Showing 21001 words to 24000 words out of 58144 words

Chapter 8 - A Bar Wa Rai Complete Books By S Reza.txt

S Reza   

12 Mar 2026

14

cewar ina sonta zan aure ko me, ai naga babu wani bukatar sanarwa domin kin sani, kuma bari kiji ko me nene ya faru da ita sai na aureta, kuma sai dai mugun nufinki ya ƙara a kanki lafiya ƙalau zata dawo" ya na faɗa ya mata wani harara sannan ya wuce ɗakinsa yana ji tana magana amma ya rufo ƙofar ɗakin ya kulle ya zauna a bakin gado ya na tunani. Anya a kwai namijin da zai ganta a wannan yanayin ya kasa jin wani abu, to ma wai waye yaron zai mata, daga ina yake, yaushe suka haɗu, shin tana ma sonsa, sannan ina suka tafi mai za suyi mata. Kishi da baƙin ciki ne ke nuƙurƙusar sa, ya kasa zama ya miƙe ya fito ya bar gidan?...📝



S Reza...✍️
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*

*°S Reza*

_First class writers association_

_My Whatsapp chanel_

*Chapter 9️⃣*
Bai fita da mota ba haka ya dinga yawo a ƙasa ya rasa ina zai je, har bakin babban titi ya zo ya tsaya ya na ta bin motocin mutane da kallo. Ganin dai kaman ya na neman mayar da kansa wani mai motsi ne yasa ya kama hanyar gida ya na tafiya ya na tunanin rashin wayon Haura da rashin hankalinta, idan ba haka ba ta yaya zata shiga motar saurayi da irin wannan shigar, ko shi da yake uba a gare ta ai bai dace ta shiga motarsa a haka ba, bare kuma wani ɗan iskan saurayi. Sai kawai ya shiga tunanin farkon kawota gidan sa ita da mamarta a matsayin ƴar aiki. Irin wahalar da Amera ta bata, duka zagi da cin mutuncin da aibatawa da wulaƙanci kuma ta na da ikon ramawa a lokacin amma ta jure. Zuwa lokacin da Amera ɗin ta kashe mata mamarta sannan kuma suka yi masa asiri har ya ce zai auri ita haura ɗin. Har zuwa lokacin da aka je gurin ɗaurin auren amma Auran bai ɗauru ba. Sai yake jin ina ma a lokacin bai dawo gida ba sai da aka ɗaura auran ai da shikenan ya huta, shi idan bai yi karya ba tun lokacin da ya fara ganin Haura a tsirara a gidan sa farkon zuwanta yaji yana sonta, gashi yanzu ta musulunta mai zai sa ba zai aureta ba, gashi bata da kowa. Haka ya dinga tunanin komai har zuwan da ƴan garinsu suka yi aka yanke wa kanwar mamarta Ɓultuwa hukunci kisa, sannan Haura ɗin ta zaɓi zama da su anan, kuma aka karya mata duk wani asiri da ke jikinta, har kawo yanzu da ta zama musulma kuma mutum mai ilimi, shine kuma ba zai aureta ba duk da wannan sadaukarwa da tayi. Tabbas ko waye wannan mutumin daga yau ya daina zuwa ƙofar gidan nan kenan har a bada. Haka ya koma gidan yana jin ita kanta Haura ɗin yau sai ya zane ta, ya tabbatar mata da cewar tana da iyaye wanda suka damu da ita.

