Showing 186001 words to 189000 words out of 205258 words

Chapter 63 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

tace "shiga maxa kiyi ina jiranki" Mimi ta shiga mama kuma ta koma daki ta matso mata maclean a jikin brush dinta. (Haka Kullum ake mata bayan tayi wankan sabulu xatai na magani a bandakin dake tsakar gida, abunda yasa batayi a na cikin daki sabida baci tiles din keyi da maganin. Bandakin waje kuma siminti ne)








Tana fitowa mama ta bata brush tayi mama ta koma daki, ta gama brush din ta daura alwala lokacin qarfe tara saura na safe.






Sabida gudun da yake shararawa ya iso da wuri, jikinsa rawa yake wanda baisan dalilin hakan ba. Faduwar gaban ta qaru dai dai lokacin da yayi parking kofar gidan, jikinsa a sanyaye ya fito ya rufe mota ya shiga gidan da sanda.








A xaune ya tarar da ita akan kujera a bakin famfo ta idar da alwala tana xaune kawai, daure take da qaton towel wanda ya saukar mata har qasa da kuma qarami akan kafadarta.








Ya qura mata ido yana kallon bayanta, duk da bega fuskarta ba amma ya hango qanqancewar da tayi da kuma duhun da tayi. A jikinta taji ana kallonta, ta dago takai dubanta bakin qofar. Kamar a mafarki ta hangoshi tsaye hannayensa xube a aljihunsa, ya rame sosai yayi fayau kana ya qara haske, sai taga ramar tayi masa kyau. Kamar yasan ta kwan dashi a ranta, kodai gixo yake matane?








Ta miqe ta nufeshi bayan sun dau tsahon 3 minutes suna kallon juna. Ta tsaya a gabansa tace "ya Bature" yace "Baby Mimi" tayi tsalle ta daneshi ya qara dagata dai dai tsahonsa ya mannata a qirjinsa, suka dunga sakin ajiyar xuciya a tare. Sun dade a haka, kafin Mimi ta tuna barinta da yayi ko waiyaye beyi ba bare kiranta a waya, kai amma ta bada kanta, babu jan aji balle nuna masa ranta ya baci. Ta sauka daga jikinsa ta daure fuska ta fara kai masa duka tana cewa cikin kuka "shine ka tafi ka barni, nayi ta shan wahala ni kadai sabida na xama mahaukaciya ko?" ya toshe mata baki ya marairaice ya riqe kunnansa yace "na tuba maryam, wlh kina raina dake nake kwana nake tashi, babu yadda banyi ba su mumy su bani ke sukaqi, dubi kikaga yadda na koma ba rayuwar jin dadi nake ba acan kewarki ta hanani sakat ishaq da Farida shedane akan hakan." basusan da mutane a gurin ba sai da sukaji Anty tace "amma kedai anyi marar wayo. Sai da kika warke sannan ya dakko qafa zai miki dadin baki irin na maxa, dacan mexoba sai yanxu?" Mimi ta juya tana kallonta, ashe hardasu Baffa da mama da Umma a gurin. Kunya ta kamata, wato a gabansu suke wannan rungume junan?








Baffa ne ya tsawatarwa Anty da cewa "ke meyasa duk kalamanki babu na alheri kona dattijantaka aciki? Ina ruwanki dasu? Mtsew Allah ya shiryeki jamila" ya shige daki. Mama tace "lale da Babana yanxu kake tafe? Shigo ciki mana" ya sosa qeya dan shima yaji kunya yace "wlh kuwa mama" yayi gaba Mimi na binsa suka shige dakin.










Mimi tana gefen qafarsa kan centre carpet, mama ta shigo ya sauka qasa suka gaisa. Sun dade suna hira yana tambayar jikin Mimi tana fada masa duk yadda akai bayan tafiyarsa. Ya tausayawa Mimi dan tasha wuya ba kadan ba, ya dunga godiyar dawainiyar da mama sukasha da ita, mama tace suje su gaisa da Baffa fita xaiyi.








