Showing 6001 words to 9000 words out of 205258 words
Chapter 3 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt
koma kalar yan can.
Ana cikin hakan girki yaxo kanta kuma a daren ya nuna zulamarsa akanta wanda hakan yasa ta dunga kurma ihu har mutan gidan suka tashi suka firfito tsakar gida, kunya ta hanashi fita baqin ciki yasa ya jawo wayar radio ya dunga tsula mata yana kwallo da ita har sai da yaji ya huce ya kyaleta. Anatada sallar asuba a masallaci ya fita itama ta tashi tasa hijabinta tasa takalma ta fita, lokacin data isa tasha gari ya fara shaaa, tashiga motar Kano bata da ko sisi tayiwa direban motar bayani bata da kudi amma insinje Kano zata bashi ya kaita har gida yayi shiru yana kallonta can yace ke yar Mal manu ce? Naga Kama, tai saurin cewa eh ni yarsa ce fadima yace to lfy naganki haka kuma anan? Tai shiru sannan yace bakomi mun taba aikin mota tare dashi ashe yata ce muje ba komi har gida xan kaiki. Kafin motar ta cika ya sai mata shayi da bread Shayin kawai ta iya sha tana Allah Allah motar ta cika sutafi dan gani take kamr Mal Ali xai biyo bayanta. Da haka motar ta cika suka daga.
Mrs Muhammad π
ππΌππΌππΌAL 'AMARIN MARYAM ππΌππΌππΌππΌ
8β£
Azahar a cikin gidansu tai mata direban motar daya kawota ne yayiwa Mal sulaiman halin da ya ganta aciki, yayi masa godiya ya shiga da fadiman cikin gida. Ransa ya baci kwarai da yaga kwanciyar bulala ajikin ta kota ina, haka aka dunga biqinta har ta warke yayyunta maza sukace aure anyi angama. Sai dai har fadima ta share 3wks a gidan Mal Ali bai nemeta ba, hakan yasa Mal sulaiman ya nemshi cikin xafin rai yanuna masa bacin ransa kan abunda yayiwa fadima, shima Mal Ali cikin nasa xafin ran ya balbale Mal sulaiman da nasa fadan tare da cewa yar tasa ragowar wani da bata da mutunci yaje ya saketa. Jikin Mal sulaiman yayi sanyi kwarai ya tara yan uwan fadima ya fada musu kuma ya nemi yafiyarta. Dama duniya makarantace Wannan avun shiya koyawa Mal sulaimn hankali ya lura cewa bada fadima sadaka bashine mafitaba gara yayi haquri har Allah ya kawo mata wanda xai sota a yanda take. Saboda haka ya bawa yan uwanta damar da suka dade suna nema a kanta, suka sakata a makatanta library ta fara xuwa inta tashi ta shiga ajin koyar sana a dinki da saqa.
Bayan shekaru 2 fadima ta goge sosai kasancewar ansakar mata mara tana fitsari babu takura, ta goge ta cika ta xama cikakkiyar mace tuni ta kware akan dinki takan dan taba saqa amma tafi maida hankali akan dinki, ta bangaren karatu kuma ta kusa kammala primary.
A na cikin hakan suka hadu da AL amin a lokacin yana service (bautar qasa) ta dawo daga skul suka hadu ahanya ya bita har gida, Sun fara soyayya ya mace akan kyakykyawa fadimatu itama tana qaunar Guy din amma tana dari dari saboda kar yaji abunda ke tare da ita, saboda haka ta kwashe komai ta fada masa kafin asamu wani daga waje ya fada masa. Ga mamakinta saiya tausaya mata tare da bata tabbacin wannan bazai rabasu ba,
Bayan dogon dauki ba dadi da kai ruwa rana da aka samu ta bangaren AL amin. Saboda a cewar Baffa Buhari bazai auri bazawara ba sai dai ya samo wata tunda yace bayason husna qanwar hajara, shi kuma AL amin din ya kafe yace ita yakeso, duk da Baffa ba ra ayinsa bane, zugar hajara ce kawai ke aiki dashi kasancewarsa namiji mai daukar xuga, shidai kawai ya tsani fadima tun kafin ya ganta saboda yanda yaga Dan uwansa na qaunarta , wannan ra ayi nasa ya hadu da xugar hajara ya jawowa fadima tsana sosai a gurinsa, a bangaren hajara kuma ji take kamar ta kashe fadima tun kafin ta ganta, gashi alokacin anmata kishiya wato Anty jamila abun ya hadu yayi mata yawa. A karshe dai Allah yayi ikonsa domin AL amin da Fadima sun kasance ma aurata.
