Showing 9001 words to 12000 words out of 205258 words
Chapter 4 - AL'AMARIN MARYAM BOOK COMPLETE PDF END .txt
Mama tana zaune kan sofa tana kallo Mimi na kwance itama kan sofa din ta tada kai da cinyar mama hannun mama cikin gashin mimin tana shafawa ahankali. Ta qaraso ta dafa Mimi sannan ta kalli mama, mama Mimi ba lfy? Ta tambaya arikice. Eh ciwon mara take tun safe tasha magani, amma har yanxu be saketa ba. Wayyo inji Faty ta janyo Mimi jikinta ta rungume tana mata sannu mimin ta gyada mata kai cike da galabaita. Ta maida mimin jikin mama ta dau kudi a jakarta tare da cewa ina xuwa ta fita. Can sai gata ta dawo da allura ta bude ta hada, ta kama mimin suka shiga dakinsu dake parlourn ta kwantar da ita a kan gadonsu sannan tai mata allurar. Ko minti biyar bataiba bacci ya dauketa. Taiyi sallah ta canja kaya tazo ta kwanta a bayan mimin bacci ya dauketa itama. Mama taji shirun yayi yawa ta shigo domin kawowa Faty abinci ta tarar dasu kwance kamar yadda suka saba Faty abaya Mimi agaba akan filo daya hannun Faty akan cikin Mimi yayin da mimin ta sa hannunta ta riqe hannun Faty. Wannan shine salon kwanciyar yayanta tun suna qanana wani sa in kuma su rungume juna suna baccin. Tai murmushi ta qarasa ta sumbacesu ta kashe musu fitila taja musu qofa.
Tun Faty na secondry skul masoya sukai mata ca kuma manyan masu kudi da yayan manyan mutane harda jinin sarauta, saΓ dai Baffa yace saita fara makaranta domin haka dokar gidan take, a bangaren Faty kuwa duk basa gabanta domin akwai tsumammiyar soyayyar quruciya aranta, duk kashe kudin da samari keyi akanta baya gabanta hasalima bata kulasu. Tanason Ahmad (yaron maqotansu wanda ke shiga gidansu gurin mama). Tun lokacin da Ahmad ya farga da manyan masu kudin dake kawowa Faty hari ya shiga tashin hankali ba kadan ba, domin ya mace akan Faty tun tana qanqanuwarta kuma da ita kadai yake tsara rayuwarsa, hakan yasa yaje ya sakawa mama kuka da roqarta ta bashi Faty indai baso ake ya kashe kansa ba. Maman ta bashi tabbaci in shaa Allah Faty bata da miji sai shi domin ta fahimci Faty ma tana qaunar Ahmad shi yasa bata kula kowa cikin manemanta.
Duk da Baffa yaso turjewa lokacin da aka gabatar masa da Ahmad a matsayin manemun Faty, domin be tabawa kamar Ahmad (talaka) auran yarsa ba, amma kafewar Faty da mama akan auran yasa dole ya sakko musamman da yaga irin dukiyar da mahaifin Ahmad din ya kawo a matsayin kudin neman aure. Domin a lokacin giyar asiri da matarsa ta dena tasiri akansa, ya kuma bawa Ahmad din gida makeke a NNDC sannan ya samar masa aiki saboda a lokacin ya gama karatunsa har yayi service. Hakan yasa Baffa yadan sakko. SaΓ dai sabanin yadda Baffa ya saba aurar da yayansa iyayensu matΓ‘ ko cokali basa siya shiyake komai kuma na bajinta. Amma akan Faty Set din gado kawai ya siya da Set din kujeru daya yaja bakin aljihunsa ya tsuke, abun ya bata mamaki kwarai ganin yadda yake banbanta yayansa da nata kamar ba yayan dan uwansa ba, amma sai ta danganta hakan da rashin San auran Ahmad din da yakeyi hakan yasa ta fitar da kudi maqudai da hadin gwiwar yan uwanta maza da Adda halima sukayi komai na bajinta suka yiwa Faty kayan daki domin na Baffa ma a dakin baqi aka xubasu, (dama dadin nema kenan) . Akayi aure amarya ta tare dakinta, da ike ance dan halak bai manta alkhairi Ahmad ya riqe Faty hannu bibbiyu ya zamo kamar bawa a gareta tana kammala karatu dayake maaikatan lfy basa rasa aiki, Baffa ya samo mata aiki kamar yadda yakeyiwa duk wacce ta gama karatu acikin yayansa, tana aiki a bangaren karbar haihuwa a AKTH wato aikin unguwar xoma (midwifery).
