Showing 138001 words to 141000 words out of 205258 words
Chapter 47 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt
dinnan zancen kawo kayan lefen ya isketa daga bakin Ahmad mijinta. Tai sallama danta na fari dady (AL Amin) wanda yaci sunan babanta yazo da gudu ya rungume qafafunta da yake a gurin mama yake tun daga yaye, na biyun kuma wato Muhsin dan kimanin shekara 2 tun safe suke gurin mama dashi dame rainonsa. Ta sunkuya ta sumbaci dady tare da cewa sannu babana, muhsin ma ya gangaro ta daukeshi tana shafa kansa. Ta zauna akan kujera gefen mama tare da bawa laure (mai rainon muhsin) umarnin ta dakko mata maltina a fridge, da kyar ta ida bari suka gaisa da mama saboda xance na cinta, suka qule uwar daki. Ta kalli mama da alamar tambaya tace mama wanene mijin Mimi? Wane irin neaman aure ne wannan bamuji neman aure ba banusan mijin ba sai kawo lefe mukaji da sa rana? π . Mama ta gyara xama cikin hikimar uwa ta gari da sigar lallashi ta kwashe zancen tas ta fadawa Faty sannan ta dora da cewa kuma shima Baffa besan har lefe zasu kawo ba, shi kudi sukace masa kawai sai gasu da kayan lefe. Kuma banaso ki dau dumi a lamarinnan tunda baffanku yace yayiwa Mimi maganar ta bada goyon baya kinga hakan ya nuna tanason yaron, kuma kodan mutan gidannan inaso ku karbi lamarinnan haka Allah ya tsara muyi mata addua da fatan alkhairi. Tace to mama ai tunda kince mimin tanaso shikenan π dama ni banaso a danne haqqinta ne, yanxu ina kayan lefen? Suna can dakin ummanku. Ta miqe ta nufi dakin Umman, tanasa qafa a falon ta fara cin karo da cosmetic din kayan lefen alamar angani duk an watsar ba a gyara ba. Umman na ganin Faty ta dan saki fuska da yake makira ce tare da cewa a a Faty har kin qaraso? Tace eh suka gaisa tare da yiwa juna murna akan auren na Mimi, ana cikin hakan ne anty ta shigo baqin cikinta sam be boyuba akan fuskarta, ta kalli Faty tare da cewa sai kuma kikaji abu babu zato? Ai bana dai yan kwantai sai aure suke, Faty da maganar ta bata ranta tayi murmushi da cewa aishi aure lamarine na Allah in lokaci yayi sai kikaga duk hassadar mutum sai anyi kuma sai kiga duk dadewarka babu aure abun ya zama tarihi. Ta fada tana duba kayan Anty da taga Faty ta dagota sai tai saurin sakin zancen tare da kama wani gadai lefenan akwati 4 da kit ne kaya kala 30, takalma qafa 5, jaka guda 3,
Sai mayafai 6. Kodan gold qaramin Set babu, babbar atamfa a cikin lefen itace cote d voire, leshi bafi tsada acikin kayan kwanaki Safna (yar antyn ce) ta saimun irinsa a gurin aikinsu biya 2 8k kinga a kasuwa baifi 6k kenan? Ai wlh a tarihin gidannan ba a taba matsiyacin lefe irin wannan ba, wai lefen mai kwalin degree a hannu kenan ta qarasa fada tare da sheqewa da dariyar mugunta π€£, sannan ta dora da cewa ana cewa jinkiri na kawo alkhairi ni dai banga alamun alkhairi ga wannan auren ba nashaji ana cewa in guga ya dade a rijiya yana jawo ruwa tsullum amma shikam gugan gidannan yayi shekaru aru aru a ruwa ya dago fayau. Faty ta dago tai qayataccen murmushi cikin qoshi da ilimi da wayewa tace "mashaallah kaya kam sunyi mu sun ishemu haka duba da babu irin tufar da Mimi bata saba indai a duniya take kuma da kudi ake siyanta, to kinga kuwa indai ka saba saka sutura me tsada ai ta lefe baxata dameka ba, kuma ai lefe bashine xaman aure ba mu alkhairin abun muke nema, kuma bamusan arxiqin da Allah ya yiwa Mimi ba anan gaba kinga kuwa be dace mu sare tundaga kan lefe ba. Tana gama fadar haka ta tattara kayan ta maida komai muhallinsa ta dubi umma wacce ke kan kujera tana kada qafa ga dukkan alamu xancen Anty akan Mimi yayi mata dadi domin ga fuskarta nan ta nuna alamar hakan. Tace Umma Allah ya sanya alkhairi ya kuma kaimu lokacin sannan ta fice . Haka sukaci gaba da shirin biki wanda xa ayishi da zarar Mimi ta gama law skul da sati daya.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
AL AMARIN MARYAM
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Page 1β£5β£
NA RAHMATULLAH (Hajia)
Kammaluwar karatun Mimi da kawo IV din bikinta abune da ya kasance a tare, kuma aranar data dawo ne Badaru yaxo domin suga juna tare da tattauna al amuran biki ( kuji fa kamar auran qauye), da taimakon yaya Faty wacce kullum sai tazo gidan saboda shirin biki ta shirya kanta cikin atamfar sΓΊper wax ja ta yafa mayafi kalar atamfar da dan takalminta shima ja plat, fuskarta tasha make up wanda ya fito da idanunta sukai tar saboda eye liner da mascara da akai amfani dasu wajan qayata idanunta. Jikinta na tashin qamshin turarurukan companyn Al rehab, domin ita a raayinta tafison Arabian perfume .