Can ma dakin Baffa sun dade da shi suna hira akan ciwon Mimi, sannan Baffa ya fita kasuwa. Ya dawo dakin mama ya tarar da Mimi yadda ya batta sai flask din kunun tsamiya da ke gabanta, amma ta kasa sha gani take kamar baxai dawo ba. Dawowarsa yasa ta saki ajiyar xuciya, ta tsiyaya masa kunun a kofi ta miqa masa ya karba ya ajiye. Mama tana shigo masa da kayan breakfast, ta kawo kayan tea sannan ta xubo masa wainar shinkafa (masa) da stew ta ajiye, ta koma ta xuba masa dumamen tuwon shinkafa miyar zogale. Sai data cika centre table din tab da kayan abinci yanata yimata sannu, kana ta fita ta basu guri ta tafi dakin masu aikin gidan suna hira.






Yana ganin fitar mama ya tashi ya xuge labulen falon ya koma kujera ya xauna ya janyo Mimi jikinsa, ta kalleshi tace "nayi missing dinka" ya hada goshinsu yace "to nunamun a aikace my luv" ta hada bakinsu ta fara kissing dinshi tana romancing dinsa. Ya saki jiki ya bar mata fagen, yau ta shayar dashi mamaki sosai daman ta iya irin wannan amma bata taba nuna masa ba? Ganin yana neman fara sambatu ta rabu dashi don ya fara nishi. Ya kalleta idonsa jajur yace "kinyi naki Mimi luv ni kuma bari in nuna miki kewar da nayi" ya sunce towel din jikinta ya dunga lasarta yana wasa da qirjinta dakyar ta tsaidashi ta hanyar nuna masa a gida fa suke cikin dakin mama.






Rashida tana dakin Mimi tana baccin safe taji maganganu qasa qasa ta tashi ta dan leqo ta labule ta hangesu Mimi xaune dirshan akan cinyarsa shi kuma yasa bisa wuyanta yanata lasheta. Ta koma da sauri dafe da qirji tace "Mimi kinyi saar miji, kinsha wuya ada amma yanxu dadi yaxo Allah ya samu danshinki"






Ta kwaci kanta ta koma kan centre carpet din tana maida numfashi, shi kuma lashe lips dinsa yake. Ta qara miqa masa kunun data xuba masa, ya karba yana kurba yana bata itama tana sha, ya gama yaci masa ita kuma bata shaawar cin komai.






Suna nan xaune mama ta shigo da sallama ta miqo mata waya Faty ce ke kiranta. Ta dauka suka gaisa Faty tace "Mimi fate fate nai miki na tsaki amma babu dan aiken da xai kawo miki" Mimi cikin zumudi tace "Allah ya Faty? Har kinsa yawuna ya tsinke ya Bature yaxo yanxu xai kawoni sai inci anan" Faty tace "to sai kinxo, ki sauri karya huce"








Bayan kashe wayar ta kalli mama tace "mama dan Allah muje?" mama tace 'ni na isa in hana? Adawo lfy" ta tashi ta shiga cikin dakinsu ita da Rashida don shiryawa.








Ta qara dauraye jikinta a toilet, ta fito ta shafa mai ta ciro wata gown zata saka. Rashida ta tsaidata ta miqo mata wata atamfarta holland irin igbo wrapper dinnan (kalar ibo) dark blue ce sosai me adon orange atamfar tayi kyau sosai, ta dinkata bata taba sakawa ba. Mimi ta kalli atamfar tace "Rashida kya bani atamfarki me tsada in saka bayan baki taba sakawa ba?" tace "Anty mimi ai kinfi atamfar a gurina, kuma kyauta na baki, ki karba ki saka kiyi kwalliya tunda da Bature xaku fita." Mimi tasa hannu biyu ta karba tace "nagode Allah ya baki dubunta Allah ya qara xumunci" Rashida taji dadin adduar Mimi tasan Mimi tafi qarfin suturar 100k ma, amma sabida karamci tana ta godia don anbata tufar da bata kai 30k ba.






