Showing 51001 words to 54000 words out of 58144 words
"Anty na sani na san komsi, Adam shine yamin komai tun ban san kai naba. Amera ta kalli Adam shima ya kalleta jin sunansa ɓaro-ɓaro a bakinta, abun da bata taɓa yi ba tun da tazo gidan tun ma lokacin tana ƴar aiki ƴar mabaraciya. Ta cigaba da fadin "Wallahi ina son Habib ne, zuciyata shi take so, bana jin zan iya zaman aure da Adam dan Allah ku saurarwni kumin uzuri, amma ina sonsa Adam so irin na ƴa da uba, dan Allah kuyi hakuri ku bar wa rai abun da yake so" Adam ya ce "Ya isa haka, abar wannan maganar daga yau, bana son a sake yinta" Adam ya faɗa a hankali. Amera ta ce "Kin bani mamaki, kuma ki sani wallahi idan har iyayen sa basu zo yau ba, sai dai ki kaishi cen garinku a ɗaura miki aure, ba dai kin ce a bar wa rai abun da yake so ba, an bar masa, an bar shi da abun da yake so ɗin" Adam ya ce "Amera ya isa haka na ce ko?" Haura ta ce "dan Allah Anty kiyi hakuri, raina ne ke so kuma ba zan iya hana ta ba, zan iya mutuwa idan ban auresa ba" Daga haka suka bar ɗakin. Abincin da kowa baici ba kenan.
Adam na toilet yana wanka ya hango motar Habib ta shigo gidan, sai ga haura ta fito riƙe da kular abinci ta shiga motar sun tafi. Ya na fitowa yaga Amera zaune a ɗakin ta kawo masa abinci da ruwa. Duk yadda ya ke cewa ya ƙoshi amma haka dole sai da yaci ta bashi magani ya sha ta ce "Ina so na faɗa maka wata magana amma ban san yadda zaka karɓeta ba?" Ya ce "Kar kimin wannan maganar domin ta wuce a gurina" ta ce "ba ita ba ce" ya ce "Ina ji?" Ta ce "Kayi hakuri kabar Haura ta auri wanda take so kaman yadda ta ce, domin yau kwana uku ina yin istahara akan lamarinka da ita bana ganin alkairi, kar kayi tunani ko kishin ta ne yasa nake faɗa haka, a'a ko ɗaya domin Ni kaina a yanzu zan so kayi auren domin samun natsuwarka, idan har ka hakura da ita ni da kaina zan nemo maka matar da zaka aura mai nagarta da asali, amma dan Allah ka cire Haura a ranka, tabbas ba alkairi bace. Adam yayi shuru a ransa yana jin ba zai iya daina son Haura ba, sai dai kawai ya daure zuciyarsa har Allan da ya saka masa ya cire masa. Ya ce "Honey ki kwantar da hankalinki babu komai kuma na yarda ta auri wanda take so. Kuma na gode da ƙoƙarin ki a gareni, Allah ya sauke ki lafiya?" Ta ce "Sannan ina zargin wani abu, amma ina so kawai ka dage da addu'a da karatun Alkur'ani mai girma domin Allah ya tsare mu, kai sheda ne akan abun da ya faru damu a baya na sakaci da addu'a, dan haka yanzu dole ne mu dage da karatu a kowani lokaci da addu'o'i" ta na faɗa ta tashi ta ɗauko masa Alkur'ani ta kawo masa itama ta ɗauko. Dama yaran tun ɗazu suka tafi school abun su. Sai da ta fara karantawa kafin shima ya fara. Sun Dade suna yi kafin su kayi addu'a ya sakar mata murmushi yana jin wani natsuwa na shigarsa a karon farko. Ta ce "Naga barci zaka yi to kayi addu'ar kwanciya barci" bata bar ɗakin ba sai da barci ya ɗauke shi dalilin maganin da ya sha. Sai da ta sake masa addu'a kafin ta fita.
