Showing 189001 words to 192000 words out of 205258 words

Chapter 64 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

weekend din ya dunga yawo da ita gidajen family nd friends har garko sunje dangin iyayensu mata nan madai magungunan tsari aka hado musu, kuma ya shige mata yayi mata famfo ta taho su koma gidansu xai kula da ita akai sa a itama so take ta bishi ta hau ta xauna tace "nimafa ya Bature so nake bika, baxan xauna ba qafata qafarka." yace "yawwa Mimi luv" yana dariya a fili yace "na shiryawa su mumy tsiya kenan akwai daru"










Babu wanda ya nunawa yaxo tafiya da Mimi ne kuma bai nuna musu ga ranar da xai koma ba har sai ran monday da safe, ya shirya ya hado kayansa kaf sukai sallama dasu Dady da mumy yace xai koma. Mumy har da cewa "amma dai jirgi xakabi ko? Naga yau da aiki kaso kayi latti" yace "a a mota xan tafi, sai gobe xanje aikin. Yanxu xan biya muyi sallama dasu Mimi" tace "to madallah Allah ya kiyaye hanya ai gara ka barta nan inta haihu ta koma" a xuciyarsa yace "tab ashe kan lokacin kewar Mimi ta xautani" mumy har bakin mota ta rakoshi tana maimaita masa ya kula taji dadi sosai dabeyi xancen tafiya da Mimi ba. Shi kuma dariya yake mata a ransa.






Acan gidansu Mimi taci kwalliya kamar yadda ta saba tana jiransa, amma yau taga yayi lattin xuwa tunda sassafe yake xuwa. Kuma ko ita bai fada mata yau xai tafi ba.








Ta kalli a gogon wayarta, takwas harda kwata, shi da ya saba xuwa bakwai da rabi, to meya tsaidashi yau? Mama ta kawo mata awarar data saka aka soya mata da kwai tace "Mimi har yanxu bakici awarar nan ba sai ta huce?" ta kalli mama duk dauriyarta ta qare tace "mama kinga ya Bature shiru har yanxu baixo ba anya kuwa lfy?" mama tace "Mimi meyasa baki da dauriya kan sulaiman ne? Tunda kikaga bai xoba ai wani uxurin ya tsaidashi, nidai kici awarar karkisa inyi wahalar banxa." ta kalli awarar takai hannu ta faraci, sai dai sam batajin dadinta duk kuwa da itace tasa mama tai mata tun jiya.






8:33 AM yayi sallama ya shigo, suka gaisa da mama dake tsakar gida kana ya shiga dakin Baffa suka gaisa yayi musu sallama da cewa xai wuce yanxu. Mama dai sai da gabanta ya fadi, don tasan da wuya aiki be dawo baya ba, Mimi da tunkan ta ganshi take cewa xata tafi Abuja bare yaxo ya kwan biyu?








Yana shiga dakin mama Mimi ta taso ta rungumshi tana ajiyar xuciya, ya shafa kanta yana murmushi tabbas ta fada tarkonsa, game din kuma xai fara daga yanxu.






Ya jata suka xauna kan kujera yana murmushin Luv yace "Mimi nifa nayi harama wucewa xanyi" ta kuma shigewa jikinsa tace "cewa xakai wucewa xamuyi ai daka fadamun tun jiya na hada kayana" yace cikin jimami "ai banajin su mumy xasu bari muje tare, sunce sai kin haihu." ya zareta jikinsa yace "bari inje karnayi latti inason isa da wuri sai anjima my luv ki kula da kanki" ya saka takalminsa sau ciki yayi waje.








Tabishi da kallon mamaki, mekenan hakan? Ya fasa tafiya da ita kamar yadda ya fada mata jiya ko kuma dai mumy ce tayi masa fada shiyasa ta ganshi a sanyaye? A fili tace "tab wlh baxata sabuba, wai bindiga a ruwa" ta miqe da gudu tayi tsakar gida, har yakai bakin qofar da xata kaishi soro, mama kuma natayi masa fatan isa lfy dan hankalinta ya kwanta da taga ya fito kuma bataji wani raddi daga Mimi ba.