*°Habib*
Suna shiga cikin palon kaman wanda aka turoshi ya rungumeta ya fara kissing dinta ta ko ta ina. Ita tsoro ma ya bata har ta na faɗuwa a tsakiyar ɗakin. Haka ya bita har ƙasan ya na ƙara jin wani sha'awar ta da son kasancewa da ita na ƙara taso masa. Cikin Wata murya ta ce "Sir Please" ta na rufe baki ya dora bakinsa akan nata Duk ya fita a haiyacinsa. Ta ƙwace bakin ta, ta sake faɗin "Please Sir ka na sona da gaske? Muddin kana sona zan iya maka komai, zan baka kaina idan har kamin alƙawarin zaka aure ni, ina sonka da rai ba da zuciya ba, amma ina tsoron ka samu abun da kake so kuma ka guje ni" duk maganar da take yi ya na ji, kuma shi kansa ya san yana sonta, ba zai iya rabuwa da ita, shi da yake jin ma zai iya mutuwa a kanta, shi kan sa har ransa yake jinta. Ta buɗe baki kenan ta ce "Sir" yayi saurin faɗin "Ina sonki ba zan iya rabuwa da ke ba, i love You with all my heart" ya karasa ya na ƙoƙarin cire rigarsa. Wani irin farinciki ne ya saukar mata, take wani so say soso ya mamaye mata ƙalbi, ta mike tsaye ta na kallon cikin idonsa wanda sai da ya kawar da kai domin wani haske da ya gani. Da kanta ta shiga cire kayan jikinta, sai da ta rage iya rigar mama da wandonsa, sannan yayi saurin ɗaukarta ya yi cikin ɗajin da ita. Ya na ajiye ta a kan gadon ya karasa rabata da sauran kayan jikin nata shima ya cire nasa. A daidai wannan lokacin babu abin da Habib ke bukata kaman ya jishi a jikinta, haka itama take da burin mallaka masa gaba ɗaya rayuwarta da zuciya ɗaya, da amincewar rai da gangar jikinta. Sosai ta bashi haɗin kai ya fara aiwatar da burinsa cike da shauƙi da jin dadin abun. Sosai hankalinsa ya bar jikinsa ya samu gamsuwa sosai wanda bai taɓa jin irinta ba a tare da Nadiya. Dukda cewar shine na farko da ya fara saninta amma ba tayi kururuwa ba kaman lokacin da ya samu Nadiya. Ƙasa da minti arba'in komai ya faru, ga jini da ya fitar mata mai yawa amma idanunta a ƙeƙyashe duk da cewar yaji kukanta amma ba mai hawaye ba. Gefe ɗaya ya koma ya na jin kansa wasai, sai kuma wani irin abu mai kama da rashin daɗi da ya ratsa zuciyarsa, juyowa yayi ya kalli gurin da take kwance ta na kallon sama. Da sauri ya tashi ya shiga toilet ya sakarwa kansa ruwa. Sosai kansa ya daina ciwon amma ya kasa samun natsuwar zuciya, sai ma wani irin kyamar abun da yayi yake yi, har ya fara jin kunyar sake haɗa ido da ita. A fili ya furta Astagfulrullah mai na yi haka, da aure na, innalillahi wa inna'ilaihi rajiun. Ya dafe kansa da lokaci ɗaya ya sara masa. Ya daɗe a cikin toilet ɗin kafin ya iya fitowa. Sai ya tsinci kansa da jin wani irin haushin ta da haushin kansa. Bai ko bi ta kanta ba ya saka kayansa ya dawo Palo ya zauna yayi shiru. Wani faifan karatun porf Ibrahim maƙari ne ya dawo masa kamar yanzu yake saurara. Inda malamin ya ke cewa "Shi fa mazinaci daga lokacin da ya ɗarsa a ransa cewar zai yi zina, suna shiga daki shida ita mazinaciyar, za'a ɗaye wannan fatar dake jikinsu, sai sun gama kafin za'a mayar musu da ita, wato abun nufi shine zunubin zina baya taɓa wankuwa domin ba'a wajen jiki yake ba. Ita Zina bashi ce, idan kayi sai an maka, sannan mazinaci maƙaryaci ne, sannan daɗin zina baya wuce na minti talatin". Ihu Habib yayi yana gasƙata maganar malamin domin gashi ya faru a kansa, mai yasa kafin yayi bai tuno da wannan wa'azin ba sai da ya gama. Nadama da tsoro da fargaba sune suka cika masa zuciya. Ji yake kaman ya gudu ya barta anan, tabbas da hotel ne wallhi ba zai bi ta kanta ba domin ya tsani ganin fuskarta ko jin muryarta. Haka dole ya tashi ya nufi cikin ɗakin domin ya mayar da ita gida ya kama gabansa.