Ta haifi yarta fari Mace ya maida sunan matarsa, wanda hakan ya kuma janyowa fadima qiyayya a gurin Baffa da matansa, saboda hajara tayi masa famfo cewa kamata yayi AL amin din yasa sunan mahaifiyarsu amma yasa sunan shegiyar matarsa. Xuwa wannan tym din gidan Baffa ya fara cika da yaya kuma arxiqinsa ya bunqasa kwarai da gaske ya gina qaton gida me part 4( gidan da suke ciki yanxu) gida me kyan gaske ginin irin wancan xamanin da daku 2 asoro na mazan gidan da seat room daga waje da rila xagaye da gidan. Tun lokacin da aka auro fadima ta tadda yara 7 a gidan 5 na hajara 2 na jamila, daga baya suka fara competition din haihuwa, a inda nan da nan suka cika gidan da yaya maza da mata amma matan sunfi yawa.
AL amin yasamu aiki a tun farkon aurensu a inda yasamu aiki a jamiar da yayi karatu wato ABU kuma yana ci gaba da karatunsa, agefe kuma yana taba aiki a wata chamber kasancewarsa lawyer, suna zaune a unguwar sharada fadima ma tana cigaba da karatunta AL amin ya tsaya mata da kansa inyana gari yakan koyar da ita, ga kuma sana arta ta dinki tanayi.
Bayan shekaru 5 da haihuwar Faty ta haifi MARYAM taci sunan mahaifiyar fadima kenan suke kiranta (Mimi). AL amin ya kasance mutum mai mutuqar San iyalinsa yanasan yayansa kwarai, yakance in Allah ya yarda Faty ma aikaciyar jinya (nurse) Mimi kuma yakance shixata gada wato lawyer, in ya fadi haka fadima kance Allah ya rayaka Barrister ya kuma yara maka sister Faty da Barrister Mimi . Yakance amin amin fadimatu.
Mimi nada 4yrs ya jefata a skul sai dai ita sabanin yar uwarta miskilace kuma mai yawan lalura da fari Sun sikila ce sai da suka je asibiti sukaji sabanin haka domin bincike ya tabbar da A S ce, kawai dai Allah ya halicceta me lalura. Alokacin kuma fadima takuma samun wani cikin, cikinta na wata 6, Allah ya dauki ran AL amin a dalilin hatsari da yayi a hanyarsa ta koma Zaria gurin da yake aiki, mutuwar ta girgiza fadima da Baffa Buhari kwarai da gaske a dalilin mutuwar fadima tai haihu lokacin haihuwar beyiba ta haifi jariri dan wata 6 babu rai. Bayan 40 Baffa ya buqaci a bashi yayan AL amin, da farko fadima da danginta sunqi amma daya kafe cewa dole ta bashi domin baza a tafi da yayan dan uwansa wani gidan ba da sunan aure.babu kunya da lokacin da yan uwan fadima maza suka nemi xama sulhu yace in fadima ta matsa tanasan rayuwa da yayanta ta aureshi taje ta riqe yayanta, lamarin da taqi yarda sam saboda tasan halin matansa da yadda suka tsaneta a matsayin faccala bare kuma ta xama kishiyarsu, sannan kuma ita bazata iya cin amanar AL amin ba ta auri wansa. Shi kuma yayi amfani da wannan damar ya kwace yayanta yakai gidansa ya watsar. Kunji yadda lamarin ya kasance.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌAL 'AMARIN MARYAM ππΌππΌππΌ
Writing&story by
Rahma Muhammad {hajia}
Editing by mmn khairat π
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Pege9β£
