Showing 15001 words to 18000 words out of 58144 words
Allah, gata kuma da kyau babu laifi. Amera ta ce "Nana wani irin tunanin rashin hankali ne wannan, amma kinsan haramun ne kiran wanda ya musulunta da arne ko, kuma duk abin da ya faru a baya ba'a sanin sa bane asiri a kayi masa, yanzu kuwa mun riƙe addu'o'i da Azkar na safe da na yamma in sha Allahu babu abun da zai iya faruwa da mu sai ikon Allah. Dan haka Please ki daina wannan tunanin na san waye mijina, ko a yau Haura ta fito da miji zai aurar da ita, mun sha yin wannan maganar da shi akan auran nata, kuma ya tabbatar da cewar duk wanda ta kawo shi zai bawa. Nana ta yi murmushi ta ce "Anty Mera kenan, to waye zai aureta ɗin idan yaji labarin ta, ina rantsuwa miki da Allah Anty babu namijin da zai iya aurantn sai dai ƴan garinsu, amma duk namiji ɗan dangi ba zasu yarda ya kwaso musu arnan daji ba, kinga kuwa Adam babu wanda zai iya hana shi, domin bashi da wasu dangi nan kusa, dan haka Wallhi Anty ki farka komai zai iya faruwa, ni dai shawara ce na baki. A haka Nana ta tafi ta barta ta shiga nazari m
Tun lokacin gaban Amera ya shiga faɗuwa ta na ta tunanin maganganun Nana. Hakan yasa tun lokacin da Nana ta bar gidan ta shiga sakawa Haura ido har ma ta sameta da maganar saurayinta, a kwana biyun ta lura da wani irin kusanci da Adam ɗin ke son samarwa tsakanin sa da ita, wanda hakan baya mata daɗi, amma dole ta dakatar da komai kafin a kai ga abin da take tsoro. Adam ya ɗago da sauri yana kallon Amera, ya ce "Wani turowa kuma ita da take karatu, kuma ma har yaushe suka haɗu da yaron, idan ma suna son juna sai a bari ta ƙarasa karatun nata kafin ayi wannan maganar turowa ko?" Ya ƙarasa yana kallon Haura ɗin da take tsaye tana jinsu...✍️
S Reza....
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*
*°S Reza ✍️*
_First class writers association_
_My Whatsapp chanel_
*Chapter 7️⃣*
Amera ta ce "Karatu kuma, wa yake ta wani karatu yarinya ta samu wanda yake sonta, to idan ma karatun ne ba sai ta yi a gidan mijin nata ba" Ta ƙarasa maganar da muryar da ke nuni da ɓacin ran da take ta ƙoƙarin danne wa. Adam ya ce "Honey wai me kike nufi ne, ko kin manta yanzu haka yarinyar nan ta na shekarar karshe a makarantar ne, kuma yanzu haka text suke yi, suna ganawa kuma sai exam, so kike a katse mata karatun nata ne saboda wani yazo ya ce ya na sonta?" Ya faɗa ya na miƙewa tsaye shima da alamun ransa ya fara ɓaci da abun da ta yi. Amera ta miƙe tsaye itama ganin zai bar gurin. Ta ce "Adam faɗi abun da yake ranka?" Ta faɗa muryarta na yi kamar zata yi kuka, domin tabbas ta gama tabbatar da maganar Nana. Shi kansa Adam ɗin sai da yaji sautin muryar tata kamar daga cikin kwakwalwar sa ta fito. Sosai gabansa ya faɗi ya shiga tunanin ko dai ta gano shirin nasa ne, sai kuma ya fara tunanin anya kuwa ba dama ya samu da zai faɗa mata gaskiya ba. Kafin yayi magana Haura ta ce "Please Daddy Anty kuyi hakuri dan Allah ku daina irin wannan abun" Amera ta kalleta ta kalli Adam ta ce "Faɗa mata gata nan, idan kuma so kake na baku guri tom" ta ƙarasa maganar da ƙyar ta na barin gurin kuka na ƙwace mata. Adam ya bita da kallo har lokacin