Showing 30001 words to 33000 words out of 58144 words

Chapter 11 - A Bar Wa Rai Complete Books By S Reza.txt

S Reza   

12 Mar 2026

28

na da alfarma a school ɗin, asalin mai makarantar abokin mahaifinta ne na sosai, ko lokacin da za'a bada aikin akwai sa hannunta dan zai iya cewa saboda ita ne ma aka ɗauke shi, kuma ko yanzu idan tayi magana za'a duba. Duk yadda Habib ya kai da doje mata amma ya kasa, komai ya faɗa sai ta ce itafa wallhi sai taje, ko ya manta da yadda aka samu aikin ne. Haka ya hakura ya barta har zuwa washegari. Ai kuwa kaman yadda ta faɗa haka ta shirya zata fita Habib ya tare mata hanya akan babu inda zata je. Ta kalleshi sama da ƙasa ta na rasa mai zata ce masa. Shi wai bai san cewar ta gane ƙarya yayi mata ba ne, tun lokacin da ya ke ta wannan surutan cewar ya ɗauki gaddara da meye meye ta gane ƙarya ne, wanda aka kora daga aiki duk yadda ya kai da ita yarda da yadda da gaddara ba haka ya kamata aga fuskarsa da kalamansa ba, babu damuwa a fuskarsa, kuma babu tsoro da fargaba da tashin hankali a kalamansa. Sai kawai ta ce "Faɗa min gaskiyar abin da ya faru?" Ta faɗa cike da ɓacin rai. Ita tunda taga yana ta hana ta zuciyar ta ta ɗarsa mata cewar Habib baida gaskiya, kuma ta sake tabbatar da hakan ɗin ne yanzu. Tabbas yana ɓoye mata abu tun ba yanzu ba, kuma tasan yadda zata yi da shi. Ya ce "Ban gane gaskiyar abin da ya faru ba?" Ya faɗa cike da mamaki. Ta ce "Kai ba yaro bane, kasan abun da nake nufi, maganar korar da kace an maka ba haka bane Habib, faɗa min gaskiyar Abin da ya faru?". Habib ya ce "Tabbas gaskiya ne, nine na bar aiki da kaina, kuma dan Allah karki tambayeni dalili, ban san mai zan ce miki ba, amma namiki alƙawarin zan samu wani aikin nan kusa. Dan Allah karki ce komai idan kina ƙaunar Allah da Manzonsa, kuma idan har kina sona saboda Allah Please Bebb?" Ya karasa harda risinawa har ƙasa. Nadiya ta share hawayen da ya zubo mata, a hankali ta ce "Haka kake so?" Ya ce "Eh bana son kimin maganar ban san mai zance ba". Ta ce "Ba zan yi ba, in sha Allahu ba zan ce komai ba". Ta na faɗa ta koma ɗaki ta cire hijjabin da ta saka ta zauna a bakin gado ta fashe da kuka.

