Showing 33001 words to 36000 words out of 205258 words
Chapter 12 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt
nawa ma bayi nake amma in ya Faty ta aiko karbar nawa wankin in shaa Allah xan hada maka da naka."
Ya danqi wuyanta ya hadata da bango, sannan cikin huci da tsabar tsanar yace "ke kin isa insaki aiki kice baki ba? Wlh baki isa ba, na tsaneki wlh da inka kashe rai babu wani hukunci a kanka da kece mutum ta farko da xan fara kashewa, maryam ban taba tsanar wata halitta a duniya kamar ki ba. Saboda haka dole kimun wanki dan ubanki" ta fusge wuyanta tayi gefe ganin yana shirin kaita lahira, tana maida numfashi tace "wanki bazanyi ba kisa kuma bisimillah ka kasheni." cikin bacin rai take furta wadannan maganganun domin ranta yakai matuqar baci da xagin da Badaru kewa ubanta.
Kafin ta ankara ya tsinka mata mari ji kike kau! π³ tayi baya cikin azama ya dora da cewa "lallai wuyanki ya isa yanka? Yauni kike maidawa magana? To dan ubanki...... "ta tari numfashinsa kafin ya qarasa. "karka kuma xagin ubana domin nasan darajarsa, kuma da yana raye wlh bazan auri wanda besan darajar iyaye kamar ka ba, maraicine ya jawomun"
Ya kuma dauketa da wani gigitaccen mari, "na xagi uban naki bayan xagima na dakeki dan haka kije ki haqoshi daga kabari yazo ya rama miki." ta dago idonta jajur " ka mareni? Wlh komai daren dadewa saina rama, wannan alqawarine na yiwa kaina."
Ya ja hannunta qiiiiii ya bude gidan ya turata waje ta fadi dabas. Sannan yace "ai basai andade ba kije yanxu ki tasoshi daga kabari kuxo ke dashi ku hadu ku dakeni, kije na sakeki kuma Allah ya isa tsakanina dake in shaa Allahu bazaki gama da duniya lfy ba."
Ya maida gidansa ya rufe, yabarta zaune babu takalmi babu mayafi. Kuma dai dai lokacin hankalin mutane ya fara dawowa kanta, aka zagayeta ana kallonta tai qasa da kanta taji duk ta muxanta. Ya qara bude gidan ya wullo mata hijabi da wayarta, jehowar da yayi tasa wayar taci screen. Ta miqe tasa hijabin qafarta babu takalmi gashi bai bari ta dakko kudi ba dan shiga Mota.
Har ta fara tafiya wata maqociyarta yar dattijuwa wacce yayanta ke shiga gidan Mimi ta biyota a baya ta tsai da ita, tace "maryam yanxu akaje aka sanar dani abunda ke faruwa, kiyi haquri indai baki cuceshi ba Allah saiya saka miki AURAN BAYA SADAKIN NA GABA." ta cire takalmin qafarta ta bawa Mimi tace saka ki tafi Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi, ta juya ta tafi tana kuka dan tana qaunar Mimi.
Cikin wani irin yanayi take tafiya, tafi kama da mahaukaciya sabon kamu sam ba kuka take ba, idonta da xuciyarta sun bushe qaraf. Jinta take ita ba matacciya ba ita ba rayayya ba, abun kamar almara aurenta ya mutu cikin wata biyar da kwana shida kacal da yin auren. Batasan mutuwar aure sam koda akan maqiyinta bare a gida irin nasu wanda bata taba ganin ko yaji anyi a gidanba. Ita kuma haka QADDARARTA take, andade ba ai aure ba, anyi ba a dade ba ya mutu. Tasan qalubalene a rayuwarta qatoto, wlh duk ixayar da take ciki gara ta haqura ta xauna da Badaru da ace aurenta ya mutu. Koda kuwa takata zai dungayi yana wucewa. Kuma da tasan zai dauki matakin saki akanta wlh da gara tayi masa wankin.
