Showing 12001 words to 15000 words out of 58144 words

Chapter 5 - A Bar Wa Rai Complete Books By S Reza.txt

S Reza   

12 Mar 2026

16

da faɗa sosai wanda ita kanta sai da ta sake kallonsa. Haura ta ce "Ban san cewar kana da mata ba, kuma bayan na sani hakan bai dame ni ba, ni dai kawai nasan ina sanka Sir, dan Allah kace kaima kana sona, wallahi ban taɓa son kowa ba sai kai, kaima ban san lokacin da na fara sanka ina jin ba zan iya rabuwa da kai na sir". Ta faɗa da iya gaskiyar ta har muryarta na rawa. Ya ce "Bana son shirme da hauka, bani waya ta zan tafi gida, mata na tana jirana, kuma daga yau karki ƙara min wannan shirmen. Haura ta ce "Kana son matarka sosai ko Sir?" Ya ce "Fiye da komai ma kuwa, bana haɗa ta da kowa" ta mike tsaye ta ce "Tom nima ina sonta fiye da komai Sir tunda kana sonta, kuma watarana zan kawo mata ziyara, domin na ɗauki number ta a wayarka. Habib ya kalleta da sauri zaiyi magana ta ce "Sir bari na kawo maka wayar, kuma dan Allah ko ruwa ne ka sha idan ba haka ba ba zanji daɗi ba, kuma ka gaida min da Anty Bebb kace ina sonta ina kaunar ta. Tana faɗa ta nufi cikin gidan ya bita da kallo. Ya na tsaye zaune a gurin ta dawo riƙe da wayar. Saida ta zauna kafin ta ce "Sir ga wayar taka" Habib ya ƙarɓa ya miƙe zai tafi. Tasowa ta yi ya matso kusa da shi ta ce "Bari na raka ka zuwa motar Sir" Har suka karasa bai ce komai ba sai wayarsa da yake dubawa. Bayan ya shiga motar ne ya ajiye wayar zai rufe motar yaji ta riƙe murfin. Kallonta yayi ya ce "Wai ke mai yasa baki da zuciya ne, dan Allah ki fita daga sabgata nace miki ni ina da mata. Haura ta kafe shi da ido har saida ya janye nasa. Ta ce "Sir ka manta abin da nace maka ɗaxu cewar zan iya mutuwa idan ka rabu da ni? Da gaske baka sona?" Sai kuma jikinsa yayi sanyi har ya ji wani irin tausayinta...📝




S Reza....
[09/07 à 14:07] S Reza: *ABARWA RAI❣️*

*°S-Reza✍️*

_First class writers association_

_My whasop chanel _

*Chapter 6️⃣*
Rau-rau ta yi da ido kamar za ta yi kuka kuma har lokacin shi ta ke kallo. Ya ce "Kamar yadda na faɗa miki cewar inda aure to dan Allah ki fita daga sabgata, bani da burin ƙara yin wani auren". Ya na faɗa ya rufe motarsa ya mata kii ya bar gidan. Ta kai minti uku a tsaye kafin ta juya ta shiga cikin gidan. Ta na shiga palon ta tarar babu kowa hakan ya sa ta shige ɗakinta, sai da ta cire hijjab ɗin jikinta sannan ta shiga toilet. Koda ta fito doguwar riga kawai ta saka ta ta barci sannan ta kashe wutar ɗakin ta kwanta. Wani irin abu take ji game da Malam Habib wanda bata san yaya zata masalta shi ba. Fuskarsa da gemunsa da yanayin murmushin sa harda ɗaure fuskar sa duk burgeta ya ke yi, tafiyarsa da ƙamshin sa, maganar sa da fushin sa. Gaba ɗaya komai nasa kyau yake mata, ta na sonsa ita kanta ta san da hakan. Sai kuma ta fara tunanin yadda zata saka shi shima ya so ta, domin ta lura yana son matarsa sosai kamar yadda ya ce mata. Haka haura ta raba dare ta na tunanin yadda za ta ɓullowa Habib har ya fara sonta. Da asuba kiran sallah ya tashe ta Kamar kullum. Bayan ta tashi ne ta ji jikinta a jiƙe hakan yasa ta yi saurin tashi ta shiga toilet ta na mamakin faruwar hakan a mafarkinta a karon farko. Bayan ta idar da salla ta sake komawa barci kasancewar ranar juma'a ce bata da class har sai Monday hakan yasa take son ta biya bashin barci. Wata karamar riga ta saka wacce ko guiwa bata wuce mata ba, ta ja bargo ta fara barci.

