Showing 201001 words to 204000 words out of 205258 words

Chapter 68 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

sunusi ya siya mata. Mimi ta dunga murna, mama ta karbi lace din takai shagonta na dinki wanda ta bude ta xuba yara maxa. Suka dinkawa Mimi buba da xani Bature kuma sukai mai irin dinkin yarbawa. Alheri kota ina barkowa yake. Bature ko tsinke bai saiwa Baby ba, Anty mami ce tayi komai har kwanan da Baby xata fara cin abinci in aka yayeta sai data aiko dashi. Ranar suna Audu ya kawo Sá da rago aka yankawa HALIMATU wacce little ta fara kiranta da MIMA. Ranar suna da yamma ya iso, Mimi ta bashi lace din fauxa ta fada masa fauxace ta kawo musu ya karba ya saka sanin matsayin fauxa gurin Mimi, itama ta saka aka dunga hotuna yana riqe da Mima. Fauxa taji dadin saka kayanta da sukayi.








Ta cigaba da rainon mima ita da mama, kuma a xamanta da Rashida ta dunga bata shawarar ta yadda ta koma ta haqura kodan Dan dake tsakaninsu. Taji shawarar Mimi, ta tatseshi kudi sosai kafin ta yadda a qara daura aure ta tare. Amaryarta dole ta kwantar da kai aka xauna lfy domin yanxu ita yakewa wulaqanci akan Rashida. Dama hausawa sunce bulalar da aka daki uwar gida da ita tananan tana jiran amarya dan haka ki dena murna dan mijinki na wulaqanta kishiyarki akanki dan wata rana ke xai wulaqanta.




Mimi tayi tas tayi kyau dake ansamu jego original, tayi shar kamar bata haihuba, tana yin arbain yaxo ya kwana suka koma tare. Mama ta dunga cewa su kular mata da mima, dan kowa yasan yadda mama ta dorawa mima son duniya fiye da komai a yanxu.








Tanata fargabar haduwarsu, kamar ya sani ya kyaleta sai data kwana 4 da dawowa lokacin ta saki jikinta sannan ya far mata. Ai kuwa ta dunga ihu suna kokawa, har ta tashi Mimi dake kan gadonta a gefe dole ya haqura karta tara masa yan aikin gidan a wannan daren. Kwana biyu ana abu daya ya gaji ya tambayi ishaq "ishaq wai in mace ta haihu qara matsewa take ne?" ishaq bai bashi amsa ba sai dariya da yunduga kyakyatawa, ya fuskanci matssalar Bature dan shima sunyi haka da Farida. Sai da ya gama dariyar ya bashi amsa "in mai kyan jiki ce tana kuma kamewa tayi tsam, musamman in suka samu kulawar jego. Kawai abunda xakai, kabi a hankali kamar daren farko da haka har ku saba" yabi shawarar ishaq, akuwa aka wuce gurin. A Kullum yakan godewa Allah da kuma fadawa Mimi cewa, shifa gani yake kamar ba daga jikinta mima ta fito ba kuma ko cikinta bai nuna alamar wata halitta ta kwanta ba, a taqaice dai Mimi tana cikin mata masu kyan jiki wannan flat tummy din da yake masifar so tananan ana masa gayu da ita.






Sukaci gaba da rainon mima,duk sanda ka duba dp din Bature mima ce a jiki, anty mami koda yaushe cikin aiken kayan mima take. Suna tsoron karta kuma samun ciki, hankalinsu ya kwanta da suka gane Mimi tana cikin irin matannan masu tsaftar shayarwa. Má'ana wadanda basa period in suna shayarwa dan haka suka sake suna gurxar amarcinsu.








Mima kyakykyawar gaske kamanninta da mumy sai qara fitowa suke, amma yar siririya ce sosai kamar little kamar yadda little tai musu fatan ta haifi irinta. Tana da sumar kai sosai kamar ta Mimi, ta taso cikin farin jinin mutane kowa sonta yake Mimi dai tana tsananin kau da kai akan mima kamar ba diyarta ba kowa ya sheda hakan.