Ta rungumeshi ta baya tsam tace "ya Bature xan bika" ya juyo ya gyara mata kwanciya kan qirjinsa kana ya kai dubansa ga mama yana dan sosa kai yace "Mimi nima inason tafiya dake, amma su mumy sunfison ki xauna nan" tace "babu ruwansu damu, ai kafisu iko akaina muyi tafiyarmu mu kyalesu ni na warke" mama tayi mata daquwa tace "πŸ–πŸ»gidanku uwar marasa ta ido, wato babu ruwanmu ko?" Baffa ya fito xai fita, matan gidanma duk suka fito jin kulle kofar Baffa xasuyi masa a dawo lfy. Ya tambayi abunda ke faruwa, kafin mama tayi magana Mimi take jikin ya Bature tace "ni Baffa ya Bature nakeson bi, kuma su mama wai saina haihu." Baffa ya kallesu duk su ukun yace "to ni narasa bayan wanda xanbi cikin ku, in nabi bayanta(mama) kisamu gaba da rigima, ke kuma maryam innabi taki uwarki tahau fushi dani tace na barki kin tafi tunda bata da juriya a kanki" Anty tace "eh gaskiya ne sabida angama da kai ba, am maidaka namijin hotiho" Bature dai yana riqe da Mimi data fara kuka, yaga abun yaqi qarewa ya dakko waya yayi text wa Faty.








Mama tace "gaskiya Baffa kawai ka hanata tafiya" Mimi ta fara kuka da qarfi tace "mama ni gaskiya baxan xauna ba saina bishi" Baffa yayo mata daquwa yace "qaniyarki πŸ–πŸ» saidata gama wahala dake tun bakisan wanda ke kanki ba shine yanxu xaki gujeta" Rashida ta fito xata tafi aiki, ta kalli drama din da ake Mimi jikin Bature rungume ko kunyar su Baffa bataji tace a hankali "da gaskiyar ki Mimi, koni na samu irin wannan tsalelen mijin banga abunda xai xaunarni gida ba koda kuwa baya sona, bare ke abun burgewa bayan kyansa ga kudi uwa uba kuma son da yake miki"






Sunanan jugum jugum, Baffa sai lallaba Mimi yake ta haqura in ankwan biyu ya kuma xuwa tabishi, amma taqi yarda saima kuka da take Bature na lallabata.










Faty tai sallama ta shigo gidan, ko gaishesu batai ba ta kai kallonta kan Bature da Mimi dake riqe da juna. Ta miqowa Bature kujerar roba ya xauna, Mimi ta dane cinyarsa ta kuma qanqameshi. Faty ta matso kusa da Mimi, mimin ta runtse ido tace "ya Faty karki dakeni, ni ya Bature nakeson bi" ta shafa fuskarta tace "ba dukanki xanyi ba maryam duk abunda kikeso shi nakeso" kana ta shige daki.






Anty tace "to uwar iyawa da kwainane taxo yanxu kuma sai yadda mukagani" Bature abun ya bashi dariya amma ya gimtse, su wadannan matan kwata kwata basa girma.








Faty ta loda kayan Mimi a qatuwar jaka ta jawota ta fito da ita, ta koma ta fara fito da magungunan Mimi, suna kallonta. Tace "Mimi badai mijinki kikeson bi ba?" tace "eh" tace "toh maxa ga kayanki nan, Allah ya kiyaye hanya ya qara baki lfy" mama ta dubeta xatai magana.