Lokacin da ya shige toilet tayi ƙoƙarin tashi zaune amma taji zafi a ƙasanta, amma haka ta daure ta zauna a bakin gadon ta na jira ya fito itama ta shiga wankan. Tunani ta keyi akan abun da taji, tabbas ta sha wahala taji zafi wanda bata taɓa jin irinsa ba, amma idan ta tuno da cewar Habib ne kuma zai aureta sai komai yayi mata daɗi saboda ta na sonsa. Ya na fitowa ta shiga itama, dama tasan yadda ake yi, ta na karantawa a cikin littatafan da take karantawa Amera, idan haka ta faru ana wanka da ruwan zafi domin samun sauƙi. Hakan yasa ta haɗa ruwan zafi ta shiga ciki, ta sake haɗa wani ta shiga, sannan ta mayar da ƙaramin wandonta da rigar mama. Tana ta mamakin abun da yasa bai dawo ɗakin ba, sannan gashi a irin labarin da take karantawa mazan ne ma suke ɗaukar matan suyi musu wanka, amma shi ya kasa shigowa, sai ta bari akan ko dai kunyarta yake ji. Ta janye zanin gadon da ya ɓaci ta kai toilet. Ta fito kenan sai gashi ya shigo ɗakin. Bai ko kalleta ba ya ce "Saka kaya zamu tafi" ya faɗa ya juya ya bar ɗakin. Ta bishi da kallo wani sonsa na ƙara shigarta, sai ta saki murmushi kawai. Haka ta fito izuwa palon. Yana ganinta ya tashi da sauri ya fita gurin Mota. Ta tsaya ta na kwallonsa, bata ce komai ba ta saka kayan nata, ta naimi gyalen da tazo dashi ta rasa. Haka ta ɗauki jakarta ta buɗe ciki ta ɗwuko wayarta taga tarin miss calls ɗin daddy. Gabanta ne ya faɗi taji wani irin tsoro mai dalili na Daddy, sai take jin kamar zai gane abun da ya faru. Da sauri ta mayar da wayar jaka ta fito daga palon ta ja ƙofar ta iso bakin motar. Budewa tayi ta shiga wanda bata gama gyara zama ba ya ja motar kamar zai tashi sama ga fuskar nan a haɗe. Kallonsa ta yi tana mamakin kuma me ya sa yake ɓata rai bayan ba haka ya dace yayi ba, shida zai yi farinciki da godiya. Ta ce "Sir me ya fa" tayi tambayar cikin rashin jin daɗin yanayinsa. Shiru yayi kamar bai jita ba. Ta sake faɗin "Sir ko dai".. da ƙarfi ya daka mata tsawar da sai da ta jita har ƙwaƙwalwar kanta. Ya ce "Please kije gida zamuyi magana gobe kaina ciwo yake yi" Haura ta sake kafe shi da wannan mayun idanun nata, amma ya ki yarda ya kalli gurin da take. A daidai lokacin kuma maganar Amera ta fado mata Ta ce "Sir gobe Lahadi Daddy ya ce na sanar da kai ya na son ganinka?" Da sauri Habib yayi mata wani kallo, shi fa gaba ɗaya muryarta ma tashar masa da zuciya take yi, har sauri yake ya kaita unguwarsu ya kama gabansa. Jin yayi shiru ta ce "Sir ka j..." Da sauri ya ce "Naji Allah ya kaimu" ya faɗa ya na mayar da hankalinsa ga tuki. Haura tayi murmushi ta ce "Sir da gaske zaka zo?" Ya ɗaga mata kai. Ya na mamakin to mai yawa yanzu muryarta bata masa daɗi, mai yasa baya jin wannan abun mai kama da so da yake mata.