Ta daura zanin rigar fitted ce me dogon hannu, dake ta rame sai ta shigeta ta dan matseta kadan. Cikin ya fito dan kurcici, wuyan rigar wagege qirjinta ya fito ta sama. Ta daura dankwalin ta shafa farar powder tasa farin man lebe ta dan maqala barima, sai taga tayi kyau kodan ta kwan biyu bataga madubi bane?










Ta fito falo ta wuce dakin mama yana binta da kallo, ta fito da mayafin mama orange da takalmi shima plat orange ta yafa mayafin a kafada tace "ya Bature taho mu tafi" ya miqe yadan yaye mayafin data rufe qirkinta dashi ya qurawa qirjinta daya qara cika dam ido. Kunya ta kamata tayi gaba tana cewa "saika taho"






Suka tarar dasu mama a tsakar gida dukkansu, sai a lokacin Bature ya gaida su Umma. Mimi tana gyara mayafinta cikin xumudi ta riqe hannun Bature tace "mama xamu tafi" mama kallon ikon Allah take, yau Mimi watanta daya da kwana uku cif tana xaune cikin qunci da rashin walwala amma cikin awa daya da xuwan mijinta mama taga farin cikin da rabonta da ganinsa a fuskar Mimi tun xuwanta sunan Faty.








Bature ya katsewa mama tunaninta yace "mama xamu dade fa har gidan mumy xamu dan banjeba nan na sauka" tace "to adawo lfy, Allah ya kiyaye" sukace amin suna riqe da hannun juna suka fita.








Ta baje a kan centre carpet din falon, Faty ta miqo mata farantin faten tsaki wanda yasha yakuwa, shiwaka da busashshen kifi ta cire dan kwali ta fara sha tana santi. Bature ya dubi Faty yace "dan Allah tsefe mata gashin nan, inaga rabonta da kitso tun wanda Farida tasa akai mata acan, kan duk ya cude ko tsagar ba a gani" Faty tace "to gaskiya kam ai bata gyaran gashi akeba a lokacin shiyasa bamu kula kanba" ta dakko kibiya tahau saman kujera tanawa Mimi tsifa qura na tashi akan, tace "tab, ga yanda qura ke tashi kuma ni sainaga gashin ya kuma haukata da yawa, kodake ance gashi bashi da xuciya in ba a gyarashi yafi fitowa." sunata hirarsu Bature na gefe yanawa Mimi sub awayarta wacce yaxo mata da ita yanxu ya kunna yasaka kudi. Mimi nata aikin shan faten.










Ahmad yayi sallama ya shigo, idonsa Mimi ya fara gani yace "kai lallai maryam jikin yayi sauqi har an fito?" sai a lokacin yaga Bature ya qara cewa "au ashe tare kuke yaushe a gari? Daga xuwa har kun mayarmun da mata baiwa kunsata tsifar kai"










Kukan Mimi ya katsesu, suka dubeta a tare da tambayarta menene? Ta kwabe baki cikin tsabar shagwaba da rigimar data koya tun bayan fara ciwo tace "Ba ya Ahmad bane ya dena sona" suka kalli juna suna qunshe dariya, Ahmad ya matso kusa da ita yace "Mimi wayace miki bana sonki" ta qara narkewa tace "da kana sona kana ji dani kana cemun mimina ko kacemun autarmu, amma yanxu duk ka dena" yadan dara kadan yace "haba Mimi, ba dena sonki nayi ba. Gano nayi gatan yayi miki yawa, ga mama da Baffa, ga ya Faty da ya Bature, sannan ga mumy da Dady. Shiyasa nace toni bari in xama Faty ita kadai tunda ita duk anbarta an tare a gurinki" ta xunbura baki tace "to nidai kaci gaba da sona kawai" yace "to angama ranki ya dade autarmu" suka dunga dariya a ciki karta gani ta kuma rigima. Dake kitson ya tsufa babu dadewa suka gama tsifar suka tafi.








