Showing 27001 words to 30000 words out of 58144 words
a Whatsapp amma bata ma ga karshen hawansa ba. Ta sake kiransa baya shiga. Izuwa lokacin ta fara damuwa, sai taje jin ko dai ta tambayi Bebb ne ko ba lafiya ba. Domin haka tayi seving number Nadiya da Bebb saboda haka Habib yayi a wayarsa. Tashi ta yi ta fito waje, ta samu yaran suna wasa abun su, ta shiga kichin ta samu Amera na girki har ma ta kusa gamawa. Ta ce "Anty sannu da aiki?" Amera ta amsa ta na murmushi. Haka ta kama mata aikin suna ta hira har suka gama. Izuwa lokacin ɗaya da wani abu, hakan yasa Amera ta ce taje ta shirya tunda ta mata ƙaryar cewar wai karfe huɗu ne zai zo. Amera ta shigo ɗakin sai ta rasa ma to wani kaya zata saka. Sai da tayi wanka kafin ta fara fiddo da kayan da zata saka. Ta na cikin haka kira ya shigo wayarta. Da sauri ta ɗaga tana karawa a kunne. Nadiya ta ce "Ina ta jiranki na nuna miki wani abu" haura ta ce "Da gaske?" Ta ce "Buɗe Whatsapp ki gani" Nan take ta buɗe suka haɗa video call. Abinci ne tayi take nuna mata shi kasancewar sunyi maganar abincin ɗazu da haura ɗin take cewar tana son ta gwada irinsa. Sosai abincin yayi mata kyau a fuska, ta shiga santi tun ma kafin ta ci. Haura ta ce "Zaki koya min yadda ake yi fa Anty, domin ina so na gwada a gida?" Nadiya ta ce "Duk lokacin da kika kawo min ziyara zan koya miki. Haura ta ce "Da gaske kike?" Ta amsa da cewar da gaske. Suna wayar Haura na ta leƙa ko zata hango shi ta cikin wayar amma ko motsi ma bata ji. Sai ta ce "Anty yanzu wannan ke ɗaya zaki ci ko tare da shi zakuci?" Nadiya ta yi dariya ta ce "Ni da yaron cikina ne, baki san masu ciki suna da cin abinci ba, ko baki ga haka a lokacin cikin Amera masifaffiya bane?" Ta faɗa ta na dariya. Haura ta ce "Antyna ɗin ce masifaffiya ko, ai da na, yanzu ta na da kirki sosai" Nadiya ta tsayar da dariyar ta ce "Na sani wasa nake miki, ki gaida min da ita kice Nadiya tana gaishe ta, bata jira komai ba ta kashi kiran. Haura ta yi shiru tana tunanin mai yasa bata so su dinga magana akan mijinta, ko dai ta santa ne.
Har ƙarfe biyu number Sir bata shiga, har zuwa uku, haka dai ta ci uban kwalliya na doguwar riga jikinta a mace musamman ma lokacin da Adam ya dawo daga masallaci ya sake tambayar ta. yadda suka yi. Har huɗu da rabi babu Sir babu wayarsa. Har karfe biyar babu labarin sa, izuwa lokacin Najib yazo gidan dalilin kiransa da Adam yayi. Domin shi Adam har ya shirya yadda zai masa idan ya zo, zai ce masa an mata miji ne, dan Allah karya ƙara zuwa, kuma karya ƙara kiranta a waya. Karfe biyar da rabi Adam ya zo palon ya sameta a zaune ta sunkuyar da kai. Ya ce "Haura bai zo ba ko?" Ya tambaya cikin tausasa murya. Ai kuwa ta na ɗago kai sai ga hawaye. Lokaci ɗaya ta fashe da kuka. Adam ya tsaya yana kallonta. Kuka takeyi sosai domin abun yayi mata zafi, yaya za'ayi ya ce zai zo amma yayi mata haka, ko ba komai ko saboda abun da ya faru jiya ai ya dace yazo saboda ya faranta mata. Adam ya ce "Haura wannan mutumin ba sonki yake yi ba, muna fuki ne, yaudarar ki kawai dama ya ke yi, ina so ki fita daga sabgarshi kinji?" Ya faɗa ya na kallonta. Da sauri ta tsayar da kukan na ta ta ɗago itama ta na kallon sa. Sai ta fara girgiza masa kai, ta kasa magana domin bata ma san mai zata ce ba. Ta na son ta ce masa ba