Showing 18001 words to 21000 words out of 58144 words
Allah ka bari wallhi tsoro kake bani, har zuciya ta fara harbawa. Ta ƙarasa tana rufe masa ido. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Nima ban san me yasa nake jin ina son kallonki ba Bebb. Da sauri ta buɗe masa ido ta ce "To kayi addu'a sai ka kwanta. Ya ce "Zan kwanta a palo. Suna zuwa palo ya kwanta ita kuma ta zauna kusa da shi ta ɗora kansa akan cinyarsa . Ya lumshe ido kamar mai barci yana ta Allah-allah ta ɗan matsa ya samu ya bar gidan. Ai kuwa kamar tasan abun da ke ransa ta ce "Bebb bari na haɗa Maka farfesu mai ɗan yaji idan ka tashi sai kaci ta miƙe ta shiga kichin duk a tunaninta barci ne ya ɗauke shi, shima ya tashi da sauri dama ƙananan kaya ne a jikinsa. Ya fita daga palon ya kunna motarsa ya bar gidan zuciyar sa na ƙara kwaɗaita masa ita da surar jikinsa...✍️
Hammm, A bar wa rai!
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*
*°S Reza*
_First class writers association_
_My Whatsapp chanel_
Chapter 8️⃣
Bai tsaya a ko ina ba sai ƙofar gidan su, yayi pakin a ɗan nesa da gidan su kafin ya kirata. Ya na sauke wayar ya ɗora kansa a jikin sitiyarin motar ya yi shiru ya na tunani. Har ga Allah zuciyar sa bata son aikata wannan abun da yake ƙoƙarin yi, amma kuma ransa na yaba wa sosai, idan zuciyar sa ta ce Allah na ganinka sai ransa ya raya masa cewar ai sau ɗaya ne kawai zai yi, kuma idan yayi zai tuba, Allah zai yafe masa. Kansa ne ya ƙara sara wa kaman zai fita, hakan yasa ya sake ƙanƙame kan ya na salati a fili, har ya fara tsoron karfa mutuwa ce zata zo masa gashi kuma ya na ƙoƙarin aikata aikin zunubi, sai kuma ya girgiza kai ya na tabbatarwa da kan sa cewar ba zai mutu yanzu ba. Kusan minti biyar bata fito ba hakan yasa ya ɗauki waya ya sake kiranta amma no amsa. Har zai sake kira yaga ta turo saƙo, jikinsa na rawa ya buɗe. Ta ce "Ina zuwa yanzu shiryawa nake yi" Ajiye wayar yayi a gefe ya kwanta a jikin kujerar ya na jiranta har lokacin kansa na sara masa. Ya lumshe ido ya na hango Nadiya a kichin ta na masa farfeso mai yaji kaman yadda ta ce masa.
*°Haura*
Sosai ta rasa ma wanne kalan kaya zata saka tun bayan da ya ce ta fito su haɗu. Idan ta ɗauko wannan sai ta mayar ta ɗauko wannan. Haka ta dinga fama har dai ta saka riga da wando ƴan kanti wanda suka matseta sosai, rabonta da kayan har ta manta amma suna mata kyau idan ta saka su. Bayan ta saka rigar ta feshe jikinta da turare sannan ta ɗauki hijjabi ta ɗora akai ta ɗauki jakar ta ƙarama ta sa waya a ciki ta fito da niyar fita. Ta na zuwa palon ta samu Amera da Salim zaune suna kallo. Ta ƙaraso cikin palon ta ce "Aunty sannu da hutawa zan je waje ana kirana. Amera ta kawar da kai gefe ta ce "adawo lafiya". Salim ya ce "Anty zan rakaki?" Ta ce "No yanzu zan dawo kaga magriba ta yi" Har zata fita Amera ta ce "Haura" Haura ta dawo da baya ta amsa ta na kallonta alamun sauraronta. Ta ce "Wanda yazo ranar ne yazo?" Ta ɗaga mata