Faty ta rigata da cewa "mama indai har na isa da maryam ki barta tabi mijinta, ku kalli Mimi da ya Bature kowa yana musu shedar sunada kunya, amma yau da kuke qoqarin rabasu kalli yadda suke xaune gabanku" mama jiki a sanyaye dan ta hango gaskiyar maganar Faty tace "kin isa da maryam fatyma, tunda kinyi hukunci suje Allah ya kiyaye hanya"








Umma baqinciki ya turnuqeta, dan ita bataqi ace auren Mimi ya mutu ba a yanxu kuma ta auri jafar ta xauna a qarqashin ikonta, dan tasan jafar baiko kama qafar Bature a dukiya ba balle Mimi taji dadi har tafi sauran yayanta. Kuma dama nufinta in auren ya mutu ko jafar bai nemi auran Mimi ba xatace yaje ya nema yadda xata gasa Mimi a matsayin surukarta ta cikin ruwan sanyi. Amma da alama burinta baxai cika ba ganin wannan sa-toka -sa -katsi da ake yanxu.








Cikin lumana da nuna soyayyar bogi tace "anya fadima kya daka ta Faty ku tura yarinyar nan Abuja bata gama watstsekawa ba? Kalli fa yadda muke fama da ita anan in ciwon ya tashi dukkanmu bare acan ita da miji kawai. Mama tace "to ya xanyi Umma? Kar inje in hanata binsa inya tafi ta tayarmun da rigima ta hanamu xaman lfy daga haka ciwo ya dawo" Umma cikin fusata da amsar mama tace "aikin banxa, ai duk laifinku ne. Kunbi kun shagwaba yarinya duk ta sangarce saikace yar shekara uku intana abu." ta juya ta shige daki cikin qunan rai. Suka bita da kallon mamaki, Anty ta saki shewa tace "toh? Ke kuma meye naki ciki khadimul shishshigi?"










Baffa ma ya wuce kasuwa, Mimi kuma ta dakko wata kujerar ta xauna gefensa Faty tana cigaba da fito da duk abunda tasan mallakar Mimi ne tana ajiyewa a waje.








Mumy ta shigo gidan baxata, takai kallonta ga Bature da Mimi dake tsakar gidan akan kujerun roba suna facing juna hannuwansu sarqe. Tai saurin dauke kanta, mama jin sallamar mumy ta fito tana cewa "Addah kece yanxu? Kodai kinada masaniyar tafiyar tasu ne?" mumy tace "jikina ne yabani anan ana daru da Mimi, har naje gurin aiki na kasa xama na taho" mama tace "ai kuwa dai taqi xama fafur gashinan an hada musu kayan tafiya"








Mumy ta harari Bature ta nufi dakin mama tana cewa "Mimi xo kiji kinji uwata" suka shige ita da mama, Mimi ta tashi xata bisu amsa kiran mumy Bature ya riqo hannunta yace "duk dadin bakin da mumy xatai miki karyi yadda, ki tubure ni zaki bi, in taqi kisaka ihu." Mimi tace "to ya Bature xanyi duk yadda kace" yace "dat is gud ma luv" ta shige ciki. Shi kuma ya qara miqewa kan kujera ya dora qafa daya kan daya yana dariyar mugunta, yasan ya dora Mimi ta hau tayi derere da wuya ta yadda da romon bakan su mumy.








Ya tashi ya shiga falon ya xauna su kuma suna uwar daki, kamar yadda ya xata mumy tasa Mimi a gaba tana mata dadin baki na ta haqura ta haihu sabida lfyarta da abunda ke cikinta, babu kalar lallashin da mumy batai mata ba. Ya kwashe da dariya harda kyakyatawa lokacin da yaji Mimi tace "mumy ai shima ya Bature yana kulawa dani, ni nafison mu tafi tare" mumy cikin quluwa tace "kenan kinfison shi akanmu?" ya saki dariyarsa a fili da yaji Mimi tace "eh nafison xama dashi donshi....." kafin ta qarasa mumy ta duma mata dundu, ta miqe tayo falo da gudu tana fitowa ya tare abarsa ya rungumeta yace "well done my dear" suka xauna suna qus qus dinsu ita da mama. Shi kuma ya raka Mimi kitchen ta dumama musu awarar da mama tai mata a microwave ta tsiyayo musu kunu a cups suka fito falo suna ci cikin nishadi.