Tana shekara daya Anty mami ta aiko da kudi da kaya akai mata birthday acan kano gidansu na sharada kuma kowa ya hallata an kashe kudi sosai. Mumy tunda aka haifi mima duk wanda xaiyi dinki acikin yayanta saita karbi ragowar kayan ta ajiyewa mima, kafin ta shekara antara mata natives sunfi akwati daya. Zuwansu kano birthday mumy ta bawa mama kayan ita kuma ta auna mima aka tsantsara mata dogayen riguna Kamar yan kanti masu jeluna, ta ajiye a gurinta dan tayi shirin dauke mima ne sabida son diyar take fiye da duk yayanta da jikoikinta (abun cikin kwai yafi kwan dadi)








Wannan karan kudin hayar gidanta yana xuwa gaba daya ta dauka ko shi mijin bai sani ba ta biya musu umra kusan su 6. Ita da Faty, mama da mumy, little da Bature. Kana ta biya wasu kudin aka hada harda yayan Faty da mima dan Mimi yanxu kudi take samu kota ina business dinta ya fadada kuma har yanxu bata daina yiwa mom adduar fatan alkhairi ba dan itace tushen komai.








Ranar da Bature yaji abunda Mimi tayi yayi mata godia da alqawuran soyayya sunfi cikin 80 leaves.






Mumy kuwa ta kasa boye farin cikinta kamar bata taba keta haxo ba, duk inda taje ko akazo mata kaji tana cewa "umra xamu ni da little da fadima. Maryam matar Bature ce ta biya mana dukkanmu" wannan karan ma matan Baffa suka kuma haukacewa, amma babu yadda suka iya dole mama ta dauki jikanta suka wuce.






Anyi umra lfy, Mimi tasha adduar fatan gamawa lfy a gurin duk wadanda ta biyawa umra din.






Basu jima da dawowa ba tayi shirin yaye mima kuma ta fadawa mama. Ana gobe xata yayeta mama taxo Abuja huxaifa ya kawota a motarta. Suka kwana, washegari juma a ta dauki mima xasu tafi, Bature kamar xaiyi kuka yace "Allah sarki mima yanxu na daina ganinki sai takalmanki da kekenki?" mama tace "to mara kunya baka isa dai ka hanani tafiya da ita ba, dan wannan yar tun tana ciki akaimun kyautarta dama jira nake a cire a gora intafi da abata" Mimi tana kallonsu tace "mama kamar yadda nayi alqawari a baya ba, na baki ita duniya da lahira, nasan xaki mata kulawar da koni baxan mata ba" tace "hakane uwata MARYAM" aka kwashe kayan mima tas har kekenta aka xuba a mota, dakyar aka banbareta daga jikin Bature tana kuka yanayi suka shiga mota suka tafi. Daga uban har yar sun bawa mama tausayi, ta dura mata freso ta bata rubutun yaye da akai mata ta jijjigata tai bacci. Mimi da Bature haka suka wuni wani iri, batasan tana son mima ba sai yanxu, gwarancin mima har gixo yake mata. Xuwa yamma zazzabi ya rufeta sosai ga ciwon nono. Yaje gurin ishaq ya karbo mata wani maganin ciwon nono wanda ya siyo musu ita da Farida a singapore dan ba a samunsa a qasar nan, tanasha ta watstsake xuwa dare kuma tayi mamakin ganin nononta bai fadi ba yananan dam dashi kamar bata haihuba maganin nada kyau shiyasa ba ko ina ake samunsa ba.






Acan kano mima ta saki ranta sabida maganin dangana da aka bata, tayi qiba sabida samun kulawa ta musamman, tuni ta shiga harkokinta ga yara a gidan ga kuma dady wanda duk abunda yaci saiya bawa mima. Kuma kulawa yake bata sosai ko shurin mima kayi cikin rashin sani saiya rama mata.






