Showing 183001 words to 186000 words out of 205258 words

Chapter 62 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

tunda sukaxo Mimi ta amshe yar kuma yarinyar bata da rigima takan wuni a jikinta sai xatasha nono Mimi ke bawa fauxa ita. Itama fauxan kuka take sosai da xata koma tace da Mimi in sunusi zai dawo qarshen wata xata biyoshi ta kuma ganin jikin. Tayi hidima sosai ta kudi data gaba, don tunda taxo mama ta huta wankin undis din Mimi da hada mata ruwan wanka da sata alwala da bata magani. Mama batasan Mimi nada masoya haka ba sai yanxu. Domin mutane ta ko ina barkowa suke dubiya wasu ta ganesu wasu kuma bata ganesu sai dai suce tare sukai skul da ita ko kuma dalibanta na legal. Abun shaawa har qungiyarsu ta CDS sunxo kuma harda kudi suka hada ta hanyar platoon officer dinsu suka bada aimata magani. Ta samu alheri ba kadanba, wasu kudi, wasu kayan dubiya, wasu kuma magani ko tofi kuma duk wanda ya kawo tana karba ta bawa Mimi da kyakykyawar niyya tunda shi magani dace ne.










Tun bayan tafiyar fauxa Mimi ta burkice tayi kukanta da yan rigimarta Rashida da mama suka lallabata tayi shiru, ana cikin haka ishaq yaxo.








Daga dakin Baffa bayan sun gaisa dakin mama ya shiga suka xauna a falo aka taso masa Mimi wacce ta fara bacci.








Tana ganinsa tasa kuka sabida tuna ya Bature da tayi, shima nan take ya karanci dalilin kukanta. Da kyar ya lallasheta suka gaisa, ya dunga yimata nasiha, bai mata xancen sulaiman ba itama bata tambayeshi shi dinba duk da azalzalarta da xuciyarta keyi nason jin halin da yake ciki. Ta tabbatar Anty gaskiya take fada tunda gashi har ishaq yaxo kano dubata amma babu ko saqon gaisuwa daga sulaiman din. Ta tambayeshi Farida, yace tana lfy tana gaisheta batasan xaixo ba.








Baffa ya leqo zai fita kasuwa kamar yadda ya saba yakan leqo yayiwa Mimi sallama da kuma tambayarta abunda takeso ya siyo mata. Yace "maryamu xan tafi me xan taho miki dashi?" tayi dan jum tana tunani, can kuma tace "alawar madara da kwan zabi dafaffe"yayi murmushi yace "yau baxa aci gobar ba kenan?" kafin tai magana mama ta fito daga daki tace "Mimi banda abinki ina xaiga alawar madara? Baffa ka bari xan bayar a siyo mata anan" yace "a a xansa a nemo a kasuwa, kwan kuma xanyi waya akawo daga gidan gona saiki dafa mata" tace "to a dawo lfy" Mimi ma tai masa adawo lfy.






Ishaq ya dawo da kallonsa kan Mimi, ya yaba kwarai da kulawar da ake bawa Mimi da gatan da take samu amma abun mamaki meke ramar da ita haka kamar me hadiyar allura?tunanin mijinta wata xuciyar ta bashi amsa. Tabbas Bature bai kyauta ba da yaqi waiwayo AL 'AMARIN MARYAM kuma dole inya koma ya bude masa wuta akan hakan koda xasu bata har abada.






Ya fita waje yasa yara suka dunga shigo da kayan daya lodowa Mimi aka cika falon dasu sannan ya dawo ya xauna. Mama ta fito tana masa godiyar dawainyar daya sha, ya tambayi mama "mama anya maryam nacin abinci kuwa? Dubi yadda ta qare ta lalace ya kamata a dunga kulawa kodan abunda ke cikinta" mama idonta ya cika da kwallar tausayi abunda ke cikin Mimi tace "wane abunda ke ciki kuma ishaq? Ai muna tsammanin Dan cikinta bashi da rai, dubi yadda ciki ya qanqance wanda a lissafinmu yakai wata 5 amma Kullum baya yake. Dan dai kawai yanxu batashi akeba ta lfyarta ake"








Ishaq ya dubi Mimi yana nazarinta da kallon qaramin cikinta yace da mama "banxo da kayan aiki ba dana duba nagani." Mama tace "bari in dakko maka na Faty wanda take mata dasu" taje daki ta dakko masa.










