Showing 39001 words to 42000 words out of 58144 words

Chapter 14 - A Bar Wa Rai Complete Books By S Reza.txt

S Reza   

12 Mar 2026

27

ya dafa ta ya lallashinta zata ji duk wannan ciwon ya tafi. Ita yanzu abun na da ya ƙara bata tsoro shi ne, ya faɗa mata ne ko dai yaya. Ta buɗe baki a hankali ta ce "Anty dan Allah kiyi hakuri ba laifina ba ne, kuma..." Da sauri Habib ya daga mata tsawar da sai da ta tsayar da sauran maganar bakinta. Ya turo kai ya fito daga cikin palon ya ɗauketa da mari mai karfi wanda sai da ta kifa a gurin. Ita kanta Nadiya ta tsorata da ganin irin wannan marin da ko Namiji a kaiwa dole ya san ammaresa bare kuma mace, macen ma wannan yarinyar, sannan yanayin ta ya nuna kamar bata da lafiya, take taji wani iri a ranta, lokaci ɗaya cikinta ya murɗa mata da karfi. Habib bai tsaya anan ba ya ɗakota ya shiga zare mata ido ya na faɗa mata maganganun da sam bata jin mai yake cewa. Batayi tunanin zai iya marinta a irin halin da take ciki ba, ko dai bai kula da yanayinta ba be, shi yasa marin yayi mugun shigarta da kyau. Jikinta ne gaba ɗaya ya ɗauki zafin marin wanda lokaci ɗaya ciwon nata ya sake tashi. Ta na jin lokacin da ya ɗagota, amma bata san mai yake cewa, jinta da sauraronta ne yayi ɓatan dabo na wasu yan daƙiƙu. Ji tayi ya sake ta sai kuwa gata a ƙasa shafar kamar kayan wanki, hakan yasa ta faɗi ta gefe kanta ya fashe jini ya fara zuba. Nadiya na ganin haka ta koma ciki tana riƙe cikinta ta ya sake murɗa mata, sai kawai ta fashe da kuka mai ƙarfi tana dafe cikin nata. Habib ganin ta zube ne yasa ransa ya ƙara ɓaci. Sai kawai ya kama hannunta da hannu ɗaya, ya riƙe a kwatin kayanta da hannu ɗaya ya fara janta. Sai da ya kaita har ƙofar gidan nasa kafin ya watsar da ita a gurin. Kasancewar dare ne yasa ya zagayo ta kanta ya sake mata gargadi da kuma faɗa mata wallahi idan ta ƙara dawowa gidan sa sai ya ɓatar da ita. Ya na gamawa ya rufe get ɗin gidan ya koma ciki ya samu Nadiya na ta murƙususun ciwon mara.

