Showing 36001 words to 39000 words out of 58144 words

Chapter 13 - A Bar Wa Rai Complete Books By S Reza.txt

S Reza   

12 Mar 2026

24

inda ta ga dama. Zama yayi apalo sai kuma ta tashi ya nufi dakin haura, nan ma ya ganshi a buɗe itama ga drowan kayan nata nan a buɗe. Nan ya fara kiran sunanta, jin shiru yasa ransa ya ɓaci, kenan dai Amera ce ta ɗauketa suka tafi gida. Ai kuwa yanzu zaije ya dawo da ita Haura ɗin, ita kuma idan taga dama ta shekara a cen. Saida aka yi sallah kafin ya nufin gidan su Amera ɗin, yana zuwa kuwa sai ga Abba zai shiga, suka tsaya suka gaisa. Abba ya ce "Lafiya dai ko Adamu?" Adam ya ce "Lafiya lau, dama nazo ne gurin Amera?" Abba ya ce "Au dama tana ciki ne?" Ya tambaya kasancewar sai yanzu zai shiga gidan. Adam ya ce "Eh suna ciki" Minti biyar ya kwashe a gurin sai gata ta fito. Ta na zuwa "Je ki fito min da ita yanzu nan?" Ya faɗa babu wasa. Amera da ya bata mamaki, ita a tunaninta biko yazo. Ta masa kallo ɗaya ta kawar da kai. Ya sake faɗin "Ba magana nake miki ba ne, idan ke kin dawo gidan ku saboda kin isa, to ita a wani dalili zaki ɗaukota Ku zo tare?" Ya sake faɗa a fusace. Amera da sai yanzu ta fara gane abun da yake nufi, sai kuma ta fara tunanin kenan Haura bata gidan ne ko yaya. Adam ya ce "Amera zan ɓata niki rai fa Wallhi, kije ki kira min Haura mu tafi?" Ya sake faɗa ganin tayi shiru. Ita kuwa ranta ne ke baci idan ya faɗa haka. Ta ce "Kaje ka naimi inda yarinya take, domin ni ban tafi da ita ba...📝

S Reza...
[09/07 à 14:07] S Reza: A BAR WA RAI ❣️


Amera na faɗa ta shige gida ta bar shi tsaya. Adam ya cika da mamaki, to me take nufi, basa tare da Haura ko yaya! Kaman ya shiga cikin gidan da kansa amma ya fasa. Ya na tsaye sai ga wani yaro yazo zai wuce, ya tsayar da shi ya ce "Shiga gidan nan ka ce Adam ya ce wai Haura ta zo" ya faɗa ya na tura yaron. A fili ya ke faɗin "Wallhi duk abun da Amera take nema dani zata samu, ba dai gidansu tazo ba, zata nuna masa cewar ta na da gida ba, ai kuwa zata cigaba da zaman gidan nasu domin dai shi ba zai taɓa zuwa da nufin dawo da ita ba. Ya na tsaye sai ga Salim da Salma sun fito daga cikin gidan da gudu suna kiran sa. Bai ko amsa ba ya ce "Salim je ka kira Anty Aisha mu tafi gida" (Haka yaran duke ce mata ) Kafin ma Salim yayi magana dan aiken nasa ya fito ya ce wai ance babu Haura a gidan. Adam ya ce "Tom na gode tafi abunka. Salim ya ce "Daddy Anty Aisha bata gidan tana gida inji Mommy" Adam ya ce "Mommy da wa suka zo gidan?" Salim ya ce "Ita ɗaya ce, kuma tana ta kuka. Adam yayi jim kaɗan ya ce "Anya kuwa Salim ka tabbatar Anty Aisha bata gidan?" Ya ce "Eh Daddy bata zo ba. Adam ya ce "No shiga ka sake dubawa" Salim ya shiga gidan da gudu, ita kuwa Salma dama tuni ta nufi gurin motar ta buɗe ta shiga. Adam dai na tsaye sai ga Salim rike da jakar makarantar su ya ce "Daddy ba ta nan, kuma Mommy ta ce ka tafi damu gida"  Adam da abun ya fara bashi tsoro ya nufi mota da sauri ya kunna ta, Salim da bai shiga ba ya zagayo zai bude amma Adam ya ce "No ku koma gida gobe zaku dawo da Mommy". Ya na jin zasu fara rigima ya sauƙo da Salma ya ja motar sa ya bar unguwar ransa a haɗe. Koda ya koma gidan bai ganta ba. Haka ya shiga duba ko ina. Karshe ya kira number ta amma a kashe, ya kira number Amera itama tun ta na shiga har ta daina. Ya shiga tura mata sako akan Wallhi duk inda ta kai Haura tazo ta fito da ita. Haka Adam har bayan sallar Isha. Karshe gidan su Maryam kawarta ya je amma nan ma tace yau gaba ɗaya ma basu yi waya ba. Wasa-wasa har karfe goma na dare babu Haura babu dalilinta. Haka ya sake komawa gidan su Amera wannan karan da kansa ya shiga har cikin gidan. Lokacin har Umma tayi barci, Abba dai yana Palo yana kallo, Amera ma tana ɗaki amma batayi barci ba.