Ya karba Mimi ta kwanta kan duguwar kujera, ya auna cikin ya kuma yi checking dinta sosai. Ya cire abunda ke kunnensa yace da mama "komai lfy, kuma abunda yake cikinta da ransa, sai dai yana fuskantar baraxanar fita a mahaifa sabida yunwa da damuwar da take ciki" mama tace "to Alhamdulillah amma Faty tace zai iya maimaita watanninsa" yace "wannan ba lallai bane indai ta dage dacin abinci" ya dakko jotter a aljihunsa ya rubuta wasu magunguna. Yace da mama "ko xa a samu wanda xai siyo wadannan magungunnan yanxu?" tace "eh bari in kira huxaifa"










Taje dakin Huxaifa dake baccin asara ta tasoshi ishaq ya cire kudi a aljihunsa ya bashi yace yaje babban chemist don ba a samu a qaramin guri manyan magungunane.








Babu dadewa ya dawo dake a machine yake ishaq ya karba ya rubuta mata yadda xata sha kana ya kwantarwa da mama hankali da cewa "wannan magungunan in tanasha ko batacin abinci baxata wahala ba kuma akwai nasa cin abinci dana qarin jini"








Ishaq dai bai tafiba sai qarfe biyun rana don saida mama ta tsaidashi yaci abinci yayi sallah kana ya tafi, Mimi na hawaye tana cewa yagaida Farida.








Bai isa gida ba sai bayan magrib, yana shiga Farida ta tashi ta rungumeshi tana cewa "ya ishaq ina kaje? Kasa na yini cikin jimami tun asuba sai yanxu?" ya sunkuya ya sumbaci cikinta yace "kano naje duba Mimi" tace "Allah? 😳" sai kuma tai rau rau tace "amma bakaje dani ba?" ya lallabata da cewa Mimi tana lfy kuma ta kusa dawowa. Haka suka shafe daren ana hirar Mimi wanda ishaq ya lura tana kawowa Farida farinciki.








Washegari da daddare har gida ya bi Bature wanda tun a harabar masallacin sallar isha yake masa magana amma Baturen ya shareshi kamar baiji ba. A dai dai falo ishaq yasha gabansa yace "sulaiman dakata, ya xa ai dan rainin hankali tun dazu ina binka ina maka magana ka shareni?" Bature ya riqe kansa dake Sara masa yace "Bani da lokacin batawa, kawai fadan abunda yake tafe dakai"










Ishaq ya danne bacin ran wulaqancin da Bature yayi masa yace "naje kano jiya, ga dukkan alamu maryam ta samu lfy sai dai tunanin wufintar da ita da kayi yana kawo koma baya a lfyarta. Yakamata kai wani abu akai, indai har soyayyar da kake mata gaskiyace ba iya bakinka ta tsaya ba" Bature ya taso da masifa yace "ni banxaci harda kai a masu cewa bason gaskiya nakewa Mimi ba, Kalli yadda na koma sabida rashinta, inba soyayya ba mai zaisa inxama haka don bata kusa dani?"








Ishaq shima cikin masifa ya balbaleshi da fada yana cewa "dole a xargeka a kan maryam duk duniya kallon mayaudari take maka, kayiwa yar mutane ciki a dalilin cikinka ta samu lalura ka kaita gida ka ajiye" Bature ya fusata kwarai ya kaiwa ishaq naushi ya kauce ya riqe hannunsa. Baqo daya shigo kashe wutar falon yaga suna shirin dambacewa ya shiga tsakaninsu ya nemi taimakon Baba me gadi wanda ya shigo dakyar ya rabasu suka fita da ishaq. Bature ya kwanta a gurin yasa kuka, wai shi ake zargi da yaudarar maryam da wufintar da ita, matarsa, aminiyarsa, qanwarsa, kuma uwar dansa dake maqale cikinta to shi kuwa wane irin butulu ne shi daxai wulaqanta matar dake da wannan ranks din a gurinsa? Baqo yaxo dakyar ya dagashi ya maidashi bedroom yana bashi haquri don yaga sulaiman ya koma wani irin masifaffe tun bayan barin maryam gidan.








