Showing 141001 words to 144000 words out of 205258 words

Chapter 48 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt

yasan acikin matansa duk wacce za aiwa yarta aure ko cokali bata siya, amma fadima abikin Faty dana Mimi ta nunka abunda ya kashe wajan sau 3, baiji ragowar abunda momy take fada ba saboda tunanin da yake, sai dai kawai ya tsinci kansa da yi mata godiyar kayan da suka kawo.


Ba yanda yaya Faty batai da Mimi ba taje wankin kai da qunshi amma taqi, da kyar fauxa qawar mimin maqociyarsu ta lallami mimin suka tafi saloon akayi mata shampoo aka gyara gashin, qunshi kuwa qiri qiri taqi zuwa dole sai yaya Faty ce tasa me kunshin tazo har gida tayi mata. Duk da cewa Badaru be bada kudin event din yan mata ba, yan uwanta sun kama gidan dan hausa inda xa ayi luncheon kawai, domin ko sun qara wani event din Mimi bazataje ba, dan luncheon dinma cewa tai ba inda xata.


Ana gobe kamune akaje kafi (jere) gidan amarya ko 2 hours masu jeren basuyiba suka dawo jiki a sanyaye, domin kuwa wata yar qaramar gida Badaru ya kama haya a wani Geto area da nufin nanne gidan Mimi. Gidan dai yafi kama da gidan student wanda suke kamawa inbabu guri a hostel, domin dan qaramin tsakar gida ne sai qofa daya wacce inka shiga xaka tadda falon da ko Set din kujeru baxai ci ba sai bedroom daya da toilet aciki sai dan kicin dan qarami daga hagun falon, irin kitchen da in kin shiga bazaki iya tsgunawa ba saboda qanqantarsa.


Wannan gida ya faranta ran maqiyan Mimi na gida (irinsu Umma da Anty da kuma wasu daga cikin yayansu) da na waje. Anty ta dunga murna tana cewa yarinya dai ko FARHAN kitchen aka sai mata a banxa tunda babu gurin xubawa, domin kuwa ala dole aka juyo da kayan Mimi gida dan abunda ya samu shiga cikin gidan ba wani yawane dashi ba, don ko fridge da cooker gas basu samu shiga ba sai dan qaramin gas aka siya mata irin na yan hostel. Direct aka wuce da kayan gidan kakakannin Mimi (gidan mal SULAIMAN) aka jibge.


Matar babban yayan su mama (Umma) da momy suka dunga masifa akan wulaqancin da gidan su badaru sukaiwa Mimi akan gida kuma haka suka samu Baffa da xancen, shima da yake bayason harkar qaranta a take ya nemi mahaifin Badaru da zancen, har yana barazanar inbasu da wuri ajiye maryam a fasa auren dan ransa ya baci shima, alh inuwa ya dunga bawa Baffa haquri da cewa wlh suma sai a qurarren lokaci Badaru ya nuna musu inda zai saka maryam kuma basu so hakan ba, amma su kwantar da hankalinsu ya kusa gama gininsa. Wannan ne yadan kwantar da hankalin masoyan Mimi, amma duk da haka qananan maganganu sunyi ta kai kawo a tsakanin mutane akan auren.


Ranar alhamis itace ranar da aka fara bikin ko ince ranar luncheon, duk yanda aka kai da lallaba Mimi ta tashi tai shirin tafiya Gidan Dan hausa gurin luncheon Sam taqi anyi fadan anyi nasihar anyi waazin duk taqi ga dukkan alamu halinta na kafiya ya motsa, ala dole aka kyaleta ganin ciwonta na daukewar numfashi na alamun tashi domin qirjinta sai bugawa yake wanda shine alamun ciwonta yana gab da tashi, duk ta yankwane tayi wata irin migues rama duk wannan cikar jikin ta xube a 10 dayz, sai idanuwa xuru xuru da qasusun wuya.