Saloon ya kaita, suka wanke mata kan akai steaming, basu da irin mayukan da take retouching dasu shiyasa ba aiba. Yana zaune akai mata aka wanke qafa sukai mata gyaran fuska. Ta fito ras, gashin ya kuma cika da tsaho ta bakin Faty.








Sha biyu da rabi sukabar gurin, gidansu wato NNDC ya wuce da ita. Suka shiga falon komai yayi qura, da takalmansu suka taka har master bed room din. Yayi qura sosai har rumfar gadon. Yaye bed sheet din ya dage rumfar gadon, ya janyota suka fada kan gadon da babu shimfida.










Ya qura mata ido can kuma ya fara romancing dinta sosai, itama ta tsinci kanta dason kasancewa dashi ta fara mayar masa da martani har takai ga balle masa botiran shirt dinsa. Sun maqale sunata yamutsa juna. Ya dakata tsam daya tuna last kwanciyarsu data nuna bataso yayi forcing dinta a qarshe ta tashi da ciwo, wannan dalili yasashi fasa abunda yayi niyya ya hadiye xalamarsa a tunaninsa insunyi ciwonta xai iya tashi kuma dole xa a gane dalili tunda saitayi wanka. Ya yunqura da nufin tashi, Mimi ta riqeshi ta marairaice tace "ya Bature ina xaka? Meya tsaidaka?" yadan fara qinqina "Mimi Baki da lfy ne" ta qara shigewa jikinsa tace "nifa na warke dan Allah karka barni haka kaxo muyi soyayyarmu" baice komai ba ya xameta ya kwantar ya shiga toilet. Tabishi da kallon mamaki, meyasa maxa ke hakane? Da itace bataso shi yakeso da koxata mutu sai yayi amma take shine bashi da raayi yanxu ya gujeta. Tace "nima maganina kenan rashin jan aji ya jawomun amma xakasan kayi da yar halak saina rama"








Ya fito da alwalarsa, yayi shirin masallacin juma a. Bata nuna masa bacin raiba ko a fuska, yace "taso in kaiki gidan Audu inje masallaci in dawo sai muje gidan mumy" ta miqe ta bishi ya rufe gidan suka fita.








Ya kaiwa yasmin ita yace ga ajiya nan ya kawo, tace "to ya Bature" dake masallacin sharada yaje bai jima ba ya dawo itama tayi sallar suka tafi.








Sun tarar mumy a Ita kadai Dady bai dawo masallaci ba, ta rasa inda xata sakasu. Ta hada musu abinci sukaci tana daga xuwa kaje ka tattagota? Yace "mumy saloon na kaita kanta duk ya cude" bayan sun gama cin abinci suka dawo kan carpet suna hira. Dady ya shigo daga sallah, Mimi tayi saurin jan mayafi ta rufa a kanta tana gaisheshi. Bature yana harararta ya riqe kafadunta ya xaunarta yace "Dady ya yafe tsugunan gaisuwarki, ki daina takura kanki" mumy ta dakko kayan kitso tace da Mimi "matso in kitse miki kannan, babu dadi xama da tsifaffen kai" Mimi dai tana kunyar Dady ta cire dan kwali aka fara yimata zanen hannu. Bature kusa da Dady sunata hira, little ta shigo daga skul take dauke da jakar makaranta. Ta kalli mumy dakewa Mimi kitso tace "kai mumy babu nacin da banyi ba kiyimun kitso kinqi sai gashi yanxu kinawa Anty Mimi, wlh nima sai kinmun" Dady ya jawota ya xaunarta gefensa yace "sai haquri uwata, kinga fa ita Mimi yanxu ta fiku matsayi gurin mumy, na farko itadin yarta ce, matar danta datafiso,sannan kuma uwar jikanta nan gaba kadan" mumy tace "kai Dady wayace maka shi nafiso? Ga autata nan me sunan mamana" little tai karaf tace "to tunda kinfisona nima kimun kitso" tace "xan miki Kinji uwata" Dady ya tashi ya shiga dakinsa ya fito da wata jaka, yaxo ya xauna yana xuge jakar yana cewa "mami ce tayo aike tun last week aka kawo na manta sai yanxu dana ganku na tuna" Suka bude jakar, kayan jarirai ne unisex da yawa amma overall sunfi yawa masu kyau da suck da takalman jarirai. Suka dunga dagawa Dady yace "Mimi tace a bawa afara ajiyewa xata dunga aikowa dasu" suka dunga daga kayan ana yaba kyansu, Mimi dai kunya ta hana ko kallon kayan tayi bare ta taba. Bature ya daga wata safa yace "wannan yar safa kamarta yar tsana cewa akai mata doll Mimi xata haifa?" little tace "ya Bature ai safar hannuce" yace "Ok" tace "now tell me Baby girl kakeso ko Baby boy" yace "bani da zabi little duk wanda Allah ya bani inaso" tace "to Allah ya baku kamar ni kuma Baby girl" yace "haba little ya xakiyimun fatan haifar kamar ke ai kafin ta girma munsha wahala, kuma wannan kafirin iyayin naki mukaishi ina in muka haifi irinki" Mimi ta dunga yimusu dariya.