*°HAURA*
Koda ya zo kusa da school ɗin ya ce shi ba zai ƙarasa ba, saboda baya so a ganshi. Haka ta sauƙa ta ƙarasa a ƙafa ta ce idan ta gama zata kira shi sai ya mayar da ita. Ta na shiga school Allah yasa da sauran lokaci. Nan take ta shiga ta zauna tana tunanin maganar Amera, wallahi ba dan tana tausayin Adam ba sai ta sa zaman gidan ya gagari Amera, amma yanzu ma tasan yadda zata yi da ita. Ta na cikin tunanin Maryam ta shigo class ɗin ta zauna kusa da ita tana mata magana. Ƙarfe goma suka tashi, tayi nufin kiransa amma tabi Maryam suka tafi gida, Maryam na tambayar ta batun Malam Habib amma take ta kawar da maganar. Koda taje gida ta samu ko ina fess, ga wani irin turaren wuta mai yaji da ya fara shiga mata hanci da ido. Da sauri ta shige ɗakinta tana tari tana zagin wanda ya kunna wannan abun. Ta na shiga ta kira Habib sai dai bata shiga. So take ta tambaye shi yaushe zasu zo domin tayi musu girki mai rai da lafiya wanda basu taɓa cin irinsa ba. Wanka ta shiga tana fitowa ta saka kayan zaman gida doguwar riga da gajeran wando. Ta sake gwada kiran number sa, ta na shiga ya ɗaga. Ta ce "Sir yaushe zasu zo ne baka faɗa min ba?" Ya ce "Wai sai da yamma zasu so" ta ce "Na dawo gida kuma ina son ganinka?" Ya ce "Nima ina gida yanzu ma na tashi a barci kuma babu kowa a gidan ban san ina suka tafi ba" ta ce "Sir ko nazo na taya ka hira?" Ta faɗa domin dama tana son barin gidan nan saboda wannan turaren wutar ya fara shigowa ɗakinta. Shi kuwa Habib dama kawai yana son ganinta ne, shi fa a yadda yake ji baya son yana yin nesa da ita ne kwata-kwata. Ya ce "Eh Please kizo yanzu" ta kashe wayar tana dariya.
Ba suyi minti biyar da wayar ba ta iso cikin gidan nasa. Tana zuwa yaji kamar an masa kyautar yanke talauci tsabar farinciki, harga Allah shi kullum ƙara sonta yake yi, kuma kullum ƙara yi masa kyau take yi. Wannan karan kam ba iya hira suka tsaya ba, sai da suka yi romantic sosai, dan har kaya sun cirewa juna, amma bai yarda ya shigeta ba. Bayan sun gama suka dawo palo suka zauna ta yi musu girki suka fara ci. Shi idan yana tare da ita har mantawa yake da kowa da komai a rayuwarsa, yana jin idan babu ita ba zai iya rayuwa ba. Ta kwanta a ƙan cinyarsa yana shafa gashin ta, suna hira sam-ama.
Sallamar da suka ji ce tasa suka mike tsaye. Mama ce da Zainab sai Nadiya a bayansu wacce itace karshen shigowa. Dama tun da suka je asibitin suke kiran number sa, amma baya ɗagawa, cikin ikon Allah Nadiya ta haifi yarinyarta mace mai kama da ubanta. A asibitin suka samu kayan jarirai suka saya na sanyi, ganin babu wata matsala ne yasa aka salamesu domin da kanta ta aihu. Kawu ne ya biya komai na asibitin suka kamo hanya. Tun a asibitin Nadiya ta faɗa musu iya abun da ta sani tsakanin ta da Haura da kuma Habib da Haura. Hakan yasa mama ta ce ba lallai idan asiri bane amma idan ma haka ne zasu taimaka da addu'a, sannan kar kawun ya yarda yaje nema masa auran kowacce yarinya. Suna tafiya tana faɗa musu labarin farkon haɗuwar ta da Haura ta online har lokacin da Adam ya koreta, anan ne Mama ta yarda da cewar aikin asiri ne.
