Showing 135001 words to 138000 words out of 205258 words

Chapter 46 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

dan iska yana zaginta da goranta mata, amma kuma duk abunda Badaru yayi bashi da laifi, shine babban mai lefi da bai riqe su da daraja ba kuma ya nuna maryam din ba wata bace.




Tausayin Mimi da soyayyarta ta dirar masa nan take, dole Mimi tace bazata koma gidan Badaru ba saboda ya zalunceta sannan ya biyota da sharri shi kuma ba bincike yahau ya xauna. Jin soyayyar Mimi yake har cikin bargonsa kuma yaji yana kunyar hada ido da ita da uwarta.






Badaru na zuwa gida ya samu Nafee a parlour tana kallo, ya kalli parlour komai kaca kaca ya kalleta da yake a kusa yake neman masifa yake sai yace "ke haka ya dace kibar guri ki xauna kina kallo dake ke jaka ce?"




Ta kalleshi sheqeqe tayi dariya tace " jakai dai, ni da kai in ban gyara ba kai baka da hannun gyarawa?" kafin ta ida fada ya kifa mata mari.






Batai wata wata ba ta dakko plate din da ta gama cin indomie yanxu ta jefa masa tana huci, sannan ta dora da cewa "ga dukkan alamu ka saba ganin tsohonka na jibgar gyatumarka shine kazo xaga gwada a kaina, to wlh duk randa ka qara dukana wlh saina sake maka kaciya 😳"






Ya tsorata da mutuqa da maganar Nafee, bece uffan ba ya shige bedroom dinsa, ya rasa abunda yake masa dadi. Shi yanxu yasan duk wanda ya fadawa abunda Nafee ke masa dariya zaiyi saboda yacce ya daukaki Nafee. Ya dunga juyi akan gado ya kasa bacci, har akai sallar laasar bai fito ba ga yunwa na addabarsa kuma yasan Nafee yau bazata bashi abinci ba. Ya tashi yayi wanka yayi sallah, ya zabo kayansa na qure adaka yasa. Gurin maryam xaije ya bata haquri ya nemi yafiyarta, yasanta da sauqin kai xata haqura su koma aurensu.




Ya samu Nafee zaune ta cokala dauri ture kaga tsiya tana sanaar (kallo), ya tsaya domin yayi mata magana, ta dauki remote ta qure volume alama batason jin abunda xaice, dan haka ya fice.






Ya dade a qofar gidan Baffa babu dan aike kuma bashi da no Mimi. Mimi ta fito domin zuwa gurin fauxa, tana sawo kai waje idonta cikin na Badaru gabanta ya yanke ya fadi ta diririce, ta juya da nufin komawa gida yayi wuf ya damqe hannunta yajata cikin sit room din dake soron farko.






Cikani, baka da hankaline xaka riqe mani hannu? "ta fada cikin fita hayyaci. Ya sassauta riqon da yayi mata, amma still yana riqe da ita karta gudu ya fara magana murya a kwance " maryam dan Allah kiyi haquri nasan na bata miki naci zarafinki na hadaki da iyayenki na tauye haqqinki na kuma toxarta ki. Amma wlh nagane kuskurena abaya na aureki ne dan shaawa amma xaman da mukai da ke nagane kyawawan halayenki da son addininki hakan ya jawo miki soyayya a gurina." Mimi tayi sakato tana kallonsa wai dama Badaru ya iya magana a hankali? Kuma dama yasan duk abunda yake ba dai dai yake ba? Tambayar da takewa kanta kenan.




A bangare guda kuma Baffa dake azumi (azumin kaffarar rantsuwar da yayi ta Mimi saita koma gidan Badaru, ya fara yau) ya dawo gida da wuri domin ya kawo salad din da yakeso a kwada masa yayi buda baki dashi. Yana xuwa soro aci burki dan jin maganganun dake fitowa daga sitroom. Da farko bai gane mai maganar ba, amma jin an ambaci sunan maryam ya gane me maganar da inda maganar ta dosa. A fili yace lallai wannan yaron bashi da kunya bari inje inyi masa tsakani da yata.






