Showing 54001 words to 57000 words out of 205258 words

Chapter 19 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

kada qafa ga dukkan alamu xancen Anty akan Mimi yayi mata dadi domin ga fuskarta nan ta nuna alamar hakan. Tace Umma Allah ya sanya alkhairi ya kuma kaimu lokacin sannan ta fice . Haka sukaci gaba da shirin biki wanda xa ayishi da zarar Mimi ta gama law skul da sati daya.






Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ




πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }


Page 1⃣5⃣




NA RAHMATULLAH (Hajia)








Kammaluwar karatun Mimi da kawo IV din bikinta abune da ya kasance a tare, kuma aranar data dawo ne Badaru yaxo domin suga juna tare da tattauna al amuran biki ( kuji fa kamar auran qauye), da taimakon yaya Faty wacce kullum sai tazo gidan saboda shirin biki ta shirya kanta cikin atamfar sΓΊper wax ja ta yafa mayafi kalar atamfar da dan takalminta shima ja plat, fuskarta tasha make up wanda ya fito da idanunta sukai tar saboda eye liner da mascara da akai amfani dasu wajan qayata idanunta. Jikinta na tashin qamshin turarurukan companyn Al rehab, domin ita a raayinta tafison Arabian perfume .


Zaune ta iskoshi a sitroom din gidan, qamshinta ya fara sanar masa ta iso, ya dago ya qura mata ido tare da hadiye wani irin abu da ya tsirga masa maqogaro ya saki murmushi aransa yana qisima bai taba ganin macen da ta birkita masa hankali ba, idan aka dauki lokaci bai samu maryam a matsayin mata ba tabbas zai iya sabawa ubangijinsa akanta, duk wani abu da ake buqata ajikin mace maryam tana dashi , wata irin muguwar sha awa yakeji akanta, feelings din dabe taba sanin yana dashi ba akan mace maryam tasa yana jinsa , shiyasa ya yanke shawarar auranta duk da baya sonta kuma baya raayin mace me shekaru da wayewarta, zai ajeta amatsayin wacce zai dunga kashe qishirwar shaawarsa akanta, sannan gefe kuma ga burin ransa wato Nafeesa a matsayin matar so. A bangaren Mimi kuwa tana hada ido da Badaru gabanta ya yanke ya fadi a fili ta furta "innalillahi wa innah ilaihi raju un " saboda tsananin firgici data shiga na ganin Badaru amatsayin mijin auranta nan da yan kwanaki, ashe wanda take zato ba shi bane? Ashe ita duk hauka take? Ashe Badamasin ma da take ganin be cika irin sharadin mijin da takeso ba , ba shine mijinta ba? Ashe kasan Badamasin ne? Shin meyasa ta dauri kanta ta cewa Baffa ta yarda da mijin da ya bata tunkan taga kalar mijin? Yanxu fisabillah ina ita ina wannan dan tsamurmurin bafillacen wanda tasan tafi tsaho nesa ba kusa ba??? Tambayoyi burjik ta dunga yiwa kanta a xuci a fili kuma tana hawaye, wata irin muguwar tsanar Badaru ta shiga xuciyarta nan take. Badaru da tun daxu yake kallon Mimi cikin mamaki, ya magantu " yanaji da ganina kin furta adduar da sai anga masifa ko abin qi ake yinta? " cikin baqin ciki da bacin rai idanunta jazur ta kalleshi tare da cewa meyasa kaimun haka? Dan me baka nemi yardata ba ko Jin raayina akanka kakai maganar gurin Baba na? Wane irin neman aure ne haka? Ya bata amsa da cewa irin neman auren da addini ya tsara, batare da tunanin komai ba tace to kasani ni Banasonka wlh πŸ˜ͺ shima cikin nasa sigar bacin ran da tsantsar rashin mutunci yace to nima anfada miki ina sonki ne? Kawai dai xan aureki ne saboda bani da xabin da ya wuce auran naki, xancen rashin neman yarsarki kuma sai kije ki tuhumi babanki wanda daga ganin sarkin power yasa miya tai zaqi, dagaji ance ina sonki yace in fito wanda hakan ya nuna baki da wani sai ni din danake shirin rufa miki asiri shine xakimun iskanci, wlh maryam bani da auran mace me shekaru kamarki kawai qaddara Allah ya doramun akanki. Ance inxo ne in mutsara lamarin biki to ni kisani bani da raayin wasu bidi 'o'i saboda haka sisina baxan bayarba nayi abunda yake wajibi wato sadaqi. Yana fadar haka yasa kai ya fice.