zata iya daina son sa ba, kuma ta fada masa cewar Sir yana sonta, domin shi da kansa yayi mata alƙawarin yana tare da ita har abada kafin ta bashi kanta. Amma tana buɗe baki sai kuka. A haka Amera ta fito ta same su. Adam ya ce "Idan da dagask ne yana sonki da yazo anyi magana Haura" tun kafin ya sauke numfashi Amera ta ce "Kaman yaya baya sonta, ka bar yarinya da abun da yake damunta mana, shi ya faɗa maka cewar baya sonta, kasan wani irin uzuri ne ya tsayar da shi bai zo ba, yanzu haka ma yana kan hanya ko kuma sherin ƙarfe ne. Ta na zama haura ta tashi ta bar gurin domin taji haushin maganar Daddy. Ta na shiga ɗaki ta sake fashewa da kuka, kuma tana sake kiran number sa. Wasa-wasa har sallar magriba babu Sir kuma har lokacin number sa bata shiga. Izuwa lokacin tayi kuka har ta gaji, haka kuma ta kira number sa har bata san adadi ba. Kasancewar gobe class ɗin ta na safe ne yasa ta bari akan zasu haɗu a school Allah yasa lafiya. A daren ma sai da sukayi chatting da Nadiya, kusan na minti talatin kafin ta kashe wayar ta kwanta. Washegari haka ta tashi babu daɗi, tayi mafarkin wai yazo sunyi magana da Daddy har an saka musu rana. Haka take yin komai sukuku babu kuzari, bata iya cin komai ba sai ruwan zafi, ta riga kowa fita a gidan. Ta na shiga class ta zauna ta dafe kai tana tunani a gurin da take zama. Haka suka gama karatu bata ganshi ba. Amma bata koma gida ba har Maryam tazo da yake ita na yamma ne nata, haka ta jiranta har aka tashi. Har ofishin sa taje ta gan shi a rufe, hakan yasa hankalinta ya tashi. Haka ta dawo gida kamar mara lafiya, sai ta kasa natsuwa, idan ta kira number bata tafiya har lokacin, gashi ta kasa fadawa kowa halin da take ciki. Ranta zafi yake mata na rashin ganinsa da ji daga garesa, har wani abu take ji mai yaji a zuciyarta. Washegari ma haka taje school tun safe har yamma babu shi babu labirinsa, sannan ofis ɗin nasa a rufe hau yau ɗin ma. Izuwa lokacin ta fara saduda, to me ke faruwa, kuma idan suna waya da Nadiya sai ta kasa mata maganar sa, kuma ko sunyi vedio call bata jin motsin sa. Abun da ta lura kaman Nadiya irin matan nanne da basa wasa da mazajensu a gurin mata, domin bata taɓa yarda ta sako mata zancen sa, wasu lokutan ma idan haura ta nuna tana son ganin hoton mijin nata sai ta share da wani zancen. Duk wata dabara da take tunanin tana da ita akan ta samu labarin sa tayi amma shiru. Bata sake shiga tashin hankali ba sai a rana ta huɗu da tazo school ta ga wani sabon malami a gurbin sa, kuma a cikin ofis ɗin sa, kuma gashi kowa na maganar wai Malam Habib ne ya bar school ɗin aka kawo wannan. Sosai students kowa ke murna banda ita da hankalinta yayi mugun tashi. A ranar bata zauna a school ba haka ta koma gida ta sha kuka harda rashin lafiya. Ta kasa fahimtar kenan saboda ita ya bar school ɗin ko dai me, to ma mai yake nufi. Tuni ta gane cewar blocking dinta ya yi, domin yanzu ta daina ma gwada kiransa. Ta rame sosai wanda kallo ɗaya zakayi mata ka gane hakan. Babu yadda Amera batayi da ita ba amma ta ƙi sanar da ita halin da take ciki. Bangaren Adam kuwa yaji daɗin rashin zuwan yaron, kuma idan ya kula har yanzu bai sake mata maganar ba. Yana so ya shiga da maganar sa yadda zata manta da wancan ɗin sai dai ganin halin da take ciki yasa ya ɗan sarara.
