Showing 162001 words to 165000 words out of 205258 words

Chapter 55 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

sai dai kash! Basa duba taurarin da suka dace da aikin" Hanifa da gwaggoriya suka dubi juna a tare, tacigaba da cewa "Duk da matarsa na yawan bata miki shiri da addua amma da anbi aikin bisa tsarin taurarinsa da tuni ankai gaci" Hanifa tai saurin tarar da cewa "yanxu meye abunyi ki taimakeni don Allah" ta dagawa Hanifa hannu alamar ta dakata sannan tace "ba a katseni in ina jawabi don nima fadomun ake ina fada" Hanifa ta qunshe bakinta tayi gum.










Uwar gida taci gaba "inbaki kawar da matarsa ba baxaki taba nasara a kansa ba don ko kinyi aiki xata bata miki, kuma shidin ma ai akwai aikinki a jikinsa don yana da raayi a kanki amma baxai tasiri ba sai kin kauda ita. Gashi kinyi dace akwai abunda ya dauke mata hankali daga yawan addua yanxu ,bayan haka ma baxamu wahala sosai ba wajen aiki akanta don acikin makusantanta akwai wanda ke aikin rabasu ita da shi." tai shiru alamar ta gama magana, Hanifa cikin imani da abunda akace tace "to yanxu ya kike ganin xa ai?" gwaggoriya kuma cewa tai "kawai a kasheta sannan ayi masa aiki ki shiga gidan kamar yadda tayi masa"










Uwargida ta kuma haska Hanifa da mudubinta wacce duk lokacin da akayi hakan Hanifa sai gabanta ya fadi. Tace "Sam ba asiri tai masa ya aureta ba kuma bata asiri, kawai hadine na soyayya." ta dubi Hanifa tace "kina da zabi guda biyu, na farko kodai a nakasata ta hanyar illata wata gaba jikinta, ko kuma a haukatata. Wannan sone kawai abunda xa a iya yi mata bayan haka babu damar raba aurensu ko kuma rabata da duniya" Hanifa ta kalli gwaggoriya cikin neman shawarar abunda ya kamata ayi.




Uwargida ta kuma kallon Hanifa tace "tana da ciki ko?" Hanifa taimata kallon mamaki, lallai aikin matarnan data raina xaici tunda harta gano cikin dake jikin Mimi. Uwargida ta katse mata tunani da cewa "inkina tunin akwai ko babu fa aiki baxai ba, don dole sai ansan matsayinta xa ai aikin" cikin imani da matar Hanifa tace "tabbas tana da ciki amma qarami ne"
Uwargida ta miqe ta fita waje ba tare da magana ba. Hanifa da gwaggoriya suka rikice da sambatun ingancin aikinta, Hanifa cewa take "wlh ji nake kamar na auri sulaiman, maryam kuwa in shaa Allah saita xama abar bawa sadaka akan titi wai ni ta kira da karuwa hmmm" tai kwafa.








Dawowar uwargida tasa sukai tsit, ta shigo dauke da wata mage qatuwa baqa wuluk ta akwantar da ita a gabanta. Ta kallesu tace "ki qaddara wannan maryam ce a xuciyar ki, sannan wannan mage tana dauke da ciki a jikinta kamar yadda maryam ke dauke dashi. Yanxu ki qaddara gaki ga maryam kuma kidau fansar abunda tai miki amma fa banda kisa" ta miqawa Hanifa wani qaton dutsen wuta, tace wannan dashi xaki amfani ki daki duk inda kikeson ya nakasa jikin ta.




Hanifa cikin tsananin farin cikin son daukar fansar cin mutuncin da Mimi tai mata da kuma baqaqen maganganun da har yanxu takejin sautinsu a kunnenta ta daga dutsen wutar ta bugawa magen dake kwance a gabanta a qafarta. Magen ta saki kukanta da qarfi "miyau" ta kuma dagawa xata kwada mata a daya qafar gwaggoriya ta tsaidata, "Hanifa me kikeyi haka kenan?" cikin farinciki Hanifa tace "gurguntata xanyi shegiya naga da qafar da xata dunga tafiya tana kada wannan qugun kinga kona aureshi ta gurgunce nice keda gida ko?"










