Showing 150001 words to 153000 words out of 205258 words

Chapter 51 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

bawa Mimi danbum nama ita da Farida cikin bokitai da kilishi, washegari uku ga sallah suka koma Abuja kamar yadda sukaxo su 4 sabida washegari talata xa a koma aiki hutun da federal ta bayar ya qare.






(Eid Adha Mubarakh, Taballallahu minna wa minkum)


******* ***** ******* ****




Sati biyu kenan da yin sallah, suna kwance bayan sallar asuba wata irin yunwa ta tasheta. Ta tashi zaune baya kan gadon, ta nufi dakin motsa jiki dake can qarshen falon. Acan ta taddashi kan gym yanata motsa jiki sai zuffa yake. Ta kalleshi "yaushe ka tashi bansani ba?" ya bata amsa "aini ban kwanta ba ina ganin kinyi bacci na fito tunda naga yanxu ke bakyason motsa jikin kin xama malalaciya" ta yamutsa fuska "wlh ya Bature ni kaina bansan abunda ke damuna ba these dayz in nayi haki nake nafi gane inta bacci" yace "inaga gajiyan tafiyane har yanxu bai barki ba" batace komai ba ta nufi kitchen samawa kanta abunda xataci.








Dafadunkan shinkafa ta dora, ta samu barkono ta dakashi ta afa kana ta yanka albasa ta xuba manja. Girkin dai gwanin ban haushi kamar girkin yar koyo, amma ya xatayi haka takeson ci. Ai kuwa tana tafasowa yaji ya cika kitchen din, sai tari take ahaka ta gama girkin ta xubo a plate kana ganin abincin kasan zaiyi yaji don ga yayan barkono nan burjik akai sai kuma manja kamar yayi magana. Gidan gabadaya ya kaure da qaurin girkin wanda shiya fito da Bature daga daki yaxo yaga ko wani abun aka dora aka manta. Yayi turus lokacin daya hangi Mimi da plate din shinkafa agaba da wannan farar safiyar sai loma take ga bottle water a gabanta robarsa sai diga take sabida sanyinsa.








Cikin mamaki yace "Mimi? Kece ke cin wannan abun me qauri haka da safe? Lfyar ki kuwa?" ta kalleshi na second 2 tacigaba da lomar shinkafarta karta huce, ya qaraso gabanta ya riqo hannun data dibi abinci xatakai baki yace "ke meke damunki haka?" tace "ya Bature don Allah ka kyaleni inci yunwa nakeji kuma wannan nake shaawarci" ya saketa ya koma kujerar dake fuskantarta ya xauna tana naxarinta, sai data cinye shinkafar nan tas ta kwankwade ruwa roba daya me axabar sanyi.






Tundaga ranar yake kula da duk wani takunta, gaba daya ta canja Kullum cikin cin abinci ta manja take safiyar duniya sai tayi wannan dafadukan tata me qauri taci in kuma ba itaba ta kwada garin kwaki tasa manja da yaji tai taci kwadayi dai kamar me, kuma duk abunda take shaawa sai taci ta qoshi take samun nutsuwa.






Ranar da abun ya isheshi cewa tai masa "ya Bature a ina xan samu magarya?" ya kalleta cikin rashin fahimta yace "meye magarya?" ai tanajin haka ta saka kukan shagwaba wai ya raina mata hankali ita magarya xata sha. Lokacin dawowarsa kenan daga aiki, dayaga abun nata da gaske ne sai ya ciro waya yaiwa ishaq text don bayason taji abunda xai fada. Ya kalleta yace "yi shiru ba magarya xaki sha ba? Tashi muje gurin ishaq sai ya fadamun inda xaa samo muje in siya miki" tanajin haka ta miqe ta saka hijab dinta na sallah ya tasata gaba suka shiga gidan ishaq.