Maryam (Mimi) da Faty, Sun taso kai daya kasancewar Mimi mai garun jiki saita xama kamar saar Faty, baxaka taba kallonsu kace Faty tabawa Mimi tazarar shekaru biyar ba. Faty ta kasance fara sol kyakykyawar mace sosai doguwa mara jiki, kamarsu daya da uwarta sak mai yalwar sumar Kai. Yayin da Mimi ta kasance doguwa me murjajjen jiki me cikar halitta, bata da qiba Sam amma duk inda ya kamata ya xamo me cika ajikin mace kamarsu qirjinta da kuma hips to ajikin Mimi dai sai Masha Allah, dangane da skin colour kuwa Mimi wata irin colour ce ba fara bace kuma ba baqa bace ko kadan, itadai gatanan kamar ruwan xuma ( honey colour) fatarta me daukar hankalice irin colour din dake matuqar tsada a duniya, a taqaice dai xamu iya kiranta Kalar bargon kaza. Bata da wani shaharren kyau a fuska irin na yar uwarta komai nata a fuska tsaka tsaki ne inka cire manyan iduwanta farare tas, sai kuma haqoranta farare tas dogaye ,itama tana da gashi sosai koma ince duk jikinta gashi a kwance ( irin matannan masu gargasa) har fuskarta gashi ne a kwance tun daga gaban goshinta xuwa sajenta har xuwa qeyarta. Amma gashin mai qarfin gaske kamar izgar doki ga cika ga tsaho wanda yasa dole mama take mata retouching tun tana qaramarta inba hakaba baya kitsuwa yanka hannu yake. Itakam tafi kama da AL amin (mahaifinta) inka kalleta tsaf komai nata sai kaga tana kama sosai da SASHA OBAMA ( yar Barrack Obama) kai kace sun hada dangantaka, babu a bunda ya hadata da yar uwarta Faty ta bangaren kama sai muryarsu da take iri daya sai kuma dimple (beautiful point) din da suka gada ta bangaren uwarsu, domin yawanci yaya da jikokin gidan sunada shi. Wannan kenan.
Sun taso da mutuqar soyayyar junansu, hakan baya raba nasaba da adduar mama domin duk sanda tasa goshinta a qasa tana adduar Allah ya hada matΓ‘ kan yayan nata kamar yadda ya hada nata da Adda halima, domin su kadai Allah ya bata (bata haihuba a gidan Baffa). Dayake Allah maji roqone ya amsa mata, ita kanta tana alfahari da yayanta inta kallesu tana tasbihi ga Allah, Faty kyakykywa tΓ‘ qarshe San kowa kin wanda be samu ba, da kuma Mimi wacce da wuya ka dora ido akanta kadauke batare da tasbihi game dukaba musamman inbaka da cutar hassada. Duk da yawan gorin da ake mata a gidan na cewa "duk macen da bata haifi namiji ba bata haihu ba " wannan maganace da Kullum saΓ Anty ( jamila) ta fada mata ita. Da yake anty kamar yadda yaran gidan ke kiranta, ta kasance mahaukaciyar mace me mutuqar kishin mama ta tsaneta da yayanta, kuma bata iya boye abunda ke xuciyarta baro baro take nuna kiyayyarta ga maman tana taqama da yayanta kwarai kuma da fifitasu akan komai da take dashi. Yayin da Umma (hajara) ta kasance makirar mace kuma karuwar cikin gida, (fir'auna a xuci Musa a kan sharshe) wacce da wuya ka gane ainihin abunda ke xuciyarta inba mugun Sani kai mata ba, bazaka taba cewa ta damu da wanxuwar mama da yayanta a cikin gidanba. Amma a gaskiyar lamari tafi Anty tsanar su, domin lokacin da aka auro fadima itace ta nemi hadin kan Anty duk da tsananin kishi da fada da suke gwabzawa a lokacin, ta shawarceta da su ajiye kishi guri guda su yaqi fadiman. Kuma ta jagoranci Anty suka bi duk wasu hanyoyi suka hana fadima haihauwa domin a cewarsu be kamata taci gadon qani sannan tazo taci gadon yayansa ba. Shiganan fita can haka sukai ta xagaye guraren na tsugune (bokaye) har sukai nasarar rufe mahaifar fadima . (nikuwa nace Allah dai be qaddara rabo tsakanin fadima da Buhari ba domin daya qaddara bokaye basu isa hana Allah ikonsa ba). A duk sanda Anty taiwa mama gorin rashin haihuwar yaya maza takance ita haihuwa ai mai albarka kawai ake nema bawai jinsi ba Allah ya yiwa wanda yabani albarka .