zuciyar sa na harbawa, ya dawo da kallonsa ga Haura. itama ta juya ta bar gurin ta na mamakin akan ɗan wannan abun ne za suyi faɗa, da zasu kwantar da hankalinsu ma Habib nata ne, zai sonta har ma fiye da yadda take sonsa, idan Aure ne zata yi, kuma da shi Habib ɗin in sha Allahu. Ta na shiga ɗaki ta ciro wayarta a chaji ta danna kiran number Habib ɗin ta na addu'ar Allah yasa ya ɗaga ko muryarsa taji. Har kiran ya katse bai ɗaga ba. Sai da ta kira sau uku bai amsa ba kafin ta hakura ta na tunanin ko dai ta shirya ne taje school ɗin amma kuma ai yamma ta yi ko taje ba lallai ta same sa ba, gashi bata san gidan sa ba ta daje, lokaci ɗaya ta tuno da number matarsa da ta ɗauka. Data ta kunna ta hau online ko zata same shi a online. Haka ta tara masa messages da yawa sannan ta nemo number Bebb da ta ɗauka a wayarsa. Har zata tura mata saƙo sai kuma ta sauƙa daga whasop ɗin ta kirata darekt call. Kira ɗaya Nadiya ta ɗaga da Salam. Haura ta amsa sai kuma ta ce mata pls ina zuwa yanzu". Ta na faɗa ta kashe wayar. Ta fara dariya ita ɗaya kamar wata mai jinnu. A fili ta ce "Muryarta a kwai daɗi babu laifi, in sha Allahu sai kin faɗa min sunan unguwar da kika da kanki. Ta na cikin haka ta jiyo muryar Adam da Amera na tashi a palo, dukda bata jin abinda suke cewa amma dai tasan faɗa ne suke yi, hakan yasa ta ajiye wayar ta nufo palon gabanta na faɗuwa, ta na fara shiga damuwa domin tasan dai duk akanta ne wannan faɗan nasu. Abun da bai taɓa faruwa a gidan ba tun bayan aihuwar Amera ɗin, ita abun nasu ma ya fara bata tsoro Wallhi, wai ko sun fita son yin auren ne ko meye. Ta na fitowa palon kuma taga babu kowa sai ta ji muryoyinso daga cen cikin ɗakin. Hakan yasa ta koma da baya ba tare da ta bi ta kan su ba.
*°Habib*
Da sallama ya shiga cikin palon gidan nasa muryarsa a sake hannunsa riƙe da baƙar leda. Ganin babu kowa yasa ya nufi ɗakin Nadiya. Ya na shiga ya sameta ta na shirin kwanciya ta saka riga ta zauna a bakin gado ta na saka soss ɗin ƙafa, fuskar nan ta ta fayau kamar babu abun da ya faru, harda murmushi ma yaga ta na masa. Shima saboda ya tabbatar mata da cewar ya amso wayar tasa ya sa ya fiddo da wayar ya kunna karatun Alqur'ani mai girma ya ajiye a kusa da ita ya na bin karatun cikin Suratul Kafiron. Bata ce masa komai ba sai ƙoƙarin kwanciya da ta ke yi. Ya ce "Bebb abinci fa, kuma ga apul na zo miki da shi?" Ya faɗa a hankali duk da ba wai yunwa yake ji ba, kawai dai ya na so ta yi masa magana ne. Miƙewa ta yi, bata ce komai ba ta fita da ledar ta kai friji sai gata ɗauke da abincin nasa da ruwa. Ta ce "Gashi?" Ya ce "Kizo muci Please?" Ta ce "Na goshi". Ɗan kaɗan ya ci abinci ya tattara komai ya mayar kichin ya shiga toilet ya sake yin wanka kafin ya kwanta a bayanta ya rumgumota yana shafa cikinta. Duk yadda Nadiya ta kai da kin basa haɗin kai a wannan ɓangaren amma ta kasa, haka dole ta bada kai bori ya hau. Sosai ya nuna mata jin daɗin sa harda mata godiya da saka mata albarka. Ita kanta taji daɗin hakan har cikin ranta. Ɗaukar ta yayi suka shiga toilet suka sake yin wanka. Bayan sun fito ne ya fara bata labarin da zai kwantar mata da hankali har barci ya ɗauketa.