Suna zuwa bakin babban titin unguwar so ya tsaya ya kalleta a wani irin yanayi kamar dole ya ce "Ki sauƙa ki ƙarasa kar a ganni kuma ayi tunanin wani abu ne, zamuyi waya idan kin shiga gida" ta ce "Tom sai goben idan kazo ko Sir?" Bai ce komai ba tana fita yaja motarsa ya bar unguwar. Bin motar tayi da kallo har ta daina ganin ta. Kallon kanta tayi ganin babu ko gyalen da ta tafi da shi, gashi har lokacin ƙasanta na mata zafi sosai, haka ta fara takawa a ƙasa har ta iso bakin get ɗin gidan nasu. Haka ta tura ƙaramin ƙofar ta shiga, ta na ta ƙoƙarin ganin ta saita tafiyar ta tayi daidai. Lokacin da taje ƙofar shiga palon sai da ta duba lokaci taga tara da kusan arba'in kafin ta shiga palon da sallama. Ganin bata ga kowa ba yasa ta nufi ɗakin ta babu ko alamar tsoro a fuskar ta. Har ta kusa barin palon ta jiyo muryar Adam na tambayar ta.

*°Adam*
Haka ya cigaba da zama ƙofar gidan ya na jiran yaga ta ita zata shigo, har takwas zuwa da rabi, har tara, hakan yasa ya koma cikin gida yana jin gabansa na faduwa haka kawai. Har zai shiga gidan ya tuno da abubuwan da ya sayo ɗazu. Ya buɗe motar ya kwaso ya shiga dasu gidan. Lokacin Amera na zaune a palon itama abun duniya ya ishe ta, ganin har lokacin Haura bata dawo ba yasa ta shiga damuwa, sosai abun ya dameta ita ba haka tayi zato ba. Adam ya ajiye mata ledar ta, ya ɗauki ta Haura ya kai mata ɗakinta, sannan ya fito ya zauna a palon ya yi shiru. Amera ta ce "Ga abinci fa?" Ta faɗa cikin murya mai sanyi. Bata ji dadin abun ba, sannan sai yanzu ta gane cewar ba haka ya kamata tayi ba. Adam bai ko nuna yaji taba, sai da ta sake magana kafin ya kalleta ya kawar da kai. Ta ce "Honey Wallhi ban san cewar fita za suyi ba, ina ce kawai hira ce yazo kaman yadda ya saba" Adam da zuciyar sa ke tafasa ya ce "Bayan kin gama addu'ar Allah yasa karta dawo lafiya, wallhi kin bani mamaki". Amera ta yi shiru. Ta ce "Kaina kasa ni yin wannan furricin amma wallhi ba zan so wani abu ya samu Haura ba, ina jinta kamar Salma da Salim, kawai banji dadin abun da kake son yi bane, idan kayi haka baka kyauta min ba, ba zan ji daɗi ba, dan Allah honey karka lalata rayuwar gidan ka da kanka Please?" Adam ya ja dogon tsaki ya tashi ya bar palon. Amera ta bishi cikin ɗakin bayan ta kwashe ledojin da ya shigo da su. Babu yadda batayi da shi ba amma ya ce shi ba zai ci abinci ba domin bashi da wannan natsuwar. Haka ya sauya kayan jikinsa ya dawo palo ya zauna, itama ta dawo suka zauna tare. Ganin tara harda rabi yasa ya tashi ya leka waje ya dawo ya wuce ɗaki itama ta bishi. Yana zama yaji alamun buɗe ƙofar hakan yasa ya tashi da sauri ya fito, sai kuwa ya ganta tana har ta kusa shiga Palo. Cikin Wata murya mai kamar an shaƙe shi ya ce "Daga ina kike Haura?" Ya faɗa ya na nufowa gurin da take.