Zaune ta iskoshi a sitroom din gidan, qamshinta ya fara sanar masa ta iso, ya dago ya qura mata ido tare da hadiye wani irin abu da ya tsirga masa maqogaro ya saki murmushi aransa yana qisima bai taba ganin macen da ta birkita masa hankali ba, idan aka dauki lokaci bai samu maryam a matsayin mata ba tabbas zai iya sabawa ubangijinsa akanta, duk wani abu da ake buqata ajikin mace maryam tana dashi , wata irin muguwar sha awa yakeji akanta, feelings din dabe taba sanin yana dashi ba akan mace maryam tasa yana jinsa , shiyasa ya yanke shawarar auranta duk da baya sonta kuma baya raayin mace me shekaru da wayewarta, zai ajeta amatsayin wacce zai dunga kashe qishirwar shaawarsa akanta, sannan gefe kuma ga burin ransa wato Nafeesa a matsayin matar so. A bangaren Mimi kuwa tana hada ido da Badaru gabanta ya yanke ya fadi a fili ta furta "innalillahi wa innah ilaihi raju un " saboda tsananin firgici data shiga na ganin Badaru amatsayin mijin auranta nan da yan kwanaki, ashe wanda take zato ba shi bane? Ashe ita duk hauka take? Ashe Badamasin ma da take ganin be cika irin sharadin mijin da takeso ba , ba shine mijinta ba? Ashe kasan Badamasin ne? Shin meyasa ta dauri kanta ta cewa Baffa ta yarda da mijin da ya bata tunkan taga kalar mijin? Yanxu fisabillah ina ita ina wannan dan tsamurmurin bafillacen wanda tasan tafi tsaho nesa ba kusa ba??? Tambayoyi burjik ta dunga yiwa kanta a xuci a fili kuma tana hawaye, wata irin muguwar tsanar Badaru ta shiga xuciyarta nan take. Badaru da tun daxu yake kallon Mimi cikin mamaki, ya magantu " yanaji da ganina kin furta adduar da sai anga masifa ko abin qi ake yinta? " cikin baqin ciki da bacin rai idanunta jazur ta kalleshi tare da cewa meyasa kaimun haka? Dan me baka nemi yardata ba ko Jin raayina akanka kakai maganar gurin Baba na? Wane irin neman aure ne haka? Ya bata amsa da cewa irin neman auren da addini ya tsara, batare da tunanin komai ba tace to kasani ni Banasonka wlh πͺ shima cikin nasa sigar bacin ran da tsantsar rashin mutunci yace to nima anfada miki ina sonki ne? Kawai dai xan aureki ne saboda bani da xabin da ya wuce auran naki, xancen rashin neman yarsarki kuma sai kije ki tuhumi babanki wanda daga ganin sarkin power yasa miya tai zaqi, dagaji ance ina sonki yace in fito wanda hakan ya nuna baki da wani sai ni din danake shirin rufa miki asiri shine xakimun iskanci, wlh maryam bani da auran mace me shekaru kamarki kawai qaddara Allah ya doramun akanki. Ance inxo ne in mutsara lamarin biki to ni kisani bani da raayin wasu bidi 'o'i saboda haka sisina baxan bayarba nayi abunda yake wajibi wato sadaqi. Yana fadar haka yasa kai ya fice.