Yau juma'a ya na da class ɗin safe hakan yasa bai koma barci ba, ya bita kichin domin ya taya ta aiki kamar yadda ya ke yi a baya. Ita kanta sai da ta tsaya kwallonsa domin taji daɗin yadda ya ke kokarin dawowa. Ai kuwa tun kafin takwas da rabi sun gama komai, suna yi suna hira. A kwano ɗaya suka zuba abincin suka ci, sannan ya tashi domin fara yin shirin tafiya. Ya na shiryawa ya na addu'ar Allah yasa Haura bata zo school ba, Allah yasa kar ya sake ganinta, ya na yin addu'ar amma wani ɓangare daga zuciyarsa na kin amsawa da amin. Har zai fita Nadiya ta ce masa idan ya dawo ya sameta a gidan Mama sai su dawo tare. Ya ce "Gidan Mama kuma Nadiya, lafiya dai ko?" Ta ce "lafiya lau kawai abu zan karɓo kuma ma ai yau juma'a zan mata gaisuwar juma'a ne. Kamar ya ce karta je amma ya ce tom sai na dawo.
Ofis ya fara shiga ya ajiye wayarsa da jakarsa Kafin ya ɗauka abun da zai bukata ya nufi class ɗin. Ya na shiga class ɗin idonsa ya fara sauƙa a gurin da take zama. Dukda ya yi addu'ar Allah yasa karta zo, gashi bata zo ɗin ba, amma sai ya tsinci kansa da jin rashin daɗin hakan. Yaso tazo ko ganinta ne kawai ya samu yayi amma ba sai mata magana ba. Haka dai yau gaba ɗaya yayi karatun jikinsa a sanyaye, duk ɗalibin da ya zo latti ma baya korarsa a tunaninsa ko itama zata zo. Amma haka lokacin sa ya ƙare ba tare da tazo ba. Bai bar school ɗin ba har kusan ɗaya sannan ya nufi masallaci yana jin babu daɗi a ransa.
*°Nadiya*
Misalin ƙarfe goma ta gama komai na gyaran gidanta kafin ta shirya ta tafi gidan Mama. Lokacin da ta isa babu kowa a gidan sai Mama kawai. Ai kuwa taji daɗin zuwan nata, domin ta samu abokiyar hira. Karfe sha biyu ta tashi ta shiga kichin ta ɗora girki. Ita har ga Allah magana ne a bakinta game da Habib kuma tayi nufin tazo suyi maganar da Mama ne, amma bata san ta yaya zata iya sanar da ita ba, sannan taga alamar kamar komai ya wuce hakan yasa ta kasa yin maganar da Mama har ta gama girkin. Misalin ƙarfe uku ya zo gidan, ta zuba masa abincin ya ci ta na lura da yanayinsa jikinsa duk yayi sanyi. Sai da Nadiya tayi sallar la'asar shima ya fita waje yayi kafin suka bar gidan. A hanya ya tsaya ya saya musu tsiri da Yorgot harda naman kaza, ya na ta ƙoƙarin nuna mata cewar komai ya wuce dukda kuwa zuciyar sa cike take da son ganin Haura ko jin muryarta. Ganin haka yasa itama ta sakar masa fuska sosai harda dariya ta na rungume shi. Wanka suka sake yi tare kafin suka baje naman nasu apalo suka fara ci. Ta ce "Bebb cikina fa yau sai motsi yake tayi wallhi, anya kuwa ba wata matsalar ba ce". Ta karasa ta na ɗora hannunsa akan cikin. Habib ya kai naman kaza bakinsa kafin ya ce "Ai wannan shine alamar lafiya jin motsin nasa, ki kwantar da hankalinki babu komai" Ta ce "Kaifa motsi sosai ne fa kamar zai fito" Bai san lokacin da dariya ta kubce masa na ya ce "To ko dai fitowar zai yi?" Har zata sake magana wayarsa ta hau ƙara. Ya ciro ya duba yaga number Haura. Ta