Shi kansa Abba yayi mamakin ganin sa. Bayan sun gaisa Abba ya ce "Ko dai matsala kuka samu ne da ita Adamu, ta ce wai kasan da zuwanta amma kuma yanzu naga ka dawo, lafiya dai ko?" Adam ya ce "Amma Abba babu komai, dama ita ɗaya yarinyar ce nazo ɗauka, ba Amera ɗin ba". Abba ya ce "Wacce yarinya, Salma kenan?" Adam ya ce "A'a Abba babbar dai wacce muke ruƙo, tare suka zo nan ɗin". Ya karasa a ɗan rikice. Abba ya ce "Ikon Allah, amma ai ni ban ganta anan ba, daga ita sai yaran na gani, kuma yaran ma ai ba yau suka zoba" Adam ya ce "Ka kira Amera ɗin Abba Allah suna tare" ya faɗa kamar a fusace. Abba da ya cika da mamaki ya ce "To ai yanzu ne sunyi barci, to ka bari zuwa safiya mana ko?" Adam ya ce "Am dama saboda a kwai..." Abba ya ce "To bari na kira ita Amera ɗin. Zama yayi apalon yana jira su fito. Ji yake kamar tana fitowa ya haɗa su duk su biyun ya musu shegen duka. Jin an buɗe labulen palon yasa ya mike tsaye. Kallon-kallon a ka fara yi. Adam ya ce "Shiga ki fito min da ita?" Ya faɗa kansa tsaye. Amera da tun da ya tafi take ta tunanin maganar sa, ita kanta abun ya bata mamaki jin wai bata nan, yanzu haka wani mamakin ne ya sake kamata jin wai har yanzu bai ganta ba, ita dai tasan ta tafi ta bar Haura a gidan, kuma kan kujera ta wuce ta. Ya sake faɗin "Nan shine gidan ku, kina da ikon da zaki zo ki zauna har tsawon lokacin da kike so, amma banda Haura, ita nine uwa da ubanta, zuwa wani lokaci kuma mijinta, dan haka tun kafin ta kaimu izuwa wani mataki ki fito da ita" Amera ta ce "Gara ma da ka dawo, bari na fito maka da yaranka su tafi gidan nasu uban kaman yadda nima na dawo gidan ubana, domin nan ba gidan ubansu bane" ta na faɗa ta Kama Hanyar zata koma. Taku ɗaya yay ya kamota ya ce "Wai Amera me kike nufi da nine, ya ina miki magana kina kawo min wani shirme banza da hofi?" Amera ta ce "Karka sake taɓa ni, nan gidan ubana nane ba gidan ka ba, kuma maganar da kake yi naga bata shafeni bane shi yasa ban saka baki ba, ita Haura ɗin nan gidan ubanta ne da zanzo da ita, ina yanzu kace kaine uwa da ubanta, to ai sai kaje ka nemeta a gidan naka". Ya ce "Me kike nufi?" Ta ce "Abun da kaji shi nake nufi". Ransa ya ƙara ɓaci ya ɗan busar da iska da baki ya ce "Nasan duk inda Haura zata je kece zaki saka ta, dan haka ko bata gidan nan kinsa inda ta tafi, saboda haka ina kika aikata, domin babu inda ta sani?". Har ta buɗe baki zata yi magana Abba da Umma suka shigo palon domin muryoyinsu ne ya tada Umma, shi kuwa Abba tun farkon maganar su yake sauraronsu, yana tsaye Umma ta zo, ganin abun nasu na son ya ɓaci ne yasa suka shiga palon.