Jage jage fuska duk ta dame saboda make up daya hade da hawaye ta shiga dakin mama, Faty ce kawai ta kula da shigowarta dakin ta sauri tashi ta tareta ta fada jikin Faty tare da qara fashewa da kuka, yaya Faty dama irin mijin da Baffa ya zabamun kenan? Sam be dace dani ba wlh banasonsa na tsaneshi bana raayin auren mutum irin wannan. Faty ta dago kanta cikin rashin fahimta tace Mimi yimun bayani yanda xan gane, ba ance kun taba haduwa ba? Tace ba shi bane sister wanda nake zato ba shi bane ππ wannan mugune wanda baya qaunata kuma ya furtamun da bakinsa, bazan aureshi ba sai dai in duk abunda za ayi ayi. Mama ta iso kansu ta tsaya cike da al ajabin abunda mimin ke fada, ta durqusa a gabansu tace Mimi babu abunda za ai wanda ya wuce ki yarda da qaddara kinsan wlh auren nan babu mai hana faruwarsa sai Allah tunda baffa ya tsaya akai, kuma turjiyarki ga wannan lamari yana nufin tashin hankalina acikin gidannan. Ta share kwalla tare da cewa mama yanxu auren dole kike nuna goyon baya ayimun? Tai saurin tareta da cewa a a wlh Mimi ko maqiyina bazanso auren dole akansa tunda anyimun banji dadi ba, bare ke yar cikina, amma inaso kiyi haquri ki dauki wannan aure a matsayin qaddara mutum baya taba gujewa qaddararsa wlh tun kan nasan waye mijin da Baffa ya xaba miki naji Sam lamarin bai munba, MARYAM indai ni na haifeki bazaki kaucewa umarnina ba, umarnina kuma gareki ki karbi wannan aure, in shaa Allah bazaki danasani ba. Ta dafa mimin tare da cewa kin yarda xakibi umarnina MARYAM? Tai saurin kwada kai tare da cewa yar halak ce ni mama bazan taba kaucewa umarninki ba, naji nagani na yarda. Kukan da take yasa dady dan yaya Faty shima yasa kuka tare da xuwa ya rungume Mimi yana share mata hawaye da cewa Anty yi shiru ki dena kuka Anty, ta kalli yaron soyayya ce me qarfi tsakaninta da dady ko uwarsa be shaqu da ita ba yadda ya shaqu da Mimi saboda a hannunsu ya tashi, tayi dariyar yaqe cike da qaunar dady tace nayi shiru Baba na ta rungumeshi suka kwanta akan cinyar yaya Faty.
Badaru tsaye qofar gidan su Nafee, yafi 30 minutes a wajen yana dakon fitowar ta amma shiru, har ya fidda rai ya juya zai tafi sai kuma gata ta fito tana yatsina wacce take nuna dab take da tayi rashin mutunci.
Ya dan matsa kusa da ita tare da cewa ranki ya dade yana washe baki π. Tai far da ido π sannan tace meya kawo ka? Ai canake kanacan gurin masoyiyarka?
Yayi saurin tareta da cewa ai bani da wata masoyiya da ta wuce ki, ai ban zaci ma zaki fito ba kusan fa sati 2 ina xuwa bakya fitowa. Ta fallara masa harara sannan tace ai dole ce tasa na fito, tunda naga rashin fitowar tawa be hanaka abunda kake niyya ba wato auren Maryam. Ta fada tare da
fashewa da kuka πͺ.
Tausayin Nafeesa da sonta ya qara qamari a xuciyarsa cikin sigar lallashi yace yi haquri Nafee wlh auren maryam qaddarace a guri..... Dakatamun βπ½ ta tsai dashi a hassale, Kullum abunda kake fada kenan a matsayin abunda xaka kare kanka a wajena kuma nagaji dajin hakan, ai wlh Badaru ka cuceni, ingama jiranka inbar karatuna sabida kai amma yanxu kaimun haka. Yanxu bani da ikon fita sai aita nunani ana zundena, wasu har cewa suke ka fasa aurena.
Nafee kiyi haquri wlh babu abunda xai hanani aurenki sai mutuwa, kuma duk masu yi miki dariya a sannu zasusha mamaki domin aurenmu na barshi daganan xuwa bayan sallah in shaa Allah.
Amma dai kasan bazan zauna da ita ba ko? Saboda haka ka nemar mun gurin zama tun wuri saboda na tabbatar bazan iya hada kishi da wata ba a kanka.
Nasani Nafee shiyasa ma na nemar mata gurin xama shi kuma wancan gidan dama nakine ke kadai keda yayan da zamu haifa.
Nafeesa ta dan sakko jin wannan furuci na badaru kuma ta tabbar har yanxu yana sonta, tace wai muga photon ta kyau ta finine naga kanata rawar kai a kanta? Yayi murmushin cin nasara yace wlh bani da photon ta amma wlh ko kama qafarki batai ba Nafeesa. Wai shin kinsan ma dalilin auranta? Nan ya kwashe abunda ke ransa game da Mimi ya fadawa Nafeesa ba tare da tunanin illar da hakan kan iya haifarwa ba nan gaba.