Habib ya sauya mata, ya shigo da halin da bata san shi da shi ba wato ƙarya, mai yasa zai dinga mata karya, ko dan ta damu da shi, ko yana tunanin samun aikin wasan yara ne, sannan gurin da zasu iya biyan sa kamar wannan ma ba wasa bane, sosai tunaninta ya tafi tariyo mata farkon auransu da shi yadda suka yi zaman hakuri. Duk yanda take son jin abun da ya faru haka ta kawar da kai bata ƙara ce masa komai ba shima haka. Kullum yana gida, daga ɗaki sai palo sai Kuma masallaci, wasu lokutan ne ma yake ɗan fita. Nadiya dai bata kara masa maganar komai ba kamar yadda ya roka, shi kuwa yana ta binciken makarantar da zai fara zuwa domin neman aiki. Daidai da minti ɗaya bai taɓa mantawa da Haura a zuciyarsa ba, sai dai yanzu ya tabbatar da cewar dama kawai sha'awar ta ya keyi, yanzu ko ya tuno ta baya jin Komai sai ma tsanarta da wani irin haushin ta da yake ji, kullum sai ya tsine mata ya kuma roƙi Allah akan karya haɗa shi da ita har abada. Yau harda mafarkin sun haɗu a hanya ta ganshi ta biyo shi da gudu yayi tana ta cewa "Sir Sir", hakan yasa yana farkawa ya fara salati domin baya ko son tunowa da ita. Haka kawai yaji jikinsa ya mutu sai yake jinsa wani iri kamar mara lafiya. Palo ya fito ya zauna yana ta bincike a makarantu kusan guda huɗu. Ya ce "Bebb zo ki gani ina sa ran in sha Allahu zan samu aiki anan?" Ya faɗa yana kiranta akan tazo ta ga makarantar. Ta ce "To Allah ya bada sa'a" ta faɗa tana cigaba da danna wayarta. Ya sake cewa "Bebb zo dan Allah a cikin wannan da wannan wanne ya kamata na yi applying, ko wannensu suna da tsari ga shi ba laifi suna da tsoka?" Ta ce "Ka zaɓi duk wanda yayi maka kawai" Ya ɗago da sauri ya ce "Bebb wai miye haka ne dan Allah, wani abu nayi miki ne?" Ta ce "Mai ka gani kuma?" Ya ajiye laptop ɗin a gefe ya dawo kusa da ita ya ce "Bebb ban sanki da fushi ba, dan Allah komai ya wuce?" Ta ce "Wai wani abu ne dama ya faru? Kana ta cewa ya wuce meye shi zai wuce ɗin ne?" Ta karasa harda dariya. Habib yayi shiru ya cigaba da aikin sa yana satar kallonta. Yana ta kokarin sako ta a hirar amma tana basarwa, abun da ya lura magana idan har ta shafi aiki ne bata so, shi yasa ya daina mata maganar. Sosai yake ta satar kallonta ganin yadda take ta aiki kamar ba mai ciki ba. Shi dai yana jin labarin yadda masu ciki ke bawa mazajensu wahala, ko na laulayi kona rashin lafiya ko iya shege, amma dai shi Nadiya kamar ma son aiki aka ƙara mata da ta samu ciki, kaman ya tambayeta ko baƙi zatayi ne ganin yadda ta dage amma ya waske. Ta ce "Bebb zaka iya komawa ciki da aikin nan zanyi baƙi yanzu Please?" Ta faɗa ta na kallonsa. Ya ɗago da nufin yin magana amma ganin yadda ta haɗe rai, kuma shine mai neman shiri, sannan dama haka take yi, shi zai ce bai taɓa ganin kishi irin na Nadiya ba, muddin zatayi baƙi yana gida to zata ce ya koma daki kar ya fito sai sun tafi, sannan bata taɓa iya haɗa shi da wata ko da kuwa kawarta ce bare kuma wacce bata sani ba. Bata da hayaniya amma tana iya hukunta shi da fushinta mai sanyi ba tare da tayi magana ko ta hana shi wanni hakkinsa ba. Ya tashi ta ce "Idan sun tafi zan faɗa maka". Ya ce "Kin san dai lokacin sallah ya kusa gara dai su tafi da wuri?" Ya na faɗa ya wuce yana jin wani kasala da kuma tuno da abun da ya faru tsakanin sa da Haura, abun da take tsoron ai ya faru, shure-shure baya hana mutuwa. Haka ya koma daki yaci gaba da aikinsa. Yana cikin aikin ne ta shiga ta kawo masa irin abun da tayi harda Yorgot mai sanyi da soyayyen naman kaza. Bata ko tsaya ba ta koma tana jin yana mata godiya. Haka dai har ɗaya da rabi ya na ta aiki. Ya samu makarantu guda huɗu da zaiyi applying wanda dukkansu ya yarda da tsarin su, kuma fatan nasara. Ya ɗauko takardusun ya shigar da baya nan sa nan take kuwa ya tura gaba ɗaya. Daidai lokacin kuma aka kira sallar azahar. Da farincikin ya shiga toilet ya ɗauro alaula ya fito ya sake duba laptop ɗin yaga da gaske ya shiga sai ya nufi masallaci.