Saboda tashin hankalin da take ciki yasa bataga nisan tafiyar gidan Badaru xuwa titi ba, kawai ta tsinci kanta a bakin titi. Ta tare dan sahu tace kaini yahya gusau (gidan ya Faty) dan koda wasa tasan bazata iya tunkarar gidan Baffa ba (gidansu)
Har bakin gate din gidan ya kaita kasancewar gidan a bakin titi yake. Ta sauka tace bari in kawo maka kudin.
Faty na zaune a parlour tanashan golden morn taga fadowar Mimi parlour kamar an jehota, ta miqe a razane tace "lfy Mimi, jikin naki ne ya tashi?" nabar dan sahu a waje ban bashi kudin ba" itace amsar da Mimi ta bawa Faty, tana fadar haka ta shige bedroom din ya Faty.
Bayan Faty ta sallami dan sahun, ta riski Mimi a bedroom dinta kwance kan gadonta tace "Mimi ki fadamun abunda ke faruwa na ganki a hargitse haka" dakyar ta daga ido saboda tsabar ciwon da kanta ke mata, a taqaice tace da Faty "ya sake ni" ko kalma daya bata qara akan haka ba ta koma ta kwanta kan Royal bed din Faty. Sama sama ta dunga jiyo salati da sallallamin fatyn.
Har akai sallar magriba ana gab dayin ta isha suna zaune a gurin da sukai sallah jugum jugum. Suna idda sallar isha Mimi ta kuma hayewa gado ta qudundune mugun sanyi takeji saboda zazzbin da ya rufar mata.
Duk yadda Faty tayi da Mimi taci abinci taqi ci, domin batajin ko maqogaronta abinci zai wuce, saboda wani irin malolo takeji a maqogaron shi beyi gaba ba shi beyi baya ba. Kuma itama Faty da take maganar itama bataci abincinba. Ta hado tea ta miqawa Mimi tace "karbi kisha kodan abunda ke cikin ki" ba musu ta karba tasha.
A haka Ahmad ya riskesu, dawowarsa kenan. Ya shiga har bedroom din yace "lfy Faty? Mimi jikin ne ya kuma tashi?" duk sukai masa shiru, Mimi tacigaba da shan tea din ya kalli Mimi " Mimina lfy? Ko muje asibiti?" nan ma shiru ya kuma kallon Faty yace " Faty na kiyi magana mana lfy?" a hankali Faty ta furta "sakinta Badaru yayi".
Ga mamakinsu sai sukaji Ahmad yace "ALHAMDULILLAH " nan take fuskarta ta nuna tsantsar farin ciki, dukkansu suka saki baki suna kallonsa.
Ya ajiye jakarsa ta office akan side bed, sannan ya haura kan gadon ya kwantar da kan Mimi a kafadarsa yace "maryam ki godewa Allah da ya rabaki da Badaru, domin bai dace da samun salihar mace irinki ba, MARYAM keep praying in shaa Allah sai kinsamu mijin da baki taba mafarkin samu ba haqurinki bazai tashi a baxan ba"
Ita dai bin kowa take da ido ga alama ta samu kurumta ta wucin gadi. Haka suka kwana gado daya da Faty, inta fara bacci sai ta farka a furgice sai dai Faty ta tofa mata addua ta maida ita ta kwantar. Ya Ahmad kuma kwana yayi yana nafila yana roqawa Mimi waraka gurin ubangiji, in yai sallama ya shiga dakin da suke kwance, yaga halin da suke ciki, a duk sanda ya shiga Mimi kanyi xunbur ta miqe zaune alamun a firgice take sai dai ya maida ita ya kwantar ya tofa mata addua. Da haka har suka wayi gari.
HAPPY EIDIL FITR, TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM.
Mrs π
[9/30, 1:03 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌAL 'AMARIN MARYAM ππΌππΌππΌ
Writing & story by rahman Mohammed (hajia)
Editing by mmn khairat
πFANTASTIC STARS WRITERS {F S W }
Page 2β£8β£
Dedicated to
Sahura Musa Mohd (ina cigiyarki)
A bangaren Badaru kuwa, sai bayan ya saki maryam sannan fargabar abunda zai biyo ta bangaren Abbansa ya shige shi. Amma daya tuna yanda ya tsani maryam da yacce ya suqe da xama da ita sai yaga ai yanci bana rago bane. gara kawai da ya saketa komai xai faru ma ya faru.