Acan kano kuma Audu ne ya samu labarin wani malami wanda ya kware sosai wajen maganin jinnu, an tabbatar masa da ingancin maganin mutumin. Yaje sukai magana ya yaba da magungunansa don yaga duk abune irin na ahlissunnah, amma yace baya xuwa gida aje axo da Mimi.








Ya kawowa su mama lbr, kuma a washegari suka shirya xuwa. Duk da anga sauqi kuma ciwonta baya tashi yanxu mama tace gara aje sabida wannan rashin magana ta Mimi yana damunta.








Ranar da mama Baffa sai Audu dake jan mota akaje. Sheshin malamin ya tambayi Baffa shin in ciwon ya tashi tana dariya ne?" Baffa ya bashi amsa "a a, kuka take in ciwon ya tashi. Kuma in dai ta dawo hayyacinta abunda take fara tambaya shine ; tayi sallah?" yace "mashaallah, anso haukatata ta hanyar sihiri, amma anyi dace tana addini sai abun ya tsaya a haka" Ansaka maryam gaba anyi ruqiuya ta kusan awa daya shiru, malamin ya miqowa Baffa wani turare a kwalba yace ya shaqawa Mimi a hanci. Sai dai ga mamakinsu taqi bari a shaqa mata saida akasha dambe da ita sannan aka saka matashi a hanci.








Ta burkice tanata ihu suka rufu ana mata karatu, sai da suka kuma shafe awa sannan ya bada wata xuma a kwalba yace a bata cokali uku. Aka bata tasha, ya kuma miqo turaren yace a shaqa mata. Wannan karon babu musu ta shaqa tace "wash kaina" ya dubeta yace "me kikaji?" tace "jin turaren nayi har cikin kaina kuma kan kamar zai fashe" yayi murmushi yace "to Alhamdulillah"






Ya dubi su Baffa yace "to anrabu in shaa Allah" suka hau godia sunaiwa juna barka. Ya hada magunguna da xuma wacce xata dungasha Kullum da safe kantaci komai da kuma dare kafin ta kwanta. A cewarsa magungunan tsarin jiki ya bata wanda in an kiyaye yadda yace ita da ciwon iska in shaa Allah har abada.










Ya fadi kudin Audu ya biya suka tafi. A mota suna tafiya Mimi a baya ita da mama yayin da Audu ke driving Baffa na gefe. Tace "ya Audu" yace "naam Anty Mimi" ta kuma cewa "ya Audu ciwon hauka nayi ko?" yayi shiru bai bata amsa ba sai kallonta da yake ta madubi. Ta juya gurin Baffa tace "Baffa na haukace ko?" shima shiru yayi mata.








Tace "ai ko baku bani amsa ba nasan ciwon hauka nayi dan Anty ta fadamun kuma shiyasa ya Bature ya kawoni gida ya ajiyeni yayi tafiyarsa" Audu cikin tsanar Anty da tausayin Mimi yace "Anty maryam ba ciwon hauka kikai ba, kuma ya Bature badan dan uwana bane wlh ba sabida lalurarki ya dawo dake gida ba. Kawai dai akwai dalilinsa nayin hakan kuma nafi kyauta xaton fushi yayi sabida su mumy sun hanashi fita dake qasar waje" tai shiru tana tunani babu wanda ya qara magana, itama din daga haka tai bacci a cinyar mama.








Tabbas kamar yadda malamin ya fada an rabu, don Mimi ta warke sosai. Tayi ragal sai damuwar rashin mijinta da kuma rashin cin abinci wanda har mama tayi fadan tagaji.








Yau lahadi Baffa ya je daurin auren yar abokinsa ya dawo, mama ta tafi kaimasa breakfast dake bai karya ba ya fita. Mimi da Dady ne kawai a falon Rashida na cikin daki tana bacci.