Cikin takaici gwaggoriya tace "Dan bura ubanki ke wace irin jaka ce? duk wannan wahalar da mukasha a iya gurguntata xaki tsaya? Dagawa xaki ki daketa aka ta haukace ta shiga duniya ta haife cikin acan, kina aurensa gida ya xama naki keda yayan da xaki haifa ita kuma bai ganta ba balle abunda ta haifa suqare ita da Dan akan titi cikin hauka"








Uwargida ta kalli gwaggoriya cikin jinjinawa da baqar xuciyarta tace "gaskiya Hajiya kin iya mugunta 😂" Hanifa cikin sauri tabi shawarar gwaggoriya ta daga qaton dutsen iya qarfinta ta bugawa magen akanta cikin rashin tausayi da imani, dakin ya gauraye da kukan magen cikin azabar da akai mata. Tanata birgima a gurin kunenta na zubar da jini, kimanin 17 minutes tana abu daya kwanin tausayi kana ta tashi dakyar tana dingisa qafa tana janta tai waje da gudu tana ihu.










Bayan fitar magen matar ta dubesu tana dariyar mugunta tace "aiki ya cika yadda wannan magen tayi haka xataita ciwo kafin daga baya ta shiga duniya a matsayin mahaukaciya me dauke da ciki. Kowane lokaci daga yanxu labarin haukacrwarta xai iya xo muku"










Hanifa ta kalli gwaggoriya bakinta yaqi rufuwa "qawata nagode da wannan shawara kinga ai duk san da yake mata ai baxai xauna da mahaukaciya ba ko?" gwaggoriya tace "inma xai xauna da ita ina xai ganta tashiga duniya?" sukai dariya cikin farinciki harda tafawa.




Hanifa ta maida kallonta kan uwargida tace "shi kuma me xa ai masa hankalinsa ya dawo kaina?" uwargida tace "babu komai, ai na fada miki da aikinki har yanxu a jikinsa itace ta hana aikin tasiri sabida taurarinta da nasa in sun hadu aikin asiri baxai tasiri ba, amma tunda kin kauda ita yanxu komai xai tafi dai dai. Maryam dai anshiga duniya sai dai uwarta ta haifi wata"








Kudi sosai ta cajesu akan aikin, babu wani jimami Hanifa ta biya suka tafi suna mata godia ita ma tanai musu. Suka hau mota suna hirar haukan Mimi suna dariya harda tafawa. Hanifa tana cewa xataso ganin Mimi a halin hauka ta fada mata cewa itace tai mata aiken a matsayin ramakon biki. Gwaggoriya tana tuqi tace "shegiya illah biyu kikai mata kin gurguntata kin haukatata" suka kwashe da dariya suka tafa. Kamar bazasu mútuba anbasu tabbacin zasuyi jiran duniya. Ta kai gwaggoriya har gida sukai sallama ta koma gida ta fara ramuwar baccin da batayi ba jiya.








Allah ya kiyashemu tabewa (amiiiinnn)






Mrs Hajia 😊
[9/30, 1:05 PM] ‪+234 706 296 6299‬: 🙆🏼🙆🏼🙆🏼AL 'AMARIN MARYAM 🙆🏼🙆🏼🙆🏼



Writing & story by Rahmatullah Muhammad (hajia)




📝FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }


Page 5⃣8⃣






Kwana uku a tsakani, tana zaune da yammaci ita kadai sai yan aikin gidan wadanda suka kammala aikinsu suke tayata hira kamar yadda suka saba. Amma yau abun babu armashi domin uwar dakin nasu yau bata da walwala ko kadan, duk da ba hade rai tayi ba amma abun nasu babu armashi don basu saba ganin haka a gurinta ba. Sun maida hankalinsu kan kallon TV, yayin da ita kuma ta xuba tagumi tana tunani.