Lokaci ɗaya suka haɗa baki wajen kiran sunan Allah saboda abun da suka gani. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil!" Suka faɗa suna ɗorawa da Auzibillahi mina-sheɗanun rajin . Mama ta ce "Habibu me zan gani haka, iskanci a gidan aureanka?" Habib kuwa a karon farko da yaji wata iriyar kunya, ya shiga kare jikinsa. Haura kuwa a bayansa ta shiga ɓoyewa tana jin itama kunyar na kamata, ko babu komai ai Mama suruka ce bai dace ta ganta a haka ba. Mama ta ce "Wacece wannan?" Ya ce "Itace yarinyar da nake faɗa miki ɗin?" Mama ta shiga tafa hannu, sai kuma kuka ya biyo baya. Nadiya ta kalli Haura ta ce "Duk abun da kika yiwa mijina in sha Allahu sai ya dawo kanki". Habib dai ya kasa magana domin ji yake kamar yaje ya rungume Nadiya, sannan ganin Zainab riƙe da jariri yasa zuciyarsa har tsalle take yi, ga kuma babu ciki a jikin Nadiya, idan ya haɗa lissafin daidai to Nadiya ce ta aihu, amma wata zuciyar ta na nuna masa Haura a kusa da shi. Mama ta ce "Ke kuma shegiya kafura tsinanniya idan baki zo kin bar gidan nan ba sai na sa an karya min ke?" Habib ya ce "A'a Mama dan Allah kiyi mata a hankali wallahi ina sonta?" Ya faɗa yana riƙe Haura da sai yanzu ta samu ƙwarin gwuiwa. Mama ta ce "Habibu karuwar kuma sheɗanuyar mai bin bokaye ita kake so?" Ya ce "Wallahi ba ƙaruwa ba ce, kuma bata bin bokaye, Allah mama Haura mutuniyar kirki ce kuma tana sona". Haura ta ce "Wallahi Mama ina sonsa babu abun da ke zuciyata sai alkairi dan Allah ki bar wa rayuka abun da suke su dan Allah Mama?". Zainab ta ce"Wallahi Mama ba haka kawai ta bar yaya ba, anya ba za'a kira malamai ba ko zasu taimaka mana, ni dai ban yarda da ita ba?" Nadiya ta fashe da wani irin kuka mai ratsa zuciya jin abun dake faruwa kamar shirin flim, wai Habib da babu ruwansa da mata shine yau yake faɗin hk. Mama ta ce "Ina alkairi a gurin wacce take bin maza a waje har cikin gida?" Adam ya ce "Mama nine fa na kirata, kuma aure zamu yi, ni na yarda da ita zuciyata na so, haka raina ma, dan Allah mama a barni da ita, a bar wa rai na ita idan na rasa ta zan iya mutuwa...📝
S Reza ...
[09/07 à 14:08] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*
*FCWA*
*21*
Mama ta ce "To kuwa sai dai ka mutu ɗin, domin ba za'a bar wa ran abun da yake so ɗin ba dan ubanka" Ta na faɗa ta na ƙaraso wa gurin da yake, ta ci gaba da daɗin "Sakar mata hannu ta bar gidan nan na ce ko na saɓa maka mutumin banza mutumin hofi kawai?" Habib ya ce "Dan Allah Mama kar ki..." Kafin ya ƙarasa ta ɗauke shi da mari wanda sai da Haura ta rintse ido domin ji tayi kamar ita aka mara. Tun da su Mama suka shigo take ta ƙoƙarin ganin ta rufe mata baki amma kaman yadda ya faru akan Nadiya itama haka Mama. Babu yadda batayi ba amma sai abun ya tafi sai kuma ya dawo. Habib ya ce "Mama kimin duka amma dai wallahi ina sonta kuma sai na aureta" Haura ta shige cikin ɗaki da sauri ta saka kayanta. Gabanta ne ke ta faɗuwa taji kamar ana kiran sunanta. Haka ta fito daga ɗakin zata fita amma Habib ya riƙe mata hannu. Ta ce "Sir ina sonka babu wanda ya isa ya raba mu, kai dai ka tabbatar ka turo anzo gurin Daddy yau kaji?" Habib ya ce "Idan ma basu zo ba ni zan zo da kaina" su dai suna tsaye suna kallon ikon Allah. Haka Haura ta fita. Mama ta bi Habibu da kallo ganin ya shige ɗakinsa bai ko ƙara bi ta kansu ba. Ta ce "Tabbas wannan ba Habibu na bane" Ta faɗa tana sakin kuka. Ta ce "Zainab