Showing 42001 words to 45000 words out of 58144 words

Chapter 15 - A Bar Wa Rai Complete Books By S Reza.txt

S Reza   

12 Mar 2026

29

dawo nan kusa ba, yayi tunanin yaran kawai tasa aka kawo. Ya so ya kawar da kai, ya nuna ko a jikinsa, amma ba zai iya ba, kukan Amera illata masa natsuwa yake yi, baya taɓa iya jure wannan bangaren, sannan gashi yaga tai masa wani haske, ga kayan da ta saka sun matse ta, kanta babu ɗan kwali, ga lallan da tayi nan jazirr a hannunta. Lokaci ɗaya raunin sa ya baiyana. Ya ce "Honey" ya faɗa a hankali. Muryarsa ce ta ankarar da Salim da ya nufo gurin sa da gudu yana kiran sunansa. Itama Salma ta fito da gudu suka rungume shi. Amera ma ta ƙarasa gurin ta rungume shi ta na kuka. Shi kansa bai san lokacin da hawaye suka fara gangaro masa ba.

Cikin muryar koka ta fara faɗin "I'm sorry honey, I'm sorry" haka kawai take faɗa tana share hawaye shi kuma yana bubbuga bayanta. Salma ta ce "Daddy ina Anty Aisha?" Ta faɗa ta na ɗagowa daga jikin daddyn nata. Shima Salim ya tambaya suna kallon daddyn nasu. Adam ya ce "Tayi tafiya zata dawo" ya basu amsa ya na ɓoye hawayen nasa. Yaran suka shiga tambayar yaushe zata dawo. Amma yayi kamar bai jisu ba ya nufi ɗakin sa da sauri. Ya na zama Amera ta shigo ta na share hawaye. "Ta ce "Har yanzu ba'a ganta ba ko?" Adam ya kafe ta da ido ganin yadda ta damu kamar ba ita ba, yaso ya nuna mata cewar shine mijin kuma gidansa ne, sannan yana da ikon da zai iya yin aure a duk lokacin da yake so, amma dai ganin nadama a fuskar ta sai ya ce "Ban san ina ta tafi ba, dan Allah idan kece kika turata wani guri ko kika mata wani abun ki faɗa min please honey, wallhi ba wai zan aureta saboda ke kin gaza min bane, ko saboda wani abun bane, a'a honey, ina yin haka ne saboda Allah, kuma na taimaka ta, amma kin kasa fahimta ta?" Ya ƙarasa yana zuwa har kusa da ita. Lokaci ɗaya Amera ta sake fashewa da kukan abun da tayi. Ta ce "Yanzu shikenan ka daina yarda da ni honey, wallhi ban san inda ta tafi ba, dan Allah nima kayi hakuri da tafiyar da nayi please I'm very sorry for everything" ta ƙarasa ta na fadawa jikinsa. Adam yayi shiru yana sauraron irin kukan da take yi. Ya ce "Ya isa kiyi shiru ya wuce, bana son wannan kukan, na yarda da ke, kuma har abada yardar da na miki ba zata goge ba" ta tsayar da kukan ta ɗago ta ce "Baka cancanci haka aguri na ba honey, kuma itama Haura ban kyuta mata ba, in sha Allahu zan tayaka neman ta duk inda ta shiga, sannan kuma na yarda ka k ka k ka aureta" ta na faɗa ta bar ɗakin da gudu tana sakin wani kukan. Adam ya bi bayanta da ido bai ko iya cewa komai ba. Tun daga ranar komai ya wuce, suka fara neman Haura, babu yadda baiyi ba ya rasa number Habib. kwana ɗaya biyu Amera bata jin daɗi ana zuwa asibiti likita ya tabbatar da cewar tana ciki sati biyu. Tun daga asibitin ta fara kuka shi kansa Adam ɗin tsoro ne ya cika shi. Ai kuwa suna zuwa ta shiga rera kuka ita dai kawai a cire bata so. Shi kansa idan a sonsa ne kawai a cire. Da ya kalli irin kukan da ta ke yi kuma tana cewa a cire sai ya dinga ganin kamar fa an fara ne.