Suka tararsu a falo, ishaq ya saka safar hannu ya matso kusa da Mimi take zaune yace "maryam muga hannunki" ta kalleshi kana ta maida idonta kan Bature dake gefenta tace "nifa lfy ta qalau" ishaq yace "munsani ai ba cewa akai baki da lfy ba just wani gwaji xa ai miki" jiki a sanyaye ta miqa masa hannun, ya qurawa tafin hannunta ido sannan yacigaba da jujjuya hannunta, ya gwale idonta yana dubawa sannan yace ta fito da harshenta. Bayan ya gama dube dubensa ya fara yimata yan tambayoyi, tambayar qarshe itace yace yaushe rabon da taga period. Ta fada cikin tunani don ita har ta manta da wani abu period don rabonta da yi tun Anty mami na nan, kardai ace ciki gareta? Anya kuwa hakane? In gaskiyane ya kamata ita ta fara sani, amma sabida ta riga ta sawa kanta baxata haihu ba shiyasa bata kawo ciki gareta ba.








Maganar ishaq ta katseta, inda yace da Farida taje da Mimi toilet tayi fitsari ya bata kwalba. Sukaje tai fitsarin, bayan fitowarsu ya shiga toilet din kamar 10 minutes ya fito da tsinken gwajin ciki a hannunsa yana cire safar hannunsa ya kalli Bature daya miqe tsaye yana jiran cewar ishaq din. Ya bugi kafadar Bature yace "sai yanxu na yarda kai din namiji ne ba mace ba kamar yadda nake fada maka abaya, na yadda tunda ga Mimi nan dauke da cikinka"






Bature ya tsurawa ishaq ido yana kallonsa, can jimawa idonsa ya kawo kwallah. Tabbas tunaninsa ya xama gaskiya Last period din Mimi itace wacce tayi Anty mami na nan, sannan kuma a xatonsa randa ya kasa bacci Mimi taqi yadda dashi har yayi mata dole a ranar ta dau ciki. Ashe shiyasa ya kasa haquri, rabone yasa yayi mata haka. Allah azeem.






Mimi kuwa kamar an dasata akan kujera haka tayi, da gaske itace keda ciki kodai mafarki take? Lallai Allah maji roqon bawa. Farida ta taba ta tana murmushin farin ciki tace "ba kuka xakiba besty godia xaki ga Allah da kuma adduar Allah ya saukemu lfy. Dama can ni ban yarda cewa baxaki haihuwa ba kawai dai abune na lokaci, gashi kuma Allah ya kawo mu"








Bature ya tsuguna a gaban Mimi, yace "maryam burina ya cika xan samu zuri a dake, ya fara share mata hawaye meye na kuka kuma?" tana dariya hade da kuka tace "kaima ai kukan kake" yace "aini kukan farin ciki nake" tace "nima haka" suka saka dariya a tare. Ishaq da Farida na tsaye na kallonsu. Yaja hannun Mimi sukayi musu sallama suka wuce gidansu. Har sun fita suka dawo yace da ishaq "Dan Allah broz banaso kowa yasani, nafiso inya bayyana kowa yagani" ishaq yace "baka da matsala"










Ranar taga gata gurin Bature sai wani riritata yake, kamar kwai a cokali.






Can dare ta tashi ta dunga addua da godia ga Allah daya nuna mata wannan rana, bayan ta idar gaban mudubi ta tsaya ta daga rigar baccinta tana kallon shafaffen cikinta wanda akacemata wai da Da aciki. Bataji tashin ba sai ganinsa tayi ta cikin mirrow yaxo ta bayanta ya xiro hannunsa yana shafa mararta a hankali sannan yana kallonta ta cikin madubin. Cikin kunya ya ta juya ta rungumeshi, ya dauketa cak ya mayar kan gadon.