shiga ki haɗa mata ruwan zafi, ta samu tayi wanka, sannan ku saka na jinjirar idan na dawo zan mata wanka". Haka Mama ta fita Nadiya kuwa a gurin ta zauna ta fara tunanin abun yi, tana kuka tana tunanin yadda zata dawo da mai gidan ta cikin hankalinsa. Kusan minti ashirin sai ga Mama tare da wani malami sun shigo gidan, har cikin ɗakin habib ta kai shi lokacin yana kwance yana kallon rufin ɗakin hawaye na kwaranyo masa. A wannan lokacin wani irin kewar haura ce ta dame shi, jira yake lokaci ya ɗan ƙara ja ya tashi yaje gidan da kansa ayi magana, domin yadda yake ji idan bai aure ta zai iya zaucewa. Jin anyi sallama yasa ya mike zaune da sauri yana zare ido ganin baƙon fuska a ɗakin sa. Kallo ɗaya malamin yayi masa ya tabbatar da cewar a kwai sihiri a jikinsa. Hakan yasa ya ce a basu guri. Mama ta fita ta koma palo ta kama Nadiya suka shiga toilet tayi mata wanka sannan ta wanke jinjirar. Malam ya fita da kansa ya samo maza guda biyu majiya karfi wanda zasu riƙe masa Habib domin yi masa aiki. Haka suka dawo palo suka yi jikun suna jiran ikon Allah.
Haura ta na fita taji kanta na sarawa, hakan yasa ta saka hannunta a cikin bakinta ta gogo yawun bakin nata ta goga shi a goshinta take komai ya tsaya. A haka ta ƙaraso gida ta samu Salim da Nana a palo zaune suna hira. Dama tsakanin ta da Nana har yau babu shiri domin muddin Nana ta zo gidan ta dinga binta da kallon banza kenan. Hakan yasa ko magana babu wanda ya yiwa wani sai Salim ne ya mata Barka da dawowa. Ta na shiga ɗaki ta ware tafin hannunta domin tayi magana da Guber amma duk yadda tayi baya baiyana, take ta shiga tashin hankali, lokaci ɗaya ta tuno da maganar Aminta akan Adam, cewar auran Habib ba alkairi bane Adam ta ke so ta aura. Tsaki tayi a fili ta shiga toilet a ranta tana jin auran Habib shine alkairi ba Adam ba. Tana fitowa ta saka kayan zaman gida ta fito ta samu yanzu harda Salma da Amera duk suna karatun Alkur'ani mai girma. Wanda ganin shigowarta ne yasa amera ɗauko musu domin su karanta, Ita dai bata yarda da ita ba, ba zata manta wahalar da ta sha a irin wannan sakacin ba. Tsayawa tayi tana kallonsu da mamaki ganin suna karatu kuma a fili. Ita da sai yanzu ma ta tuna da cewar rabonta da yin Sallah tun da ta dawo bare kuma karatun Alkur'ani, sosai zuciyarta ke mata wani irin Abu kamar mintsini kamar tafiyar tsutsa, a ranta tana jin bata son wannan karatun da suke yi. Sai kawai ta koma ɗaki ta zauna ta ci gaba da lalubo Guber amma shiru. gaba ɗaya gidan yayi mata zafi ta ɗauki waya ta kira Habib taji a kashe, sai taji kamar ta kurma ihu. Ta sake fitowa ta nufi ɗakin Adam da sauri. Ta na shiga ta samu ya na barci abunsa, ga fuskar nan tasa fayau, har zata zauna taji an buɗe an shigo. Ido biyu sukayi da Amera tsaye tana kallonta. Ta ce "Bayan kince baki sonsa mai kuma kike nema a gurinsa?" Haura ta ce "Anty dama fa akan maganar masu zuwa ne, kawai mun yanke idan sun zo za'a ɗaura auran shine nake so na faɗa masa" Amera ta ce "Idan ya tashi za'a faɗa masa" haura ta ce "Dan Allah Anty.." Amera ta katse ta da fadin "Idan ya tashi na ce Zan faɗa masa dan Allah ki bar shi ya wuta mana?" Tana faɗa ta nuna mata hanyar fita. Haura ta fita tana waigawa kuma tana mamakin sauyin da amera ɗin ke mata yanzu, ko dai ta fara zarginta ne, ta aiyana a ranta. Amera ta dawo ta sake tofe Adam da addu'a ta fita. Nana ta bi Haura da kallo har ta shige ɗaki.