Tun lokacin da ya fara janta a ƙasa ta dawo zahirinta amma ta kasa magana, sosai ko ina na jikinta ke mata ciwo. Koda ya jefar da ita duk tana jin abun da yake faɗa, har ya koma ciki ya rufo get ɗin. Ta kai minti biyar a haka kafin ta iya tashi zaune ta na kallon ƙofar gidan. Wani irin sanyi ne ya fara ratsata, ga kuma gefen kanta hagu da dama da ta bugu amma ɗaya bai fashe ba, gurin dai yana mata zafi sosai, dayan gurin kuma jini na fita kaɗan-kaɗan. So take ta tashi amma ta kasa, hakan yasa kawai ta fashe da kukan da babu sauti domin shi kansa kukan babu ƙarfin yin sa. Kaiwa sunan Aminta take kira a cikin kukan ta na cewa tazo ta taimaketa zata mutu tazo ta tafi da ita. Tayi kuka sosai kafin kuma tayi wani abu da hannu yadda take yi a baya kafin a ƙwace mata tsafin ta. Sai dai duk yadda tayi abun yaƙi yin aiki, haka ta dinga gwada abubuwan da ta iya amma kowanne baya aiki, dama tunda aka rabata da komai bata taɓa gwada yin wani na tsafi ba sai yanzu da take cikin wannan masifar kuma wai akan son wani. Lokaci ɗaya ta tuno lokacin da Sarkin garin Garuk yake tabbatar mata da cewar muddin zata zauna anan kuma zata amshi addinin musulunci to dole sai an karya mata duk wani asiri da tsafin da yake jikinta, kuma a lokacin batayi tunani sau biyu ba tace ta yarda. Kuma take aka karya komai da komai ciki kuwa harda rage wa nesa kusa da suke yi, da kuma warkar da ciwo nan take harda tsayar da jini da dai duk wani abu da ya shafi tsafi da suke yi. Sosai take kuka tana jin ta kamar wata mara gata ƙaskantatciya a cikin mutane, mara galibu. Sai kawai ta sake kwantawa a gurin ta na addu'ar ina ma ta mutu kawai anan sai taje ta haɗu da Aminta. Cikin kukan nata ta tuno da daddynta da kuma anty Amera. Idan ta tuna da maganar Daddy na cewar zai aureta sai ta ji cewar ba zata iya ba, ai gara ma ta mutu batayi aure ba akan ta auri Daddy, ita Sir take so, kuma har yanzu bata ji ko sau ɗaya son da take masa ya ragu, idan akansa ne sai dai ya kashe ta, amma tabbas sai ta rayu da shi kuma dole ya cika mata alƙawarin da ya ɗaukar mata. Ta kai minti ashirin a gurin kafin ta iya miƙewa tsaye kamar ƴar maye, ta buɗe akwatin kayan nata ta ciro wani ɗankwali ta ɗaure gurin ciwon nata, sannan ta ciro wayarta da wata ƙaranar jaka. Ta zuba kuɗin ciki a jakar sannan ta ɗauki wata rigar sanyi ta saka. Ta na ganawa ta kalli gidan Habib na tsawon minti ɗaya kafin ta fara barin gurin a hankali cike da karfin hali. Ta na tafiya ta na rawar ɗari har ta bar unguwar. Bata iso bakin titi ba sai kusan sha biyu na dare. Anan ta tsaya a bakin titi duk motar da ta gani sai ta tare amma babu wanda ya tsaya. Har ta hakura sai ga wata farar mota kamar ma sabuwa. Tana ɗaga mata hannu ta tsaya. Ta ƙarasa gurin mai motar ta ce masa Katsina zata je. Ya kalleta sama da ƙasa kafin ya ce "Nima cen zanje, amma zan kwana a hotel zuwa biyar na safe zan tafi, zaki iya jira na?" Ya faɗa yana kallon yanayinta, ba dan ya na son kuɗi ba shi ina ma zai tsaya neman fasinja. Ta ce "Dan Allah kayi hakuri kawai mutafi zan biya ka ko nawa kake so". Ya ce "Hanyar ce ina tsoron bi kuma motar ba tawa bace" ta ce dan Allah ka taimaka min bani da lafiya ne Please" ta faɗa da ƙyar, wanda mutumin shi kansa ya lura da bata da lafiya ne. mutumin ya ɗan yi jim sai ya ce "Zaki biya dubu sha biyar?" Haura ta ce "Zan baka dubu ashirin". Ai da sauri ya buɗe mata gidan baya ta shiga. Suna fara tafiya ta ce "Please kafin mufita anan ka sama min maganin zazzaɓi da abinci da ruwa kaji?" Ta faɗa har lokacin rawar sanyi ta ke yi, ga yunwa da take ji. Mutumin ya ce "ina kuɗin?" Kafin ma ya rufe baki ta miƙo masa dubu biyar. Ya amsa suka ci-gaba da tafiya. Saida suka iso wani guri kafin ya tsaya ya saya mata komai da tace ya kawo mata, ai kuwa take ta ɗan ci abincin kaɗan, ta sha maganin ta kwanta ba tare da ta ce masa komai ba ta na jin har lokacin sanyin na ratsa ta, haƙwaranta sai haɗuwa sukeyi. Mutumin dai yana tuƙi ya na juyowa ya na kallonta, har ga Allah ta fara bashi tsoro, gashi har yanzu bai ga asalin fuskantar ba, gashin kanta ya rufe mata fuska, sannan ga rigar jikinta itama mai gashi ce. Haura kuwa kasa ma yin barcin tayi sai tunanin yadda yan garinsu zasu tarɓeta take yi, inama Aminta na raye, ina ma Ɓultuwa na raye, inama babanta na raye, yanzu idan ma taje garin sai dai taje gidan dangin babanta, ko na mamanta, sosai take tariro komai na garin da al'ummar cikin garin. Wata zuciyar na cewa kar taje wata zuciyar na cewa ta haka ne kawai zata iya mallakar Sir dinta, dole ta cikawa ranta burinsa na samar masa da abun da yafi so koda kuwa zata rasa ran nata. Idan ta tuno da abubuwan da suka faru sai ta ƙara jin ƙwarin gwuiwa na zuwa musamman yadda yake nuna mata cewar ya tsaneta, bayan kuma ya lalata mata rayuwa. Amma idan ta tuno da rayuwar ƙazanta da dabbanci da rashin ƴanci da kuma jahilci da suke yi a garin Garuk sai taga anya kuwa zata iya zama a garin. Hatta cimarsu ma ba irin wannan ba, hatta shigar da sukeyi. Haka take ta tunanin har suka iso cikin garin Katsina, izuwa lokacin ta fara yin zuffa alamun zazzaɓi ya fara sauƙa. Koda ta duba a gogo wayarta ƙarfe biyu da minti uku. Har lokacin gurin da ta bugu yana mata ciwo, kuma bata jin karfin jikinta kwata-kwata. Mai motar ya ce "Munyi sauri ko?" Ya faɗa yana kallon fuskarta a karon farko. Ta ce "Nan Katsina ne?" Ya ce "Eh kin ga an samu cigaba ko? Hanyar ta zama kamar a Abuja ko? Da alamu kin kwana biyu baki zo ba ko?" Ya shiga jera mata tambayoyi duk saboda ya samu alkairi. Haura ta ce "Ga kuɗin ka" ta miƙa masa dubu ashirin ɗin sa. Ya ce "Ina zaki je a daren nan?" Ya faɗa ganin ta bi hanya ta fara tafiya. Bata tanka masa ba, ta cigaba da tafiya. Bata manta komai ba, kuma ba zata iya kasa gane hanyar garinsu ba, domin a ƙwaƙwalwarta komai yake. Haka ta nusa cikin dajin nan ta fara tafiya, baka jin motsin komai sai kukan tsuntsaye, tafiya kawai take yi tana tunanin rayuwar da tayi a garin kafin su fita gaba ɗaya ita da Aminta. Ganin kaman bata sauri ne yasa ta fara haɗawa da gudu. Har karfe huɗu tana cikin dajin, ji take kamar ma acikin dajin take, duk da ciwon da jikinta ke mata bai hana ta zage ba, tana haska ko ina da wayarta. Lokacin da ta fara cin karo da tarko irin nasu, kuma ta hango wani ƙaton dutsen dake kusa da garin nasu, sai wani daɗi da sanyin daɗin ya fara Ratsa ta, take ta naimi wannan gajiyar ta rasa. Bata ƙara jin dad'i ba sai da ta ganta a kan wannan dutsen kuma tana hango cikin garin Garuk. Batayi mamaki ba ganin garin yana nan yadda ta sanshi, sai ma wasu tsare-tsaren da suka yi na hana baƙuwar fuska shiga garin nasu. Ta na cikin tafiya taji an shaƙe mata wuya ana mata magana da yaren garin nasu. Kafin ka ce me an zageta wasu mazaje su biyar. Sun saitata da kifiyoyi. Sai da yayi mata ƙamshin mutuwa kafin ya sakar mata maƙogaro. Nan take ta shiga tari tana kakarin amai domin ta shaƙu. Ta ɗauki minti ɗaya tana tari kafin cikin yaren masu ta ce "Meye haka Haura ce fa, baku gane ni ba ne?" Ta faɗa ta na zare musu ido, domin duk babu wanda bata gane ba a cikin samarin, a lokacin da take garin duk ta take su gagara da iya tsafi. Lokaci ɗaya suka kalli juna. Wanda ya shaƙeta ɗin ya ce "Haura tiii attt chuhhh azzt kit ataaau butullitu (Wato Haura dama kina raye baki mutu ba?) ya na faɗa suka kurma wani uban ihu suka yi sama da ita suna kiran sunanta suka yi cikin gari da ita, duk inda suka wuce sai an bar abun da ake yi an biyo bayansu, dukda dare ne amma ga al'umma kamar safiya, ba'a ajiye Haura a ko'ina ba sai gaban sarkin garin Garuk.

