Showing 3001 words to 6000 words out of 205258 words
Chapter 2 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt
mmn khairat
πFANTASTIC STARS WRITERS {F S W }
Page 5β£
NOTE : ina bawa makaranta haquri da kuskuren da nayi wajen sunan yar uwar fadima ADDA KHADIJA, asanin sunan da tasarin labarin yazo dashi shine ADDA HALIMA. Saboda haka daga yanxu xamuji sunan ya koma Haleema memakon khadija, nagode ayi haquri π.
Yau ta kama Monday Wanda yayi dai dai da kwanan fadima uku a gidan auranta, xuwa wannan lokaci bataga koda giftawar me gidan nata ba balle ya mata magana, matan gidanma babu wacce ta taba nuna tasanta balle ta bata abinci, bata damuba dan babu abunda ba a kawota dashiba na bangaren kayan abinci, da yan kudadenta da yan uwanta suka hada mata dan haka hankalinta kwance yake kamar tsumma a randa. Tayiwa yayanta shirin makaranta tsaf cikin uniform, 7:00 ta fita ta kulle dakinta da nufin kaisu makaranta, taxi ta tara da yake awancen tym din babu a daidaita sahu, ta kaisu har cikin afoshin shugabar makarantar ta basu haqurin rashin ganinsu ta aka dade ba aiba ta fada musu mahaifinsune ya rasu, tayi mata gaisuwa ta kuma tausayawa yaran dama yaran Sun Shiga ranta saboda tsaftarsu da yalwar gashinsu, da yake sai shida na yamma suke tashi makarantar hade take da islamiyya tace xata dawo ta daukeso, ta raka Mimi ajinsu nursery 1 sannan ta raka fati dake ajin qarshe na primary.
Da yamma ta koma ta dakkosu kamar yadda tayi alqawari, ko takan mijin nata batabi ba balle tambayarsa izinin fita, tunda ya kwada mata xaman kanta xatai a gidan itama ta quduri aniyar hakan. Taxi na saukesu a qofar gidan ta dakko kudi da niyyar bashi saiga motar Baffa da alama dawowarsa daga kasuwa kenan daga kasuwa, ya kalleta cike da mamaki sai kuma duk ya
diririce ya shige cikin gidan
,atsakar gidan duk mutanen gidan na tsaye batasan dalilin tsaiwarsuba itadai ta bude dakinta ta shige.
Da daddare bayan isha tana tsakiyar yaranta tana koya musu home work, Ahmad yayi sallama ya shigo, ya gaisheta cike da girmamawa ta amsa itadai tana qaunar yarannan musamman data fuskanci matsalar matar uba da yake fuskanta, uwarsa ta mutu wajen haihuwar qaninsa, mahaifinsa alh Nasir me kudin gaskene kuma dan boko ya auri wata matar wacce ta mallakeshi tamaida Ahmad bawanta kuma ta rabashi da ubansa, ta katse tunaninta tare da cewa Ahmad idonka kenan? Sai yanxu? Ko makarantar sai yanxu aka tashi? Ya sunkuyar da kansa tare da cewa a'a mama yau hajiya ce tasani wankinta tun safe sai yanxu nagama ko makarantar ma banjeba (yana nufin matar babansa) ta kalleshi cikin damuwa tace bakaje makaranta ba Ahmad? Kayi kokari ka dunga xuwa makaranta inka dawo sai kai mata aikin, ko bakaso na baka auran Mimi? π inbaka xuwa makaranta bazan baka auran uwata ba, yayi dariya tare dayin qasa da kansa yace