*°Habib*
Sosai Nadiya ta shiga ihu ta na faɗin cikin ta. Haka ya ɗauketa izuwa asibiti. A cikin daren aka samu ciwon ya lafa, aka saka mata ruwa da allura. Haka Habib ya kwana a tsaye duk ya shiga damuwa. Ai kuwa da safe ya kira Mama ya faɗa mata, ba'a daɗe ba kuwa sai gasu ita da ƙanwarsu Zainab ɗauke da abinci da kayan shayi da ruwan zafi. Suna ajiye wa Zainab ta juya kasancewar zata tafi school. Ko minti biyar basuyi da zuwa ba Habib ya tafi gida domin yayi wanka ya kuma kwasowa Nadiya kayan da zata saka. Ya na fita ita kuma ta farka. Ganin Mama yasa ta fashe da kuka na gaske. Hankalin Mama ya tashi, babu irin tambayar da batayi mata ba amma sai kuka ta keyi ta ƙi cewa komai. Gashi ance ta ci abinci taƙi ci, haka Mama ta dinga fama da ita amma sai kuka. A haka Habib ya dawo ya same su. Ya na shigowa ta tsayar da kukan ta na kallonsa. Tun kafin yayi magana Mama ta ce "Wai me ke damunta ne, tun ɗazu tana ta kuka lafiya dai ko, me likitan ya ce?" Habib ya karasa gurin da take ya ce "Bebb ya jikin?" Tayi banza da shi sai ma harara da ta bishi da.
A haka likitan yazo ya samesu ya kira Habib ɗin ya faɗa masa cewar ya lallaɓa ta har lokacin aihuwar ta yayi idan ba haka ba zai iya rasa cikin dama uwar gaba ɗaya, domin ko yanzu ma Allah ne yasa sun kawota asibiti da sauri, sannan abu na gaba ta dinga samun huta, a daina yawan ɓata mata. Sosai likitan ya faɗa masa abubuwan da za'a kiyaye mata. Sannan ya rubuta musu sallama.

Koda suka dawo gida sai yamma Mama ta koma sannan kuma ta ce Zainab zata dawo nan gidan da zama har lokacin da zata aihu domin ta rage mata aiki. Haka suka yi kwana biyu Nadiya bata ce masa um ko um-um ba. Duk irin tambayar da yayi mata sai dai ta kalleshi ta kawar da kai. Har maganar Haura yayi mata ya ce shi wallahi babu abun da yake tsakaninsa da ita, karta bari zuciyarta ta raya mata karya akan Haura. Duk abinda ya ce sai dai tayi hawaye ko ta kawar da kai. Yanzu kullum sai ta tashi cikin dare tai ta yin Sallah wanda shima ganin haka yasa ya tashi ya bita. Gaba ɗaya ta sauya, magana bata iya yin mai tsayi koda kuwa da Zainab ne, kullum cikin shiru da tunani. Bangare daya kuma Habib shima bai tsaya wajen tuba akan abun da yayi ba, bashi da addu'a sai Allah ya yafe masa, kuma karya ƙara haɗa shi da haura ko a mafarki. Yau sati biyu kenan da tura takardun neman aikin sa, amma yayi rashin sa'a duk babu wanda suka kira shi. Izuwa lokacin cikin Nadiya ya shiga wata na takwas, yanzu komai na gidan Zainab ce ke yi, shi kansa Habib ɗin baya zama sosai, kullum cikin fita neman aiki amma gaba ɗaya babu sa'a, izuwa yanzu sun gama haɗa komai na kayan aihuwa domin dama tun lokacin da suka tabbatar da cikin suka fara shiri. Izuwa yanzu hankalin Habib ya fara tashi na batun rashin wannan aikin, babu irin fadan da Mama batayi masa ba na sakin aikin da yayi, duk da kuwa ya ca masa sharri aka masa. Nadiya kuwa kaman yadda tayi masa alƙawarin ba zata ƙara saka baki a maganar aikin sa ba, haka ko yaje mata da maganar sai tayi banza da shi ko tace Allah ya bada sa'a to ta ce ma to. Wannan lamari nata ya fara ɓata masa rai. Yau misalin ƙarfe takwas bayan sun gama cin abinci ya riga ta shiga ɗaki, yana jiran tazo ta faɗa masa wai me yayi mata ne da ta sauya haka. Ta na shiga kuwa ya fara magana ta inda ya ke shiga da fita daban. Ita kuwa ko magana bata masa ba ta shinfiɗa dadduma ta tada salla. Haka abun ya cigaba da tafiya, shi a ransa yaso ace Kafin ta aihu ya samu aiki amma abun babu sauƙi. Dole shima ya ci gaba da binta a yadda take so ɗin, idan ta tashi cikin dare tana sallah sai yayi ta mamakin ta, watarana ya tashi watarana kuma yayi kwanciyar sa.