kai. Sai ta gyra Zama ta ce "Idan kinje kice masa Daddynki ya ce idan har da gaske ya ke yazo gida a ganshi, kuma kice ke an hana ki tsayayuwa da mutum muddin ba aure ne ya kawo shi ba. Kafin ta yi magana kiransa ya shigo wayar amma sai bata ɗaga ba saboda Amera na mata faɗa. Ta ce "Tom Anty zan faɗa masa" Ta na faɗa ta na rubuta masa message ta tura masa. Amera ta sake cewa "Kin dai ji abin da nace miki ko? Kuma duk abun da ya baki ki amsa, sannan ki dage masa ke dai aure kike so, karki yarda koda ya na da mata kice kina sonsa a haka. Haura dai sai to da to kawai take cewa ta na sauraronta. Sai lokacin Amera ta yi mata kallon tsaf ta ce "Je ki cire wannan hijjab ɗin ki saka gyale yadda zai ganki da kyau" Haura ta buɗe baki zata yi magana Amera ta ce "Ke har yanzu baki da wayo, waye ya ce miki ana zuwa hira da hijjabi yanzu, su kansu samarin ba son sa sukeyi ba ya na rage miki daraja a idonsu, sunfi so su kalleki da kyau domin susan abun da zasu aura. Suna shiga ɗakin ta shiga duba mata gyale ita dai Haura ta na tsaye ta cika da mamakin wannan sabon salon kulawar daga antin tata. Amera da ta samo gyalen har guda uku ta zarosu ta kallettta ta ce "To ki cire hijjabin mana kin tsaya kina kallo na kamar wata bakuwa. Haura ta cire hijjabin jikinta Amera ta yi tsaye ta na kallonta. Ita kanta sai da ta ɗan haɗiye yawu domin ganin yadda kayan suka kamata, komai nata ya baiyana a fili kamar wata ƙatuwar ashawo. Sai ta rasa mai zata ce mata domin dai ta sani bai dace ta fita a haka babu hijjabi ba, kai ko a cikin gida ne bai dace ta zauna a haka ba bare kuma ta fita zance gurin saurayi, ai wannan bada damar aikata iskanci ne. Amma da ta tuno da cewar mijinta fa zata ƙwace mata ai sai cewa ta yi "Gashi kinyi shiga mai kyau amma kin wani ɗaura hijjabi ta yaya zaki burgeshi, yanzu yafa wannan abun ki ga yadda zaki koma" Ta yafa mata wani ɗan ƙyamurmirin gyale sannan ta shiga zuzutata tana koɗa ta. A haka suka fito har palon gidan. Ta ce "Idan kinje kuma karki manta da abun da na faɗa miki akan aure kike so, sannan kuma karki manta fa gobe Lahadi kice ya zo inji Daddy. Haura ta ɗaga kai ta na jin wani ƙwarin gwuiwa na zuwar mata, in dai akan Malam Habib ne har fiye da haka ma zatayi. Ta na fita Amera ta samu guri ta zauna ta na sauke ajiyar zuciya. Wata zuciyar ta ce "Yanzu hakan da kika yi kin kyuta kenan, shin idan ƴarki Salma ce zaki iya barinta ta fita waje da irin wannan kayan da nufin hira, shin meye laifin Haura, itafa har yanzu bata san komai ba. Jikinta ne yayi sanyi sai take tunanin waima tun farko mai yasa ta yarda ma suka riƙe ta ne, kuma tunda suke da ita bata taɓa cutar da ita ko kuma ta mata wani abu na rashin kunya ba, gashi ta na jin maganar ta, shin koda Adam ya aureta meye nata aciki, mai zata ragu da shi. Ai tana zuwa nan da tunani ta miƙe tsaye ta ce "Wallhi ƙarya ne, ba zata saɓu ba, bata isa ba, da ta auri mijina Gara ma ko tsirara ne ta dinga fita waje wallhi.