Mumy ce ta fara fitowa ta gansu, taso su hada ido da Bature tai masa harara amma yaqi yadda su hada idon yayi qasa da kansa, ta matso kusa tace "ai dama nasan kaine ka hure mata kunne shiyasa taqi xama" mama tana fitowa tace "itama da halinta Adda, tunkan yaxo take cemun xataje Abuja gurinsa"










Mumy tace "to tunda kun nace sai kun tafi tare saiku bari xuwa gobe nayi waya garko Yadukko taxo kuje tare kuma nayiwa Aisha waya ta dawo ku tafi tare. (yadukko yar uwace ta kusa ga hajja kakarsu Mimi, takanxo lokaci xuwa lokaci kano gurin hajja ta kwan biyu ta koma don mijinta ya mutu kuma tagama aurar da yayanta kaf) yace "to mumy muna godia" sai alokacin ta samu damar fallara masa harara tace "ka dena murna, don rahoto xan tura yadukko yimun, tana fadamun abunda baimun ba xanxo in taho da ita" yayi shiru yana sosa kai.






Yinin ranar suna maqale da juna cikin dakin mama, yayin da maman keta faman hadawa Mimi kayan da duk take ganin xasuyi mata amfani intaje can. A daren yadukko taxo Aisha ma ta dawo, tanaji mama na cewa yadukko dan Allah ta kula da duk lokatan shan maganin Mimi da kuma turare karta bari Bature ya hana aiwa Mimi turaren. Yadukko dake over acting ce tace "shidin banxa ya hana? Dako naci qaniyarsa." mama tana dariya tace "yawwa yadukko" tasan bata da wasa shiyasa suka yanke shawarar dakkota ita da mumy.








Washegari da safe mumy taxo, taxo da kaya niqiqi tabawa Mimi tayi tsaraba. Aka hada da kayan da mama itama ta siyo mata aka cika highlander dinsa taf da kaya har sai da motar tai qasa. Mimi tasha kwalliyarta cikin sabon lace din da Faty ta kawo mata jikinta har rawa yake xasu tafi, bakinta kuma yaqi rufuwa.








Mama jikinta yayi sanyi da wannan rawar kan Mimi, sai take ganin kamar ajali ke kiranta in banda haka ai Mimi mai tsananin kunya ce. Mumy ma tunaninta kenan, itadai kam wannan tafiya bata kwanta mata ba dandai babu yacce xatai ne.






Wajen qarfe tara suka gama shiri tsaf su yadukko da Aisha har sun fita sun shiga mota, su Mimi ake jira da suke sallama da iyayensu. Jikin mama ya kuma sanyi lokacin da Mimi hartakai qofar fita ta dawo ta riqe hannun mama tace "mama ki yafemun" mama tace "bakimun komai ba maryam" tayi murmushi tace "ni dai kawai ki yafemun" tace "na yafe miki maryam Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi" ta juya ta riqe hannun Bature dake tsaye bata qara waiwayowa ba suka fita. Mama ta faki idon mutanen dake tsakar gidan ta share kwallah. Mumy kuwa kasa daurewa tayi ta bisu waje.








Ta samesu suna shirin shiga mota ta kalli Bature taci serious tace "sulaiman ga maryam nan, amana, duk sanda ka dubeta ka tuna cewa ita din marainiya ce." ya xago ya dafa kafadar mumy yace "na karbi amanar ki, in shaa Allah baxan baki kunya ba" ta rungumeshi shi da Mimi ta juya ta koma ciki.








Sun daura sit belt ta dubeshi ta dafa hannunsa tana murmushi tace "SULAIMAN meka tanadarmun a gidanka?" ya kafeta da ido yace "MARYAM soyayya, qauna, kwanciyar hankali da kuma kulawa wacce baki taba ji ko gani ba. Sune abunda na tanadar miki in shaa Allah" ta murmusa suka sarqe hannyensu tace "Allahu yasha'u"






Su yadukko dake bayan mota sukace "amin" yayi Addu'a ya tada mota suka hau titi.








Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ



Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)




πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }


Page 6⃣4⃣




Dedicated to
ANTY SIS




Sun isa lfy, sukayiwa kano waya suka sanar, sai a lokacin mama ta samu kwanciyar hankali tacigaba da harkokinta.