*°Haura*
Mamaki da tsoro da firgice ne suka kamata lokaci guda saboda abun da ta gani. Wani irin ihu ta saki mai karfi wanda daga haka bata sake sanin inda take ba sai yamma liss lokacin rana tayi jaa zata fadi. A hankali ta buɗe idonta, bata sauke shi a kan na kowa ba sai kan na Aminta. Da Karfi ta kira sunan Ammin tata ta amsa itama hawaye na zubowa daga cikin idonta na murna da farinciki. Ganin daga ita sai ita ne a ɗakin yasa Haura tashi zaune da kyau, tana ta kallon Uwar Tata, tana jin wani abu mai kama da kafi daɗi daɗi, ji take kamar ta tashi ta goyata tayi ta rawa, amma hawaye da kukan dake cinta na murna ta kasa aiwatar da ko ɗaya. Kafin ta iya samun damar magana aka buɗe ɗakin wani kyakkyawan saurayi ya shigo ɗakin ya na tambayar Ammin da rayensu wai hauran ta farka, kafin ma ya karasa yayi ido biyu da ita. Haura na ganinsa ta kira sunansa da ƙarfi tana nufar sa. Ta ce "Guber Ammi ce wannan, dama bata mutu ba?" Ta faɗa tana chakume wuyan Guber wanda babu riga a jikinsa ko wando, sai wata fata da ta rufe masa alaura. Ita kanta Ammin haka take zaune amma ita ta daure girjinta da wani tsimma, sai kuma wata farar mayafi da Haura ɗin ta kasa gane a ina ta samo shi ta yafa a kanta. Ya ce "Eh Haura bata mutu ba tana raye" ya amsa shima hawaye na zubo masa na kewar ta da yayi. Guber shine abokinta na yarinta, kuma wanda ake cewa zai aureta a lokacin. Sosai Haura ta sha kuka har saida Ammin ta rarrasheta, Guber ma ya bata hakuri, da ƙyar ta daina kuka tana ta tambayan abubuwa ana bata amsa suna ta hira. Mutane wannan yazo wannan yazo, sai take kallonsu kamar wasu halittun da ban ba irin nata ba, tun daga haka ta tabbatar da cewa zata iya zaman garin nan ba. Ganin dai Haura na da tambayoyi da take son mata ne yasa Ammin ta tambayeta mai ya dawo da ita. Kallon Guber ta yi. Ammin ta ce ta fadi komai babu damuwa. Guber yayi dariya yana tsokanarta da ko ta dawo suyi Aure ne.