Sosai wata dabara ta fado mata, ranar Alhamis wato gobe bata da aji gaba ɗaya, kuma ta na son ganin sa, domin ji take kamar idan bata gansa ba zata iya yin hauka, hakan yasa ta shiga bugar cikin Nadiya. Ta ce "Gobe muna da biki a unguwar ku?" Kasancewar ta faɗa mata unguwar, kuma bata taɓa zuwa ba, amma babu nisa sosai da tasu unguwar. Nadiya ta ce "Ke dan Allah, ashe dai zaki zo min kenan ko?" Haura taji Kamar ta ce eh lokaci ɗaya amma ta ce "Ai ba lallai Antyna ta barni ba, saboda tare zamu zo". Nadiya ta ce "A haba dai, sai kace wata yarinya ƙarama" Haura ta ce "To ai yarinyar ce, ni da ko fita ba'a barina nayi" Nadiya ta ce "To ni idan kun zo sai ki haɗa ni da ita nayi mata magana, ina dai Amera ce ko?" Haura tayi dariya ta ce "Itace amma fa babu ruwana idan ta balbale ki". Sukayi dariya suka ɗora da wani hiran.
Haura ta sauke wani ajiyar zuciya lokacin da suka gama wayar. Ta ke wani farinciki ya cika mata zuciya harda murmushin son ganinsa. Ta na zuwa gida ta tarar Amera bata nan, babu kowa a gidan domin ta tafi da yaran. Kichin ta shiga ta fara musu girki, ta na cikin yi ne taji tsayuwar motar Adam. Cen kuma ta ji sun shigo gidan gaba ɗaya harda yaran. Jin haka yasa ta fito falo tana musu maraba da dawowa. Salim da Salma suka zo da gudu suna ɗaneta. Adam ya amsa ya na mata sannu da gida. A ranar su kansu sun lura da sauyin da ta samu, yau tana ta fara'a har dare. Ai kuwa washegari tun safe ta kira Nadiya ta ce suna hanya. Karfe goma na safe tace mata suna gidan bikin amma ita sai karfe biyu zata zo. A lokacin ne kuma take shirin fita daga gida, ta saka jar abaya ta shafa janbaki ta yafa mayafin a kanta kaman yadda ta saba. Haka ta bar gidan izuwa unguwar su Nadiya ta na hanya ta kiranta akan cewar ta turo mata da number gidan domin gata a hanyar gidan ita ɗaya. Nan take kuwa ta tura mata. Cikin lokaci kaɗan kuwa mai kekenapep ya kawota har ƙofar gidan bayan ta bashi wayar ya duba address ɗin. Bayan ta sauƙa ta bashi kudinsa sannan ta nufi cikin gidan kanta tsaye, zuciya da gangar jikinta na azalzalar ta...📝
S Reza...