mama ni fati nakeso, Mimi qanwatace, tayi dariya tace toooo π, itama fatin inbakai karatu ba bazan bakaba, fati dake gefe tayi tsagal tace mama ni ko baiyi karatuba ina sansa a haka. Gaba daya suka saka dariya har Mimi da bata cika dariya ba sai murmushi. Mama tagabarta masa da abinci yaci, har xuwa taran dare sannan yai sallama yatafi, mama tace da safe inyayi shirin makaranta yaxo ya karya , tai shirin bacci suka kwanta tare da yaran a kan gadonta kasancewar tai musu tarbiyyar rashin fitsarin kwance tundaga yaye suke dena fitsari, tuni sukai bacci sai ita ta rage, taji sallama tare da shigowa cikin dakin, ssukai ido 4 dame me gidan nata, yayi saurin sunkuyar da kanta ga alamu nauyinta yakeji, "kixo dakina inasan ganinki yanxu " yana gama fada ya juya ya fice. Taiwa yayanta adduar bacci ta lullubesu da blanket ta dora hijab kan kayan baccinta tanufi dakin mijin nata. Koda taje bayan kwane-kwane na borin kunyar rashin kulata da halin da taga yayanta a cikin gidan, sai maganar ta dunga hada yaran cikin motar gida ana kaisu makaranta bai amince mata qara fita bada ixininsa ba, da yake namiji dai sunansa namiji sai jin hannunsa tai a jikinsa alamu haqqinsa na aure yake nema, π tunda ya fara bata dago kanta ta kalkeshiba balle ta tayashi abunda yakeyi, har yakai ga kwantar da ita akan gadonsa alokacin tayi yinqurin hanashi abunda yake wanda shi kuma alokacin yakai matuqa wajen San cimma burinsa hakan yasa ya samata qarfi ya fiya buqatarsa. Tayi kuka a wannan dare kuma ta tabbatar da tarasa Al amin har abada, tun kafin asuba tabar dakin nasa takoma nata tai wanka ta kwanta. Tsahon daren intace ta runtsa tayi qarya.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌAL 'AMARIN MARYAM ππΌππΌππΌππΌππΌ
Writing & story by rahma Muhammad {hajia}
Editing by mmn khairat
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Page 6β£
BAYAN WANI DAN LOKACI.
Xuwa wannan lokacin tuni fadima wato (mama) ta zama yar gida agidan Baffa domin ta ware ta fuskaci qalubalen rayuwar dake tunkaro ta. Yayanta Kullum suna jikinta, babu abunda ke fitar dasu gidan sai xuwa makaranta, har Ahmad da yake qaunar yayanta shima ta jima da maidashi dan gida, tana qaunar yaron kamar ita ta haifeshi kuma tana tausaya masa kwarai da gaske, safe har xuwa dare yana da kwano a wajenta ma ana tana bashi abinci ta dauke hidimar karatunsa tsaf kamarsu bashi kudin makaranta dinka masa uniform da kuma tilasa masa xuwa makarantar. Da yake dan halak ne yaron, yana mutuqar girmamata da yi mata biyayya kamar ita ta kawoshi duniya. Duk da baqar maganar da takesha a cikin gidan nacewa ta samu dan daba nata ba tayi ruwa tayi tsaki a harkarsa . Bata taba kulasuba saboda dan Allah takeyi kuma aranta takance Da da dukiya ai ba ai musu mugunta, kuma da basai wanda ka haifa ne lallai yake jin qankaba .