Cikin wata iriyar murya Ammin ta daga mata tsawa bayan ta gama jin komai da take son ayi mata, kuma ta basu labarin rayuwarta da abun da Habib yayi mata, amma banda abun da suka aikata, kaman dai yadda ta fadawa su Adam. Ta ce "Yanzu-yanzu ki tashi ki koma muddin wannan abun ne ya kawo ki". Haura ta kalli Ammin nata, tabbas wannan ba ita ba ce, idan ma ita ce to a kwai abun dake faruwa, aminta da take goyan bayanta akan komai, bare kuma irin wannan cin amanar da aka yi mata. Guber ya ce "Haura Ammi musulma ce yanzu haka, ta na yin Sallah ba tare da kowa ya sani ba, kuma ko yanzu muna shirya yadda zata bar cikin garin Garuk ne saboda taje cen tayi adininta. Ammin ta ce "Bana son naji kinyi maganar nan da kowa, sannan shi wannan mutumin da kike so bana son taraiyar ki da shi, Adam nake so ki aura shine ya taimake ki, a lokacin da baki da kowa, shine mutumin da ya samar miki da ilimi da wayewa da komai na rayuwa, sannan karki ƙara batun ƙarɓar tsafi. Da sauri Haura ta toshe kunnenta ta ce "Ammi bana sonsa, shi Daddy na ne, ba zan iya auransa ba, ni Habib nake so, kuma shi zan aura, wallahi bana son daddy".

Kwanan Haura goma sha shida a garin Garuk, izuwa lokacin sun sanar da cewar kawai ziyara ne tazo, kuma har wannan lokacin babu yadda ba tayi da Ammin akan a dawo mata da tsafinta ba amma Ammin ta ƙi. Kuma ta ce ta bata labarin yadda ta musulunta amma ta ce mata sai ranar da ta shigo cikin gari zata bata labari. Haka Haura ta shirya komawa ba tare da ta samu komai ba, taje tayi sallama da Sarkin garin Garuk ya saka mata albarka irin tasu, shima sai da yayi mata tayin sake karɓar tsafin amma ta ce bata so. Guber ne zai rakota wanda har cikin gari zai kawo ta da izinin Sarkin garin. Bayan tayi sallama da yan garin da Aminta ne suka kama hanya. Sai da suka gangara ƙasan dutsen bayan garin kafin Guber ya ƙyalƙyale da wata shegiyar dariya. Itama Haura ta bushe da dariya, sai da suka yi mai isar su, domin sun tuno da lokacin baya, haka suke yi shi da ita, komai nasu ɗaya, duk inda zasu je tare, ayi wanka tare aci abinci tare, hakan yasa yafi kowa sanin damuwarta a lokacin da kuma yanzu da abun da ya faru da ita ɗin ya tsaya masa a rai domin ta faɗa masa cewar harda fyaɗe yayi mata. Guber ya ce "Bayan duk wannan abun da ya miki kuma yace ba zai aure ki ba, ita kuma Ammi wai a rabu da shi, to wallahi sai ya mutu ko kuma ki aure shi ko dai matar sa da cikin jikinta su mutu, wa ya faɗa masa ana yiwa ƴan matan Garuk fayɗe dan ubansa, ba dan ma Allah yasa bani da ikon shiga gari ba da yau zai mutu a daren nan wallahi". Ya ƙarasa da mugun ɓacen rai.   Haura ta daka masa tsawa ta ce "Bana so ya mutu, domin ina sonsa, idan ya mutu nima mutuwa zanyi, kawai kai dai bani abun da zaka bani, aure nake so muyi, bana so matarsa ta mutu domin tana da kirki". Guber ya kama hannunta na dama ya chaka ƴan yatsansa guda biyu kaman wanda zai ƙwaƙulo wani abu. Sai kuwa ga wani haske yana fitowa daga cikin idonsa yana shiga nata, wani abu kuma mai kamr blue (kore ) yana fitowa daga yatsun hannunsa yana shiga hannunta. Ƙasa da Minti ɗaya ya gama shiga sai ga Haura ta zube a ƙasa kamar wacce aka ɗaga aka maka da ƙasa. Guber ya busa mata iska sai kuwa gata ta miƙe tsaye. murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa ya buɗe mata hannunsa ta zo da gudu ta shige suka fara masayar maganganu da yaransu na alƙawarin zata dinga sanar dashi komai. Sai da ya rakota har bakin dajin kafin ya koma. Ita kuma ta shiga Motar Abuja bayan an saka mata akwatin ta a baya, ana tafiya tana tunano yadda zata kasance da abun sonta. Ana ajiye ta a tasha ta kama hanyar gida a ƙafa, wanda ko minti biyar batayi ba ta iso unguwar tasu hannunta riƙe da a kwatin kayanta da ta tafi da su. Ta tura get ɗin gidan ta shiga da sallam. Lokacin rana ne Adam baya nan Amera ce sai yaran da yau babu school. Salma ce ta fara hangota hakan yasa ta kira sunanta da karfi tana nufarta. Amera da barci ya fara tafiya da ita ta fara da mamaki. Dukda gabanta ya faɗi amma sai da ta nuna farinciki. Haura ta nufota da sauri ta rungumeta. Nan take Amera ta ɗau waya ta kira Adam ta faɗa masa. Ko minti biyar baiyi ba sai kuwa ga sallamarsa a palon...📝