Ana iddar da sallar isha, ya hada tea murtuk ya soya kwai 5, kamar shi ya siya. Ya dake cikinsa sannan ya sheqa wanka ya xaba shadda, ya samu turaren Mimi ya feshe jikinsa da shi. Ko lura da cewa turaren mata ne bayi ba. Yaywa gidan su Nafee tsinke.
Tare suka fito da dan aiken da yaje kiranta kamar jira take, ko gaisawa bata bari sunyi ba ta fara qorafi "Badaru anya kuwa kana sona? Anya kuwa xaka aure ni? Nifa na fara yadda da maganar mutane da suke cewa yaudara kake"
Ya danyi dariya π yace "Nafee ko gaisuwa babu za a fara da qorafi" tace da maganar na yini tana damuna.
Yace to "ki fara shirin bikin ki nan da wata biyu masu xuwa" ta waro ido tace "bayan sallah fa kenan" yace kwarai kuwa tace "wace sallah? Yace wacce sallah ke gabanmu yanxu? " tace in nayi lissafi dai dai qaramar sallah kake nufi domin yau kwana 8 ko 7 ya rage a fara axumi"
Yace yawwa yar gari, kin gane kenan. Ta daka tsalle tace "da gaske?" yace "wlh da gaske nake" ya qara murmusawa yace "kuma daya albishir din da xan miki shine : ke kadai ce dani yanxu" tai far π tace "kamar yaya?" yace "mun rabu da maryam daxu"
Wannan karon tanayin tsallen ta fada jikinsa (kuji rashin kamun kai) ta qanqameshi duk kuwa da cewa basu taba hakan ba. Yayi saurin cireta a jikinsa jin yana shirin loosing control. Wannan dare haka suka sha hirar soyayya cikin nishadi saboda matsalarsu ta tafi (maryam) tare da hirar yadda aurensu xai kasance.
***** ****** ****** *****
Karfe taran safe 9:00 am a gidan kakanninsu tayi musu bisa shawarar Ahmad da kuma rakiyarsa, domin ita kanta bai yadda da nutsuwar Faty ba a lokacin shi yasa ya hanata driving. Yasan tunkarar Baffa da lamarin mutuwar auren Mimi ba karamin balli zai tayar ba, shiyasa yace abi abun takan surukan Baffa ko zai zo da sauki.
Babba gidane me cike da kango a da, amma yanxu da yayansa suka xama wasu sun bigeshi sun maidashi na tsamani da tsari. A katafaren parlourn gidan sukai masauki hajja na kan kujera, yayinda mal manu kekan well chair ( saboda girma baya iya tafiya)
Tiryan tiryan Faty tai musu bayanin lamarin tun rashin lfyar maryam da kuma halin data tsinceta a gidan Badaru har xuwa jiya da auren ya qare.
Hajja tunda aka fara take share kwallah, mal manu kuwa baice komai ba sai wayarsa daya dakko ya kirawo mama yace ta sameshi gida yanxu, sannan ya kira Baffa ma ya fada masa.
Tana gurin aiki kiran ya risketa, dan haka ta kasa nutsuwa. Tasan ba qaramin abu bane zaisa Baba kiranta a wannan lokacin, sai ta barwa kanta kawai Hajja ce ba lfy. Taje office din Principal din ta naimi excuse ganin bata taba hakan ba kuma da alama a rude take yasa ya barta.
Kusan tare suka iso da Baffa, domin shigarsa kenan taxo. Ganin motarsa a kofar gida yasa ta qara rudewa. Tana saka kai parlourn gabanta ya yanke ya fadi, dan ganin Mimi ta tsummace rabonta da ita tun randa aka kaita gidan miji (halayyar uwa ta gari bata xuwa gidan yayanta sai da babban dalili) ta samu gefen centre carpet ta xauna.