Ta na barci Salim ya shigo ɗakin ya na kiran sunanta da karfi kamar an turoshi, ta buɗe ido zata yi magana taga haske ya cika ɗakin. Da sauri ta duro daga kan gadon ta ɗauƙi wayar ta domin duba lokaci. Ganin takwas harda minti biyar ya sa ta kama hannunsa suka fito ta manta da iya rigar barci ce ajikinta kawai. Ta na fitowa palon da nufin shiga kichin gurin Amera saboda jiyo motsinta da tayi a cikin shi kuma Adam ya fito cikin shirin sa na zuwa gurin aiki riƙe da hannun Salma. Kallo ɗaya ya yi mata ya yi saurin kawar da kai ya na jin wani irin kasala na son kama shi. Haura da bata kula da yanayin ta ba ta ce "Daddy good morning?" Ta faɗa ta na ƙarasowa har gabansa. Muryarsa na rawa ya amsa ya na ƙoƙarin ha na kansa sake kallonta amma ina zuciyar sa ta yi rinjaye akan son ganin abun da bai dace ba. Ya sake ɗaugo kansa a karo na biyu ya sauke a kanta sai yaji natsuwarsa ta kau, ya tsinci kansa da karewa halittar jikinta kallo kasancewar komai a bayyane suke, ya na shagwaltuwa da hakan har ya na jin wani annashuwa na son kama shi, zuciyar sa na raya masa cewar lokaci yayi da zai ƙarasa aikin ladan da yayi niyya. Muryarta ce ta dawo da shi zahirin sa. "Daddy har ka shirya zaka tafi kenan, kaci abinci ne?" Adam ya ɗan sosai kai ya ce "Am a am ai na dawo tun ɗazu, ai sorry eh yanzu zan tafi sai na dawo" Ya karasa ya na barin gidan Salim da Salma suka shiga mata Bye-bye suna bin Daddy a baya.

Haura ta ƙarasa kichin ɗin ta buɗe ta shiga ta na godewa Allah ma da yasa yau bata da class. Amera da ta juyo jin an shigo. Suna haɗa ido ta ce "Meye haka haura, a haka kika fito babu kaya a jikinki, ko kin fara hauka ne?" Ta ƙarasa ranta a mugun ɓace. Da sauri ta kalli jikinta sai ta toshe baki ta ce "Haba Anty babu kaya kuma, rigar barci ce fa, bari na je na sauya to". Ta na faɗa ta juya ta koma ɗaki domin sauyawa. Binta da kallo Amera ta yi ta na mamaki Allah dai yasa lokacin da ta fito Adam ya fita bai ganta a haka ba. Har zata cigaba da aikin amma sai ta kasa ta fara tunanin wannan iya shegen, sam ba zata saɓu ba, dole ta taka mata burki, ba zata juri wannan karuwancin ba, ko kuma tunda dai har an samu wanda ta fara so kawai ta turo shi yazo a faɗa masa ita ɗin wacece idan zai iya auranta a haka ya aureta ta kama gabanta, ai sunyi wanda zasu iya. Ajiye aikin ta yi ta fito palo har lokacin ta na jin haushin abun da ya faru, dama kwana biyu ta fara lura da yarinyar kamar ta na son tsoro da sabon salon rayuwar da bata santa da shi ba, to dole ta dauki mataki tun yanzu. Zaune ta samu Haura ɗin ta zuba abinci amma ta kasa ci sai kallon guri ɗaya kawai ta keyi bata ma tasan ta zauna ba. Amera ta ce "Magana nake son yi da ke Haura?"