Mumy duk weekend saita turo an dauki mima ankai mata ita ta kwan biyu acan. Kuma Kullum little tana bisa hanya mumy tana cewa taje tagano mata mima kar mama tana wannan haqurin nata matan Baffa su dunga yiwa mima mugun hali yadda dukaiwa Mimi. Duk sanda little taxo tana komawa mumy da saqon qalau taga mima, kuma tana ganin mama baxata bari a taba mima ba balle ai mata mugun abu dan bata de haquri akan mima ko kadan.








Mima yar gatan iyaye da kakanni duk sanda taje gidan mumy saita dakko make up kit din Anty little kamar yadda take kiranta, ta xauna ta dame fuskarta kamar yadda taga little nayi. In little ta farga da barnar mima saita duddumeta intai kuka kuma taxo tana lallashinta.








Mimi da Bature kuwa soyayya aka balle kamar farkon aurensu, suna planning na calendar ko withdrawal method, dan Bature yaqi yadda suyi allura ko saka roba yace duk suna da illah kamar yadda ishaq ya fada masa.




****** ******* ******** **






Tafe take cikin motarta sanyin AC na bugata, tagaji liqis yau sunyi mahawara mai zafi a court amma Alhamdulillah sunyi nasara. BARRISTER MARYAM AL 'AMIN ce, wacce ta fara aiki shekara uku da suka wuce a matsayin lauyan mai xaman kanta wacce ta fito daga chamber din AL 'AMIN MEMORIAL CHAMBER. Itace ta qirqiri chamber din ta xuba lauyoyi irinta kwararru a qoqarinta na tunawa da babanta. Kowa yasanta akan aikinta sunanta yayi fice ne sabida tsayawarta wajen kwatowa yaran da akaiwa fyade haqqinsu da kuma matan da maxa kan saki su barsu da wahalar yaya, wanda ta haqiqance wayan sakin aure shike maida yara marayin tilas daga nan kuma yasa yara kwarara kota ina suna nemanrwa kansu abinci hakan kuma ke kawo yawaitar fyade. Duk wanda yasan maryam yasanta da sanyin hali da nutsuwa, amma in irin wannan case din yaxo gabanta babu mutunci Sam tsayawa take ta fafata tayi ragargaxa harsai anwa wanda aka kama sukunci. Barrister Mimi kenan, lauyan kare yara da mata kuma lauyan mijnta SULAIMAN A AZEEZ, domin a komai nasa na dukiya itace take tsaya masa.








Ta shigo falon a gajiye, ta cire rigarsu ta lauya, sanye take da suit riga da skirt ta dora Baby hijab a wuyanta. Ta rage kayan jikinta ya rage daga ita sai shirt da skirt. Ta nufeshi yana xaune akan carpet yana latsa system as usual. Yana ganinta ya dauke system din kan cinyarsa dan bawa Mimi maxauninta ta hau ta dare shi, yana cewa "hannu da xuwa my luv, ya shariar taku? Nasan kinyi nasara kamar yadda kika saba" ta zare glass din idonsa tana shafa gashin bakinsa da yatsanta kana ta kwanta akan qirjinsa ta kewaye hannunta a qirjinsa shima ya kewaye qugunta yana shafa gashinta tace "ya Bature munyi nasara kam, amma nasha wuya fa lauyan da gayen ya dauka yana da wayo amma qarshe Allah ya dorani kansa" yace "mashallah tashi muje wanka dama kenake jira" ta miqe ya dauketa suna dariya suka shiga bed room.








Sai da mima ta shekara biyar sannan Mimi ta samu ciki, watan haihuwarta na tsaya ya dau hutu itama ta dauka, Germany yakeson kaita ta haihu dan yace baxata qara haihuwa a 9ja ba tunda ta sha wahala a wancan karon. EDD dinta ya nuna saura 9 dayz ta haihu su kuma saura 7 dayz su tafi kamar yadda yake a visarsu. Suka wuce kano dan tanan zasu tashi.










Tunda sukaxo Kullum da daddare yan uwansa da matansu na kusa kan shigo bayan isha a hadu duka a babban falo aita hira sai goman dare suke watsewa.