Yana buɗe ƙofar palon gabansa ya fadi wanda bai san dalili ba, da sauri ya dafe gurin ya fara karanto addu'o'i domin sosai gaban nasa ya fadi. "Good afternoon Sir?" Ya tsinkayo muryar ta kamar daga cikin kansa ko daga sama, kuma kamar daga zuriyar sa ta fito. Sautin muryar ya dinga masa yawo a kunne, kuma kamar a mafarkin da yayi da ita ɗazu. Ya juyo da sauri ya hangota zaune a gurin cin abinci ita ɗaya sanye da irin kayanta wannan karan jar abaya tana masa murmushin nan nata mai tsaya masa a zuciya. Wani yawu ya hadiya mai kauri yana kallonta. Ta ce "Kaje kayi Sallah ka dawo ina jiranka, idan ka daɗe zan iya kwana saboda kai Sir, kasan bana iya jure rashin ka" ta ƙarasa ta na kanne masa ido ɗaya, kuma maganar a hankali wanda ba dan hankalin sa na gareta ba ba lallai ya ji ba. Habib yaji kamar zai kasa tsayawa. Yana cikin haka yaji alamun tafiya ai da sauri ya fita ba tare da yace komai ba. Yana fita ya tsaya yana kallon cikin palon daga waje, ya mutsutsuka idonsa da karfi ya buɗe. Lokaci ɗaya ma ya rasa me ma yake faruwa. Saida yaji an fara sallah ya tuno da abun da ya fito da shi. Ya nufi masallaci yana tafiya yana yana leƙen baya. Yana kusa da saitin motarsa yaga anyi rubutu da irin abun da aka taɓa yi masa da shi a makaranta. "Sir I miss You, I come over u Sir, I come to see u Sir, Sir I'm in your house Sir. Gaba ɗaya haka ta dinga rubutawa a jikin motar. Da sauri ya shiga sharewa yana jin wani sabon masifa da tashin hankali har cikin gida, yana ganawa ya nufi masallaci kamar yayi kuka. Koda ya fito sai ya tsinci kansa da tsoron shiga gidan, kuma yana tsoron ƙin shiga ɗin. Wai ma to a ina ta santa, wama ya nuna mata gidan nasa?...📝



S-Reza...
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*

              _FCWA_
            
_Whasop chenal_
https://whatsapp.com/channel/0029VaBJBOr8vd1H4qb9rd1a
                *Chapter 13*
Dole ya danne zuciyar sa ya koma cikin gidan domin kuwa rashin komawar babbar matsala ce a gareshi. Da sallama ya shiga gabansa na faɗuwa, zuciyar sa na raya masa abubuwan da bai ma san adadi su ba, babban abun da ya ke tsoro bai wuce Haura ta tona masa asiri ba, kuma ya lura yarinyar bata da hankali sam-sam, kanta rawa yake yi. Hauran ce ta amsa sallamar sai ya kasa ɗaga kai ya kallesu dalilin ganin Nadiya a gurin. Kasa tafiya yayi sai kawai ya samu guri ya zauna domin so yake yaji wacce irin hira suke yi, kuma ma yaushe ne har Nadiya ta san haura, ko dama sun san juna ne. Tambayoyi ne furjik a kansa wanda dole ya ɓoye abansa domin babu wanda zai tambaya a wannan lokacin. "Nadiya ce ta miƙe ta zuba masa abinci sannan ta kalleshi ta ce "Ga abincin bari na kai maka ɗaki ina tare da baƙuwa ne?" Ta ƙarasa ta na wucewa ɗakin. Ya sani bata son ganinsa a palon ne saboda baƙuwa, shi kuma yau ba zai bar palon nan ba har sai wannan da take kira da baƙuwar ta tafi. Nadiya kuwa bata san cewar Habib ya fita ba, sai da taga ya dawo yanzu. Sai da gabanta ya fadi lokacin da ta ji sallamar sa, bata ƙara cika da mamaki ba sai da taji Haura ta amsa masa sallamar da wannan muryar tata wacce ita ma da take mace sai da tayi mata daɗi, bare kuma Namiji kamar Habib. Hakan yasa ta ƙara jin wani iri a ranta na rashin daɗi da tsoro, bata wasa da miji ko kaɗan, bata sakin fuska ta wannan bangaren. Ta na cikin haka taga ya zauna a palon kuma ya kunna tv ya raƙe ƙara ya na kallo, wato dai anan zai zauna. Abun da ya fara zuwar mata shine ya ganta kuma yaga ta burge shi, shine yasa ya zauna domin ya dinga kallonta. Hakan yasa ta zuba masa abincin ta wuce da shi ɗaki domin kawai ya zauna yaci a ciki. Har ta kusa shiga dakin da abincin ta tsinkayo muryar sa ya na faɗin "Bebb a koshe nake, ki bari zuwa anjima sai naci, kin manta ɗazu kika haɗa min kayan ciye-ciye, to har yanzu ban cinye ba". Ya faɗa yana kallon tv show ɗin da bai ma san mai suke yi ba. Juyowa tayi ta na so su haɗa ido amma yaƙi yin hakan, ta kalli gurin da haura take zaune taga su take kallo. Babu yadda ta iya saboda kar ta bada shi a gaban bakuwa yasa ta dawo da abincin.