*°HABIB*
Sosai kansa ya fara juyawa yana jin kamar ana yin sama da shi, lokaci ɗaya ya daina ganin kowa da komai sai wani abu mai kama da gajimarai na sararin samaniya. Shi kuwa Malam sai karatu yake yana kallon yadda Habib ɗin ke ta muzurai yana ƙoƙarin ƙwacewa amma yasa maza majiya karfi sun danne shi yana yin wasu surutai marasa kan gado. Sosai yake ta kararo karatun ayoyin Alkur'ani yana yi. A daidai wannan lokacin kuma a cen garin Garuk Guber ya yi nasara tseratar da Ammi, sai dai abun da bai sani ba shine an ganshi, hakan yasa tun kafin ya dawo aka sanar da Sarkin garin. Ai kuwa dokar garin ce duk wanda aka samu da cin amanar garin to sare masa kai ake yi nan take. Sannan shi laifinsa ma biyu ne, na ɓoye Ammi da kuma na tsera tar da ita, sannan a ka samu tabbacin cewar ya bawa Haura tsafi a ɓoye, bayan kuma ta bar addinin da suke yi, hakan yasa aka gurfanar da shi a gaban fada. Kuma a tsarin dokokin garin Garuk ba'a musu akan abun da kayi, domin komai da kayi za'a nuna maka shine ba wai zargi ko hasashe bane, hakan yasa Guber bai ja ba ya ce tabbas anyi haka, sannan aka nuna komai kamar ana kallon Film. Nan take aka fara karya duk wani tsafin dake jikinsa, wanda hakan na nufin na jikin Haura ma zai karye. Wannan dalilin ne yasa ɗazu Haura ta kasa samunsa, sannan taji kanta na sarawa, kuma taji kamar ana kiran sunanta. A daidai lokacin da aka fille kan Guber, a daidai lokacin ne Habib ya saki wani atishawa mai karfi, ita kuma Haura ta suma a gurin da take. Malam yaci gaba da karatu har sai da ya kai aya kafin ya tsaya. Ya ce "Ku sake shi?" Ya faɗa yana kallon samarin da suka danne Habib. Suka sake shi. Malam ya ce "Alhamdu lillh, tsarki ya tabbata ga Allah buwayi gagara musali!". Kowa yabi Habib da kallo ganin ya ɓingire da barci. Malam ya kalli Mama ya ce "In sha Allahu yana farkawa zai dawo yadda yake" ta ce "Ba zai sake yin maganar ta ba Malam?" Malam ya ce "In sha Allahu babu shi babu ita, dama aljani aka saka masa ajiki yake amfani da shi, ana bawa aljanin umarnin yin abu wanda za'a ga kamar shi ne yake aikatawa, kuma aljanin yanzu haka ba ya tare da shi". Mama ta fashe da kukan farinciki, itama Nadiya kukan ne ya cika mata baki. Malam ya ce "Zan je na dawo kafin ya tashi, zan zo masa da rubutu, kuma ina so nayi muku tunatarwa idan ya farka?". Mama ta ce "To malam