A hankali ta ke tafiya har ta fito daga cikin gidan, ganin bata ga motarsa ba ne ya sa har ta ciro wayarta zata kira sai taga ya haske ta fitilar motar sa. Hakan yasa ta nufi gurin cikin takunta mai ɗaukar hankali. Babu kowa a unguwar kuma gashi duhu ya fara yi, tafiya ta keyi cike da iyawa da ɗan sanyin ta da yake a zubin halittar ta. Haka take ita, bata da tsoro, haka kuma bata da kunya sannan bata da riƙo, ta na da sanyin jiki harda ta magana, shi yasa sam bata ko ji komai ba sai rashin daɗin yanayin nata amma ba tsoron kar wani ya ganta ko kunya ba. Ta na zuwa bakin motar zata shiga motar Adam tazo ta wuce ta kusa da ita a hankali. Ai kuwa ta na ganinta ta buɗe ta shige, shi kuwa Habib ya figi mota a tamanin ya bar unguwar. Tun lokacin da ta fito ya kafe ta da ido, komai nasa ya tsaya chak da aiki ciki kuwa harda tunanin sa da hankalinsa, ganin ta tsaya ne bai san lokacin da ya haske ta da fitilar motar ba. Duk taku ɗaya da take yi wani abu ne ke ɗarsuwa a ransa game da ita, babu inda yake kallo sai kan girjinta da suke a tsaye kamar zasu tsone masa ido. Jikinsa har wani rawa yake yi halittar sa kuwa ta gama amsawa ji yake kamar ya haɗiyeta kowa ya huta, a yanayin da yake jinsa komai ma zai iya faruwa dashi akanta . Wani irin abu ne mai kamar da idan bai santa ba zai iya mutuwa tsikar jikinsa har tashi sukeyi, har wani sanyi-sanyi ne ke kama shi ya na hango shi tare da ita a wani yanayi. Shi bai taɓa jin irin abun akan wata mace ba ciki kuwa harda Nadiya matarsa, shin wannan so ne ko sha'awa ko kuma me. Sosai ya rikice ya kafe ta da ido har ta shigo motar. Ya na jin ta rufe bai ce mata komai ba ya figi motar suka kama hanya. Saida suka bar cikin unguwar kafin cikin wata matsiyaciyar Muryar da ta ƙarasa illata sauran kuzarin nasa ta ce "Sir ina zamu je?" Ta faɗa ta na kwallonsa cikin so da ƙauna da shaƙi irin na wanda yaga abun sonsa a tare da shi. Sosai take son Malam Habib, idan bata gansa ba har wani zazzaɓi ne ke kamata, ta na sonsa domin Allah, kuma da zuciya ɗaya, yanzu haka da suke tare sai take jin kamar a cikin aljannar duniya take. Habib da ya ƙarasa rugujewa ya ce "Wani guri zamu je" ta sake cewa "Sir kayi kewata kuwa?" Ta faɗa ta na ɗora hannunta akan nasa wanda yake kan gurin saka giya. Ai da sauri ya taka burki ya kallettta, ji yake kaman ya rungumeta a cikin motar ko zai daina jin abun da yake ji. Ido ɗaya ta kanne masa sannan ta sakar masa murmushi ta na ƙara matse hannun nasa. Ji yayi kaman zai narke a gurin, gaba ɗaya ya naimi kuzarinsa da ƙarfinsa ya rasa. Ta ce "Sir akan hanya fa ka tsaya, Please mu tafi". Haka ya zame hannunsa ya tada motar ya fara gudu ya na jin ko magana ba zai iya yi ba, bai tsaya a ko ina ba sai wani ɗan ƙaramin gida. Saida ya sauƙa ya buɗe Get ɗin kafin ya shiga da motar ya yi pakin sannan ya dawo ya rufe get ɗin. Ya buɗe mata ta fito yayi gaba ta bishi abaya ta na tunanin ko gidan waye nan, gashi dan ƙarami yayi mata kyau. Babu wani tsoro ta bishi a baya har cikin gidan.