A haka ya dawo ya taddasu, suka dunga yimasa sannu da xuwa suna fita. Ya xauna kusa da ita, ga mamakinsa bata kulashi ba ko nuna tasan yana gurin a tunaninsa bata lura da xuwansa ba saboda zurfin tunani. Ya kira sunanta "Mimi" ta tago ta kalleshi na yan seconds kana ta maida taguminta, babu sannu da xuwa, babu drinks din data saba kawo masa inya dawo, babu rage masa kayan jikinsa balle aje ga hada masa ruwan wanka.






Ya tashi ya nufi kitchen, aransa yana tunani. Ada can yasha ji ana cewa Mimi miskilace ta gaske amma bai dau abun da wani mahimmanci ba balle da suka xauna yaga kyawawan halayenta, amma yanxu kam yaga illar wannan muskilancin. Yau kwana uku kenan tana masa halin ko in kula ko kuma yace tana gaba dashi, domin bata tanka masa kuma inyayi mata magana iyakacin amsarta eh ko a a duk da cewa na yau yafi tsanani.








Ya dakko ruwa yasha kana ya dakko lemo ya xuba a cup ya nufo falo, yasha rabi kana ya rage mata kamar yadda ya saba duk sanda yasha ruwa ko wani abun saiya bata ragowarsa tasha. Ya nufi bakinta da cup din, ta bude tashanye lemon tas ya ajiye cup din. Xaman jugum jugum ya biyo baya, ya gaji ya tashi da jakarsa ya nufi bedroom. A fili yace "Sam baxan yadda da wannan hali ba maryam, ai wannan ya zarce muskilanci ya koma mugun hali" bai fito ba sai magrib yayi wanka da shirin masallaci, ya wuceta a falo tana zaune inda ya barta.








Sai bayan isha ya dawo, yayi mugun mamaki daya sameta inda ya barta ko xama bata gyara ba. Cikin tsoronta yake a halin yanxu da hanxari ya taho gunta baice komaiba ya dagata yayi ciki da ita, ya cire rigar jikinsa yaje bathroom ya hada mata ruwan zafi ya dauketa yaje yana mata wanka, kallonta yake cikin mamakin halin data tsiro dashi. Ya gama yayi mata brush da alwala kana suka fito. Lotion ya shafa mata iya hannye da qafa, ya dakko mata doguwar shadda light yellow me laushi ta saka. Yasa mata dadduma da hijab ta kawo sallar magrib da isha tana idarwa ta miqe ta cire hijab din babu addu'a balle shaf'i wal wutir. Idonsa akanta, gashin kanta butsu butsu atsefe yake kuma tayi kusan kwana uku bata kwanceshi ta tajeba, ribbon din duk ya sakwarkwace.








Ya tako inda take tsaye ya kama hannayenta ya riqe yana kallon fuskarta, ta sunkuyar da kanta yajata sukai falo kan dinning ya xuba musu abinci a plate daya yace mata "maxa muci maryam" ta fara juya spoon ba tare data kai abincin bakinta ba. Ya qura mata ido cikin tausayin halin data saka kanta aciki, duk da babu kwalliya ko dis a fuskar amma ta masa kyau gashinta ya barbaxo gaban fuskarta ta rame kadan sabida damuwar data saka kanta ciki. Ya matso kusa da ita har kafadarsu na gugar juna ya dafa dan qaramin cikinta daya fito das ta cikin rigar yace "maryam daure kici abinci ko dan danmu dake cikin ki" ta dibi kadan ta kai bakinta daganan bata kuma ci ba. Shima ya dakata dacin nasa ya riqo hannunta duk biyun cikin nasa yana murxawa yace "maryam Dan Allah menayi miki kike irin wannan fushi haka babu ji babu gani?" tai shiru babu amsa yagaji da jiran cewarta ya kuma cewa "Dan Allah in akan Hanifa ne kiyi haquri, na tuba Mimi na, na baki haquri kuma tun a lokacin kin nuna kin haqura amma yanxu kin tsiro da fushi muna cikin xamanmu me dadi. Maryam kiyi haquri mu xauna lfy yan watanni muke da aure be dace ace haka ta fara bullowa tsakaninmu ba" har yanxu shiru batai magana ba, ya dakkota ya dorata kan cinyarsa yana shafa cikinta yana cewa "Baby na ka tayani bawa mamanka haquri, nayi missing dinku sosai. Mimi tunda kika tsiro da wannan hali naki duk gidan babu dadi har maids dinki basa walwala Mimi duk sun damu da halin da kike ciki, fadamun duk abunda kikeso inyi miki ki daina wannan fushin my luv" tai rau rau cikin muryar kuka tace "ni gidan ya Taheer nakeso naje" ya shafa kanta yana murmushi yace "wannan shiyafi komai sauqi my luv tashi muje" ya dakko mata siririn gyale ta rufe kanta suka tafi.