Zumbur ta dawo daga tunanin da take yi ta kalli Amera sai taga fuskar nan tata a ɗaure. Ta ce "Anty ina kwana?"

Amera ta amsa da cewar "Lafiya, magana nake son yi da ke?"

"Tom ina jinki Anty" Haura ta faɗa ta na bata hankalinta gaba ɗaya. Ta ce "Shi wannan da yazo gurinki yaushe kuka haɗu, kuma sanki yake yi ko dai kawai Soyayya ce ta kawo shi?" Ta faɗa ta na kuma kafe haura ɗin da kallon da ta kasa gane masa.

Haura ta ce "Anty saurayi nane" ta faɗa iya haka kuma tayi shiru. Ran Amera ya ɓaci domin bata son shiru-shirun wannan yarinyar. Dama tasan ba zata taɓa faɗa mata gaskiya ba.

Ta ce "To idan da gaske auranki yazo yi kice masa ranar Sunday Daddynki na son ganinsa"

Haura ta ce "Mai zai zo yayi masa?"

Ta ce "Yazo ayi maganar aure mana, ko ba auranki yazo yi ba?"

Da sauri ta ce "Eh aure ne amma kuma ai" sai tayi shiru. Ta faɗa tunanin yadda ma take sonsa shi kuma ko a jikinsa.

Amera ta ce "Koma meye kice yazo idan yazo ai Daddy ɗin zai masa magana. Yanzu dai ki gama cin abincin ki haɗa wannan sauran kwanunkan ga cen sauran tukwanan da na fara wankewa, sai ki haɗa ki wanke tunda yau soyayya yasa kin makara baki fito kin yi aiki ba. Ta na faɗa ta mike ta bar gurin

Haura ta fara cin abincin ta na tunanin maganar Amera. To ita da bai ma ce ya na sonta ba ina batun zuwa ayi maganar aure. Ita bata san cewar da hakan zai faru sai ta fi kowa murna ba. Bata gama cin abincin ba ta kwashe ta kai kichin ta gama wanke komai kafin ta koma ɗaki. Waya ta ɗauka ta danna kiran number sa, wanda tun ɗazu take ta saurin tazo ta kirasa ko Allah zai sa ya ɗauka taji muryarsa kawai. Sai dai har ta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kira tayi shima ba'a ɗaga ba. Sai ta tura masa saƙo. Bayan ta tabbatar da ya shiga sai ta nemo number Bebb ta danna kira ta na sakin murmushi. Saida ta kusa tsinkewa kafin aka ɗaga. Ta cikin wayar Nadiya ta yi Sallama. Haura ta amsa. Ta ce "Wacece?" Haura ta ce "Aisha ce" Nadiya ta ɗan shiga tunanin wacce Aisha ce haka. Kafin ta yi magana ta ce "Ina zuwa" ta na faɗa ta kashe wayar.

A ranar babu inda taje dama ita idan ba school ba bata fita ko ina, sai dai idan Amera zata aikata gidan Umma ko gidan Nana ko kuma gidan su Anty Khadijah. Haka ta uni a cikin ɗaki tana ta chatting da Nadiya wacce har suka ɗan saba, so take ta san har gidan Malam Habib yadda zata bashi mamaki ta nuna masa tabbacin ita fa sonsa take yi. Sosai suke ta shan hira da Nadiya kaman dama sun san juna, a cikin hirar ne Nadiya ta gane Haura bata jin Hausa sosai, domin ko a rubutun ma a kwai kurakurai sosai, haka idan tayi mata voice not shima zata ji Hausar bata fita sosai.

