Showing 204001 words to 205258 words out of 205258 words
Chapter 69 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt
tuna musu tunda sunyi nadama.
Wannan karon shekarar Abba 3 Mimi tai wani cikin dan Bature cewa yayi gara suyi su gama karsu jera dasu mima. A cewarsa aure xai mata tana qare secondry skul zai aurawa Dady, jidda kuma yar ishaq xai aurawa Adil dan Audu. Ya hadasu ya kaisu jamiar Madina suyi xamansu can suna karatu da aurensu.
Cikinta yana 7 months sukaje yawon bude ido qasashe daban daban ita dashi da mima da Abba. Dubaice ta qarshe daganan xasuyo gida.
A Dubai sun fito xasu wata shago sanye take cikin doguwar riga baqa me duwatsu farare hannu da gaban rigar ta nade kanta da mayafin rigar tayi kyau sosai ta qara haske sabida jin dadi tana riqe da hannun abba shi kuma Bature yana dauke da mima yar 9 years wacce tai bacci a kafadarsa suna tafiya suka hadu da Badaru.
Suka tsaya aka gaisa, yayi qiba sosai ya dunqule, Mimi tai mamakin ganinsa nan dan tasan a singa yake kasuwanci to meya kawoshi Dubai sarin Kaya kamar yadda yace. Shima a nasa bangaren dubanta yake, har abada bazai daina danasanin sakin maryam ba. Tace "ka koma saida kayan mata kenan?" yace "eh tun da dadewa amma wancan kasuwancin ma ban barshiba ina tabawa" ya shafa kan ABBA yace "mashallah wato Maryam tsautsayi da kuma rabon wadannan kyawawan yaran da xaki haifa ya rabamu" tayi murmushi ta kauda xancen da tambayar yayansa nawa. Yace "guda bankwai ne" tace "bakwai?" cikin mamaki. Yace "eh ai bayan Nafee na auri wata yar abokin abba, to ita tana da biyu Nafee tana da 5" tace "Allah ya rayasu" yace "amin" mama ta tashi daga bacci ta juyo tana kallonsa yace "yan mata ya sunanki?" kamar ankunna radio ta fara xuba "ni sunana HALIMA SULAIMAN AZEEZ. Mumy ma sunanta Halima sulaiman, mutane na kirana MIMA. Amma Anty little da friends dina a skul suna cemun preety , ABBA kuma yana cemun ya mima, Dadyna kuma yana cemun my lovely mumy" Mimi tai mata tsawa tace "stop it Mimi, u talk too much" Abba kafin a tambayeshi sunansa yace "ni kuma sunana AL AMIN SULAIMAN, ana cemun Abba mamana tana cemun abbana ya mima na cemun broda. Mama tace nima innasami qani zai dunga cemun ya Abba" ya fada yana taba cikin Mimi. Kunya ta kamata ta ture hannunshi. Badaru yace "mashaallah Allah ya rayaku ya baku ilimi mai amfani yasa kuyi koyi da kyakykyawan halin mahaifiyarku" Bature yaja hannun Mimi sukai gaba yace da Badaru "amin amma kyakykyawan hali sukam sun tsotsa a nono, so ko bakai musu addu a ba suna dashi." Badaru ya bisu da kallon shaawa yaran ko yace family din sun burgeshi.
Mimi sunayin gaba ta kalli Bature tace "meye hakan da kayi kenan?" yace "Mimi luv ban taba ganin mutumin da yayimun abu na kasa mantawa dashi ba irin Badaru, ina jin tsanarsa innna tuna shiya fara saninku diya mace sannan kuma ya azabtar dake shiyasa na kasa yafe masa" ta fuskanci kishi ke damunsa, ta sanyaya murya tace "amma ai kai kuma kaina fara so a rayuwata" ya juyo yana kallonta ya hadata da yayansa ya rungume yana jin qaunarsu.
***** ************* ******
Xaune suke kaf dinsu cikin qaton falon gidan mumy, birthday din Dady ake yau na cikar shekarunsa 75 a duniya wanda Mimi da yasmin suka shirya kuma suka dau nauyi.