A qafa suke tafiyar tunda kusa suke tsiran maifi gidaje 5 ba, yana riqe da hannunta har cikin babban falo. Sun taddasu zaune kan dinning da kidz dinsu suna dinner, har gurin suka isa aka gaggaisa kana suka hadu gaba daya suna cin abinci. Mimi dai bata saki jikinta ba kamar yadda yake xato kuma batacin tuwon shinkafar dake gabanta, yadan dubeta yace "maryam ci abinci mana" Anty Rabi ta dora da fada mata ta dunga cin abinci sosai sabida abunda ke cikinta don xata iya jigata kuma ta jigatashi in batacin abinci sosai. Ganin sunyi mata caaa yasa taci loma uku dakyar duk kuwa da son tuwo da take da kuma uwar yinwar dake sakadarta. Ya Taheer baice komaiba amma yana kallonta cikin nazari.








Har goman dare suna gidan suna hira, ita kuma hakimar tana kan kujera a lafe bata samusu baki a cikin hirar amma fuskarta ta dan saki ba kamar daxu ba da suka shigo. Bature ya gaji kwarai so yake yaje ya kwanta sannan ya lallashi miminsa da kalaman soyayya su shirya don yagaji da wannan quncin nata.










Ya fara gyangyadi da hammar qarya duk don ya Taheer yace su tafi dare yayi, amma yaji yayi shiru sai zaqulo wata hirar yake. Ya qara wata hammar yace "Mimi taso mu tafi nagaji so nake in kwanta" tanajin haka ta koma kan kujerar da ya Taheer yake ta riqeshi tana kuka tace "ni baxan koma ba, nidai kabarni anan babu inda xanje" yayi sototo yana kallonta cikin tsananin mamaki ya yabawa makircin mace kwarai da gaske wato Mimi wayo tai masa ta shinfida masa gadar xare ta yaudareshi ya kawota gidan ya Taheer sannan ta nuna musu cutarta yake wato dai a fakaice qararsa ta kawo kenan? Ya danne duk wani bacin ran data haddasa masa ya kuma cewa "haba mana Mimi luv kefa kikace inkawo ki kuma nabi umarninki na kawoki sai kuma kiqi komawa? Daure ki taso mu tafi da safe xan dawo dake in xanje aiki."






Ta kuma shigewa jikin Taheer tace "wlh bazan bika ba, ka tafi kabarni, banason wannan gidan baxan koma ba."








Ya Taheer ya dago daka kallon Mimi dake jikinsa ya maida kallonsa ga Bature dake tsaye. Ya fara harar Bature, ya dafa kan Mimi yana kallon Bature yace "sulaiman yanxu wannan yarinyar kake cuta? Wannan salihar baiwar kake zalunta? Tun daga shigowarku naga yanayinta nasan akwai abunda ke damunta, amma ka bani kunya, ban zaci haka daga gareka ba. Aurenku da yan kwanaki har ka sako matsala cikin xamanku? Dama ka auretane don raba zumuncin iyayenku mata? Kasan matsala acikin aurenku na nufin matsala ga family dinmu gaba daya?"