Haka dai aka dade aka barta a gida daga ita sai kakarta (hajja maryam) wacce taci sunanta kenan sai kuma mama da tace ina xata yarta babu lfy? Hajja ce ketaiwa Mimi nasiha da falalar yadda da qaddara mama na gefe tana shafawa hajja mai a qafarta saboda wankan da tayi, nasihar ta shigi Mimi sosai saboda kwatancen da hajja tai mata da mama mahaifiyarta da kuma irin quncin da ta shiga a dalilin damuwarta, a fili hajja ke nuna San Mimi fiye da duk wasu jikokinta tanason yarinya fiye da tinanin me karatu.


Mama kuwa ko kallon Mimi batason yi saboda kwantsamewar da Mimin tayi, kuma sau tari in ta kalli Mimi sai taga kamar tana kallon hoton rayuwarta ne ta baya, domin itama haka ce ta kasance gareta lokacin aurenta na fari. Ta maida hankalinta kacokan kan kula da hajja ( mamanta) wacce tazo bikin Mimi da nufin sai angama xata tafi.


Bayan magriba yan bikin da babu amarya suka dawo, atsakar gida suka jiwo muryar anty na cewa wannan wane irin biki ne kamar na bagudajiyar qauye? Biki lami kuma dan abun kunya event daya? Neman kudi anan dai beyi rana ba wlh, shiyasa amaryar taqi xuwa ta qirqiri ciwon qarya πŸ˜„. Ai wlh ba a taba abun kunya a gidannan irin wannan ba domin ko taron suna ake a gidannan anayin shagalin da yaci uban wannan kai andaiji kunya wlh, lallai kwantai beyi ba, πŸ˜‚ dama haka bikin yan kwantai yake komai tsiya 2 ? Allah ka cigaba da bawa yayanmu miji da wuri tun suna da quruciyarsu. Babu wanda ya kulata a dangin mama da suka cika gidan domin hajja ta hana a tanka mata a cewarta wanda ya tara jama a baya fushi ko fada in yayi fushi to ya bata taronsa.




Washegari juma a aka daura auren MARYAM AL AMIN da BADARU MOHD INUWA akan sadaki 50k, kuma a take Baffa ya kirata ya bata sadakinta kamar yadda addini ya tanada, tana shiga daki ta wullar da kudin sadakin ta sa kuka, sai mama ce ta dauke kudin. Washegari akai yini anan gidan babu wani armashi qarfe biyar aka tafi kai amarya kasancewar unguwar da xa a kaita da nisa sosai da kyar aka fito da ita daga gidan domin ta qanqame mama tana kuka da kyar momy ta banbareta daga jikin Maman tai waje da ita tasata a mota, momy da wata yar uwar su Baffa (qanwace a gurinsu baffan) mama saude suka shiga aka tafi kaita.




Mrs😊[9/30, 1:04 PM] β€ͺ+234 706 296 6299‬: πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌAL 'AMARIN MARYAM πŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌπŸ™†πŸΌ



Writing & story by rahman Mohammed (hajia)


Editing by mmn khairat
πŸ“FANTASTIC STARS WRITERS {F S W }


Page 5⃣5⃣








Yayi mamaki kwarai daya tadda Mimi gidansu dake NNDC, ta gyara gidan qal komai need da taimakon sabuwar yar aikin da mumy ta samo mata. Kamar ta shiga xuciyarsa dama wanka yakeson yi yaje gidan mama ya dakkota sai gashi ya sameta gida, afili yace kai mace mai hankali da tunani tayi a arayuwa.








Ranar tasha aiki don gaba daya maxan wato qannansa da ishaq anan gidanta suka sha ruwa. Ta fuskanci a dabi ance Bature meson nasa yaxo kusa dashi ne don duk sanda yan uwansa sukaxo gidansa yakan rasa inda xai sakashi.






Ana gobe sallah aiki yai mata yawa sosai ita da Aisha sunan sabuwar me aikin ta kenan. Ansanar da ganin wata tun tuni, ta kwaba funkaso kana adaren tai miyar agushi ta soya naman kaxa da yawa tayi zobo tasa a fridge.