ke gabansa ya bada wani irin sauti, da sauri ya dafe ƙirjin nasa yana jin kamar ya daga. Ya ɗan kalli gurin da Nadiya take yaga shi take kallo, nan take yayi saurin dawowa natsuwarsa. Ya saka wayar a silent ya cigaba da sauraron Nadiya da take nazartar yanayin da ya shiga. Ya na ji kira na shigo masa ya na son ɗauka amma yana tsoron abun da zai iya faruwa, hakan yasa ya hakura. Wayar Nadiya ce ta hau ƙara ta miƙa hannu ta ɗauka ta ɗaga a gabansa. Gaban sa ne ya sake yin wani mummunan faduwa jin kamar Muryar Haura ta cikin wayar. Hakan yasa ta na sauke wayar ya ce "Wacece?" Ta ce "Nima ban santa ba, baƙuwar number ce, kuma ta ce tana zuwa. Yayi shiru yana tunani, wai me wannan yarinyar take nufi ne dole ne fa yasan yadda zai ɓullo mata, domin baya son wannan alaƙar da take kokarin ƙullawa da matarsa. Lokacin da Nadiya ta buɗe whasop sai taga an ajiye mata saƙo da number ɗazu. Da sauri ta buɗe tana karantawa. Dariya kawai tayi ta bata amsa. Ganin ta na online ne yasa ta tanbayeta a ina ta samu number ta. Haura ta ɗan yi dariya itama kaman ta ce mata a wayar mijinta amma ba yanzu ba, so take sai ta je har gidan nata kafin tasan burinta. Ta ce "Nima a wayata naga numbar shine yasa na kiraki naji ko ke kin sanni. Nadiya ta ce "A ina kike? Kuma yaya sunanki? Haura ta ce Sunana Haura. Ta ɗora da faɗa mata unguwar da take. Nadiya ta ce "Kai gaskiya ban taɓa zuwa unguwar nan ba. Ta ce "Ke yaya sunanki?" Itama ta faɗa mata sunanta harda unguwar da take kuma ta sheda mata cewar tana da aure. Haura sai farinciki takeyi jin abun yazo mata da sauƙi. Ita kuwa Nadiya yanayin Hausar yarinyar ce ke burgeta, gashi daga ji yarinya ce ƙarama ko daga yanayin maganar ta babu tunawa. Haka suka sha hira da ita kamar dama sun saba. Washegari ma da safe saboda ita ta buɗe online ai kuwa ta sameta nan ma suka ɗan taɓa hira harda turawa juna hotuna.
*°Habib*
Tashi yayi zaune cikin dare yana salati gaba ɗaya ya tsorata. Wutar ɗakin ya kunna tsoro na mamaye sa. Mafarki yayi wai Haura ta shigo gidan nan har cikin ɗakinsa suna cikin aikata abun Nadiya tazo ta ritsa su, kuma Haura ɗin ta daɓawa Nadiya wuƙa a cikin ta. Da sauri ya nufo gurin wayarsa yana duba lokaci. Ganin biyu da arba'in yasa ya faɗa Toilet. Koda ya fito ya ɗauki wayarsa domin komawa dakin Nadiya sai yaga 3 miss calls. Hakan yasa ya duba. Kaman ya kirata amma ya fasa. Sai ya kasa komawa barci yayi zaune yana tunani ya dafe kai. Shi kansa zuciyarsa na son ganinta amma yana danne wa. Yana cikin haka barci ya ɗauke shi, babu abin da yakeyi sai mafarki da ita, mai kyau da mara kyau, mai hankali dama marasa hankali. Haka yau ko sallar asuba bai samu ba, ya tashi duk jikinsa a sanyaye, ga wani irin ɗokin son ganinta da ya tashi da shi kamar wanda aka dasa masa a safiyar nan. Haka ya ke komai babu kuzari kamar mara lafiya, ko abinci kaɗan yaci ya kwanta a kan doguwar kujerar palon ya na ta tunanin yanda zai samu ganinta yau.
