da ubansa ta zaga. Amera da an gama cika ta da mamaki da irin wannan kafcen kamar wani shirin Film. Gaba ɗaya ma ta kasa magana domin har ga Allah Adam ya gama shayar da ita mamakin da ya ce, a gabanta babu ko kunyar idonta. Adam da ransa ya ɓaci cikin tsawa ya ce "Kaman yadda na faɗa miki cewar ba zan je gurin shi yaron domin na bashi haƙuri ba, Kuma aure tsakanina dake dole sai an daura, zanyi haka ne domin na tseratar dake daga sharrinsa. Sai a lokacin Amera ta ce "Wallhi girma dai ya faɗi, kuma anji kunya, yarinyar ta ce bata sonka amma tsabar rashin sanin ciwon kai har kana faɗin zaka aureta a haka, Kenan Auran dole kenan, saboda bata da iyaye, saboda ita ba yar gata ba ce ko, saboda ba kaina ka haifeta ba ko, yarinya ta nuna ga abun da take so har ranta amma zaka mata isa da nuna cewar kaina ka isa da ita, to Wallhi babu wanda ya isa yayi mata auren dole, ai ba kai ɗaya ne kake da iko da ita ba" Tana rufe baki ya ɗauke ta da mari, ya ɗora da faɗin "Nafi ƙarfin ki tsaya kina ɗaga min murya har haka, ni mijinki ne ba ɗan ki ba, dake da haura duk kuna ƙarƙashin iko nane, kuma kaman yadda na faɗa na sake faɗa gobe za'a ɗaura auran Haura kuma dani, idan kuma kin isa ki hana?" Ya ƙarasa yana sake nuna ta da hannu. Amera da marin ya shigeta da kyau, ta dafe gurin idanunta sun cika da ruwan hawaye, ta ɗago tana kallonsa. Ta ce "Adam ni ka mara?" Tayi maganar hawayen na gangaro mata. Ya ce "An mareki, ko zaki rama ne?" Ya tambaya yana kafe ta da ido. Amera tayi shiru amma ta zuba masa ido, shima idonsa na cikin nasa, shi kansa idonsa kama wanda yayi kukan sun haɗu sunyi jaa sosai, fuskarsa har wani karkarwar ɓacin rai take yi. Sun kai minti ɗaya a haka ziciyoyinsu na tafarfasa. Juyawa tayi ta koma ɗaki. Shi ma ya dawo da kallonsa ga haura ya ce "Kinji duk abun da na ce ko? Gobe za'a ɗaura miki aure, ina so ki manta da wancen yaron ba sonki yake ba" yana gama faɗa ya bar gidan gaba ɗaya.
Number Najib ya nemo ya kira yana tanbayarsa ina yake. Kasancewar yamma tayi lokacin ya dawo gida yasa ya sheda masa cewar ya na gida. Ai kuwa ya ɗauki mota ya nufi gidan. Yana hanya yana jin har lokacin ransa a ɓace yake, sosai Amera ta ɓata masa rai, ita kuma Haura ta bashi mamaki, kaman shi zata ce bata so, ita bata san cewar tun ba yau ya ke sonta ba, ita bata san cewar son da yake mata tafi wanda ita take wa yaron ba. Ko sallama babu ya shiga palon ya samu suna zaune suna kallo. Khadijah ta ce "Yayi ina uni?" Ya amsa da lafiya ya kalli Najib ya ce "Ina so zaga zamarwa Haura wakili gobe za'a ɗaura mata Aure Please" Najib ya ce "To kai fa ba zaka iya tsaya mata ba ne?" Ya ce "Haba mana Najib, kaman baka san komai ba, nine zan aureta, kuma a gobe" na faɗa maka ne domin ka zauna da shiri, gobe juma'a. Khadijah ta ce "Ko dai wannan mutanen na garin nasu sun sake dawowa ne, sun zo sun sake asirce mana kai ko yaya?" Khadijah ta faɗa a tsorace. Adam ya ce "Idan kina sake sa baki a wannan maganar sai na tattakaki mara kunya kawai" Adam ya faɗa kamar ya kai mata mari. Najib ya ce "Ikon Allah wai Adam lafiyarka kuwa, me ke faruwa ne, karfa kazo ka aikata aikin da ka sani, ya kamata ka faɗa min abun dake faruwa?" Cike da faɗa ya ce "Kamar yaya na faɗa maka abun da ke faruwa, ina ce dama na faɗa maka cewar zan aureta, ko yau ne kawai kasan da maganar ne, please bana son wani dogon tambaya idan zaka zame mata wakili na sani idan ba zaka zama ba to na samu wani. Ya na rufe baki Najib ya ce "Ka samu wani, amma ni kam babu ruwana wallhi" Khadijah ta gyada kai alamar amincewa da maganar mai gidan nata. Adam yayi musu kallo ɗaya ta girgiza kai ya bar gidan. Bai tsaya a ko ina ba sai gurin wannan malamin da ya taɓa zuwa gunsa a wancen lokacin domin ya daura musu aure. Koda yaje ya samu malamin baya nan. Haka ya kamo hanyar gida yana tabbatarwa kansa cewar zai dawo gobe, ai dama gobe juma'a. Ya na son Haura sosai, kuma wannan ita ce hanyar da zai bi domin ya sameta, yasan bayan auran zata fara sonsa. Ya na zuwa kofar gidan yaga get a buɗe, da sauri ya shiga da motar ya dawo ya rufe. Yaga ƙofar palo ma a buɗe. Gabansa ne ya faɗi ya karasa yana jin wani irin tsoron da bai san na meye ba. Ɗakin Amera ya leƙa yaga bata nan, ga drowan kayanta duk a buɗe, tsaki yaja aransa yana jin taje duk