Xaman gidan Baffa xamane na kowa kansa ya sani, saboda ko su matan ajunansu ba jituwa sukeba kullum fada suke kamar masu ganin hanjin juna gasu da ido akan yayansu, baki isa koda kauda buta kisa dan wataba sai dai kisa naki. Amma auro musu fadima da akai sai yasa suka hada kai saboda su yaqeta. A Kullum cikin goranta mata suke me yawon aure aure ta auri qani ya mutu ta auri yayansa, gashi abun takaicin Sun koyawa yayansu wannan dabi a tayi mata rashin kunya da yi mata habaici, yayansu maza ne dai babu ruwansu domin bazatace ga ranar da wani aciknsu yayi mata wani abu na batanci ba. Duk sanda xatai girki a gidan babu mai tayata da koda dauke cokali ne haka xatai girkin ta gama a wahale kasancewar bata saba girkin gidan yawa ba. Yayanta kuwa ganin idonta baisa anfasa dukansu ko xaginsu da aibatasuba, amma abun burgewar shine bata taba nunawa tasan anai musu hakan ba balle tayi magana, wannan ya qara baqanta ransu domin anayine domin tayi magana ko ranta ya baci, kawai dai abunda tasani shine bata yarda tabar yayanta da qazanta ba ko yunwa ko jahilci ta tsaye musu tsayin daka akan wadannan abubuwan. Agabanta xa a dakesu kuma asakasu aikin da ko ita data haifesu bata sasuba saboda aikin yafi qarfinsu amma saita kau da kai. A irin hakan wata rana Adda Halima yayar fadiman taxo ta tarar Anty jamila na dukan Mimi kamar xata kasheta wai kawai dan ta aiki mimin siyan omo kanti ita kuma mimin tace Mata mama tace babu kyau mata suje kanti sai dai maza, shine ta kamata tana duka Lamar ita takawota duniya babu wanda yayi yunqurin ceton mimin har uwarta dake can falonta tana dinki a kan keke tayi burus kamar ba yarta ake duka ba, sai Faty daketa kuka tana ihu tare da kiran azo atemaketa Anty xata kashe mata yar uwa. Ana cikin hakan Adda halima ta shigo gidan Kai xaye taje ta angaje jamila ta kwace Mimi tare da dauke Jamilan da Mari, sannan ta dora da cewa me wannan yar ficiciyar yarinyar tai miki kike mata irin wannan dukan? Shiru Anty jamila tai saboda Marin da akai mata ya shigeta, sai Faty ce ta mayarwa da Adda halima yadda akai . Tace yayi dai dai akan taqi xuwa aikenki kike mata wannan dukan? In gaskiya ne abun naki meyasa baki aiki naki yayanba? Ta juya ta kalli ragowar mutanen gidan da suka fito kallo sannan tace wlh tlh ku kiyayi taba yaran nan, marayun Allah kun hanasu sakat, me suka yimuku? Magana ta farko kuma ta qarshe wlh duk Randa wani acikin ku da yayanku ya qara sa hannu akan yayan fadima wlh kotuce xata rabamu. Tana kaiwa nan ta kama hannun Mimi da Faty tayi waje dasu ta xubasu a motar da aka kawota driver yaja suka tafi, kotakan fadima batabi ba saboda da ranta ya baci kuma tasan fadiman najin abunda akeyi tayi shiru.
Bangaren fadima kuwa sukuku tayini Baffa na dawowa da magriba taje ta sameshi da kukanta akan yakaita gidan Adda halima, ganin tana kuka yasa bai tambayi baasiba saboda ya dauka addan ce ba lfy yasata a mota suka tafi. Koda sukaje addan kin kulata tai ta hangi su Mimi da Faty a dining Sunayin dinner tare da yaran Adda da kuma dady mijinta tuni Sun sake cikin yara da yake yawanci akwai sa anninsu acikin yaran addan. Fadima taje ta riqe hannun adda tare da saka kuka, tace yi shiru fadima aini bakimun komai ba face amanar yaya da Allah ya baki kika kasa kula dasu kuma na kwashesu inke bakiso ni inaso, sai alokacin Baffa yaji abunda ke faruwa, wasa wasa dai adda ta hana fadima Yaya tun ana ganin wasa takeyi har dady da Baffa sukasa baki amma ta qeqashe qasa tahana, da yake ance da uwa sai Allah koda Mimi tagamacin abinci ta kyalla ido taga mamanta ai saitai gurinta da gudu ta kwanta jikinta, da haka Baffa yace tabar yaron ta taso su tafi ta miqe ta yafa gyalenta Mimi ta riqe hannun uwarta xata bita adda ta bita ta dauketa ta saka ihu, ta ajiyeta Tare da cewa maxa bita dan gidanku uwar taki da batasan ciwonki ba tana xaune xa a kasheki tai shiru, Faty take gefe taga suna shirun fita tace da Adda mummy nima xanbi mama, ta riqe baki tace au kema? π€ to ai kun kunyatani xo kibita in ankasheku ta huta. Da haka ta bawa fadima yayanta tare da ja mata kunne sosai.