Bangaren Adam kuwa yana fita daga gida ya nufi school ɗin su Salim ya ajiye su kafin ya nufi gurin aikin Najib gaba ɗaya ya na ta saƙe-saƙe a ransa game da lamarin Haura. Bayan sun zauna Adam ya ja dogon numfashi ya busar da iska daga bakins ya na ƙoƙarin ganin ya samo makamar zancen da zai yi domin najib ɗin ya fahimci halin da yake ciki. Najib dai sai kallonsa yake yi ya na mamakin ko me yake damunsa har haka da kasa sakewa. Adam ya shafo daga tsakiyar kansa har gemun sa ya ce "Najib I'm serious about it, please karka ɗauki maganata da wasa dan Allah?" Ya ƙarasa ya na haɗa masa hannu alamun roƙo. Najib ya ɗan yi dariya mai sauti ya ce "To ai ba sai ka faɗa ba, kowa ya dubeka yasan cewar you're serious friend. Adam ya ce "Aure zan ƙara Najib, kuma Haura nake son aura"  Ya faɗa yana kallon Najib kaman shine zai bashi auran Haura ɗin. Najib ya kafe shi da ido ya tunanin abubuwan da suka faru a baya, zuciyar sa ta shiga tariyo ma wacece Haura ɗin. Kusan minti biyu bai iya cewa komai ba har Adam ya kaji da jiran amsar da zai bashi. Ya ce "Kayi shiru kuma kasan shawara nake nema?"  Najib ya ce "Adam wallahi baka da hankali, yarinyar da sanadiyyar ta har ta kusa raba ka da matarka, yarinyar da ta sakawa matarka aljanu gaba ɗaya ta addabi kowa, ita ce kake cewa zaka aura, to kai yanzu zaka iya kwallon idon Amera kace mata zaka auri Haura, wato saboda kaga ta na da hakuri ta yarda yarinyar ta zauna a gidanta ko, to bari kaji wallahi muddin kajewa Amera da wannan zancen sai ta dawo Amera mai ciki har ma fiye da haka, wannan wani Irin cin amana ne. Da sauri Adam ya mike tsaye ya ce "Allah ba zai nuna min wannan Ameran ba in sha Allahu, kuma ai duk wannan abun ba ita ba ce tayi, ita bata ma san tayi ba. Najib ya ce "To yanzu kuwa zata yi wanda tasan tayi, haba Adam, ko kai a kayiwa wannan abun ba zaka ji daɗi ba, nifa bari kaji maganar gaskiya wallahi har yanzu ban gama yarda da wannan yarinyar ba, tsoron ta nake ji dukda dai kace yanzu bata tare da komai amma dai ni ban yarda ba. Adam ya ce "Haba Najib meye kuma na dawo da abun da ya wuce, shekara nawa muna zaune da ita amma bata nuna komai ba, wallhi bata tare da su, ta musulunta ta dawo kamar kowa bata tsafi bata komai normal take kamar kowa, please ka fahimce ni?"  Najib ya ce "Idan shawara kake nema to dan Allah Adam ka rabu da wannan yarinyar, iya wannan taimakon da kayi mata ma ya isa haka, haba wannan yarinyar ita kaɗai ce mace ne Adam, idan da asiri akayi maka kenan yanzu iya shege ne ko me. Adam ya ce "To idan na barta waye zai aureta a haka, muddin ina son cika aikin alkairin da nake yi shine auranta, Karka manta fa yanzu bata da kowa sai mu, kuma duk wanda yazo da nufin auranta idan yaji asalinta ba zai aureta ba. Najib ya ce "Wai ita yarinyar ta na sonka ne, kuma kaji ta bakin Amera akan hakan?" Adam ya ce "Bangaren yarinyar babu damuwa, sai dai ita Amera ɗin ce ban san yadda zata karbi maganar ba, shine nake so kaje ka fahimtar da ita dan Allah. Najib yayi masa wani irin kallon baka da hankali. Ya ce "Amma dai baka da hankali ne ko, ok Kai da ka shirya abun ba zaka iya ba sai ni, to ko ni ban goyi baya ba bare baje na fahimtar da ita, ni ma ban fahimta ba. "Adam ya sauke ajiyar zuciya. Najib ya ce "Adam kenan, inaga ka manta bura'uban da ya faru a gidan ka ne a baya shi yasa kake son dawo da wani sabon domin ka huta yanzu, to ni dai na baka shawara saboda haka Allah ya bada sa'a ubangiji yasa ayi a sa'a. Adam ya amsa da amin. Ya ce "Dan Allah karka sanarwa da Khadijah wannan maganar yanzu?" Najib ya ce "Au itama tsoronta kake ji kenan" ya ce "Ina son bin komai a hankali ne.