Ya fara magana "Mimi ki fadi duk abunda kikeso inbaki ko in miki sabida kinmun abunda yasani farinciki wanda bantaba yiba" ta matso jikinsa ta kama hannunsa tace "ya Bature kome nace kaimun xaka iya?" ya riqo fuskarta yace "in shaa Allah indai inada iko dashi xanyi miki" ta xama serious tace "so nake kaimun alqawari baxakaimun kishiya ba iya rayuwarmu" yayi gaggawar sakin fuskarta dake tafin hannunsa ya kauda kai gefe yace "maryam meya kaiki irin wannan maganar?" tasa hannu ta juyo dashi tace "azatona basai na nemi wannan alqawarin ba xakaimun shi, amma sai gashi bayan na karya billena na nema har turjemun kake. Ca nake sabida bani da damar haihuwa a koda yaushe kana iyayin aure amma yau da muka tabbatar da mun sami Dá ai ya kamata in san matsayina ko?" ya juyo yana kallonta, ranta a bace yake don ta daure fuska tamau ya kwantar da kanta akan cinyarsa ya fara magana "maryam bakya gani inna dauri kaina nai miki alqawari Allah yakan iya jarrabata da qarin auren? Wanda yin hakan xaisa mutuncina ya xube a idonki ki dunga kallona a matsayin maqaryaci?" ta katseshi "dakata, nagane inda ka dosa ada naxaci sabida rashin haihuwa kana iya qara aure, amma yanxu nagane sabida baka aureni budurwa ka sami budurci a tare dani ba shiyasa xaka buqaci aure anan gaba" ya riqota don ta fara qure haqurinsa cikin bacin rai yace "karki kuma hada shirmenki da cewa bansameki budurwa ba, ai nasan da hakan na aureki kuma haka nayi raayi. Yadan sassauta murya, maryam bani da raayin xama da mace sama da guda daya amma bansan ko nan gaba ba sannan duk yan uwana da iyayena kinga wanda yake da mace sama da daya? Mu abun kamar a jininmu ne da mata daya muke rayuwa amma fa ban miki alqawari ba wannan maganar babu ita" ta fusge daga riqon da yayi mata ta juya masa baya ta kwanta batace komai ba.








Ya bita da kallo saroro, me kenan? Fushi tayi? Ya matsa kusa da ita cikin kwantar da kai yace "Mimi nayi lefi amma kiyi haquri kinji karkiyi fushi" tai kamar bacci take, yasa hannun ya dagota ya fara mata susar qadangare a bayanta. Ta fara dariya babu shiri tana tureshi ya riqeta gam har saida suka shirya, yace "da kina nema ki bata mana wannan kyakykyawan yanayin da wani shirmen tunaninki ki fara fushi dani bakisan fushin me ciki bata sauka da wuri ba?"








Ma masallacin asuba bayan idar da sallah ya fadawa limamin asakashi a addua matarsa nada ciki yana barar adunga sata a addua Allah ya rabasu lfy. Ya kawo kudi ya bayar.








A office ma yau sai walwala yakeyi yana faran faran da kowa aciki kuwa harda Hanifa da suke yar tsama kwana biyu baya amma yau sabida yana cikin farinciki sun shirya. Biyar nayi ya nufi gida.








Mimi kuwa tashi tayi ta tarar ya fita don yanxu ita da bacci sun daura abota, tana shirin dora abunda takeson ci Farida ta shigo taxo musu da taliyar hausa dafaffiya da manja da yaji suka zauna suka dunga ci sai da suka tashi da ita tas kana masu aiki suka gyara gurin su kuma suna gefe suna hira.








Sai da aka kira laasar Farida ta tafi xataje tasa hannu a girkin dare, Mimi kuwa tana sallah wanka tayi tasa wani blue din wandon Jeans da yellow din shirt. Fes yaxo ya sameta, yana xuwa ya buqaci baqo ya tattaro masa duk wani maaikaci na gidan.