Cikin yayan mumy babu wanda babu har Anty mami dake nesa taxo. Mimi tana kusa da mama da mumy a xaune tana fama da qaton cikinta suna aikin hada kayan rabo a qatuwar jakar takadda me dauke da photon Dady wacce xa a raba in anjima da yamma. Abba kwance akan cinyarta, Mima ta tsallako taxo itama ta kwanta akan cinyarta. Abba ya hau ture kanta wai saita tasan mai a cinyar mamansa. Mimi ta daga mima a jikinta da cewa "ke tasar mai a cinyar babarsa, haka kawai ki hanamun babana sakewa" Anty mami tace "mima taho kinji mamana, kema in banda nuna qoqon usuli meye na xuwa jikinta ki kwanta keda kike da iyaye da yawa, dan tsabar gata ma ke kakanninki iyayenki ne" mama ta dubi Mimi tace "Mimi anya baxaki dena runquma dannan a cinya ba kina fama da qaton ciki" tana shafa kan abba tace "haba mama! Babana ne fa, kuma duk kunfison mima shi bamai yimun kara akansa shiyasa nake lelen abina" tace "ai shikenan"
Audu ya shigo ya kallesu Cikin shaqiyanci yace "mumy, gaskiya ke kyakykyawa ce, abu daya yayi miki cikas, kedin gajeriya ce. Da ace duguwa ce wlh sai dai shugaban qasa ya aureki" tayo masa daquwa tace "Dan ubanka haka ubanka ya ganni da gajartar ya aureni kuma na haifi dogo kamarka" aka kwashe da dariya, ya kalli yasmin yace "honey babu magana?" ta harareshi kawai dan haushinsa takeji dan yayi mata wayo taje ta cire robar planing yayi mata ciki wanda ita bata shirya masa ba. Rabonta da haihuwa tun Adil. Ya kada kai ya fita, mumy ta riqe haba tace "oh ni halimatu, tun kana haifar danka saika haifi jikanka. Audu ya maidani kamar kakarsa" aka kuma kwashewa da dariya, Faty tace "wlh mumy ya Audu da Lubna halinsu daya, sun iya shaqiyanci."
Bature ya shigo shima ya kallesu duka ya xauna kusa da mumy ya dafata yace "my lovely mumy, ina alfahari dake" tayi murmushi tana shafa kansa. Ya dubi Mimi yace "Mimi luv" ta bashi amsa "yaya luv" akaci gaba da hira can ya kuma kallonta yace "Barrister MARYAM" ta kuma bashi amsa "ENG SULAIMAN" ya tashi xai fita har yakai qofa ya juyo yace da Mimi "Haj mairo" a karo na uku ta kuma bashi amsa da cewa "Mal manu" ya xaro ido yace "lallai ma yarinyar nan ni kike cewa Mal manuπ³" tayi far da ido tace "nima yaya meyasa kacemun mairo π?" aka kwashe da dariya ana kallonsu cikin burgewa, mumy tayo musu daquwa tace "ππ» kunga yara muna zaune xai fadar sunan iyayenmu suke" Anty mami tace "yi haquri mumy Romeo da juliet ne suke soyewa a gabanku" aka kuma dariya gaba daya.
Anty mami ta bisu da kallo, suna burgeta. Bata yadda true luv yana existing saita dubi BATURE da MIMI.
Kamar yadda mumy tai hasashe adalilin kusancin yasmin da Mimi, yasmin ta koyi wasu halayen Mimi. Kuma Mimi tasan yadda tayi ta shirya Anty mami da yasmin suka dawo kamar da aka koma xaman lfy. Lamarin yayiwa Audu da mumy dadi tunda kowa nasu ne cikin yasmin da Anty mami.
Ina miqa godia ta musamman ga
Maman Khairat
Maman shukra
Anty sis
Sadnaf
Maryam Baita usman
Hudallah (mrs JH)
Huraira Yabo
(wanda da taimakonsu ne da kuma qarfafa gwiwa na ida rubuta wannan novel)
Ban manta da kuma ba
Maryam (besty na)
Wasila (saqonki ya isoni)
Maryam sani mani
Diyar khatibi
Da duk wata maryam(my maryams)
Godiya ta musamman ga daukacin yan grp din
Hudallah and Rahmatullah novels
Fahimta novels
Hausa novels
S A AZEEZ Novels (maman khairee)&
FANTASTIC START WRITERS (F S W)ππΌ
Ina godia ga daukacin masoya fans din AL 'AMARIN MARYAM, wanda na samu damar ambata da wadanda lokaci bai barni na fada ba. Masu bugomun waya da masu yimun text harda masu biyoni in box. Dafatan ni da ku gaba daya xamuyi koyi da kyakykyawan halin "MIMI LUV"π
Tammat bihamdulillah.
Sai munhadu a sabon novel dina in Allah ya kaimu 2018.
Ms Hajia π