°*Adam*
Wasa-wasa har kwana uku babu Haura babu Amera babu kowa a gidan nasa, yaje har gidan su Maryam akan ta kaishi gidan su saurayin Haura din amma ta ce masa bata sani ba, ya ce To a ina suke haɗuwa ta ce masa makaranta dai ta sanshi. Haka ya je makarantar aka ce masa ai ya daɗe da barin aiki anan. Ya ce To dan Allah a bashi address ɗin sa, amma aka hana shi akan basa yin haka. Gaba ɗaya Adam ya zama wani kala kamar mara lafiya, bai taɓa tabbatar da cewar yana son Haura har haka ba sai yanzu. Ji yake ina ma bai faɗa mata ba, sai dai kawai yaje a ɗaura, shi san bai ma damu da rashin dawowar Amera ba domin shi dai ya sa a ransa cewar ai ba shi ne ya koreta ba. Bangaren Amera kuwa babu yadda Abba da Umma ba suyi da ita ba amma ta ce ba zata koma ba har sai yazo da kansa ya ce ta koma kuma ya fasa maganar auran Haura da yake da niyya, hakan yasa Abba ɗin ya shiga buɗe mata wuta saboda shi yafi ganin laifinta, ai shi Adam ɗin ba shi ya ce ta tafi gida ba da zata ce sai yazo zata koma. Ya ce "To idan kin mata waye Adam bari na tuna miki, lokacin da kike da cikin yaran nan wani irin iya shege ne bakiyi masa ba, kin zagi uwarsa, kin zagi ubansa, kuma duk suna kabari kwance, amma yaron nan bai taɓa koroki gida da nufin yaji ba bare aje ga yin saki. Haka kika fasawa ƙanwarsa kai dan kawai tazo gidan ki. Sannan shi kansa har wuƙa kin chaka masa, kin sa shi asara marasa lissafuwa duk wai saboda kin yi ciki, ita kanta wannan yarinyar da yace zai aura har kika dawo gida ke ce silar mutuwar uwatar, haka ya sha samo miki masu aiki duk kina dukansu kina kora, daga karshe ma shi da kansa ya bar miki gidan saboda kawai baya son ya ce ke kitafi, saboda yana sonki, to ke idan kina da mutunci da tunani dan ya ce zai auri wannan yarinyar ke ba mai goya masa baya bane, gashi yarinyar ma da kin san halinta kin san abun da zata iya, kuma gata babu ruwanta, yarinya ma mara son hayaniya. Abba na ajiye wa Umma ta ɗora da nata. Ta ce "A lokacin ma babu irin rigimar da bata haɗa wa Nana da Nasiru ba, ta ce wai ba sonta yake yi ba, yanzu gashi tun da a kayi auran Nana bata taɓa dawowa gida ba, ke yanzu ma ba abun kunya ba ne ace kin dawo gida saboda mijinki zai ƙara aure, bayan kowa yasan irin abubuwan da kika yi lokacin da kina da ciki. Umma ta ƙarasa itama tana goyon bayan Abba.