To tundaga wannan lokaci akasamu sauqin abun domin suna shayin Adda halima sosai domin itadin bata barin ta kwana kuma tsaf Sun san xata aikata abinda ta fadadun koma fiye da haka. Tundaganan babu wanda ya qara yunqurin dukan yayan fadima sai dai kyara da hantara da xagi. Ni kuwa nace zagi ai zagawa yake kuyi tayi π.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌAL 'AMARIN MARYAM ππΌππΌππΌ
Writing & story by rahama Muhammad {hajia }
Editing by mmn khairat
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Page7β£
ASALINSU
Mahaifin Maryam su 2 ne a gurin iyayensu wanda suke fulanin gombe usul awani da ake kira kaltungo, Baffa Buhari shine babba sai AL AMIN wanda yake shine mahaifin su maryam din tun suna yara qanana iyayensi suka rasu, sun taso agurin dangi har xuwa girmansu Buhari secondary skul kawai ya gama ya tsunduma kasuwanci da yake anbar musu gadon dukiya sosai, dakadan dakadan kasuwancinsa ya bunqasa har ya kasance maxaunin Kano State saboda itane cibiyar kasuwancin arewancin qasarnan. Yana kasuwancinsa a kasuwar singa na sai da kayan abinci da kayan masarufi, da quruciyarsa sosai yayi aure saboda kudi da yake dashi, ya auri matarsa Hajara (umma) kamar yadda yayanta ke kiranta.
AL amin kuma yafi maida hankali a karatu, duk da yayan nasa yaso kwarai ya tsundumashi harkar kasuwanci ya dunga gocewa har daga baya ya fahimci bayaso ya qyaleshi .
Yayi karatunsa na Law anan ABU zaria ya kammala yaje Law skul dake Lagos ya dawo. AL amin matashin saurayi fari tas kyakykyawan gaske kamar yayan nasa Buhari. Ya dawo xaman gida a inda umma hajara ta dunga yimasa cushen qanwarta husna wadda take gidan a lokacin tana yiwa Umma xaman dabaro a dalilin haihuwar da tayi, tun be ganeba har ya fuskanta hakan yasa ya dena shigowa cikin gidan sosai indai ba kamawa tayi doleba duk abunda xaiyi yana yi ne iyakar shagonsa dake qofar gidan. Saboda sam husna batai masa badan bata da kyau ba sai dan bata cikin jinsin matan dake burgeshi .
Ta bangaren mahaifiya kuma asalin mahaifiyar su MARYAM bafulatanar ce domin iyayenta fulanin garko ne ta jihar Kano, su 9 mahaifiyarsu mai suna MARYAM (hajia) ta haifa da babansu mal SULAIMAN guda 7 maza kuma sune manya sai Adda halima sannan Fadima wato mahaifiyar su MARYAM itace kuma auta mazaunan unguwar tudun maliki.