Arziqin Baffa ya bunqasa kwarai domin yanxu har gina gidaje yake yana siyarwa ko ya saka haya ga gidan gonaki da yake dasu wanda yake kiwon kaji, kifi , raguna da kuma shanu. Mutanen da sukecin abinci a qarqashinsa suna da yawa, xuwa wannan lokaci ya aurar da yayansa mata da dama, kuma baya aurar dasu sai ya kaisu sun sauke farali (hajji) kusan ma yarinya tana gama secondry a gidan yake kaita maka, dayake yawanci bibbiyu suke tashi yaran gidan saboda tare Umma da Anty ke haihuwa sai dai tsiran watanni. Duk da cewa baiyi karatun boko mai xurfiba ya bawa yayansa ilimi domin dukkansu sai sun haura secondry yake aurar dasu kina fara jami a level 100 xuwa 200 saiya aurarki kya qarasa agidan mijinki. Kuma bai yarda da bawa karabuti auran yayansa ba, domin yace bazai sayar da akuya ta dawo tana cimasa danga ba, sai wanda ya tara (mai kudi) komai rufin asiri sosai yake bawa auran yayansa. Kuma Allah ya dafa masa akan hakan domin wadanda yake muradin yayansa su aura shi Allah yake kawo musu (masu kudi) kasancewar yayan nasa kyawawa gasu da kwalliya da kuma ilimi domin yawanci Baffa suke yowa kuma Baffa kyakykyawan bafullacene.
Sai dai ta bangaren yayan mama ba haka lamarinsu ya kasance ba a gidan domin Faty tuni ta gama secondry har ta shiga school of Nursing (makarantar koyan aikin jinya) amma ko airport Baffa bai kaitaba bare saudia dan sauke farali. Da mama taji zafin abun amma daga baya saita barshi abisa ajizanci irin na Dan Adam, musamman data duba alkhairinsa na kaita saudia shekaru 3 abaya, sai ta goge laifin rashin kai Faty, dabeba. Baffa yana muqar San mama domin kuwa bambamci tsakanin mama da sauran matansa a bayyane yake, mama macece mai tsari kwalli tsafta iya girki Kullum cikin kwalliya take yatsunta basa rabuwa da kunshi hakan ya qarawa kyanta armashi da soyayyar miji Baffa a Kullum godewa Allah yake daya qaddara masa auran fadima ,domin shi mutum ne besan gayu da tsafta matansa kuma basu da lokacin wannan saina gasar haihuwa saboda gado.