Tun hudu ta tashi ranar sallah ta dora tuwo, ta dafa shayi wanda yaji kayan qamshi sosai. Ta koma ta taya ya Bature shirin tafiya idi, 7:30Am ya gama ya fito cikin falon inda tagowar yan uwansa ke jiransa don tafiya idi. Fuskarsa ta nuna tsantsatsar farin cikin da yake ciki ganinsu kowanne da cup din tea din da Mimi ta dafa yana kurba, suka dinga gaisheshi yana amsa tare da yimusu barka da sallah. Ishaq kuma ya miqa masa hannu suka gaisa. Mimi ta miqa masa cup din nasa shayin, yana kurba da sauri don sunso yin late. Yana ajiye cup din ta matso ta dora masa hularsa ta gyara masa ita sosai kana suka tafi.








Kafin su dawo wadda ta bawa aikin waina (masa) da sinasir da kawo don ita aikin ya mata yawa shiyasa ta bada aikin ita kuma tai miyar.








Ta shimfida musu ledar cin abinci babba akan centre carpet ta jera musu duk nauin abincin da tayi akai sannan ta kawo ruwa da drinks na kwali ta hado da xobo da kunun ayar da tayi yanxu duk ta ajiye da isassun plates. Matansu suka dunga kawo nasu abincin sallar duk wacce ta kawo Mimi anan take ajiyewa. Farida ce ta karshen kawo nata girkin. Ita kuma yasmin uwar malalata snacks tayi da pepe chiken.






Ta xuba na na gidan mumy ta bawa Aisha kudin napep ta tafi kaiwa, na gidansu kuma mama tace ta turo huxaifa ya karba don bata da dan aike. Tanata sauri don tanason kafin suxo tai wanka. Faty ma dan aikenta ta bawa nata abincin ya juya mata dashi.








Ta koma daki ta gyarashi, dama shi kadai ya rage bata gyara ba. Tai wanka kwalliya sosai tayi don ta dade batai kwalliya ba sannan kuma koba komai ai tayi kwalliyar sallah. Ta danyi rama bamai muni ba sabida azumin wata daya ba wasa bane, acikin kayanta wanda ta dinka na biki ta dakko wani lace ta saka har yanxu bata gama sakawa ba don tafi saka qananan kaya. Ghana Weaving ne akanta shiku yayi tsam, ta kafa dauri mai steps ta fito da gaban goshinta inda aka dau kitson. Tasa turaren wuta a bunner na jiki ta turare jikinta kana ta saka na daki ta dunga bi dashi kusufa kusufa na gidan tana turareshi ta dire a kitchen.








Suna shigowa falon qamshin turare dana abinci ya musu maraba, komai tsaf gwanin shaawa. Suka zazzauna suna sabe riguna xaa kwashi girki shi kuma ya nufi kitchen don wanko hannu. Ya samu gumbiyar tasa a tsaye tana cire wayar bunner daga jikin socket din wuta. Ta bayanta ya lallaba ya zagaye hannusa a qugunta ya kwanto kansa akan wuyanta yana shaqar qamshinta. Kitchen din qal dashi kamar ba aciki akai aikin abincin sallah ba, sai qamshin turaren wuta yake.