Suka hadu a falo suna mamakin wannan kira, ya dubesu bayan sun amsa gaisuwarsa. Yace "inason kowa ya maida hankali akan aikinsa sosai duk da kuna qoqari amma a qara musamman wadan da ke kula da part din madam. Banaso ko tsinke inga tana daukewa sabida tana da lalura irinta ciki a halin yanxu". Mimi take gefensa kunya ta kamata ta sunkuyar da kai sabida harda yan tsaffin dake aiki a gidan a gurin da matar me gadi. Suka rude da yimasa murna dafatan Allah ya inganta. Ya amsa ya dubi moses wato kukun gidan yace "daga yau na hanata shiga cikin aikinka ka kiyaye duk abunda takeso xata fada maka ka dafa ko kuma ta koya maka yadda akeyi" ya amsa yes sir"








Yakai dubansa ga grace da kuma dayar wato Ester yace?"kune masu tsaftace shashinta sabida haka a kula da kyau kar abar guri da danshi ta zame in hakan ta faru Allah ya kiyaye daureku xanyi" suka amsa da girmamawa sannan ya juya ga Aisha sabuwar me aikin da suka taho da ita daga wacce mumy ta samo musu yace "Aisha daga yau kece me kula da cikin dakin Mimi da tsaftace toilet dinta da duk wani motsinta wanda ya danganci nan kema ki kiyaye" ta amsa da "to" ya dubi Mimi yace "madam hakan yayi miki?" ta gyada kai kana tace "amma ni banji ka fadan aikina ba kuma kasan xama haka baxai yiwu ba motsin yanada amfani" ya dubeta yace "ki dunga gyara gado kina shiryamun drawer ta sai Aisha tayi ragowar" tayi dariya tace "ina neman alfarma abarmun gyaran dakinmu da toilet, innaji baxan iyaba na nemi taimako" ya kasheta da murmushi yace "anmiki"








Ya dubi matan wato maaikata mata yace "Don Allah kar a ringa barinta ita kadai, indai anganta ita kadai ko kuma in mutum ya gama aikinsa yaxo ya debe mata kewa don batason kadaici qofa a bude take ga kowacce mace a cikinku." ya dubi yan tsaffin guda biyu yace "Don Allah Baba duk abunda takeso ko yake da hadari ga masu lalura irin tata sai a fada mata" suka amsa suma kana ya sallamesu. Yakai dubansa ga Bako yace "Bako sai a kula sosai a tabbatar kowa yana aikin dana dorashi akai, ita kuma maryam duk abunda takeso in sun fada maka koda bana kusa ayi qoqarin samar mata" ya amsa cikin girmamawa sannan yayiwa Mimi fatan sauka lfy.








Bayan isha ya dawo masallaci ya shiga wanka, ita kuma tana dakin tanata xarya daure da towel so take ta shiga bathroom din suyi wanka tare kamar yadda ya dade yana buri amma ta kasa. Can ta runtse ido ta shiga, ya bita da kallon mamaki yana xaune cikin qaton bahon wanka wanda ya cika ruwan dumi da sabulan ruwa sai kumfa ke tashi da qamshi. Mamakinsa ya qaru lokacin da yaga ta cire towel din ta nufeshi, ya qurawa jikinta ido komai ya qara girma daga bobs dinta har hips wanda ada bai kula ba sai yanxu jikin ya kuma haske tas. Ta shiga cikin bahon, ya janyota tsakiyar qafafunsa yasa soso yana wanketa ya fara yi mata magana a kunne "Mimi luv amma dai inkin haihu jikinki baxaiyi wannan abun ba ko?" tace "wanne kenan?" yace "wannan murmurdrewar ciki ya yakutse stregcht mark (nankarwa) ko kuma kiyi tumbi wannan plat tummy din naki ya baci" cikin dariya tace "inyayi hakan dena sona xakai?" da sauri yace "Allah ya sawaqe just banaso ne amma ni koya kika xama ina son abata a haka" tace "to ai duk akwai maganinsu inba nayi, amma dai ba lallai bane jiki jiki ne wasu basai sun haihu ba in sukai qiba sukeyi, wasu kuma koda qibar da haihuwar basayi is defense da irin kyan jikin mutum. Amma dai manya na cewa ba a gane kyan mace saita haihu sabida lokacin in jikinta bashi da kyau duk sai tai ragaf jikinta ya baci in kuma me kyauce wato jikinta xakaga kamar bata haihu ba saima tsam da jikinta xaiyi tayi kyau sabida sabon jini yaxo mata." yace "to in shaa Allah kina cikin masu kyan jikin"