Haka Adam ya bar gurin ya nufi gurin aikin sa. Har lokacin shi bai ga wani abun tashin hankali anan ba, ai yasan itama Ameran zata so zama da haura ɗin domin bata da matsla komai zata taimaka mata sosai, gashi yara sun saba da ita, ga maganar aihuwa da har yanzu babu labari kuma shi yana son yara sosai. Gaba ɗaya haka ya uni yana ta ƙarawa kansa ƙwarin gwuiwa domin yasan Amera bata da matsla. Haka ya tashi a gurin aiki ya nufi gida yana jin Gara tun yanzu Amera ta san halin da ake ciki, kuma zai fara nunawa Haura ɗin cewar yana sonta domin ta san da abun, idan ma akwai wanda ta fara so sai ta tsayar da shi.

Da sallama ya shiga gidan lokacin Salim da Salma da Haura ne a palon suna kallo. Salam ce ta fara amsawa ta nufi gurinsa da gudu, Salim ma yabi bayansa, Haura kuma ta mike tsaye tana masa maraba da zuwa. Adam ya amsa yana kallon yadda duk kalar doguwar rigar da ta saka sai tayi mata kyau. Ya ce "Happy juma'at Mubarak" ya faɗa yana kallon ta. Ta ce "Daddy yau baka dawo ka tafi da Salim masallaci ba?" Adam ya ce "Na manta yau ba anan nayi Sallah ba ne. Yana faɗa ya na shigowa cikin palon. Saida ya zauna kusa da ita abun da bai saba yi ba kafin ta ce "Daddy sannu da dawowa ya aiki?" Ta faɗa kamar kullum idan ya dawo, kaman yadda Amera yake yi, kuma suma yaran suke yi. Kafin ya amsa sai ga Amera ta fito daga daki itama sanye da doguwar riga ta atamfa mai adon ƙananan duwatsu a ƙirjin rigar. Sosai Amera ta iya ɗwukar wanka wanda shibkansa ya shida hakan. Ta yi masa kallo ɗaya ganin gurin da ya zauna, sai ta kawar da kai ta ce "Yau da wuri haka ka dawo ne haka honey?" Ya ce "Eh mun tashi da wuri shine nace tunda ban dawo gida ɗaxu ba kawai bari nazo sai a sha hira" ta zauna nesa dasu ta na sake masa sannu da aiki. Adam ya amsa yana satar kallon Amera da yaji yanayin muryarta kamar ta sauya. Haura ta mike tsaye zata bar palon Amera ta tsayar da ita. Ta sake haɗe rai sosai domin ranta ya ɓaci. Ta ce "Honey nayi magana da yarinyar nan akan wanda yake zuwa gurinta, kuma ta tabbatar min da cewar suna san juna shine na ce mata ta ce masa ranar Sunday yazo kana son ganinsa domin aji idan da gaske yake a tsayar da lokaci. Ta ƙarasa tana tuno maganar da sukayi da Nana ƙanwarta ranar da tazo.

Nana ta ce "Anty Mera a duk lokacin da na shigo gidan nan naki naga wannan yarinyar wallahi sai gabana ya faɗi, idan na tuno da cewar arniyar daji ce kuma ba musulma ba, sannan idan na tuna da cewar a baya adam ya kusa ya aureta, sai nake tsoron kar fa watarana yazo miki da maganar zai aureta, tunda kinsan halin sa da son taimako, ko a baya ma abin da ya faru kenan daga taimako, kuma kinga yanzu ta ƙara girma ta zama budurwa ko ina ya ciko masha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login