S Reza...
[09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*

*FCWA*
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
*Chapter 18*
Bai ko jira an amsa masa sallamar ba ya shigo cikin palon da sauri ya na kiran sunanta. Ya na zuwa kusa da ita ya tsaya ya na kallonta, itama shi take kallo idanunta ƙur a kansa babu alamar tsiro ko nadama akan abun da tayi. Kafin yayi magana ta ce "I'm sorry Daddy please kayi hakuri" Ta faɗa ta na marairaicewa alamun abun tausayi. Adam da gaba daya jin daɗin ganinta ya kawar da ɓacin ran da yake ciki. Ya ce "Ina kika je?" Ta ce "Daddy ina makaranta fa, cen na koma da kwana amma yanzu na dawo Please I'm sorry kaji" Ta ƙarasa ta na yi kamar zata yi kuka. Ajiyar zuciya ya sauke yana rasa mai kuma zai sake ce mata. Amera ta ce "Shiga ɗaki ki huta ko?" Ta faɗa ganin sun tsaya cirko-cirko kowa ya ƙi magana. Ai kuwa da sauri Haura ta nufi ɗakin ta Salim da Salma dai suna manne da ita. Ta na shiga daki Adam ya samu guri ya zauna yayi shiru. Amera ta ce "Sannu da dawowa" ya amsa ya na kallonta. Ta ce "To sai ga shi dai Allah ya dawo da Haura gida lafiya, sai mu godewa Allah" Adam ya ce "Kin yarda da inda tace taje? Idan da makaranta ta je Maryam zata sani, kuma ko da naje school ɗin na tambaye ta amma an ce bata zuwa". Amera ta ce "To yanzu dai ba ta dawo ba? Sai kawai ayi abun da ya da ce" Adam ya ce "Zuciyata bata kwanta ba, ba zan ɓoye miki ba kawai ta na faɗa min cewar gurin saurayin nata taje". Amera ta ɗan kawar da kai gefe kafin a hankali ta ce "Kasan idan zuciya ta na son abu to bata cika ganin aibun wannan abun ba, sannan zuciya ta na yin uzuri ne wa wanda take so koda kuwa akan ƙarya yake" Amera ta ƙarasa ta na kallonsa. Adam ya ƙura mata ido kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce "Tabbacin soyayyar gaskiya shine kishin abun da kake so, tabbas idan baka jin kishi idan wani ya raɓi wanda kake so to babu shakka ba sonsa kake ba, Honey ina son Haura sosai son da ban san iya adadin sa ba, idan da kinsan yadda zuciyata ke zafi da wannan abun da tayi da kin tausaya min" ya ƙarasa ya ne dafe saitin zuciyarsa. Amera ta ce "Na sani kuma..." Ta ke kuka ya kufce mata, ta kasa ƙarasawa. Ai kuwa tayi cikin ɗaki da sauri, ya bita ya na kiran sunanta.

Haura na shiga ɗakin cikin minti ɗaya ta gyara ko ina harda cikin toilet. Ta kwanta a kan gadon tana kallon sama. Tana ji su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login