Dady yaja Bature daurin auren dan abokinsa, Mimi kuma mumy ta jata bed room dinta tana shirya drawer Mimi na kwance kan gado suna hira, babu yadda Mimi bataiba mumy ta bari ta shirya mata kayan amma taqi tace tai hutawarta ita data tashi daga ciwo.






Sunanan har akai sallar la asar, mumy na mitar ina suka tafi suka dade haka, ya bar Mimi bai maidata gida ba har sai lokacin shan maganinta ya wuce. Suna haka Lubna taxo, ta xauna kusa da Mimi da cewa "a a yar tsanar ya Bature, yau nayi farin xuwa na tadda ki gidan ya jikin?" Mimi bata fuskanceta ba tace "wacece yar tsanar?" Lubna tace "ke mana" tace "yaushe kika sakamun wannan sunan?" Lubna tai far da ido tace "tun washegarin kaiki da naga yadda yake daukanki kamar yar tsana na saka miki" Mimi tahau qifta mata ido wai tayi qasa qasa kar mumy tajisu. Lubna ta matsa tai qasa da murya tace "ikon Allah wai Mimi dauke da cikin ya Bature, to ya akai kukai cikin? Cewa yake kixo kuyi ko ke kike kai kanki?" Mimi ta galla mata harara tace "ki xama quda ki shiga dakin ki gani mara kunya" Lubna ta kuma kecewa da dariyar shaqiyanci ta juya ta kalli mumy taga hankalinta baya kansu ta kuma cewa "ana ganinku simi simi kamar mutanen kirki, amma wai kun iya lalube juna" Mimi ta yunqura xata kaiwa Lubna duka ta kufce tai waje tana dariya, Mimi ta bita a dai dai kofa sukai karo da Bature daya shigo. Ya riqeta ya tambayarta menene? Tace "Lubna ce ta tsokaneni xan bita in rama" yace "yi haquri kyaleta xan rama miki yanxu ba daya kukeba karki fadi garin binta." taqi haqura ita kuma lubna sai gwalo take mata, sai da mumy tasa baki ta haqura.








Basu bar gidan ba sai bayan isha shima saida mumy ta matsa masa sannan yaje ya siyo mata kayan ciye ciye ya maidata.








Washegari ma yaxo ya dauketa suka dunga xaga gidajen yan uwa har gidan hajja, sunji dadin ganinsu ta dakko musu maganin data karbo musu na tsari ta basu da bayanin yadda xasuyi amfani dashi ta kuma maimaita Bature yayi amfani dashi ko ransa ya baci don takakkiya tayi har garko ta karbo musu tana cewa "inbanda iyayen yanxu sa turaku Abuja babu tsari ai dole a jefeku bare anga sai daukaka kuke samu" bata barsu haka ba sai da tayiwa mumy waya tace ta kula su tabbar Bature yayi amfani da maganin. Ai kuwa mumy ta hanashi sauka a gidansa anan gidanta ya xauna kuma ta tsaye sai da yayi amfani da maganin.








Acikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login