Abba ya zaunar dasu ya tambayi Adam abun da ya faru. Nan take ya kwashe komai ya faɗa masa harda maganar auran Haura ɗin da zai yi da kuma ɗaukota da Amera ɗin tayi a cewar sa. Dukda Abba ya cika da mamaki amma ya tambayi Amera abun da ya faru. Itama ta faɗi daidai da abin da ya faɗa amma ta ce ita ko magana ma batayi wa Haura ba lokacin da zata fito. Adam ya ce "Wallhi Abba karya take yi, saboda kishi ne yasa ta boyeta". Amera ta ce "Kishin wa kai, Allah ya tsare ni Wallhi, daga kai har ita baku isheni kallo ba bare nayi kishi". Umma ta daka mata tsawa ta ce "Idan kin san ke ce kika boye masa yarinya ki faɗa masa inda take kafin ranki ya ɓaci?" Umma ta faɗa cike da takaici. Amera ta fashe da kuka ta ce ita Wallhi bata san inda take ba. Shi kansa Adam din izuwa yanzu ya tabbatar da cewar ba ita bace ta boye ta, amma to ina zata je. An daɗe ana abu ɗaya kafin Adam ya hakura zai tafi, Abba ya ce Amera ta tashi ta bishi, Amera ta ce babu inda zata je, shi kansa Adam ya na fita yaja motarsa ya bar unguwar. Ya koma gida ya cigaba da zaman jiran amma har sha biyu, har karfe ɗaya karshe dai dole ya hakura. Washegari ma babu Haura babu labarin ta, izuwa lokacin kam ya tabbatar da a kwai matsala, ko dai gidan saurayin ne ta tafi, tuno da hakan yasa jikinsa yayi sanyi, sai kishi ke danunsa, gaba ɗaya gidan yayi masa wani shiru babu kowa.