"Ina uni" Dukkanin su suka tsinkayo muryar Haura tana gaida Habib cike da salo mai jan hankali. Kasancewar hankalinsa na gurinsu yasa ya san da shi take. "Am um umm la laa lafiya lau, ya gida ya karatu to madalla" ya amsa a rikice tsoro fall muryarsa. Daga haka kuma kowa yayi shiru suna cin abinci shi kuma ya kallo biyu. Jin shirun yayi yawa ne yasa Haura faɗin "Anty gidan nan naku yamin kyau sosai, Allah yasa saurayina ya gina min irinsa". Nadiya ta ce "Amin" ta faɗa kamar bata so, domin ta cika sosai, sai hararar Habib take yi, kuma hankalinta duk yana kansa. Haura da ta lura da hakan sai taji daɗi, ai kuwa sai cewa tayi "Bari na ɗan zazzaga naga gidan da kyau" Nadiya ta ce "Ba yanzu zaki tafi ba ko?" Ta tambaya da wata irin siga da saida Habib ya kallosu. Haura ta ce "Anty ai babu damuwa na fadawa Anty Mera cewar sai yamma zan koma, nace idan ta gama ta wuce kawai zan dawo da kaina. Nadiya ta yi shiru bata ce komai ba. Sai mamakin ƙarfin halin yarinyar da take yi.