*°Adam*
Haka suka kwana da Amera kowa na fushi da kowa abun da bai taɓa faruwa tsakanin su ba, koda sun samu saɓani baya shafar mahallinsu amma wannan karan kowa ya hau dokin naƙi. Washegari asabar baida aiki haka ya uni a gida bai ce mata komai ba haka itama bata ko bi ta kansa ba, sannan yau gaba ɗaya ta hana Haura zaman Palo ganin ya hakaikance a gurin, bayan yaci abincin rana ne ya bar gidan ya nufi gidan Najib. A cen ya zauna suna ta hira da Khadijah ya na son ya faɗa mata batun Auran nasa amma yana tsoron tijaranta, domin ai yasan bakinsu a haɗe yake da Amera, haka ya hakura da sanar mata idan komai ya tabbata zata ji. Bayan sun fito ya kalli Najib ya ce "Wallhi har yanzu na kasa sanar mata wannan maganar fa, kuma abun da zai baka mamaki shine ta gano cewar ina son yarinyar, domin yanzu haka da nake baka wannan labarin fushi take yi da ni, kuma ta fara zuga yarinyar akan ta cewa yaron da yake zuwa gurinta ya turo gida, sannan yau gaba ɗaya ta hana ta zaman Palo sabo da ina gida" Adam ya ƙarasa maganar kaman wani abun tausayi. Najib ya ce "To ka hakura mana fisabillahi, kana zaune lafiya da matar ka sai kace dole?" Adam ya ce "Eh kusan dole ne ai, domin ina sonta kuma ina tausayinta sannan kuma ina son na ƙarasa aikin alkairi na". Najib ya ɗan yi murmushi ya ce "Gaskiya ne, to tunda dai kace ta gano kawai ka faɗa mata gaskiya mana. Adam ya ce "kamar yaya gaskiya?" Ya ce "Ka ce mata kana son ka aureta saboda kana tausayinta" Adam ya ce "Najib sai anjima har yanzu ba zaka fahimci abun da nake nufi ba". Ya na faɗa ya shige motarsa ya bar gidan. Ganin magriba ta kusa ne yasa ya ƙarasa gurin masu biredi ya sayo musu ya haɗo kayan shayi harda su Yorgot holandiya da shawarma da fiza da naman kaza. Sosai yayi siyayya mai yawa lokacin har an fara sallar magriba. Haka ya ware na Amera ya ware na Haura da na yaran sannan ya kamo hanyar gida, a ransa ya na fatan su shirya da Amera a wannan daren, ita kuma Haura daga yau zai fara nuna mata gaskiyar nufinsa yasan ba zata ƙi ba, dama shi bada matsla da ita, Amera kawai yake tunani. Ya na tuƙin ya na tunanin yadda zasu kwashe da Amera duk da yasan bata da kafiya, ta na da hakuri da sauƙin hali.