Ta juyo tana kallonsa, tace "har kun dawo?" bai bata amsa ba sai kallonta da yake ya furta sunanta "MARYAM" ta amsa naam "ya Bature" ya zarce da fadar "Allah yayi miki albarka ya biya miki buqatunki na alkhairi ya bamu zuria ta gari, Allah yasa kedin ki xama uwar gidana a Aljannah" idonta cike da kwallah jin dadin adduar da yayi mata tace "ya Bature amin, amma me nayi akaimun wannan kyakykyawar addua?" ya kamo fuskarta dab da tasa yace "a cikin abunda baifi wata hudu ba da auren mu kin cikamun burikana da yawa, burina wanda kika cika yau shine hada mana abincin sallah da kikai ni da yan uwana da qannena, haqiqa na dade da wannan buri inga na hada taron sallah irin wannan sai gashi ba tare dana fada miki ba kinyi hakan. Gashi kinyi mun kwalliya kin gyaramun gida kinsani farin ciki maryam Allah ya biyaki da aljanna" ta amsa da amin. Ya kamota ya rungume tai saurin tureshi ya kalleta dason qarin bayani tace "xaka kwancemun daurin danayi da kyar" ya kamata ya cire dankwalin yana cewa "ai dama ban gama ganin wannan kyakykyawan kitson ba, saina saka anjiqashi xanji dadi" tana dariya tace ."ka makaro yaro babu way" shima dariyar yayi yace "ni xakiyawa wayo ai nasan qalau kike lokacinki beyi ba, haba Mimi luv nayi qoqari fa tun kan axumi a matsayi na na ango" ta kwashe da dariyar shaqiyanci tace "ango ko angogu?" ya kamota yace "xakiga angogu don ke xan goge in anjima" ya manna mata rafar yan hamsin sabbi yace "wannan ki sallami yara kana ya bata ta yan 200 ita sababbi yace wannan kuma nakine barka da sallah" ta sunkuya har qasa tana masa godiya yai saurin riqota yace 'adana godiyar ki in anjima kyamun a gado' ya wanke hannunsa ya fita cin abinci gurinsu ishaq falo.








Itadai tea kawai ta iya sha taje ta kwanta don gajiya, shi kuma suna gamawa ya fita shi dasu audu gaisuwar sallah gidajen yan uwa.








Baccinta baiyi tsaho ba tanayi ana tashinta sabida sai baqi take yan yawon sallah da masu kawo abinci. Qarshe ma sai falo ta dawo ta kwanta, sabida Aisha nata zaryar tashinta. Da azahar ta tashi dole tai sallah, ta fara yan ciye ciyen fruit da tasan xasu kawo mata niima ajiki har gumba ta dama da madara ta shanye. Wajen uku matan suka shigo su yasmin, Farida da sauran matan yan uwansu da suke layi daya suka cika falon anata hira cikin nishadi Mimi ta dakko musu kajin data soya da kunun aya suna ci ana maida yacce akai. Basu tafi ba sai magrib kowacce ta koma gidan mijinta don suma maxan sun dawo har sun wuce masallaci.










Wanka ta farayi kana tai sallah ta jira isha itama tayi, sannan tayi kwalliyarta cikin fitted gown ta atamfa mai dogon hannu budadde daga qasansa. Bata daura dankwali ba ta saki jelolin kitson.










Yana shigo falon da ita yayi arba a kame a falo, idonsa cikin nata yace "kai Mimi badai gayu ba, bari nai wanka naxo naga wannan wankan" ya shige ciki.










Tana nan zaune ya fito, ya xauna kusa da ita ya jawota ya dorata kan cinyarsa yana binta da ido. Tadanji kunyar kallon da yake mata tace "bari in kawo maka abinci" ya katseta "barshi ban tare da yunwa ai" tace "fruit salad fa? " yace "dakko musha" ta miqe tana takawa a hankali yabi tafiyarta da kallo yana murmushi. Ta dakko ta dawo ta xuba masa ya karba ya kuma maidata maxauninta akan cinyarsa yanasha yana bata yana kuma yan tabe tabensa. Hirar batayi wani nisa ba yace suje su kwanta.










Sosai yake nuna yana buqatarta tadan janye tace "ya Bature ka bari sai gobe mana nagaji" yace "haba mana Mimi luv kar muyi haka kinsan yadda nakeji kuwa? Kuma ai bamu tabayi a wannan garin ba ki bari mubar tarihi mana" dama itama jin baki ne don tanaso dan haka ta bada kai bori ya hau. Sambatu ya dunga yi mata sosai, lallai abun in anayi a marmarce yafi dadi kuma anfi riritaka 😜 tunanin Mimi kenan ganin yadda duk ya rude kamar yau farko.