Jage jage fuska duk ta dame saboda make up daya hade da hawaye ta shiga dakin mama, Faty ce kawai ta kula da shigowarta dakin ta sauri tashi ta tareta ta fada jikin Faty tare da qara fashewa da kuka, yaya Faty dama irin mijin da Baffa ya zabamun kenan? Sam be dace dani ba wlh banasonsa na tsaneshi bana raayin auren mutum irin wannan. Faty ta dago kanta cikin rashin fahimta tace Mimi yimun bayani yanda xan gane, ba ance kun taba haduwa ba? Tace ba shi bane sister wanda nake zato ba shi bane 😭😭 wannan mugune wanda baya qaunata kuma ya furtamun da bakinsa, bazan aureshi ba sai dai in duk abunda za ayi ayi. Mama ta iso kansu ta tsaya cike da al ajabin abunda mimin ke fada, ta durqusa a gabansu tace Mimi babu abunda za ai wanda ya wuce ki yarda da qaddara kinsan wlh auren nan babu mai hana faruwarsa sai Allah tunda baffa ya tsaya akai, kuma turjiyarki ga wannan lamari yana nufin tashin hankalina acikin gidannan. Ta share kwalla tare da cewa mama yanxu auren dole kike nuna goyon baya ayimun? Tai saurin tareta da cewa a a wlh Mimi ko maqiyina bazanso auren dole akansa tunda anyimun banji dadi ba, bare ke yar cikina, amma inaso kiyi haquri ki dauki wannan aure a matsayin qaddara mutum baya taba gujewa qaddararsa wlh tun kan nasan waye mijin da Baffa ya xaba miki naji Sam lamarin bai munba, MARYAM indai ni na haifeki bazaki kaucewa umarnina ba, umarnina kuma gareki ki karbi wannan aure, in shaa Allah bazaki danasani ba. Ta dafa mimin tare da cewa kin yarda xakibi umarnina MARYAM? Tai saurin kwada kai tare da cewa yar halak ce ni mama bazan taba kaucewa umarninki ba, naji nagani na yarda. Kukan da take yasa dady dan yaya Faty shima yasa kuka tare da xuwa ya rungume Mimi yana share mata hawaye da cewa Anty yi shiru ki dena kuka Anty, ta kalli yaron soyayya ce me qarfi tsakaninta da dady ko uwarsa be shaqu da ita ba yadda ya shaqu da Mimi saboda a hannunsu ya tashi, tayi dariyar yaqe cike da qaunar dady tace nayi shiru Baba na ta rungumeshi suka kwanta akan cinyar yaya Faty.


Badaru tsaye qofar gidan su Nafee, yafi 30 minutes a wajen yana dakon fitowar ta amma shiru, har ya fidda rai ya juya zai tafi sai kuma gata ta fito tana yatsina wacce take nuna dab take da tayi rashin mutunci.


Ya dan matsa kusa da ita tare da cewa ranki ya dade yana washe baki 😁. Tai far da ido πŸ™„ sannan tace meya kawo ka? Ai canake kanacan gurin masoyiyarka?

Yayi saurin tareta da cewa ai bani da wata masoyiya da ta wuce ki, ai ban zaci ma zaki fito ba kusan fa sati 2 ina xuwa bakya fitowa. Ta fallara masa harara sannan tace ai dole ce tasa na fito, tunda naga rashin fitowar tawa be hanaka abunda kake niyya ba wato auren Maryam. Ta fada tare da
fashewa da kuka πŸ˜ͺ.


Tausayin Nafeesa da sonta ya qara qamari a xuciyarsa cikin sigar lallashi yace yi haquri Nafee wlh auren maryam qaddarace a guri..... Dakatamun βœ‹πŸ½ ta tsai dashi a hassale, Kullum abunda kake fada kenan a matsayin abunda xaka kare kanka a wajena kuma nagaji dajin hakan, ai wlh Badaru ka cuceni, ingama jiranka inbar karatuna sabida kai amma yanxu kaimun haka. Yanxu bani da ikon fita sai aita nunani ana zundena, wasu har cewa suke ka fasa aurena.


Nafee kiyi haquri wlh babu abunda xai hanani aurenki sai mutuwa, kuma duk masu yi miki dariya a sannu zasusha mamaki domin aurenmu na barshi daganan xuwa bayan sallah in shaa Allah.


Amma dai kasan bazan zauna da ita ba ko? Saboda haka ka nemar mun gurin zama tun wuri saboda na tabbatar bazan iya hada kishi da wata ba a kanka.


Nasani Nafee shiyasa ma na nemar mata gurin xama shi kuma wancan gidan dama nakine ke kadai keda yayan da zamu haifa.


Nafeesa ta dan sakko jin wannan furuci na badaru kuma ta tabbar har yanxu yana sonta, tace wai muga photon ta kyau ta finine naga kanata rawar kai a kanta? Yayi murmushin cin nasara yace wlh bani da photon ta amma wlh ko kama qafarki batai ba Nafeesa. Wai shin kinsan ma dalilin auranta? Nan ya kwashe abunda ke ransa game da Mimi ya fadawa Nafeesa ba tare da tunanin illar da hakan kan iya haifarwa ba nan gaba.