Faty ta kuma yi musu bitar abunda ya faru tas (dan ma Mimi bata fada musu waye haqiqanin Badaru ba da irin azabar da yayi mata). Baffa ya miqe ya watsawa Mimi kallon kinwa kanki, dagani akwai magana a bakinsa kuma bai yarda da abunda Faty ta fada ba, amma ganin idon surukansa yasa bece komai ba. Yace "ni natafi kasuwa dan nakusa makara"
Mama ta kasa dauriya da abunda ya samu Mimi tasa kuka, hajja da tun dazu take kukan itama ta qara volume Faty itama tasaka nata kukan. Mimi ganin mama da Faty na kuka (mutanen data fiso fiye da komai) itama ta saka nata kukan (tunda abun ya faru sai yanxu tayi kuka.
Kamar jiran nata kukan suke, kowa yayi shiru da nasa kukan parlourn yayi tsit sai sautin kukanta. Faty ta yunqura xata tashi taje gurinta mal manu yayi mata alama ta zauna. Sai da tayi 43 minutes tana kuka baji ba gani, sannan tayi shiru dan kanta.
Mal manu ya garo kujerarsa yaxo kusa da ita ya dafa kanta "MARYAMU kiyi haquri kinji, wata rana sai lbr, haqiqa mijinki ya cutar dake, amma kiyi haquri wlh duk wanda ya toxarta aure saiya wulaqanta, sakayyar aure a duniya Allah ya ke yinta. Allah ya baki wanda ya fishi, in shaa Allah wannan hawayen da kika xubar a dalilin baqin cikin aure sai Allah ya sa kin xubar da hawayen farin ciki fiye da wannan, Allah ya albarkaci rayuwarki" duk suka amsa da Aminnnnnnnn
Faty ta miqe xata tafi gurin aiki, mama ma ta miqe. Mimi tai saurin tashi tabi bayan mama. Hajja tace "maryam da kunyi xamanki anan kin dan murmure bakyaje wannan gidan naku haka ba suyi ta kasaki a fefe ana tallanki.
Mama tace "Hajja barni intafi da ita, hankalina sai yafi kwanciya" Mal manu yana jinsu yayi musu shiru domin daga uwar (mama) har yar (Mimi) tausayi suke bashi. Sai yake ganin rayuwar Mimi kamar ta mama acan lokacin da ya wuce, tabbas tarihi yana shirin maimaita kansa akan Mimi. Yana fata itama nata qarshen labarin yayi kyau (Mimi) kamar inda na fadimarsa yayi kyau. Yanason yarinya fiye da duk jikokin da yake dasu, yana ganin wasu halayyar MARYAM (matarsa Hajja) a tare da Mimi kamar haquri da sanyin hali, biyayya da kuma ibada. Kai hatta tafiya Mimi irin ta hajja take yi, afuskane kawai basa kama (tafi kama da mahaifinta AL AMIN, kamar photocopy dinsa ce) yana wannan tunanin har suka fita tsakar gida. Ya kwalawa mama kira "Fadimatu" ta amsa "naam Baba"
Ta sameshi yace "duk sanda kikaga tana kuka karki hanata, kibarta tayi ya isheta, baqin cikin zai ragu. Rashin kuka alokacin da abun kuka ya sameka kan illata lfyar kwakwalwa, shiyasa daxu na barta tayi kukanta, tashi kije Allah ya yi muku albarka ke da zuri ar ki" tace amin Baba Allah ya saka da khairan.
Umma kawai suka samu a tsakar gida tana yanka salak, ta tashi ta bisu har daki tana cewa "maryam meya sameki haka duk kika tsummace? Jiya nake cewa baffanku ya kamata aje a ganoki, tunda aka kaiki babu wanda yaje (kuji qarya)" sukai mata shiru har ta gama surutunta. Daga dakinsu gurin Anty ta nufa ta kai mata kanun labarai, tun kafin a gama fada mata ta nufi dakin mama.