Fadima ta gamu da iftila'in rayuwa tun tana yar shekara 7 wani Mara imanin wanda ba asan ko wanene ba Yayi Maya fyade (rape) yayi mata kaca kaca wanda hakan ya jawo mata baqin jini a lokacin yan matancinta dan kaf saida akaiwa sa anninta aure amma ita babu labari har ta shekara 14 (kasancewar ba makarantar boko sukeba, dan mal sulaiman yayansa maza kawai ya yadda suyi ilimin boko ) a zamanin budurwa mai shekaru 14 babbar budurwace sosai kuma da kunya a ganka da yarka a wancan lkcin mai wannan shekaru babu aure, duk wanda ya fito neman aurenta sai yan unguwa su tareshi su fada masa abunda ya faru kanta, daga haka har aka dena xuwa gaba daya. Ba tare da shawarar kowa ba Mal Suleiman ya dauki auran fadima ya bawa wani abokinsa direban babbar motar haya (Wanda yake sana arsu daya shima matuqin mota ne) mazaunin qauyen maberaya ta jihar sokoto a wancan lokacin a yanxu kuma zamfara. Saboda xaman fadima haka ya dameshi kwarai, yayiwa Mal Ali bayanin abunda ya faru a kan fadima shi kuma yace yaji ya gani ba komai aishi Me rufa masa asirine.
Lokacin da yaxo da maganar aurar da fadima ga Mal Ali hajia ta shiga mugun tashin hankali ita da yan uwan fadiman karma Adda halima taji lbr domin tana mugun San fadima, amma dole sukai haquri saboda sanin halin ubansu mafadacin gaskene.
Haka akai biki aka kai fadima gidan Mal Ali dake maberaya, gidan gandu bayan matansa 2 da yaya 17 harya aurar da wasu ma, ga kuma tagowar yan uwansa dake cikin gidan. Haka dai suka baro fadima uwa ta mutu saboda tunda akai maganar aurenta da Mal Ali ta koma wata iri kamar mai tabin hankali, suka rabu suna kuka ita kuma tana binsu da ido kamar zararriya.
Saida ta kwana 2 bataga angon nata ba, anabata abinci agidan irin cimar mutanen qauye wanda ganin bataci suka dena kai mata dan yanda aka kai haka aka dakkoshi, dan abun motsa baki da kayan fulawa na kayan garar da aka kawota dashine takeci, bata fitowa sai xata bandaki wanda take mugun kyama domin ko wanka takasayi a ciki. Arana ta ukun ne ta fito ta wanke bayin cike da tashin xuciya saboda jikinta ya dameta da ciwo tana buqatar wanka tayi wankan tafito tarar da mutan gidan sun cika tsakar gida da daurin qirji suna ganinta aka hau dariya da habaici ko kallo basu ishetaba ta shige dakinta.
A daren ne kuma mijin ya shigo dakinta tare da kazarsa ta amarci, alkcin yake fada mata wai tafiya yayi kudu dakko kaya shiyasa taji shiru amma gashi ya dawo suci amarci π. Duk yadda yakai da sweet mouth (dadin baki) fadima taqi amince masa, ya haqura ya kyaleta har kwanakin girkinta suka qare ya bar dakin, girki ya kuma dawowa kanta ya dawo dakin da sam cimma burinsa saboda ya kwaditu kwarai da fadima kyakykyawar mace jajur da ita ga quruciya, koda taqi yarda dashi yaso kwada mata qarfi ta saka masa ihu dole ya haqura ya kyaleta saboda gidan yawa suke ga yayansa da jikoki cikin gida da kunya aji tanai masa Ihu.
Saida aka shafe wata biyu cur a haka xaman gidan sam ya gundureta kwarai, duk sanda ta fito tsakar gidan da nufin yin wani abu zata tadda cincurundun matan gidan a gidin bishiya suna ganinta xa a ce " ritayar birni sai qauye ga gwallin ga shafe shafen amma anrasa miji a birni sai a qauye " sai a tafa a kwashe da dariyar cike da shaqiyanci irin na shegun qauye (shegu qauyawa πππ) . Duk da tana dakewa ta nuna bata gane da ita sukeba amma abun yana damunta. A bangaren mijin ma dangantaka tsakaninsu tayi tsami, saboda taqi yarda dashi ya dena bata dan kudin kashewa da yake bata da kuma lallabawar da yake mata shima tsakaninsu sai hantara aganinsa hakan zaisa da yadda dashi. Tayi baqi ta rame ta fita hayyacinta duk ta