Mama ta dade da samun shaidar karantun NCE a kwalejin horar da malamai ta tarayya (FCE), domin bayan kammala secondry school dinta a gidan galadima taci gaba da karatu bisa shawarar Adda halima wacce a lokacin take B ED (Bachelor in Education) a FCE din domin mijin Adda (Alh Abdul Aziz) dan bokone na qarshe saboda haka a hannunsa ta fara karatu tundaga yaqi da jahilci har takai matakin samun degree. Da farko Baffa yaso hana mama karatu, amma ta burkese masa dole ya yarda saboda son da yake mata da kuma tausayinta da yakeji na rashin qara samun haihuwa saboda yana sane Kullum cikin gorin haihuwa take a gidan, koda komawarta makaranta matan gidan basu wani damuba tunda ba sanin darajar ilimin sukayi ba, sai data kammala mijin Adda halima ya samo mata aiki a wata junior secondry school sannan suka nemi yiwa Baffa bore saboda baqin ciki da hassada, shi kuma yace duk wadda xatai karatu acikinsu kofa abude take kuma intagama da kansa zai sama mata aiki. Dole sukai shiru domin sunsan basu da tym din karatu.
Soyyar dake tsakanin Faty da Mimi baki bai iya fadarta, Faty yarinyace mai dattako da sanyin hali. Ta bangarenta bata hada San Mimi da komai ba, za a iya cewa tafisan Mimi da ita kanta, sai kaiwa Faty laifi ta haqura amma in kaiwa Mimi ta yini tana fushi dakai. Mafi yawan qawayenta sunan MARYAM garesu kuma tana qawance dasu ne ta dalilin alaqar sunansu da Mimi. Bata cika xama a gidan Baffa ba mafi yawan rayuwarta tana yinta ne a gidan mummy (Adda halima) dake rijiyar zaki. Mummy nada yaya 7 maza 3 mata 4. A cikin yayan mummy akwai saar Faty da kuma saar Mimi. Duk da gidan mummy gidane na yan gayu da daula hakan besa Mimi cika san xaman gidan ba duk kuwa da qaunar da mummy kewa Faty da Mimi, tasamu Faty dai amma Mimi Kullum tana jikin mama. Lokacin da mama ta tafi aikin haji 3yrs back dole tasaka Mimi xaman gidan mummy. Datai duba na tsanaki sai ta gano abunda yasaka Faty San xaman gidan, wato daddy. Mijin mummy mutum ne baisan iyalansa kuma ya sakar musu abunda sukaga dama shi sukeyi, (ba irin sakarwar da xata xama ba tarbiyya ba) Kullum yana cikinsu in dare yayi a hadu ayi karatu ya koya musu sannan a dasa hira har 10 pm sannan kowa ya nemi makwanci, hakan yajawo Faty San xaman cikinsu saboda inda ta taso tsangwama kawai suka Sani daga gurin yan uwansu wato yayan Baffa.
Abunda ke daurewa mama kai shine batasan dalilin da yasa anty da Umma suka tsani Mimi fiye da Faty ba, ita a ganinta in qiyayyace Faty ya kamata afi zafafawa ita fiye da Mimi, domin kuwa in kyau ne kaf iyalan gidan Baffa sai dai su xamo a bayan Faty domin babu wanda ya isa ya hada kafadarsa da Faty ta fannin kyau, amma memakon suyiwa Faty hassada kodan kyanta sai ya zamo Mimi akewa. Amma mamakin mama ya qarene a lokacin data fuskanci tsanar Mimi ta samo asaline fisa tsananin soyayyar da Maman da Faty kewa mimin, sai ya zamo anaiwa Mimi abune kodan mama taji haushi kota tanka musu. Hakan yasa ta gayyato dauriya ta qara akan wacce take da ita akan Mimi in anmata abu ta kau da kai, duk da ciwon da abun ke mata.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
AL 'AMARIN MARYAM
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
Writing & story by Rahma Muhammad {hajia}
Editing by
Mmn khairat π
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Page 1β£0β£
Faty tai sallama dakin mama daga makaranta take, sanye da fararen kaya Sol (uniform) da dan hijab iyakacin gwiwar hannunta.