Sai dai muryar Badaru ta katse masa hanxari inda yaci gaba da cewa "maryam ki tunano rayuwar auratayyarmu me dadi πŸ™ˆ, ke bakya tunawa? Wlh kullum cikin kewarki nake da mafarkinki, ki dawo muje mu zauna duk abunda kikeso zan miki duk yan uwanki na gidan miji ke kadaice kika rage, kin wuce xaman gida ki dawo dakinki shine rufin asirinki"








Ta katseshi da cewa "xaman gidanmu yafiyemun zaman gidanka, kuma lokacin da sakeni ka wurgoni kofar gida baka duba cewa na wuce xaman gida ba sai yanxu? Rayuwar auratayya kuma da kake fada kaika santa har take maka dadi, abunda kawai zan iya dorarwa aciki shine: fyaden da kakemun duk daren duniya. Abubuwan kuma da kayimun a duk xamanmu na barka da mahaliccinka shi zaimun sakayya." tana kaiwa nan ta fusge hannunta ta kifawa Badaru mari, kafin ya gama mamaki ta kifa masa wani 😳.






Ta dora da cewa " yau alqawari ya cika, lokacin daka mareni a gidanka na fada maka cewa wlh saina rama gashi kuma na rama din. Zagin ubana kuma da kayi kace inje in haqoshi a kabari, bazan rama ba, domin nasan darajar iyayena sannan nasan duk daren dadewa naka uban xaije inda nawa yaje. Gida kuma basai nace karka kuma xuwa ba, saboda bata dalilina ka fara xuwa gidanba."






Baffa dake sauraransu yayi murmushi cikin jin dadin abunda Mimi tayi yace "yar halak kenan, tayi alqawari ta kuma cika maryam jinin Al amin ce domin ga halinsa nan a jikinta.


Ta fito ta koma gida memakon gidansu fauxa da tayi niyyar xuwa, shiyasa bata kula da Baffa ba dake tsaye a qofar fita. Badaru ya gama mamaki ya jawo qafafuwansa jiki babu kwari yayi hanyar waje, yaci karo da Baffa. Baffa ya nunashi da yatsa yace "karka kuma xuwarmun gida, in kuma ka kuma xuwa xan hadaka da hukuma" yana fadar haka ya shige gida.






Washe gari lahadi da yammaci aka aiko kiran Mimi, har taqi fita mama tace taje in Badaru ne taxo ta fada mata. Sai dai me tana fita taga Badamasi a tsaye. Tana ganin mutuncinsa dan haka tai masa iso sit room.




Ya xauna suka gaisa a mutunce ta tambayeshi mutan gida da gurin aikinsa. Yayi farin ciki ganin maryam din ta fara dawowa hayyacinta ba kamar lokacin da tana gidan Badaru ba, ya dunga hasketa da murmushi yana kuma jinta a xuciyarsa. Yayi mata jajan mutuwar aurenta, tace ba komai iyakacin xaman da Allah ya nufa kenan.




Ya karanto mata abunda ke cikin xuciyarsa, ta dunga kallonsa a kidime ba tace komai ba ta miqe da nufi fita. Yayi saurin shan gabanta yace "maryam wlh babu inda xaki sai kin fadamun matsayina a xuciyarki, inbaki manta ba nina fara sonki Badaru furtawa ya rigani indai ba so kike inyi hauka a kanki ba ki amshi soyayyta" itadai babu baka sai kunne, domin kanta ya daure da yawa.