Lamarin da yayiwa Nafeesa dadi kwarai da gaske, domin tasan halin Badaru baya qarya hasali ma ya tsani maqaryacin mutum, kuma tasan abunda ya fada mata harga Allah hakane a xuciyarsa. Shiyasa ta saki jiki sukaci gaba da hirarsu ta soyayya kamar ba abunda ya faru.


Mrs Muhammad 😊
[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ
AL AMARIN MARYAM
πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ


πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS
{F, S, W}


Written by
RAHMTULLAH (Hajia)




Dedicated to
MARYAM BAITA




Page 1⃣6⃣


Kwanaki kadan bayan hakan Mimi tai wata irin muguwar rama ta fita hayyacinta, kallo daya xakai mata kasan akwai abunda ke cinta a xuci. Duk da ba fita tayi rabon i v ba, acewarta a turawa kowa ta waya inda hali ma a haqura da shagali a bikin a daura aure a kaita.


Abubuwa da yawa sun taru sun cudewa mama da yaya Faty da duk ma wani masoyinsu, ta bangaren mama dai abu da yawa na damunta, babban abunda yafi damunta kuwa shine damuwar halin da Mimi take ciki, na biyu kuma abunda Baffa Yayi mata. Abunda ya faru dai shine : abunda yayi a bikin Faty shi ya maimaita akan Mimi koma ince har gara Faty akan Mimi domin kuwa tunda ya sai set din kayan gado guda 1 da saitin kujeru yaja bakin aljihunsa ya tsuke daga haka ko tsinke be kuma siya ba, abunda yayi mugun baqanta ran mama da duk yan uwanta, domin a xaton mama Baffa xai saki jiki yayiwa Mimi kayan daki kamar yadda yake yiwa yayansa kodan albarkacin biyayyar da tai masa akan mijin da ya bata. Ita tunaninta abunda yasa yayiwa Faty haka a lokacin aurenta dan bayasan auren da Ahmad ne, amma sai taga sabanin haka domin har gara kayan Faty akan na Mimi, kenan Baffa ya na nuna mata yayan Al amin daban da nasa tunda ga banbancinnan yana nunawa qiriri, amma duk cikin lamarin Baffa wannan yafi bata mata rai fiye da rashin kai yayanta sauke farali kamar yadda yakewa yayansa domin a cewarta xuwa maka lokacinsu ne bayi ba. Ta kuma qudure a ranta cewa lokaci yayi da xata takawa Baffa burki akan yayanta.


Ita kanta Faty da bata cika daukan abu da xafi ba wannan karon taji zafin Baffa kwarai akan abunda yayi.


Da yake dangin mama ba matsiyata bane da ita kanta maman da Faty suka fidda kudi naqudai Adda halima da yaya Faty sukaje suka lafto siyayya daga kan kayan kicin da kayan qayata falo komai acan acan, sukaxo suka lafce kayan a tsakar gidan Baffa, duk girman tsakar gidan sai da kayan sukai ragowa aka dora wasu kan wasu. Cikin falon mama kuma danginta ne cike taf tunda da kan Adda halima (momy) har xuwa kan matan yayyensu da kuma yayansu, bakajin komai sai tashin hira da shewa cike da nishadi.


A dai dai wannan lokacin kuma matan gidan na cikin dakunansu cike da baqin ciki. Umma dai anata bangaren tun lokacin da aka kawo lefen Mimi har xuwa kayan auren da Baffa yayi mata tana cikin farin ciki, domin ita macece wadda bataso taga anfi yayanta, to ganin komai na Mimi tsiya tsiya yasa hankalinta mugun kwanciya, domin taga Mimi batafi yayanta ba, amma ganin wannan uban Kaya da dangin uwar Mimi suka kawo yasa murnarta komawa ciki.




Bangaren Anty kuwa kusan tafi Umma shiga tashin hankali akan wannan kaya, domin ita Sam batason cigaban wani koda kuwa dan uwanta uwa daya uba daya, bare kuma Mimi yar kishiyarta wacce tafi tsana a duniya.