[09/07 à 14:07] S Reza: A BAR WA RAI!❣️
S-Reza
Chapter 12
Ta na shiga da motarsa ta fara cin karo a ɗan madaidaicin harabar gidan wanda ya yi mata kyau gashi ɗan ƙarami amma a wadace. Sai da ta tsaya ta ƙarewa motar kallo sosai ta na jin yadda ta yi kewar motar har cikin zuciyarta, jakarta ta buɗe ta fiddo da abun rubutu ta fara za na abun da take son zanawa sannan ta wuce ta na jin wani irin farinciki na ratsa ta, har wani lallausan murmushi take saki ita ɗaya. Tabbas ta tabbatar nan gidan Sir ne domin irin wannan daɗin da farincikin dole sai a gurin da ya dangance shi. Number Nadiya ta kira ta ce mata gata a ƙofar palon ta zo ta buɗe mata. Minti biyu da yin wayar sai ga Nadiya ta buɗe ƙofar. Ido biyu suka yi, yayin da bakin Nadiya har kunne tsaɓar farinciki da murnar ganinta, ta ware hannunta alamar tazo ta rungumeta. Haura kuwa lokacin da ta haɗa ido da ita sai gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, haka kawai taji zuciyarta ta harba da ƙarfi, wani mugun abu taji a zuciyarta mai wahalar fasaltawa, musamman ma ganin wannan cikin na jikinta. Sai take jin kamar itace ta tare mata hanyar da zata bi domin cikar burinta, sosai zuciyarta ke bada wani irin sautin fat-fat da sauri da sauri kamar zata fito daga ƙirjinta. Batayi tunanin zata iya jin hakan a tare da Nadiya ba, ko dama saboda basu taɓa haɗuwa bane yasa taji tana sonta, kenan dama kawai tana sonta saboda bata ganta a gidan Sir ba. Haka Nadiya ta ƙaraso da ita cikin palon ta zaunar da ita tana cigaba da mata maraba har lokacin shinfiɗar fuskar nan tana shinfiɗe da annuri. Dole ta kawar da kai ta shiga amsawa ta na murmushin da iya karsa fatar baki. Kafin ka ce wani abu sai ga shi ta fara cika mata gaba da abubuwan sha da ci wanda tayi musamman domin ita, sai janta da hira takeyi. Ta ce "Ina so na shiga toilet Please?" Haura ta faɗa a hankali, domin har ta gaji da hirar da take mata, ina wallahi ba zata iya ba, Gara kawai tayi abun da ya kawota, tana jin tsaf zata iya mutuwa idan ta cigaba da sauraron ta. Nadiya ta nuna mata toilet ɗin dake palon. Ai kuwa ta tashi da sauri ta shiga.
*°Habib*
Sosai barin aikin da yayi ya fara damunsa musamman lokacin da yaje gida ya faɗawa Mama. Bayan ganin askin da yayi ne yasa take tanbayarsa lafiya dai yake ko, ya amsa mata da cewar lafiyarsa lau. Saida suka gama gaisawa kafin ya shigar mata da maganar dukda cewar ya ɓoye mata asalin abun da ya faru. Sosai Mama ta fara Salati ta na kama baki, sai kuma ta fara tambayar sa mai yayi musu da zasu koreshi, amma haka yace mata babu komai kawai shari ne na wasu mutanen. Haka ya bar gidan bayan ta masa faɗa sosai sannan ta ke tambayar sa wani aiki zaiyi yanzu ya ce zai sake neman aikin koyarwar ne, nan ta masa fatan alkairi ya bar gidan, har tana cewa idan za'a iya zuwa a basu hakuri to ya fadawa Nadiya sai ta samu mai makarantar domin ta inda aka hau tanan ake sauka. Amma yace mata ko anje ba zasu hakura na. Daga nan gida ya koma domin fuskantar Nadiya, tun a hanya yake tafiya yana tunanin mai ma yasa bai tsaya ya yi dogon nazari ba kafin ya ajiye aikin, ai ko tana school ɗin zai iya koyarwa, kawai zai ɗwuke kai da ita ne ya dinga korar ta ko ya kaita ƙara gurin shugaban makarantar wataƙilla ma a koreta, kuma gashi ma wannan shekarar ita zata fita daga school ɗin gaba ɗaya. Take nadama da tausayin kasa ya cika shi, yanzu a ina zai samu aiki yadda aiki yake da wahalar samu a Nigeria. Haka ya dawo gida duk ransa babu daɗi, sai tsinewa abun da ya haɗa shi da Haura ya ke yi, ta cuceshi ba zai yafe mata ba ta bata masa rayuwa. Yana shiga gida ya samu Nadiya na waya, bai ce mata komai ba ya wuce ta ya shiga daki. Da sauri ta kashe wayar tabi bayansa da sauri. Ta na shiga ta samu ya bata baya, hakan yasa ta karewa askinsa kallo, ita a ranta yayi mata kyau dama haka zai koma yin askinsa ma da taji daɗi, tun lokacin da yayi askin ita kadai ce tace yayi kyau, kuma ko lokacin da ta faɗa kawai ya jita ne, amma yasan dalilinta na faɗin haka, amma in ba haka ba, tana ganin yadda ya koma kamar wani soloɓiyo amma tace yayi kyau, tabbas yin aski mamalo yana ragewa mutum kwarjini da cika ido. Kamar daga sama taji muryarsa ya na faɗin "Bebb an koreni a gurin aiki" ya faɗa ba tare da ya juyo ba.