Da yaga taqi magana saiya kamota ya sata a bango yayi mata rumfa da qirjinsa yasa hannu ya katangeta ta inda duk motsin da tayi saita taba jikinsa. Yakai fuskarsa dab da tata ya fara magana "Mimi ki laluba xuciyarki bazaki rasa soyayyata aciki ba, ba halinmu daya da Badaru ba soyayyar da nake miki bazata bari in cutar dake ba, xan kula dake xan baki yancinki, xakiyi duk abunda kikeso, bazan tauyeki ba irin rayuwar da kike mafarki xakiyi. Maryam fargabar me kikeyi? Bazan akiyeki kusa ba balle a dunga yi miki surutu, can gurin aikina xan tafi dake sai dai kixo da yawo."




Ganin cewa kamar baya cikin hayyacinsa yasa tayi niyyar yimasa dabara. Dan haka tadan dauke kanta daga fuskarsa, yayi saurin dawo da fuskarta kusa da tasa har tanajin numfashinsa, yace "yimun magana a haka in san cewa mafarkina ya kusa xama gsskiya." tayi qasa da murya tace "kadan bani lokaci inyi tunani inkuma yi istikhara"




Tunda ta fara magana, ya lumshe ido yana shaqar hucin bakinta. Sai data gama sannan yace "to shikenan, xanso hakan nima kuma nima zanje inyi sallatul istikhara. Saboda haka wani satin xan dawo saboda gobe xan koma Dutse" ya dakko kudin da ya ware zai bata 10k ya lalubi hannunta ya manna mata.




Ta kalli kudin ta kalleshi tace "ai basai ka bani kudi zan soka ba." ya kalleta hankalinsa ya kuma kwanciya da ita yace nasani maryam amma ai kyauta ce. Tace "nasani amma ka riqe wata rana ka bani" yayi murmushin cin nasara yace "to my soul"


Ya nemi ta bashi no dinta tace wayar na gida kuma bata ruqe no dinba, dan haka ya bata tasa xata kirashi. Dake ya makance a soyayya be gane cewa wayo taimasa ba, ba musu ya dakko katinsa na gurin aiki ya bata.




Mama tayi matuqar kaduwa dajin wai Badamsi keson Mimi, tace "duk da ba haramun bane ai ana barin halak dan kunya, kuma naji dadi shine gari. In shaa Allah ko wanda sunansa ya fara daga BA bazaki auraba. Yazaki qara fita yayi haukansa ya gama"






Ranar litinin ranar Baffa ya dau azuminsa na qarshe, kuma yau ya shirya tunkarar mama akan fushin da take dashi.




Da yamma ya shiga har dakinta, ya sameta xaune a kan kujera Mimi tana kwance tayi pilo da cinyarta tanacin chocolate. Tana ganinsa ta miqe daga kwanciyar, mama tace mata Mimi shiga ciki. Ba musu ta shige bedroom din.






Baffa ya xauna ya fara da bata haquri akan dukkan abunda ya dade yana yimata da kuma godia akan tunasar dashi da tayi, kana ya dora mata da abunda baban Badaru ya kawo masa yaji a waya da kuma abunda yaji da kunnensa Badaru na fadawa Mimi. Yace yagane kuskurensa kuma ya canja daga yanxu, kuma Dan Allah ko anan gaba taga yana nufin kauce hanya a wani abun tayi gaggawar tunasar dashi, domin yagane itadin macen arxiqice. Sannan yayi mata xancen tumunin takabarta yasa an fitar mata a kotu tasamu gidaje biyu da wajen miliyan biyu (saboda andade ana juya kudaden) ya karbi acct no ta da nufin tura mata kudaden ya kuma danqamata takaddun gidajenta.




Ya kwallah Mimi kira, ta fito ta tsuguna. Rayuwa kenan duk wanda yayi haquri zaiga haske domin wai yau Baffa ke neman yafiyar Mimi da kuma bata haquri akan abunda duk ya faru a baya.




Mimi tana hawaye tace "komai ya wuce Baffa, kai ubanane duk duniya bani da wanda ya fika, nima ka yafemun abunda nayi maka rannan saboda bani da xabi sai hakan shiyasa nayi" yace baki komai ba MARYAMU Allah ya miki albarka ya baki abokin xama nagari sakamon biyayyar da kikaimun.