Yauma sun hadu dukkansu, anata hira kamar yadda aka saba, Mimi na gefe guda ta baje ta tasa robar pop corn dinta agaba tanaci, wanda ya xama shine abincinta yanxu Kullum sai anje kwari an siyomata shi me madara. Cikinta yayi wani irin mugun girma wanda ake ganin kamar yan biyu ne. Tun jiya take jin ciwo amma tana sharewa dan tasan wasa farin girki haihuwar mima da haka ta fara amma sai data kwan ta wuni sannan ta haihu. Yanxu ma wani azabar ciwon kwankwaso takeji ko sauraran hirarsu batayi. Farida ta dubeta tace "besty yaya? Ko jikin ne?" ta kalleta itama da nata cikin dan kusan tare suka samu tace "a a ummu jidda (haka take kiranta yanxu) babu komai inason xuwa toilet ne" Bature ya miqe da sauri yaje ya dagata, dan inta xauna bata iya tashi saiya dagata, in kwanciya tayi bata iya juyawa saiya juyata sabida girman cikin. Xai rakata tace ya barshi yanxu xata fito fitsari xatai.






Ta wuce bedroom ta tsuguna akan gwiwarta tayi gofo dan baxata iya tsugonon fitsari ba. Wani masifaffen fitsari takeji amma ta kasayi sai nishi take.


Acan falo sukaji shirun yayi yawa yasmin ta tashi ta bita. Ta dawo da gudu tace da mutanan falon "wlh haihu xatai" Bature yayi wuf ya shige dakin, Audu kuma ya kira Faty a waya yace tai maza tazo mimi na labour.










Lokacin daya shiga kan Baby ya fito, ya gigice ya rasa yadda xaiyi tace "ya Bature ka zaremun Babyn" yace "to ya akeyi maryam?" tace "kunnansa biyun xaka dafe ka zaro" yayi yadda tace ai kuwa saiga qaton da namiji akan tiles din bandaki. Sunanan ahaka mahaifa bata fado ba, ita kuma sai ajiyar xuciya take yana mata hannu duk sun dame cikin jinin haihuwa, Faty ta iso, ta shiga ciki tasa safa ta taimaka mahaifa ta gado, baby ya cika gida da ihu. Faty tace "ya Bature dan fita ka bamu guri in gyarasu" ya watso mata harara yace "da Allah uwar iyayi kiyi mata abunda xakiyi mata kawai, ni dana karbi haihuwar?" tanajin haka tace "to riqeta in kwarfe mata jini" ya riqeta ta kwarfe jinin, Mimi ta kalleta tace "ya Faty sai anmun dinki ko?" tace "a a Mimi baki qaru ba, Allah ya baki da sauki."




Mama da mumy sukaxo a tare Audu ya kirasu ya fada musu, mama ta karbi gyara Mimi, mumy kuma ta yiwa Baby wanka. Cikin qanqanin lokaci sukai fes gida ya dau turaren wuta, aka fito da Baby su yasmin anata dauka da sauran mutane farida kuma cewa take yadda besty batasha wuya ba nima baxan sha ba ko ya ishaq? Sai yace mata eh maman jidda. Sai sha biyun dare suka watse, ya shigo bedroom din dauke da Mima a hannunsa tana tamai surutu. Su mama duk suna ciki, ya nemi gefen gadon ya xauna inda Mimi keshan tea.






Mima ta dane cinyarsa tace "ABBA wai kaine Dady na, Maman Abuja kuma mamana?" ya sumbaceta yace "eh mana ai shiyasa nake ce miki my lovely mumy, amma waya fada miki?" tace "yaya Dady ne" Bature yace "kinga wannan Babyn kuma qaninki ne" tace "to Dady na" ya dakko Baby yana kallonsa, kamarsu daya dashi sak, duk da yaron jaririne kamarsu da Bature bata buya ba. Ya miqe ya kwanta akan gadon yasa Mima da Babyn a tsakaninsu da Mimi sukai baccinsu, mama da mumy suka fita suka bar musu dakin.