Babu abun da Amera ke yi sai kuka. Sosai komai ke dawo mata, ita kanta ta na mamakin abubuwan da tayi a wannan lokacin, to amma ai an ce ba ita kadai bace lokacin, amma dukda haka Adam yayi ƙoƙari. Hakan yasa ta shirya kayanta ta haɗa kan yaranta ta ci alwashin ita da kanta zata shawo masa kan Haura ya aura ko bata so, domin tunda haka ta faru ko bai auri Haura ba zai auro wata wacce bata san halinta ba, amma Haura fa, kishiya ce Amma bata da maraba da ƙanwa koma ta ce ƴar cikinta, ta sanan Haura ba zata cutar da ita ko yaranta ba, hasali ma yaran sunfi sabawa da ita, tun farko ma mai yasa bata danne zuciyar ta ba, mai yasa bata tumo da abubuwan alkairin Adam a gareta ba, mai yasa bata tsaya ta bashi gudun mawa ba, shi za'a samu irin Adam a duniya kuwa, tabbas bata kyauta ba, kuma ko ba komai itace dai sanadiyyar rasuwar ita mamar haura ɗin, mai yasa ta bari kishi ya mantar da ita komai, lokaci ɗaya ta tuno da cewar marinta fa yayi, sai kuma tayi murmushi tana tuno ita mari nawa tayi masa lokacin. Sai da ta gyara jikinta sosai harda sabon kitso da lalle sannan ta nufi gidan nata...📝