Anty Rabi ta dubi Bature dake tsaye yana sauraran fadan Taheer kana ta maida kallonta ga Mimi wacce ke kwance kafadar Taheer din tana kuka wurjanjan. Ta matso kusa da ya Taheer tace "Abban sayyeed kabar fadan haka, lamarin aure ba a bawa mutum daya laifi, ka bawa Bature dama ya kare kansa mana" ya tareta da cewa "sulaiman shine babba sabida haka dole yayi haquri da maryam, kuma tunda kikaji ta dau matakin qin komawa gidansa abun babba ne."








Bature ya hadiye yawu dakyar yace "ya Taheer kayi haquri na karbi lefina in shaa Allah baxan kuma ba" jin haka jikin Taheer yayi sanyi ya dan yimusu nasiha da yin haquri a xaman aure kana yace "maryam tashi ku tafi Kinji ki dunga haquri da mijinki" duk da bata da taurin kai sunyi mamaki lokacin data noqe wuya, alamar baxata bishi ba.








Anty Rabi tajata daki don tambayarta meyayi mata haka wanda ya hanata komawa, amma juyin duniya Mimi taqi magana qarshe ma tasa kuka. Ganin haka ta fito falon ta samesu Taheer na qara yimasa fada. Mimi ta nemi guri ta kuma xama, Taheer ya matso gabanta cikin lallashi yace "maryam yi haquri ku tafi, gobe in nadawo aiki xanxo har gida ki fadamun abunda yayi miki, amma kafin nan ina nemar masa afuwa ki tashi ku koma"










Ta dubi ya Taheer bata da niyyar tashi ta saka kuka. Bature xuwa yanxu ransa ya gama baci da rainin hankalinta ya matsa kusa da ita ya riqo kafadarta ya fara magana .










"maryam karki raina mana hankali kinji, waye sa'anki anan? Ki fada mana abunda nayi miki kinqi, maryam sai yanxu xaki tsiro iskancin baxaki xauna dani ba? Sai da kikaga baxan iya rayuwa me dadi ba inbabu ke? Sai da kikaga farin cikin mahaifanmu ya ta'allaqa akan Dan dake cikinki? Meyasa kikeson duk saka wadannan mutane cikin baqin ciki? To wallahil azim in bacci kike ki farka, baxan sakeki ba koda bakya sona dole ki xauna dani, aurenmu mutu ka raba."








Kalamansa suka sakata saka sabon kuka, shima hawaye yake. Ya Taheer da Anty Rabi kuma tuni suka koma bayansu suna kallon wannan almara.






Bature ya miqar da ita tsaye ya fara jan hannunta yana cewa "taho mu tafi ko in sabeki in maidake dan dole, muguwa wacce batasan soyayyar gaskiya ba sai yaudara, wacce batasan farin cikin kowa ba sai nata"






Yayi gaba yana janye da hannunta ita kuma tana turjewa, taku daya, biyu, ana uku ta yanke jiki ta fadi wanwar. Sukayo kanta da gudu suna jijjigata da fadar sunanta, shi kuwa Bature na tsaye yana kallonta yasan Mimi pretending tayi don karta bishi.








Suna aikin jijjigata a gigice tana kwance sanbal shi kuma ya na tsaye hannu a aljihu yana kallonsu. A zuciyarsa ya raya bari yayi maganinta, yanufi kitchen ya bude freezer ya dakko ruwa me sanyi har ya fara qanqara ya nufi falon. Yasan dai ko suman gaske tayi ya xuba mata wannan ruwan zata farko balle pretending.








Yana xuwa ya bude ruwan daga tsaye ya fara tsiyaya matashi a fuska, sai dai har ya kusa juye mata goran ruwan Faro ko yatsanta be motsa ba. Ya Taheer ya daka masa tsawa da cewa "sulaiman! Kai mahaukacine da xaka dunga xuba mata wannan ruwan me sanyi? Baka ganin halin da take ciki ne?" yayi saurin yarda gorar ruwan don ya fara tsorata.








Ya fara kuka yana jijjigata da fadar sunanta yana cewa "maryam ki taimakeni ki tashi, maryam karki mutu ki barni, ki tashi maryam xan barki anan gidan tunda nan kikeson xama baxan qara tilasa miki xaman gidana ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login