Yaci gaba da juyata son ransa wai yana mata wanka, yace "Mimi amma dai yanxu na tashi daga rago ko tunda na miki ciki?" ta hade rai tace "gaskiya ni ya Bature banason irin wannan zancen sai kace wasu yan iska😞" yana dariyar zolaya yace "ai kuwa kowa ya ganki yaga yar iska tunda ga shedar iskancin nan a jikin ki. Haka kika dunga bina kinamun wayo kika amshemun samartaka har saida kika maidani Dan iskan nima 🤣" ta fara kukan shagwaba tana bugunsa, ya sassauta dariya yace "sry na janye Mimi luv nine dan iskan tunda na hanaki sukuni saida nai miki ciki" haka suka dunga wasa acikin ruwa har kusan taran dare, kana suka shirya suka fito yin dinner.










Ta xage tayi white rice da stew din da akai sosai, yana kallonta asace alama cikin nata mai sauki ne don duk abunda ta samu ci take tayi nak sai dai in kwadayin ya motsa.










Washegari ma kafin ta tashi bacci ya fita, ta dunga takaicin halin da wannan ciki ya sakata taita baccin asara har mijinta ya fita tana kwance. Ta lalubi wayarta ta kira baqo tace masa in akwai inda xa a sami wainar gero da quli a nemo mata ita takeson ci.










Ya fita nema babu dadewa ya dawo ya samota awani gidan abinci anqawatata da kabeji, ta karba tanaci Farida ta shigo suka faraci tare amma Sam wainar babu dadi wadda ake a Local area tafi dadi. Farida tace mata taxo su fita xata supervising gidan abincinta daga nan su biya shagonsu suga yadda ake tafi da cinikin.








Ta kirashi a waya ta fada masa inda xasu, yace adawo lfy amma su kula sosai sabida abunda yake tare dasu.






Farida ke tuqin suka isa gurin. Mashaallah komai tas da tsafta anata shige da fice, masu kula da gurin kamar suyi musu sujjada Mimi tace akwai tradicional food? Cikin girmamawa sukace wanne xa a kawo musu a ciki? Tace " tuwon dawa da miyar kuka" suka kawo ta wanke hannu taci Farida sai yamutsa fuska take ita bai mata ba. Daganan can boutique dinsu sukaje, Mimi a xuciyarta tace kudi shegu ganin yadda ake wani basu girma duk da sun girmi duk yaran shagon. Suka duba komai har sabuwar order din da akayo da kuma record na ciniki komai babu matsala kana suka tafi.








Baqo ne ya siyo tandar wainaganin Mimi yanxu bata da abun so kamar wainar gero da yar tsala kuma wacce ake siyowa bata mata yadda takeso, yace matarsa ta dunga yi mata duk sanda takeso. Matar me gadi tace akawo ita tadau nauyin wannan, hakan yasa Kullum da safe Mimi ke samun abun breakfast irin wanda takeso. Bature yaji dadin wannan abu da sukayi sun tayashi son abunda yakeso.










Cikin yan kwanaki kadan tai wani irin kyau ta dashe tayi tas ta xama fara sol sabida ciki, kulawa kuwa har kunya takeji wani sa in duk wata halitta ta gidan hankalinta nakan Mimi. Bature ya dauke mata komai na hidimarsa, sau tari kafin ta tashi ya fita aikinta a gidan kawai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login