Yau Litinin ne, kuma tun safe bata ga alamar zai tafi aiki ba, domin tunda suka karya yake gida, bai fita ba sai kusan goma, kuma da zai fita ya faɗa mata cewar gidan Mama zaije, idan bata manta ba duk ranar da bashi da school yana faɗa mata domin su zauna a gida suyi hira harda game da daidai abubuwan da zasu ɗebe musu kewa. To amma yau bai faɗa mata cewar yana da class ko babu ba, bata kawo komai ba, ta bari akan ko sai yamma zai shiga school. Ko yanzu ta zo ne da nufin tanbayarsa sai gashi ya na sanar da ita da kansa. Kuma ko kafin ta sake cewa komai ya ɗora da faɗin "Dama kwanakin baya na faɗa miki cewar ana so a ƙulla min gadar zare ne, kuma sun yi nasara, amma Allah yasa hakan shine mafi alkairi, na yarda da kaddara a duk yadda tazo min" ya karasa ya na karasa cire dogon wandon jikinsa ya ɗauko wani gajere ya saka. Nadiya ta tsaya ta na ta kallonsa, da yake ya santa da dogon tunani gata mai amfani da ilimi, ko daga maganar Nadiya kawai zaka san tana da hankalin magana, ya sani zata iya karya masa zuciya da tambayoyin ta masu gama da tuhuma. Hakan yasa ya buɗe baki zai yi magana amma ta riga shi ta ce "Bebb ban gane kora ba, kora fa gaba ɗaya kenan kabar school ɗin ko yaya?" Ta faɗa ta na jin wani irin tashin hankali mai lasisi na tirar mata, aikin da shine rufin asirinsu, aikin da kafin a samu sun sha wahala, aikin da sanadiyar sa ne rayuwarsu ta sauya, aikin da saboda shi ne yasa yanzu suka fi ƙarfin komai na rayuwa, aikin da bata mantawa ita kanta sai da ta sha wahala kafin sabuwar sa. Ya ce "Eh Bebb kora gaba ɗaya" ya faɗa shima yana tuno irin rayuwar da suka yi a baya. Kamar daga sama yaji ta watso masa tambayar da bai zata zatayi masa ba, kuma ta ɗora da cin albashin da yasan Wallhi sai tayi domin yasan ba zata ɗauki lamarin da wasa ba, itama ta sha wahala Kafin ya samu wannan aikin. Ta ce "Wai ma wani laifi ne ake tuhumar ka da shi ne?" Ta tambaya ta na kallonsa. Lokaci ɗaya ya rikice. Ta ɗora da faɗin "Gobe zan je school ɗin kuma in sha Allahu komai zai warware karka damu, gaskiya zata fito muddin shirri ne aka yi maka to za'a gano gaskiya". Ta ƙasa da tabbacin da shi kansa ya san zata je ɗin. Ya sani zata je ɗin, kuma da sharri ne aka yi masa zata iya wanke shi saboda ta