Mama na gefe na share hawayen farin ciki, ta dunga godewa Allah. Tace da Baffa nagode da kulamana da dukiya da kayi. Amma inaganin wadannan ka karba ka riqemun."




Yace "riqe abunki Haj Fadima, nadai riqe na yayana Faty da maryam kuma suma na rubuta da shedu saboda halin rayuwa, gidajen dai xantsaya a xuba yan haya." tace to duk yadda kayi nagode.






Yace " to ai bazan yadda kin huce ba sai kin karbi girki, ga cefane can nakawo inaso aimun special girki dan azumin nake kuma nadade banci delicious dinki ba."






Mama ta miqe tabi bayanshi tana dariya tace " yau kuwa xakici domin xan tabbatar maka na huce." Umma da Anty da tunda ya shiga dakin mama suke tsaye suna jiran suga abunda xa ai suka qiqim qiqim ganin mama da Baffa tare suna dariya. Mimi ma ta biyo bayansu da nufin taya mama girki itama tana tata dariyar.




Mrs 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ




πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }

Writing & story by
Rahma Muhammad {hajia}


Editing by
Mmn khairat 😍



Page 1⃣4⃣




Cike da farin ciki Baffa ya shiga gidan, gami da kwalawa mama kira tunda daga tsakar gida, ta fito a gigice saboda Jin kiran farautar da yake mata ta iskeshi daki gami da yimasa sannu da xuwa. Ya amsa yana washe baki kamar bebe yaga wawan zama (Lol) sannan ya dora da cewa wani abun farinciki ne ya samemu fadima shiyasa ki ganni gida yanxu, wato yaronnan dan wajen Alh Inuwa shine yaga Maryamu yace yanaso, kuma ga dukkan alamu akusa sukesan auren dan Alh inuwa da kansa yayimun maganar ni kuma nayi dattako nace kawai in sun shirya su kawo kayan aure kawai ayi. Mama ta kalleshi shagarai tare da daure fuska tace, Alh wannan wane irin neman aure ne sai kace auren yar tsana? Daga yaro yaga Mimi yace yanaso sai ace ya fito anbashi? Ita mimin baza aji raayinta ba? Kuma banaji ma Mimi tasan maganar domin da tasani xata fadamun, sannan shin kayi bincike akan yaron? Ko kuma dan ansan mahaifinsa shikenan? Aure fa in anaso a zauna lfy sai anyi da yardar maauratan, kuma naga ai bakai da Alh inuwa ne zakuyi xaman auren ba, yaran ne masu xama saboda haka inaga ku basu dama su fahimci juna inyaso daga baya insun dai daita kwa shiga lamarin. Baffa dake kallon mama tun da ta fara magana a dage tare da fallara mata harara wacce ita sam bata kula ba, ya magantu da cewa sai yanxu nasan ke babbar mahaukaciya ce fadima. Ta miqe tsaye tare da qara daure fuska tamau tace hauka kuma? Yau kuma nice mahaukaciyar? Nan da nan kuwa ya dai daita nutsuwar domin ya farga da kasassabar da yayi (ya tuna da fadima yake magana wacce Sam bata daukar irin cin mutuncin da yakewa ragowar matansa, ta nuna masa tasan ciwan kanta dan haka ko fada xai mata yakan tausasa kalamansa) dan haka yanxu ma sai yayi saurin yin kwana da cewa ai kece naji kina qoqarin yiwa Allah butulci, shekarar maryam din nawa ana neman miji? Ba a taba budurwa mai shekarunta ba kaf danginki da nawa, sai yanxu Allah ya kawo kice ga xance ga magana. Ta kalkeshi tace ni ba butulu bace kuma ba butulcewa nai ba inaso ne dai a gina auren akan fahimtar juna da soyayya, amma tunda haka kace shikenan Mimi yarka ce kana da ikon xaba mata miji, Allah ya sanya alkhairi yasa tsohuwar gida ce. Yawwa yanxu kikayi magana fadima da tun farko abunda kikace kenan ai da ba a tsaya sa insa ba, amin Allah ya yi miki albarka cewar Baffa.