Mimi nakan centre carpet kwance cikinta ya dameta da motsi, ta kalli Dady dake homework tace "Dady na xo kaji" ya matso kusa yace "gani maman Abuja" tace "tokaremun cikina irin yadda kake yimun dinnan, ya dameni da motsi" yace "to, sannu mama" ya xauna yasa qafarsa duk biyun ya danne mata cikin sosai cikin ya takure guri daya ya kasa motsi kamar yadda takesa Dady yayi mata Kullum.






Suna cikin wannan hali mama ta shigo, ta dubesu a razane tasa salati wanda ya janyo hankalin Baffa dake daki ya taho da sauri ya dauka ciwonnne ya tashi.










Ganin Mimi a xaune yasa yace "menene fadima?" ta nuna masa Mimi dake jikin kujera Dady ya take cikin tace "Baffa kaga wannan aiki da suke" ta kaiwa dady duka tace "daga mata ciki dan ubanka"








Mimi tace "mama nifa nasashi, wlh damuna yake da motsi babu dadi shiyasa...... " Baffa yace "qaniyarki πŸ–πŸ» dan gidanku ba dole ya dameki da motsi ba bakyacin abinci." mama dai har yanxu kallonta take cikin mamakin wauta da danyen kai irin nata tace "inanan bansani ba xakiyi kisan kai, motsin ai shine lfy, da yana ciki xaki hanashi sukuni? To wlh ki kiyayeni karkiga ina lallabaki Allah akan dannan sai nayi miki duka" ta juya ga Dady tace "kai kuma dan banxa Kullum xancenka mama xata haifar maka mata ashe kaine me tayata kukashe matar taka" ya xaro ido yace "na daina mama, ni banason matata ta mutu" abun ya bawa su Baffa dariya suka dara a tare.








******** ******* ********




Acan Abuja kuwa yau kusan kwana goma da fadan sulaiman da ishaq kuma tun daga ranar basu qara ganin juna ba, abunda basu tabayi ba a tarihin rayuwarsu ace suna gari daya amma sun kwana goma ko a waya basu tuntubi juna ba.








Bature yasha wahalar da bai taba shaba a ratuwarsa cikin wannan kwanaki, babu ishaq babu Mimi, ya tsani kowa ya tsani komai duniya ta masa xafi ya rasa inda xaisa kansa yaji sanyi. Ya qara tara suma a fuskarsa da kansa. Ya rame sosai kamar ba cikakken babarbare ba.
Abinci inyakai bakinsa daci yakeji ga azabar ciwon kai daya sarqeshi.










Ranar alhamis da abun yayi masa yawa saiya tura takaddar neman hutu xuwa ga DG. Ko 30 minutes ba aiba aka kirashi ta landline din office din ya tashi yaje kiran mr Alex.








Kallon sulaiman yake cikin tausayawa yace "baka fadi adadin hutun da kakeso ba cikin takaddarka?" yace "bansan kwana nawa tafiyar xata daukeni ba, inason xuwa ganin jikin madam ne, in da sauqi baxan dade ba." yace "to kaje duk sanda ka dawo saika dawo aiki, Allah ya bata lfy" ya amsa yayi godia ya fita. Mr Alex kallonsa yake cikin tausayawa, shi gani yake kamar sulaiman din ya tabu, tabbas inyahana sulaiman hutu yasan yana iya ajiye aiki akan matarsa wanda baya fatan hakan don ma aikatarsu tana buqatar mutane irinsu sulaiman sabida gaskiyarsu adalilin matsalar zirarewar kudin rarar man fetur da ake samu Kullum acikin qasar nan wanda wasu masu fada aji suke wawushewa.








A dai ranar wajen 9:32 pm ya shiga gidan ishaq, ya samesu falo suna hira Farida na kwance jikinsa. Ganinsa yasa ta tashi, shi kuwa ishaq fuskar shanu yayi yacigaba da kwanciyarsa tare da qure volume din TV. Abun ya bawa Farida mamaki dan batasan sunyi fada ba. Kallon Bature take inda ya kuma ramewa yayi busu busu dashi tabbas ya mace itace gatan namiji yanxu da Mimi tananan da ya za ai tabar mijinta haka?