*°Habib*
Lokacin da ya koma gida ya samu Nadiya a Palo har ta sake wanka. Ya ce "Wai a ina kika san wannan yarinyar?" Yayi tambayar kaman a fusace. Gaban Nadiya ne ya faɗi a ranta tana jin tsoron ko dai ta masa kyau ne, domin tun da suka fita ta kasa samun natsuwa. Ta ce "Ka kaita gidan ne?" Ta faɗi haka domin taji ko ya ga gidansu. Ya ce "Bani wayarki?" Ya faɗa har yana jan tsaki. Wayar ta miƙa masa ya shiga Whasop, ya ga number Haura a farko an rubuta Aisha. Goge numbar yayi ya ce "Bana son alaƙarki da wannan yarinyar domin ban yarda da ita ba, kuma ba mutuniyar kirki bace". Ta ce "Wai me ya faru ne, duk ka tsorata ni, ka santa ne da har ka gane ba mutuniyar kirki ba ce?" Habib ya ja tsaki wanda yanzu ya zama masa farulla magana ɗaya biyu sai ya yi. Ya ce "Ana ruwa yaci makadi kina ganga ta jiƙe, wani abokina ne ya ganni da ita shine yake faɗa min wai ƴar isa ce, tana bin maza, shima ya taɓa kamata da abokinsa, kuma ta zubar da ciki har sau biyu". Nadiya ta dafe girji ta ce "Ita Aisha ɗin, wannan yarinyar da gaba ɗaya ma nawa take?" Habib ya ce "Haka tace miki sunan ta Aisha? To karya ne sunanta Haura". Nadiya ta ce "Haura kuma? Wani irin suna ne wannan?" Habib yace "Oho dai, idan zaki yi hankali da ita kiyi ni dai na faɗa miki gaskiya bana sonki da ita kwata-kwata". Haka ya shiga ɗaki ya bar Nadiya da tashin hankali, nan take ta goge number Haura tayi blocking din ta a ko ina. Sosai komai ke dawo mata tun farkon alaƙar ta da ita, sai take ganin wata killa ma Habib ɗin ne yayi mata kyau shine ta biyo ta wannan sigar domin ta haɗu da shi. Haka ta uni gaba ɗaya lamarin ya tsaya mata a rai.  Habib kuwa wanka yayi ya sake kaya ya ɗauko laptop ɗin sa ya shiga duba inda ya tura neman aiki, ya tabbatar da komai daidai. Sai kuma ya faɗa tunanin lamarin Haura, sai yanzu yake kara yin da ya sanin barin aikin sa, ai ko a haka ba zai yarda ya sake bari ko magana ya haɗa su ba. Lokaci ɗaya yayi shiru yana tunanin irin kukan da yaga tana yi, ta na faɗin wai zata mutu, zuciyarta na mata zafi, ko kaɗan bai ji tausayinta ba, har ma ji yake ina ma ta mutu ɗin da yafi kowa murna. Daga yau zai fara tuba akan abun da yayi in sha Allahu. Haka suka uni a gidan suna ta mayar da lamarin Haura. Misalin ƙarfe takwas suna zaune suna cin abinci suka ji ana buga ƙofar palon nasu, Nadiya ta miƙe ta je ta buɗe tana tambayar waye?" Tsayawa tayi chak kamar wacce ta suma a tsaye tana kallon Haura janye da ƙaramin a kwati. Daga gurin Habib ke tambayar waye, amma Nadiya ta kasa magana, gefe ɗaya kuma ga wani irin rama da ya baiyana a jikin Haura ɗin.

*°Haura*
Ta yi mugun mamaki jin abun da Adam ke faɗa wai ya na sonta, kuma wai da aure, duk irin zafin da ƙirjinta ke mata a lokacin sai da taji komai ya tsaya mata. Daga kuma lokacin ta fara masa kallon wanda baya son ganin cigaban rayuwarta, shi bai san so bane, shi bai san Habib kawai take jin zata iya rayuwa da shi kawai bane, bai san bada zuciya kawai take son Sir ba sai da rai!. Lokacin da taji maganar da Amera take faɗa na cewar ko saboda ba shi ya haifeta ba, ko saboda yaga bata da Kowa, wannan kalmar ce tasa ta shiga tunanin to wai ita ɗin ma wacece tun farko, mai ya faru da ita, gaba ɗaya komai na rayuwarta na baya ta goge shi tun lokacin da ta karbi musulunci, amma a yau sai ta fara tariyo komai, ciki kuwa harda garinsu na Garuk da mutanen ciki da irin rayuwar da suke yi, sosai ta tuno da irin gatan da take da shi a garin, domin dama ko a baya Ɓultuwa ce kawai matsalar su ita da Aminta, da kuma laifin da suka yi, idan bata manta sarki da yazo gidan Adam an wanke ta daga laifin, kuma Ɓultuwa ta mutu. Ta na cikin haka taga Amera ta wuce da jaka, hakan yasa ta miƙe tsaye ta shiga ɗakinta ta jawo akwatin ta, zuciyar ta kawai ta raya mata cewar gidan Sir zata je, akan dai Daddy ya aureta gara taje gidan Sir ta zauna, idan kuma yaki ta faɗa wa matarsa gaskiyar abun dake tsakanin ta da shi to ita da kanta zata faɗa mata. Da wannan tunanin ta fita daga gidan Adam ta iso gidan Habib. Babu ko tsoro ta buɗe ƙaramin get ta shigo har cikin harabar gidan, sannan ta tsaya ta fara buga musu palo. Murmushin dole Haura ta aro ta na sakarwa Nadiya ganin ta tsaya tana kallonta. Jin muryarsa yasa ta jawo jakar zata shiga shi kuma lokacin ya ƙaraso gurin ya na kallonta. Gabansa ne ya bada wani rass zuciyarsa tayi tsalle ta tafi shawagi na wasu lokuta. Ganin zata shigo yasa Nadiya faɗin "Ke ina zaki shiga ne munafuka maƙaryaciya?" Ta faɗa ta na tare mata hanya. Haura ta dago ta kalleta jin abun da tace, to ko dai ya faɗa mata abun dake faruwa ne, to idan ya faɗa mai yace mata. Ta na cikin wannan tunanin taji Nadiya ta sake faɗin "Munafuka ki ka ce min sunanki Aisha ashe ƙarya kike yi Haura ne sunanki?" Ta sake faɗa ta na kuma tare hanyar. Kafin Haura ta yi magana Habib da har ya fara zufa domin shi ganinta da jaka ne ma ya ƙara rikita shi. Ya ce "To wai ma gidan uban wa zaki je ne harda jaka, kuma ba yanzu kika bar gidan nan ba da zaki dawo? Bebb kin ga abun da nake faɗa miki ko, Wallhi wannan yarinyar munafuka ce" ya ƙarasa ya na kallon cikin idon Haura da ke bashi tsoro a duk lokacin da ta ɗora masa su. Haura da har lokacin zuciyar ta zafi take mata, gashi babu wani ƙwari jikinta, hasali ma harda jiri take ji sosai. Ta ce...📝