Itama Nadiya bayan ta gama komai ta zauna a kusa dashi tana chatting tana dariya domin ta tambaye shi ko bashi da lafiya ne ya ce mata lafiya lau yake. Yana cikin kallonta wayarsa ta fara ƙara. Da sauri ya duba ganin itace yasa har jikinsa rawa yake yi ya ɗaga yana barin palon. Nadiya ta bisa da kallo har ya turo ƙofar. Shiru Habib yayi yana sauraron kukan da take yi na Ratsa zuciyarsa kamar ya ce mata dan Allah tayi hakuri karta nakasa masa zuciya da wannan kukan nata. Ta ce "Sir ina ta kiranka tun jiya baka daga ba, gaba ɗaya jiya da yau ban ganka ba babu school, Please ina son ganin ka?" Ta karasa da kukan da takeyi. Ya sauke ajiyar zuciya muryarsa na rawa ya ce "Zaki iya fitowa yanzu?" Ya faɗa wanda shi kansa bai san ma ya faɗa haka ba. Sai da yayi furricin kuma ya yi saurin toshe baki ya na katse kiran. Da ƙarfi ya daki kansa ya na faɗin Meye haka me nake yi haka ne, me nake nufi. Ya na cikin haka Nadiya ta bubbuga ƙofar ta na kiran sunansa. Kafin ya amsa kuma sakon Haura ya shigo wayar tasa. Kallon ƙofar ɗakin yayi kafin ya kalli wayar da wani sakon ya shigo. Ya ce "Yes Bebb I'm okay" ta ce "Ka buɗe min kofar zan shigo?" Ya mike ya buɗe mata ta shigo ta na bin sa da kallo. Ta ce "Bebb ko dai asibiti ne zamu je Please?" Ya girgiza mata kai ya ce "Idan na sha magani nayi barci komai zai wuce, dama fa kawai ciwon kai ne kaɗan. Nadiya ta ce "Ciwon kan shine kaɗan, amma ɗazu kace lafiya kake, ai ni nasan a kwai abun dake damun ka, amma kace babu komai, waye ya ce maka ana wasa da ciwo, bari na kawo maka magani. Ta na faɗa ta fita da sauri ya bi ta kallo. Ta na fita ya buɗe sakon ya fara karantawa. Ya fito ya karanta na biyun. Shiru yayi ya na sake karanta saƙon da kyau, yana son rubuta mata amsa amma wata zuciyar na hana shi, haka ya shiga gurin yin reply ya fara rubuta mata sunan gurin da zasu haɗu ɗin kamar yadda ta tambaya. Ya na gamawa ya danna send ya na kallo har ya shiga. Minti ɗaya da shiga sai ga kiranta. Da sauri ya ɗaga yayi shiru. Ta ce "Ban san gurin ba, kawai kazo ƙofar gidan mu sai ka ɗaukeni mu tafi tare" ta faɗa da wani irin annashuwa a muryarta, shi kuma yayi shiru ya kasa magana zuciya da ransa na azazzala shi. Zuciyar ce ke zaiyano masa surar ta, da irin kyawawan fuskantar ta, da yanayin surar jikinta har yaji yana son sanin su yau ɗin nan, a hankali ya ce "Naji zan zo yanzu" ya faɗa yana kashe wayar sai kuma ga Nadiya ta shigo ɗakin riƙe da ruwa da maganin ciwon kai. Zama tayi kusa da shi ta ɓallo masa maganin ta ce ya buɗe bakin kaman yadda akewa yaro ƙarami. Ya buɗe yana kallonta. Ta saka masa maganin sannan ta miƙa masa ruwan ya sha. Ta ce "Zaka kwanta anan ne ko palo zaka je?" Tayi maganar tana kwallonsa. Ganin ya na ta kallonta kuma bai ce komai ba ne yasa ta ce "Bebb lafiya kuwa, irin wannan kallon ai sai ka tsorata ni" Ganin bai daina kallonta bane kuma bai ce komai ba sai ta miƙe tsaye ta ce "Bebb dan