Ya kalli ishaq yace "inason gobe inje kano xan dakko Mimi ko sun yarda ko basu yarda ba kota warke ko bata warke xan iya xama da ita haka" ishaq tunda Bature ya fara magana ya kashe TV din gaba daya, sai da ya gama yace "yes! Kayi dai dai, ko wayone kai musu ka satota xamu tayaka kulawa da ita ko Farida" tace "eh mun baka goyan baya 100% ka dawo da ita ko anan gidan saimu xauna tare" daga haka hira ta balle suka xauna akaita plan din yadda xa a taho da Mimi gobe da dabarun da xaiyi ya satota. Sun dinke kamar basuyi fada ba, sukaci abinci da ishaq ya bashi maganin ciwon kai ya dauki mota suka fita ya kaishi aski aka gyara masa fuska aka wanke masa qafa tare da yanke masa farce. Ishaq ya kalleshi yace "harka fito kayi kyau amma da kayi wani dugujunjun ai inkaje haka saika furgita mimin" sai 12; 00 AM suka dawo, sukai sallama don yace da asuba zai wuce.






A daren bacci yayi sosai sabida kawai yasan gobe xaije yaga Mimi kuma su dawo tare.






Qarfe hudu ya tashi yayi wanka ya hade cikin designers suit ya baza perfumes masu azabar qamshi kamar xashi neman aure, yasa jakarsa a mota yasha Coffee daga masallacin asuba ya wuce kano yana tuqi cikin nishadi yanajin fefen karatun qur ani.








Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ



Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)




πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }


Page 6⃣3⃣


Dedicated to
ANTY SIS




Cikin daren juma'a suna kwance ita da mama akan gado, ta juyo ta fuskanci mama dake bacci ta qura mata ido tana kallon kamanin Faty da ya Bature a fuskar mama. Mama ta farka taga Mimi na kallonta babu ko qiftawa tace "meya faru? Ko jikin ne?" Mimi ta matsa jikinta tana cigaba da kallonta tace "mama" tace "naam autata" babu kunyar data sabaji a yau tace "yaushe xan koma Abuja?" mama ta kalli Mimi cikin mamaki ashe Faty tayi gaskiya da tace Mimi tunanin mijintane ya hanata watstsakewa. Ta katse tunaninta tace "sai kin haihu xaki koma" Mimi dajin haka ta tashi a raxane ta xauna tana kallon mama tace "nan da wata hudu zuwa biyar fa kenan?" mama tace mata "kwarai kuwa" tace "tab, wlh ni tafiya xanyi." mama ta dubeta tace "au Mimi kin gaji da xama danine?" tace "a a mama ba gajiya nayi da xama dake ba, gani nai dai na warke kuma ya Bature ma ancan yana kula dani. Gara in tafi kema ki koma aiki" mama tace "to babu inda xaki dan gidanku, daga ke har Baturen ai ba hankali gareku ba, sai kin haihu xaki tafi inyaso ko randa kika haihu ne ki diremun dan kujecan ku qarata ke dashi"








Tasa kuka tana cewa "ni wlh saina tafi Allah baxan xauna ba" mama najinta tai mata shiru har tagaji tai bacci sannan ta gyara mata kwanciya tai mata addua tace "rigimammiya ta xama sai kace yarinya abu kadan tasa kukan shagwaba tana bori, in anmaidaki abunjan haka xaman rainonki xaiyi ko aikinsa?"










Da safe ta tashi fuska daure ita a dole fushi take ance baxata koma Abuja ba. Sassafe akai sadakar wainar da Mimi keyi duk juma a tun kan tai aure, bayan an watse Baba lami daya daga cikin masu aikin gidan ta leqo dakin mama tace "mama ansauke ruwan wankan Mimi" mama tace "to sannu Baba lami" tasa Mimi agaba ta shiga bathroom din cikin daki tai wankan sabulu kana ta rakata waje tashiga bandakin tsakar gida ta kai mata ruwan maganin da Baba lami ta dafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login