Xamansu mai dadi ya dore a cikin kwanakin sallar, sai kace yau sukai auren bata da kewa ko kadan Kullum cikin baqi take ko yan uwanta ko nasa ko matan abokai. Duk wanda yaxo bata rasa abunda xata bashi.








Har sun fara azumin sittash shawwal, lokacin CDS dinsu yaxo tana kano ta shirya cikin kaki xata tafi ya kalleta yace "corper weeee" tana dariya tace "waaa" taje ta dawo har clearance ta samu. Sai sallah da kwana goma sukai shirin komawa. Su hudu suka tafi a mota ishaq da Bature agaba ita da Farida abaya. Farida da dai an harbu don kusan a cinyar Mimi taje Abuja duk kuwa da maganar da Bature ke mata na ta danne masa mata.








Tarayyarsa da Hanifa tananan a yadda take, har yanxu bata saduda ta daina bautawa na tsugune ba Kullum kudinta suna can. (ni kuwa nace dama kin tashi kin shaidawa mai duka gwanin hukunci da wannan yawon da kike ke a kode xaninki a kode ga asarar dukiya)








Basu jima da dawowa ba hutun sallah suka sami baquncin Anty mami taxo 9ja Abuja yin wani aiki kuma a gidan su Mimi ta sauka, Mimi na ganinta gabanta ya yanke ya fadi amma duk da haka ta danne taje ta taro ta ta karbar mata akwatin hannunta tana cewa "sannu da xuwa Anty mami" tana wani yatsina da basarwa ta banbare Mimi daga rungumar da tai mata, ta samu guri a falon ta harde. Mimi da hadiman gidan suka dunga xarya dan samar mata abun buqata, sai da suka cika centre table din gabanta da nau ikan abinci da kayan motsa baki sannan Mimi taje ta gyara mata daya daga cikin bedroom din dake part din duk da a gyara yake tasa sabon bedsheet da maganin sauro na feshi ta turaren wuta kana ta kai mata jakarta da akwati dakin ta dawo falo gurinta don su gaisa.










Ta durqusa har qasa daga gefenta tana gaidata. Ta juyo tana hararta tace "amma dai kya bari in ci abinci in huta kafin ki isheni da gaisuwarki ta fi'ili" duk da Mimi taji haushin maganar saita danne a fuskarta bata nuna komai ba tace "to" ta tashi ta xuba mata abincin ta shiyaya mata ruwa da lemo ta tura mata gabanta sannan ta koma gefe ta rakuye.










Dake isowar yamma tayi tana cikin cin abincin ya Bature ya dawo, ya nuna farin cikin ganinta sosai ya matsa kusa da ita kamar xai shige jikinta suka gaisa tana fada masa aiki taxo na company dinsu kuma xatai 2 wks ne. Mimi ganin ta amsa gaisuwar Bature duk da tana cin abincin itama ta matsa ta kuma gaisheta. Bature ya kalleta yace "Mimi sai yanxu xaki gaisheta?" kafin tai magana Anty mami ta rigata da cewa "eh ai wai ita isashshiya yanxun ma ganinka yasa ta gaisheni inaka da bakaxo ba baxan samu arxiqin gaisuwar ba, nafi awa daya a gidannan amma ko kallon inda nake batai ba sai yan aiki take ba order a kawon abinci ga mayunwaciya" ya juya yanawa Mimi kallon tuhumar abunda tayi. "ta danne duk wani mamakinta na qaryar Anty mami ita cikin qasqantar da kai tace "yi haquri Anty gani nayi kinacin abinci shiyasa na bari ki gama ki nutsu saimu gaisa, bakyayo doguwar tafiya tun daga wata qasa in tareki da gaisuwa ba" cikin gamsuwa Bature ya jijjiga kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login