Lamarin da yayiwa Nafeesa dadi kwarai da gaske, domin tasan halin Badaru baya qarya hasali ma ya tsani maqaryacin mutum, kuma tasan abunda ya fada mata harga Allah hakane a xuciyarsa. Shiyasa ta saki jiki sukaci gaba da hirarsu ta soyayya kamar ba abunda ya faru.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
AL AMARIN MARYAM
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F, S, W}
Written by
RAHMTULLAH (Hajia)
Dedicated to
MARYAM BAITA
Page 1β£6β£
Kwanaki kadan bayan hakan Mimi tai wata irin muguwar rama ta fita hayyacinta, kallo daya xakai mata kasan akwai abunda ke cinta a xuci. Duk da ba fita tayi rabon i v ba, acewarta a turawa kowa ta waya inda hali ma a haqura da shagali a bikin a daura aure a kaita.
Abubuwa da yawa sun taru sun cudewa mama da yaya Faty da duk ma wani masoyinsu, ta bangaren mama dai abu da yawa na damunta, babban abunda yafi damunta kuwa shine damuwar halin da Mimi take ciki, na biyu kuma abunda Baffa Yayi mata. Abunda ya faru dai shine : abunda yayi a bikin Faty shi ya maimaita akan Mimi koma ince har gara Faty akan Mimi domin kuwa tunda ya sai set din kayan gado guda 1 da saitin kujeru yaja bakin aljihunsa ya tsuke daga haka ko tsinke be kuma siya ba, abunda yayi mugun baqanta ran mama da duk yan uwanta, domin a xaton mama Baffa xai saki jiki yayiwa Mimi kayan daki kamar yadda yake yiwa yayansa kodan albarkacin biyayyar da tai masa akan mijin da ya bata. Ita tunaninta abunda yasa yayiwa Faty haka a lokacin aurenta dan bayasan auren da Ahmad ne, amma sai taga sabanin haka domin har gara kayan Faty akan na Mimi, kenan Baffa ya na nuna mata yayan Al amin daban da nasa tunda ga banbancinnan yana nunawa qiriri, amma duk cikin lamarin Baffa wannan yafi bata mata rai fiye da rashin kai yayanta sauke farali kamar yadda yakewa yayansa domin a cewarta xuwa maka lokacinsu ne bayi ba. Ta kuma qudure a ranta cewa lokaci yayi da xata takawa Baffa burki akan yayanta.
Ita kanta Faty da bata cika daukan abu da xafi ba wannan karon taji zafin Baffa kwarai akan abunda yayi.
Da yake dangin mama ba matsiyata bane da ita kanta maman da Faty suka fidda kudi naqudai Adda halima da yaya Faty sukaje suka lafto siyayya daga kan kayan kicin da kayan qayata falo komai acan acan, sukaxo suka lafce kayan a tsakar gidan Baffa, duk girman tsakar gidan sai da kayan sukai ragowa aka dora wasu kan wasu. Cikin falon mama kuma danginta ne cike taf tunda da kan Adda halima (momy) har xuwa kan matan yayyensu da kuma yayansu, bakajin komai sai tashin hira da shewa cike da nishadi.
A dai dai wannan lokacin kuma matan gidan na cikin dakunansu cike da baqin ciki. Umma dai anata bangaren tun lokacin da aka kawo lefen Mimi har xuwa kayan auren da Baffa yayi mata tana cikin farin ciki, domin ita macece wadda bataso taga anfi yayanta, to ganin komai na Mimi tsiya tsiya yasa hankalinta mugun kwanciya, domin taga Mimi batafi yayanta ba, amma ganin wannan uban Kaya da dangin uwar Mimi suka kawo yasa murnarta komawa ciki.
Bangaren Anty kuwa kusan tafi Umma shiga tashin hankali akan wannan kaya, domin ita Sam batason cigaban wani koda kuwa dan uwanta uwa daya uba daya, bare kuma Mimi yar kishiyarta wacce tafi tsana a duniya.
Ana cikin hakanne saiga Baffa ya dawo diban wani katin daurin aure domin wanda ya fita dashi ya qare, ya tsaya turus ganin kaya sun cika gida ya kwallawa Umma kira suka fito tare da Anty (kamar ita aka kira), yace mata wannan kayan fa? Momy wacce ta fito daga dakin mama tace sannu Baffa ya juya tare da cewa haj halima ashe Kina ciki? Suka gaisa tai masa Murnar qaratowar biki sannan ta dora da cewa, dama kayane ta fada tare nuna kayan, muka kawo tamu gudumnawar babu yawa. Wata irin kunya ta rufe Baffa wacce tunda yake bai taba jiba, nan take ya fara nadamar abunda yakewa fadima akan yayanta, har yake tambayar kansa shin meyasa yayi haka kuma meye ribar nuna bambamcin da yake tsakanin yayansa da yayan dan uwansa guda daya da ya mutu yabar masa, gashinan dai abunda beyi ba danginta sunyi mata kamar yadda sukai a bikin Faty,