S Reza....
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*

FCWA

                          Chapter 17
Kasancewar yamma ne tayi sa'a baya nan. Haka ta shiga gyara gidan ta na hawaye, ta shiga tuno lokacin da take da ciki da suka je supermarket yin sayayya har faɗa ya haɗa ta da yarinyar soja, karshe Adam ne ya sha dukan. Ta sake tunowa da mai sayar da kwai inyamuri na ƙasan layin su da shima rigama ya haɗa, a ranar idan bata manta ba Adam ya mareta, amma itama ta rama. Bata manta lokacin da tace masa ya tashi ya tafi aiki ƙarfe shida na safe ba. Bata manta lokacin da ta hana shi zuwa gidan Khadijah ƙanwarsa ba, bata manta lokacin da ta biyo shi da wuka har suka fadi ta chaka masa a wuya ba, bata manta lokacin da ta naushi Ammin Haura a haƙarƙari har ta mutu ba. Bata manta lokacin da tsabar masifa da tashin hankalin ta har ya rubuta mata wasika ya bar mata gidan na wasu kwanaki ba, bata manta lokacin da ta kusa illata masa mazantakar sa ba. Ta na cikin wannan tunanin taji ya turo ƙofar palon ya shigo. Kallo ɗaya ta yi masa gabanta ya faɗi ganin kamar yayi shekaru yana jinya, duk ya rame ya koma kamar ba shi ba. Cikin muryar kuka ta ce "Sannu da zuwa honey" ta faɗa kuka na kufce mata.  Adam kuwa yau a gajiye ya dawo daga gurin aiki, izuwa yanzu ya tabbatarwa da zuciyar sa cewa Haura gurin saurayinta ta tafi, kenan dai da gaske bata sonsa. Ransa ya sosu ainun kuma yayi ƙoƙarin ganin ya takaice ta amma zuciyarsa taƙi bashi goyan baya, haka dole ya cigaba da jinyar zuciyarsa akan Allah ya dawo da ita kuma ya tsare masa ita. Haka yayi aikin yau kamar bashi da lafiya, a ransa ya bari dole ne ma ya koma school ɗin nan domin a bashi number Habib, idan ma sun ƙi zai faɗa musu abun dake faruwa, kuma gashi za su fara exam a sabon wata. A lokacin da ya buɗe palon da Salim ya fara cin karo a cen gefe yana danna waya, lokaci ɗaya zuciyarsa tayi wani sanyi ganin yaron. Har ga Allah yana son Haura, kuma da zuciya ɗaya yake sonta, amma baiyi tunanin Amera zata iya zaɓar rabuwa da shi akan hakan ba, shi dai yayi alƙawarin ba zai dawo da ita ba duk abin da take ganin shine daidai kawai tayi. Ya na cikin haka yaji muryarta hade da kuka ta na masa barka da zuwa. Sosai ya tsorata, domin bai kawo cewar zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login