Tun daga nesa ya hango wata figigiyar yarinya cikin wata shegiyar shiga wacce idan da ƴarsa ce babu abun da zai hana bai zane mata mazaunai ba dan ubanta. Tsabar yadda ta ɗauki hankalinsa ma bai tsaya duba fuskantar yarinyar ba sai jikinta da surar ke ɗaukar hankalinsa a kallon farko. A zuci yake tunanin wacce sabuwar yar duniyar ce kuma suka samu a wannan unguwar haka da bata tsoron idon mutane, ko dai bakuwa ce suka samu. Saida yazo kusa da ita kafin ya kalli fuskarta. Kallo ɗaya yayi mata kuma gabansa ya faɗi ganin kaman Haura kaman kuma ba ita ba. Sai dai bai mata kallo na biyu ba ta shege cikin motar da sauri kuma suka bar gurin. Sosai gabansa ke faduwa kaman yabi bayansu amma ya nufi gida yana addu'ar Allah yasa ba ita ba ce, amma dai tabbas ita ce ya gani. Ya na pakin ɗin motar bai ko bi ta kan su shawarma ɗin ba ya shiga gidan kaman an koroshi da sanda. Lokacin babu kowa a palon ita da yaran duk sun shiga sallah. Da Karfi ya shiga kiran sunan Amera har ya na cin karo da kujera. Jin bata amsa ba ya nufi ɗajin ta. Ya na shiga ya samu ta na sallah. Hakan yasa ya fito ya nufi ɗakin Haura harda gudu. Tun daga nesa yaga ɗakin a rufe amma sai da ya ƙarasa ya tura ƙofar ɗakin da karfi. Ya shiga ya na kiran sunanta cikin wani irin ɓacin rai, haka ya shiga duba ko ina har cikin toilet harda ƙarƙashin gado kaman mai neman kaza. Lokaci ɗaya ya tabbatar da cewar ita ce ya gani kenan da wannan shigar kuma ta shiga motar wani. Ya fito daga ɗakin ya sake nufowa ɗakin Amera lokacin ta idar itama ta fito falo domin yanayin nasa ya bata tsoro. Ya ce "Ina Haura?" Ya faɗa da ɓacin ran da yazo masa har wuya, wani irin kishi ne da bai san ya na da shi ba yayi masa karan tsaye a maƙogaro. Ta ce "Dama ajiyar ta ka bani ne?" Itama ta bashi amsa a haɗe domin ta shirya masa, yau zata ga karshen rashin kunyar sa. Da karfi ya ce "Kece kika barta ta fita da wannan shigar kamar wata karuwa, kuma ta shiga motar wani suka tafi?" Ya ƙarasa muryarsa na rawa, ya na jin muddin ta ce eh to tabbas zai iya marinta a yanda yake jin zuciyarsa. Ita kanta saida gabanta ya faɗi jin cewar ta shiga Mota harda tafiya. Itafa tayi tunanin hira ne za suyi a nan ƙofar gidan ba wai mota zasu shiga su je wani guri ba, to ina zasu je. Ta ce "Wai Adam ita wannan Haura ɗin yarinya ce da bata san daidai da rashin sa ba, saurayinta yazo hira ta shirya ta je me kake so nayi, kana so na ce karta je ne alhalin kuma ta isa yin hirar?" "Bance karta ƙara fita ba?" Ya sake faɗa yana matsowa kusa da ita. Ta kalle shi ganin kamar marinta yaje son yi. Ta ce "Mai yasa baka faɗa mata ba?" Adam ya ce "Na lura baki da hankali ne da zaki barta ta fita a haka, ke mahaukaciyar ina ce, idan da ƴarki ce zaki yarda ta fita a haka,?" Amera ta ce "Adam nice mahaukaciyar kuma mara hankali?" Ta tambaya cikin muryar da bai taɓa jin ta da ita ba. Ya ce "Eh! Ai kinfi haka ma, akan wani kishinki na banza da hofi wanda ba zai hana ni abun da nayi niyya ba, kina son ki cutar da rayuwar yarinya wacce bata zauna dake da komai ba sai kyautatawa da biyayya, amma kin fara ɗorata a hanyar banza saboda da kawai mugunta da son zuciya, wallahi kinji kunya". Amera ta yi mutuwar tsaye ta na share hawaye, ta rasa me zata ce sai kwallonsa ta keyi hawaye na ƙara zubo mata. Ya ce "Wallhi Muddin wani abu ya samu wannan yarinyar ke ce, kuma ba zan bari ba" ya na faɗa ya yi hanyar ɗaƙin sa. Amera da maganar ta suɓuto daga bakinta ta ce "Ai har yanzu baka faɗi abun da kake son faɗa ba, kuma in sha Allahu ba zata dawo gidan nan lafiya ba sai naga abun da zaka yi. Ta faɗi maganar har cikin zuciyarta, sai take addu'ar Allah yasa ma yaron karya dawo da ita sai yayi mata fyade ya wulakantata, kai idan ma ta kama ta dawo da ciki domin taga abun da zai yi. Adam ya juyo har zai shige ya dawo da baya ya ce "Mene ne ban faɗa ba,