*°Haura*
Miƙewa tayi ta fara zazzaga cikin palon ta na yi tana cigaba da jan Nadiya da hira game da cikinta ta na tambayar yaushe ne zata aihu. Ta bi ta bayan kujerar da yake zaune tana tafiya kanta a sama ita a dole saman ɗakin take kallo. Ta na zuwa saitin inda yake, ta shafa masa wuya ta wuce. Ta sake dawowa ta gabansa tana tafiya tana yabon palon da kayan cikinsa. Ganin haka yasa ya nade ƙafafuwansa domin karta taka shi, a tsorace yake sosai, ya na jin rashin daɗi ace Nadiya tasan abun da ya aikata. Ta shiga kichin ta dubo ko ina tana ta yabon gidan. Ta dawo ta zauna tana kallon Nadiya ta ce "Anty gida fa yayi kyau, yanzu idan na tafi sai kuma suna ko?" Nadiya dai sai murmushin yaƙe takeyi domin lamarin ta ya fara fitar mata akai, gashi yarinyar sai kwarjini take mata. Haura ta ce "Anty bari nayi miki wanke-wanke yau na hutar da ke ko dan saboda Baby". Nan take ta fara haɗa kayan ta kai kichin ta ce "Shikenan abun da za'a wanke?" Ta tambaya domin ta na so ko dai tace ita ta shiga ɗakin habib ta kwaso ko ita Nadiyar ta shiga. Nadiya ta ce "Ai Aisha da kin bari ma, babu komai zan iya yi fa" Haura ta ce "Ba komai anty ai yaune kawai kinga sai ki huta. Nadiya na shiga ɗakin ta ƙaraso gurin da yake da sauri ta ce "Kace mata kaine zaka kaini gida domin ina son magana da kai, idan kuma ba haka ba wallhi zan kwana ana kuma zan faɗa mata komai dake tsakanin mu" Ta na faɗa ta koma gurin ta da take ta tsaya. Habib kuwa wani irin sabon tsanarta ne ke ƙara taso masa idan tayi magana, tabbas shima zai so yayi magana da ita domin ya faɗa mata matsayinta yanzu, dole ya zazzage ta idan ta kama ma harda duka domin ta fita daga sabgarsa, ta fita a rayuwarsa. "Bebe "Bebb "bebbbb!?" Ta faɗa da ƙarfi ganin kamar hankalin sa ya yi ɓatan dabo. Amsa yayi yana kallon Nadiya tsaye a gabansa ashe har ma ta fito daga ɗakin bai sani ba. Ya ce "A ina kika samo wannan yarinyar mai ido a tsakar ka, mara kunya mara kamun kai haka?, tazo sai zazzaga mana gida take tana ta surutu?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye sai zare ido yake yi, kuma haɗe da borin kunya. Nadiya ta kafe shi da ido tana jin faɗuwar gaban nata na ƙaruwa. Tsoro ne ke son kamata amma ta dake ta ce "Shi ne yasa ka zauna a palon bayan kasan bana so?" Sannan ina ruwanka da ita?" Ya ce "Okay haka zaki ce, to tazo ta bar min gida, karna sake ganin ta, kina kallon idon ta kinsan bata da kunya, kuma ni ban ma yarda da ita ba wallhi, kawai ta bar min gida yanzu". Ya ƙarasa yana nufar kichin ɗin kamar gaske. Har ransa yana so ta bar gidan ko dan ya samu ya warware mata komai. Ita kuwa Nadiya taji daɗin abun da yayi, kuma har ranta Itama tana so ta tafi ɗin amma ba zata so ayi mata haka ba. Da sauri ta tsayar dashi ta ce "Zan mata magana Please ka bari?" Haka ya dawo palo ya zauna, dama borin kunya ne, sai kuma ya tashi ya shiga ɗaki. Wani tinani tayi domin ganin kamar hakan zaifi, bata so ta bari a wulakanta mata baƙuwa ba, musamman ma Haura da yau ne suka fara haduwa.

Haura kuwa duk abin da sukeyi tana jinsu. Hakan yasa tana shigowa ita kuma ta gama wanke-wanke sai kawai ta ce "Anty zan tafi, Anty Mera wai Daddy na faɗa yace mudawo tare?". Nadiya ta ce "Kuma tun yanzu ki bari ayi sallar ƙarfe huɗu mana ko?" Ta ce "A'a anty Daddy yana da faɗa, idan kin aihu zan zo suna". Tana faɗa ta fito daga cikin kichin ɗin bayan ta wanke hannu kuma ta na dariya. Nadiya ta ce "Ina zuwa?" Ta shige ɗaki. Habib yayi mata wani irin kallo ya ce "Wawiya mara kamun kai! Wallahi kinji Kunyar rayuwarki, ace kina bin namiji har gida saboda tallan kai, to bari kiji wallhi ni na fi karfin ƙazamar mace irinki stupid kawaii". Ya ƙarasa yana ja da baya ya kawar da kai. Haura ta yi shiru tana sauraronsa. Bata iya cewa komai ba har Nadiya ta fito. Ta miƙa mata baƙar leda tana mata Allah ya kiyaye hanya. Ƙasa ƙar ɓar ledar tayi domin zuciyarta da tayi mata zafi, ji take kamar a mafarki irin kalaman da suka fito daga bakinsa, sannan ga irin kallon da yake mata. Ta ce "Anty kisa uncle ya ajiye ni a gida Please ban san Daddy ya min faɗa idan ya ga na koma gida ni ɗaya?" Nadiya ta ce "Bebb pls aje min ita a gida dan Allah?" Ya kalli Haura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login