A taqaice dai Germany din daba ajeba kenan, tunda abunda xai kaisu Allah ya kawoshi cikin sauqi. Ranar suna yaro yaci sunan "AL AMIN" Mimi tayi murna da sunan da babanta da yasa tana kiransa ABBA.




******* ****** *********






Rayuwa ta tafi, Mimi ta xama attajira sosai, ko aikinta ya isa ya riqeta balle business dinta wanda ya zama gagarumi ita kanta batasan adadin dukiyarta ba. Duk sanda ta fidda xakkah asibiti take xuwa ta gaida marasa lfy a fito mata da wadanda suke da lalura babu kudin magani kona aiki ta biya musu kuma dama ta dade da wannan buri tun tana qaramarta, sai kaga mutum ya rasa ransa ko ya nakasa akan kudin da basu taka kara sun karya ba, shiyasa take xuwa can takai zakkah.








Gidan Baffa kuwa tuni Al amura sun dai daita, abunda kuwa yasa hakan shine; anty tayi wani zazzabi mai zafin gaske wanda yasata sanqarau daga baya kuma tayi jijjiga tasha wuya sosai kamar baxata tashi ba, Allah yayi da ragowar shan ruwanta a gaba. Ana ganin abun ya warke amma ina dan saidata shekara biyu cis tana jinya komai sai anmata. Ansha wahala tun yayanta nayi har abun yayi tsaho suka dakko mace matashiya tana kula da ita dan babu manya duk sunyi aure sai qanana guda biyu. Mimi itace kan gaba wajen nemawa Anty magani da yawon asibitoci manya na kudi duk da yayanta sunayi amma ita tafisu hidimar kudi. A qarshe dai ta warke ragal, abun dadi kuma sai Anty ta shiryu ta wannan hanya, ta nemi gafarar mama da Mimi da duk wanda taiwa mugun abu. Ta kwantar da kai sosai dan yanxu ko magana bata dameta ba saita wuni batace komai ba, sai dai ka ganta da casbaha. Umma ganin abokiyar burminta abunda Allah ya aiko mata, itama tayi saurin watsar da makamanta ta nemi yafiyar kowa aka xauna lfy. Girman da Baffa yaso taja a matsayinta na uwargida taqi ada yanxu ta dakkoshi ta dorawa kanta. Ta riqe gida sosai tsakaninta da kowa girmamawace. Mama itace qaramarsu kuma duk tafisu sauqin kai ta basu hadin kai gida yayi dadi Yayi kyau xaman lfy ya samu xama daram.






Mimi itace attajira a gidan, kowa yasan haka babu wanda ya kai ko rabin dukiyarta, in biki ya tashi takansa aje shagonta na sai da furnitures a debowa amarya kaya iya girman gidanta. Ta daukewa Baffa wannan nauyin, in kkuma namiji ne xata hado lefe na kece raini ta kawo. Tuni ta qara gyara gidan ta saka AC taiwa su mama kayan daki iri daya sak. Ta dakko masu girki wanda itace ke biyansu in sun gama wacce take da girki aikinta kawai rabo.




Baffa kuma aikin hajji ta biya masa yaje, ranar har kuka yayi yace "abunda na gaxa yi miki yau kinmun Maryam Allah ya jiqan mahaifinku Aminu" mama ta kama qasa sosai itama har private skul Mimi da Faty suka bude mata anan Hotoro bayan layinsu bayan tayi retire a aiki.






Baffa ya kance "fadima haihuwar yaya mata tai miki amfani, yayan da ake miki gori akan baki haifi namiji ba gashi sun cika miki daki da jikoki maxa (Faty yayanta 4 duk maxa) wannan shi ake kira da "Goran duma me yado" kai madallah da haihuwar ya mace" duk sanda ya fadi haka sai jikin su Umma yayi sanyi dan sunsan da su yake. Mamace tace Dan Allah ya dena

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login