Ana cikin hakanne saiga Baffa ya dawo diban wani katin daurin aure domin wanda ya fita dashi ya qare, ya tsaya turus ganin kaya sun cika gida ya kwallawa Umma kira suka fito tare da Anty (kamar ita aka kira), yace mata wannan kayan fa? Momy wacce ta fito daga dakin mama tace sannu Baffa ya juya tare da cewa haj halima ashe Kina ciki? Suka gaisa tai masa Murnar qaratowar biki sannan ta dora da cewa, dama kayane ta fada tare nuna kayan, muka kawo tamu gudumnawar babu yawa. Wata irin kunya ta rufe Baffa wacce tunda yake bai taba jiba, nan take ya fara nadamar abunda yakewa fadima akan yayanta, har yake tambayar kansa shin meyasa yayi haka kuma meye ribar nuna bambamcin da yake tsakanin yayansa da yayan dan uwansa guda daya da ya mutu yabar masa, gashinan dai abunda beyi ba danginta sunyi mata kamar yadda sukai a bikin Faty, yasan acikin matansa duk wacce za aiwa yarta aure ko cokali bata siya, amma fadima abikin Faty dana Mimi ta nunka abunda ya kashe wajan sau 3, baiji ragowar abunda momy take fada ba saboda tunanin da yake, sai dai kawai ya tsinci kansa da yi mata godiyar kayan da suka kawo.


Ba yanda yaya Faty batai da Mimi ba taje wankin kai da qunshi amma taqi, da kyar fauxa qawar mimin maqociyarsu ta lallami mimin suka tafi saloon akayi mata shampoo aka gyara gashin, qunshi kuwa qiri qiri taqi zuwa dole sai yaya Faty ce tasa me kunshin tazo har gida tayi mata. Duk da cewa Badaru be bada kudin event din yan mata ba, yan uwanta sun kama gidan dan hausa inda xa ayi luncheon kawai, domin ko sun qara wani event din Mimi bazataje ba, dan luncheon dinma cewa tai ba inda xata.


Ana gobe kamune akaje kafi (jere) gidan amarya ko 2 hours masu jeren basuyiba suka dawo jiki a sanyaye, domin kuwa wata yar qaramar gida Badaru ya kama haya a wani Geto area da nufin nanne gidan Mimi. Gidan dai yafi kama da gidan student wanda suke kamawa inbabu guri a hostel, domin dan qaramin tsakar gida ne sai qofa daya wacce inka shiga xaka tadda falon da ko Set din kujeru baxai ci ba sai bedroom daya da toilet aciki sai dan kicin dan qarami daga hagun falon, irin kitchen da in kin shiga bazaki iya tsgunawa ba saboda qanqantarsa.


Wannan gida ya faranta ran maqiyan Mimi na gida (irinsu Umma da Anty da kuma wasu daga cikin yayansu) da na waje. Anty ta dunga murna tana cewa yarinya dai ko FARHAN kitchen aka sai mata a banxa tunda babu gurin xubawa, domin kuwa ala dole aka juyo da kayan Mimi gida dan abunda ya samu shiga cikin gidan ba wani yawane dashi ba, don ko fridge da cooker gas basu samu shiga ba sai dan qaramin gas aka siya mata irin na yan hostel. Direct aka wuce da kayan gidan kakakannin Mimi (gidan mal SULAIMAN) aka jibge.


Matar babban yayan su mama (Umma) da momy suka dunga masifa akan wulaqancin da gidan su badaru sukaiwa Mimi akan gida kuma haka suka samu Baffa da xancen, shima da yake bayason harkar qaranta a take ya nemi mahaifin Badaru da zancen, har yana barazanar inbasu da wuri ajiye maryam a fasa auren dan ransa ya baci shima, alh inuwa ya dunga bawa Baffa haquri da cewa wlh suma sai a qurarren lokaci Badaru ya nuna musu inda zai saka maryam kuma basu so hakan ba, amma su kwantar da hankalinsu ya kusa gama gininsa. Wannan ne yadan kwantar da hankalin masoyan Mimi, amma duk da haka qananan maganganu sunyi ta kai kawo a tsakanin mutane akan auren.


Ranar alhamis itace ranar da aka fara bikin ko ince ranar luncheon, duk yanda aka kai da lallaba Mimi ta tashi tai shirin tafiya Gidan Dan hausa gurin luncheon Sam taqi anyi fadan anyi nasihar anyi waazin duk taqi ga dukkan alamu halinta na kafiya ya motsa, ala dole aka kyaleta ganin ciwonta na daukewar numfashi na alamun tashi domin qirjinta sai bugawa yake wanda shine alamun ciwonta yana gab da tashi, duk ta yankwane tayi wata irin migues rama duk wannan cikar jikin ta xube a 10 dayz, sai idanuwa xuru xuru da qasusun wuya.


Haka dai aka dade aka barta a gida daga ita sai kakarta (hajja maryam) wacce taci sunanta kenan sai kuma mama da tace ina xata yarta babu lfy? Hajja ce ketaiwa Mimi nasiha da falalar yadda da qaddara mama na gefe tana shafawa hajja mai a qafarta saboda wankan da tayi, nasihar ta shigi Mimi sosai saboda kwatancen da hajja tai mata da mama mahaifiyarta da kuma irin quncin da ta shiga a dalilin damuwarta, a fili hajja ke nuna San Mimi fiye da duk wasu jikokinta tanason yarinya fiye da tinanin me karatu.


Mama kuwa ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login