Juyowa tayi suka haɗa ido, lokaci ɗaya Komai da ya aiyana zai mata suka fara zama tarishi a cikin zuciyarsa. Kanta tsaye ta ce "Daddy shine fa yazo, kuma na fadawa Anty, sannan na masa magana akan yazo gebe kana son ganinsa kuma ya ce zai so?" Ta ƙasa da sakin murya. Adam yayi jim, zuciyar sa na jin wani ɗaci. Ya ce "Yanzu Haura a haka kika fita da Namiji baki ji kunya ba?" Ta ce "Daddy ba zan ƙara ba" ta ƙarasa kamar mai roko. Adam yaji wani sanyi jin yadda tayi maganar. Sai kawai ya tsinci kansa da tausayinta, ya kasa ma yin wata tambayar. Ya ce "Karki sake fita babu hijjabi, sannan ki je ki kwanta gobe idan yazo zamuyi magana, kuma daga yau karki ƙara fita gurin kowa har sai kin kirani kin sanar min. Ta ce "Tom Daddy na ji". Har ta fara tafiya ya ce "A kwai shawarma da Yorgot da na kawo miki a ɗaki ki sha kafin ki kwanta". Ta amsa cike da farinciki da jin dadi. Ya na juyowa yaga Amera tsaye ta na kallonsa. Ta ce "Shikenan faɗan da zaka yi mata dama? Hakan shine matsayi uban da yasan ciwon ƴarsa? Ko kunya baka ji yarinya na kiranka Daddy Daddy amma kana tunanin auranta, yarinyar da zata iya bin saurayi a haka kana tunanin babu soyayya a tsakanin su ne, to Wallhi tun wuri muddin baka son zubar da mutuncinka a idon ta ka barta da wanda take so, kar daga kiran ka Daddy a koma kiranka da Dade domin wallhi tana son wannan saurayin nata, amma idan ka ɗauki haka a matsayin kishi daidai ne, idan kuma kayi tunani akai shima daidai ne. Ta na faɗa ta juya ta nufi ɗaki ta kwanta abunta, tana yadda da irin wannan hanyar da zata bi akan ta tsaya ta na tashin hankali da shi, ai in sha Allahu ko ya furta mata ba zata so shi ba, ita zata kara tsoratar da ita da nuna mata yin hakan zata cutu ne...📝
[09/07 à 14:07] S Reza: *A BAR WA RAI!❣️*

*°S Reza*

_First class writers association_

_My Whatsapp chanel_

                         *Chapter 1️⃣0️⃣*
Bai ce mata komai ba shima ya shige nasa ɗakin a ransa yana jinjinawa kishin Amera, domin yasan dai idan ba kishi ba yaya za'ayi ta ce wai Haura zata iya cewa bata sonsa, ai wannan maganar banza ce, ta san yadda kuwa haura ta ɗauke shi da har take tunanin zata iya cewa bata sonsa, Allah dai ya kaimu gobe zai bata mamaki, idan ma ta kama kawai auran za'a ɗaura ko a cikin satin nan ne, ba sai ya bawa kansa wahala ba, domin dai shine mai ba da auren kuma shine mai karɓa. Ɓangaren Haura kuwa ta na shiga ɗakin ta zauna a bakin gado ta shiga cire kayan jikinta domin sun daneta kamar ta saka ƙaya. Ta na gamawa ta shiga toilet ta sake yin wanka da ruwan ɗumi kafin ta fito ta saka rigar barci ta nufo kichin domin ɗiban abinci saboda wata azabbabiyar yunwa da take ji kamar an mata sata a cikinta. Haka ta zuba kaɗan domin taji Daddy ya ce mata ya kai shawarma ɗakinta, ita dama bata wani iya cin abin ba sosai baya mata daɗi a baki, shi yasa ma ta je zubo abincin. Ta haɗo da ruwan gora ta dawo ɗaki ta zauna. Ta jawo ledar ta buɗe taga shawarma harda nama ga Yorgot. Murmushi tayi ta na jin dadi a ranta da wannan ɗawainiyar na Daddy, sosai take alfahari da daddynta saboda abubuwan da yake mata, ya zama dole ta daina duk abun da ya ce baya so. Ta na ci ta na tunanin abun da ya faru tsakanin ta Habib. Ita ko kaɗan bata yi nadama ko kuma tsoron wani abu ba, ita har cikin ranta daɗi take ji, wani irin shauƙi ne ke kamata idan ta tuno da abun. Sosai ta ci abincin da naman, ta bar iya shawarmar ta kai kichin ta ajiye. Ta na dawowa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login