Maryam kwance saman gadonta acan hostel na law skul rubda ciki take tana danna system, qarar Waya ya katseta daga typing din da take a system din, ta tsurawa screen din wayar ido gabanta na dukan 3 3 , tun tana qanqanuwarta ta tashi da tsananin tsoron Baffa da kuma dison qiyayyarsa acan qasan zuciyarta saboda halin ko inkula da yake da al amarinsu, duk da cewa mahaifiyarsu awancan lokacin tana boye musu lamarin baffan garesu kafun su girma su gane, sai kuma alokacin mama take yawan cemusu halin Baffa garesu ajixanci ne irin na Dan Adam. Amma AL AMARIN MARYAM na jinkirin aure da kuma takura gami da gorin Baffa akanta yasa dison qiyayyar Baffa ta samu girma a zuciyar maryam wanda takai tayi yado ta zama tamkar bishiya mai rassa, domin ji takeyi kamar ta raba auren Baffa da mahaifiyarta domin auren Baffa ba abunda ya qari mama dashi sai muzgunawa da gori daga gurin matansa daga gareshi kuma xa a iya kiran abun da yaudara domin kulawar da take kwadayin yayanta su samu inta aureshi basu sameta ba. Wayar ta sakeyin qara akaro na wajen 4 wanda hakan ya yankewa maryam tunaninta, tai shahada ta daga wayar. Ta gaisheshi cike da tsoro da firgici, ya amsa farai farai tare da tambayar karatunta da kuma lokacin kammalawa, lamarin daya daure kan maryam tamau, acikin ranta ta farta Baffa da tambayar karatuna? 😳 first in history.


Bayan hakanne kuma ya zayyano mata dalilin kiranta a waya akan maganar Badaru, sai da ta nutsu kwarai sannan ta gane wadanda yake nufi domin ita tamanta da haduwarsu, amma kuma tayi mamaki dajin cewa wai har ana zancen qarbar kudi ba tare da sun zanta da wanda ya nuna raayin a kanta ba, (domin ita a zatonta wanda yayi mata magana shike sonta wato Badamasi) amma da yake mama batai musu tarbiyyar ja da maganar Baffa ba sai kawai tace masa to Baffa Allah ya xaba mana abunda yafi alkhairi, yaji dadin furucinta kwarai ya dunga samata albarka. Koda ta kashe wayar tunani ya cikata to meyasa yaya Faty da mama babu wanda ya mata maganar ko dai suma basu sani ba? Sannan ta shiga wassafa siffar guy din da azatonta shine Badarun, ta dan tabe baki 😏 tare da furtawa a fili "yayi babu laifi he is handsome " amma ba irin mijin da nake mafarkin samu bane duk da bashi da muni amma bashi da tsahon da nakeso daga da namiji " πŸ™ˆ ta rufe idonta cike da kunya kamar wani yana ganin. Wannan dare dai haka ta qareshi cikin tunanin irin nata salon neman auren cikin gaggawa wato haka Allah ya shirya mata kuma dama fauxa (wata qawarta yar unguwarsu) tasha fada mata in Allah ya tashi bata miji in shaa Allah gaba daya zai fito jinkiri zai kawo mata alkhairi, ta miqe cike da farin ciki da kwarin gwiwa ta dauro alwala ta tada sallah aranta tana cewa ashe nima zanga ranar aurena, ashe ankusa a daina yimun gorin aure 😊.

Ranar jumaar data kasance aranar aka karbi kudin auren Mimi da kuma lefe, da misalin qarfe 2:30 pm Faty ta shiga dakin babarta afujajan, daga gurin aiki take. Yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login