Mimi tayiwa Farida waya ta fada mata sun dawo, babu jimawa suka shigo da ishaq. Mimi da Farida suka rungume juna suka sa kuka kana suka furta sunan juna a tare.






Bature ya fada musu yadda ya dakko Mimi, ishaq yana dariya yace "shege sulaiman kasan takan tsiya" yayi dariya yace "ai mumy bata barni haka ba, sai data hadoni da wata kakarmu yar tijara muka taho tare" haka suka xauna sunata hira, ya tashi yayi wanka ya shirya suka fita da ishaq yace da Mimi xaije ganin wani gidan mai da yakeso ya siya. Yayiwa safna waya, tana gurin aiki yace inta dawo ta biyo gida gurin Mimi ta tayata gyara bedroom dinsu.








Safna tana dawowa ta shigo suka hadu ita da Aisha, suna gyara dakin Mimi na xaune sun hanata komai sunce ta huta.






Suka gyara dakin tsaf safna ta ware kayan wanki ta hada wadanda suke buqatar sirri ta xuba a washing machine ta wanke ta shanya suka fesa turaruka masu qamshi. Sai yamma suka tafi.








Bai dawo gidanba sai goman dare, lokacin harta gaji da jiransa. Ya shiga wanka, ta bishi bathroom din, ta sameshi a bayan labule cikin shower ta rufe masai ta xauna akai tace "ya Bature har yanxu baka gama ba?" yace "eh Mimi luv, kinsan yau ango nake dole in cuccuda sosai" tace "hmmmm" kawai, ta gaji da jiransa tayi brush dinta ta fita taje tai shirin bacci ta kwanta.






Tajishi jikinta yana lasarta, ta watstsake ta kunna bed side lamp ta dubeshi. Ya sakar mata murmushi yace "Mimi luv ya kika tashi?" ta tureshi, ya qara shige mata yana romancing dinta tace "Stop it" yace "haba Mimi luv yaushe rabon da mu kasance haka" yacigaba da abunda yake, tace "fyade xakaimun ya Bature?"








Jim kalmar fyade data ambata ya tsaida abunda yake yana dubanta. Ta qara da cewa "lokacin da nake buqatarka ranar a kano ai qi kayi, amma yanxu dake kaine kake buqata kana qoqarin forcing dina" jikinsa sanyi qalau yace "wlh Mimi bana qi biya miki buqatarki bane wancan lokacin don toxarci ni kaina a lokacin ina da buqatar data fi taki. Amma na tuna cewar wancan lokacin kinqi na tilasa kika samu lalura shiyasa na haqura karnayi ciwonki ya tashi." ya janyota ya rungumeta yace "Mimi tun a wancan lokacin nayi alqawari baxan kuma ba, nayi na farko kinyi ciki, na biyu kinsamu lalura in shaa Allah baxan na uku ba dan bansan abunda xai faru ba" ya kashe masu fitila suka kwanta, sai taji tausansa. Tayi bacci ta barshi shikam sai da yayi da gaske ya runtsa.








Washegari bayan sunyi karatunsu na al qur'ani ya motsa jiki yaxo ya kwanta, ta dubeshi tace "yau baxaka fita aiki bane?" yace "nayi dauki hutun 1 wk" Yadukko tayi knocking tace "maryam fito kiyi wankan an sauke ruwan." tace "to" ta fita sukayi wankan harda turare ta dawo, ya dakko xumarta ya bata tasha suka koma bacci. Sai 10:00 AM suka tashi sukayi wanka da breakfast ya fita gurin cinikin gidan man. Kafin ya fita saida ta tabbatar Anty Rabi da Farida suka shigo.








Ranar ma cikin mutane ta yini dan safna ma ta kuma shigowa, sukayi ta riritata, ya Taheer ma ya shigo daya taso aiki. Safna har tausa tai mata, Mimi tana cewa "haba Anty safna ki bari mana Aisha taimun" tace "barni nayi miki matar yaya dan da bakyanan munga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login