Tana xuwa tace "maryam!π³ yanxu cikin ne yasa kika tarkato kika taho gida? Yara qannan bayanki suna gidan miji a zaune inma cikin ne sai dai mugansu dashi ya girma? Koda yake da alama cikin na wahalar dake duba da yadda duk kika qare, yo uwarki ce har yanxu bata daina abun mutanen da ba, wai ita kunya bata xuwa gidanku mu ba haka muke xarya gidan namu yayan ba" itama har ta gama haukanta basu tanka musu ba. Mama ta tashi tana tunanin hali irin na matan gidan wai ai wata biyar ba a ga mutum ba, amma in anganshi ko irin nuna murna nan ta yaushe gamo.
Mama ta dumamawa Mimi tuwon shinkafa miyar kuka tasa yajin daddawa ta isketa har bedroom kwance a saman gado ta kai mata "mimina tashi kici" ta girgixa kai alamar bataci mama ta hayo gadon ta dagata ta zaunar da ita tace "nasan mutuwar aure Mimi, nasan ciwon sakin aure. Musamman saki irin naki na wulaqanci amma babu yadda zaki da hukuncin Allah, barin kanki da yunwa bashine solution ba." ta karbi tuwon ta faraci, mama ta qura mata ido tana kallonta, tana son gano cikin da akace Mimi tana dashi. Ita sam abun bai mata dadi ba, dan dai babu yacce xatai da hukuncin Allah ne.
Acan kasuwa kuwa Baffa yini yayi yana xirga xirgar neman Badaru, tun yana xuwa da kansa har ya gaji ya dunga aika yaransa. Sai dai amsar dayace baixo kasuwa ba yau, kuma abun kamar hadin baki shima abban Badaru yau be zoba. Kuma Badaru yaqi xuwa kasuwar ne saboda yasan sai Baffa ya nemeshi.
Koda ya koma gida bai nemi mama ba duk kuwa da cewa ita keda girki, ta karbi girki da yamma. Wanda hakan ke nuna laifin Mimi ya shafeta, itama ta fison haka. Tasa yarta da jikanta (Dady dan Faty wanda ke xama a hannun Maman) agaba sukai kwanciyarsu.
Sai dai yadda Mimi ta kwana jiya, haka ta kwana yau. Ta dunga farkawa a firgice, kuma duk farkawar da tayi xataga mama xaune tana kalkonta. Farkawa ta qarshe da tayi tasamu mama tana sallah. Ita sai yanxu ta tuna in masifa ta sameka kana addua. Dan haka ta miqe taje tayo alwala ta fara sallah kamar motsatstsiya, duk sujjadar da tayi takance "ALLAH HUKUNCINKA NE WANNAN BANYI FUSHI BA, ALLAH KA QARAMUN JURIYA"
Da sassafe Baffa ya yiwa gidan alh inuwa tsinke, yana bacci xuwan kiran Baffa ya iskeshi. Sama sama suka gaisa Baffa ya karanta masa abunda Badaru yayiwa Mimi. (saboda da abun ya tayar masa da hankali, abunka da wanda ba a taba sakarwa ya ba). Wata irin kunya kunya ta rufe alh inuwa, ya tashi ya shiga gida yace da Baffa yana xuwa.
Yasamu Umma a kitchen ya labarta mata abunda Badaru yayi, gabanta ya yanke ya fadi ta xauna dabas a qasa tana sallallami tace "alh meye abunyi yanxu? Har Badaru yayi saki ba tare da saninmu ba. Maxa kirawoshi yazo ya maida ita tunkan abu yayi nisa" ba musu ya dakko waya, dan shima abunda yake shirin yi kenan.
Dajin kiran ABBA da sigar da yayi masa magana, yasan lbrin sakin ya ruskesu. Saboda haka ko wanka beyi ba ya tashi ya nufi gidansu yana qudurce cewa sai dai ayi duk wacce xa ai amma wlh ya gama xama da maryam.
Dake Bahaushe yace baya bata da kadan, be dade da fita ba mumy (Adda halima) yayar mama