S Reza
[09/07 à 14:07] S Reza: A BAR WA RAI ❣️

FCWA

Chapter 16

"Sir ka faɗa mata abun dake tsakanin mu ne Da kai ko? Ta yarda zaka aureni?" Haura ta faɗa hawaye na zubowa daga idanunta, sannan yanayin muryar da tayi maganar kana ji kasan bata jin dadi, ji take inama ya ce mata eh Nadiya ta yarda zai aureta. Kafin ma Habib ya magantu Nadiya ta ce "Abun da ke tsakanin ku! Dama kin san shi ne?" Nadiya ta faɗa cikin wata murya mai sanyi domin abun da take ji game da haura ba zai faɗu ba. Habib yayi saurin faɗin "Bebb Kinga abun da nake faɗa miki ko, kin dai gani da idonki ko, to wallahi babu ruwana duk abinda ya faru, ko ɗazu da na tafi Kaita gida idan kinji irin maganganun da take yi babu daɗin faɗa, kuma gashi a gabanki ta na sake faɗa, ƴar isa ce fa sosai ta bugawa a jarida ina faɗa miki Bebb". Habib ya faɗa kaman a rikice wanda da Nadiya ta lura da kyau zata gane ya fita daga haiyacinsa. Nadiya ta kalleshi ta kalli Haura. Sai kuma ta ce "Da gaske sunanki Haura?" Ta tambaya ta na kallon Haura ɗin da ta rame mata daga ɗazu zuwa yanzu. Haura ta ɗaga mata kai, sannan ta ɗora da faɗin "Ya faɗa miki komai ko?" Nadiya ta ce "Kin bani mamaki Aisha au sorry Haura, ashe kin shiga jikina ne saboda mummunan manufa a kan mijina ko, to in sha Allahu mijina yafi karfin ki, kuma ki bar min gida yanzu kafin nasa yayi miki shegen duka anan gurin, bana son ganinki na tsaneki Allah ya isa tsakanina da ke". Ta ƙarasa ta na zubar da hawaye domin da gaske ta tsorata da haura, yarinyar ta fitar mata a kai, ta na son mijinta, duk wani abu da zai sa wata mace ta nuna cewar tana son mijinta to tabbas ko wacece zata yi tsayuwar daka sai taga wannan matar ta hakura. Haura da izuwa lokacin ji take kamar ta samu guri ta zauna tsabar ciwon da jikinta ke mata, ga gajiya da zazzaɓi duk sun haɗar mata, maganar ma dole ce tasa yake yi, ga wani irin maradin son ganinsa a kusa da Sir ɗin ta da ya cika ta, ji take da ya zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login