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
AL 'AMARIN MARYAM
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
Writing & story by Rahma Muhammad {hajia}
Editing by
. Mmn khairat π
πFANTASTIC STARS WRITERS {F S W }
PAGE 1β£1β£
Kyakykyawar budurwace yar kimanin shekaru 25 da haihuwa, skin colour dinta kadai ya isa jawo hankalin duk wani lafiyayan namiji fadawa tarkonta bare aje ga dirinta wato structure cikakkiyar fuska gareta me dauke da π darara farare kal, komai na fuskarta matsakaicine wato mastada 'a kamar yadda muka siffanta abaya, bakinta dananne kadan dauke da haqora masu kyau farare kal, wanda daka gani kasan ana ziyartar Dental clinic duk bayan wata 6 domin wankesu, koyaya ta motsa bakinta dimple dinta saiya bayyana. Duk da a ganin mutane MARYAM ba wata kyakykyawa bace compared to yar uwarta faty, ni dai anawa ganin MARYAM kyakykyawar gaskece, saboda ba lokaci daya xaka kalleta ka gano kyan nata ba, nooo sai ka nutsu sosai sannan xaka gano baiwar kyau da Allah ya azurta MARYAM dashi. Bayan haka kuma aiba fuskar mace kadai ake kalla ajikinta asan cewa kyakykyawa ce, da yake mafi yawan mutanenmu sunfi gane cewa farar fata itace kyau, wanda Sam ba haka abin yake ba. Hannayen ta dauke suke da wasu irin xara xaran yatsu wadanda aka tara musu farce (kumba) dai dai misali ma ana ba zaqo zaqo ba, gashi an qawatasu da jan lalle hannu da qafa, qafarta mai ban shawa awa yar dundubus kamar jikinta, yatsun qafarma kamar na hannaye suke zara zara. Gashin kanta wanda cikar budurci tasa ya qara haukata da tsaho da yawa ya kwanta luf saboda amfani da mayukan gyaran gashi irinsu MEGA GROWTH, kwanciyar nada nasaba da retouching da yake samu duk bayan 8 wks saboda shampo baya wuce sati 8 akan Mimi zai fita, fuskarta kawai inka kalla kasan tana gashi saboda gashin dayacika gaban goshin hadi da sajenta. MARYAM AL 'AMIN kenan (Mimi). Wacce yan watanin kadan baya ta kammala degree dinta a fannin sharia (law) a B U K.
AL 'AMARIN MARYAM ya farane tun daga kammala secondry dinta ko ince angane AL amarin ne alokacin da yakamata ace Mimi tana da manema (samari), duk wanda yaji ko yaga Mimi zaiyi mamaki kwarai ace bata da saurayi daya tilo koda na rage dare ne. Duk da cewa Mimi macece mai farin jinin mata a lokacin da take jami a, amma hakan yanada nasaba da kwakwalwa (brain) da Allah ya hore mata, hakan yasa tayi qawaye yayan manyan mutane da kuma dai dai ita yan middle class, wasu sular qawancensu saboda kamun kanta da gayu da kuma kwakwalwar da take dasu wasu kuma sunasan Mimi ne saboda haduwar jini. Sai dai a bangaren samari ba hakan take ba ga Mimi, domin xata iya cewa tunda takai xamanin yan matanci bata taba wata 1 cikakke da saurayi ba, to samarin ma duk gasunanne ma ana yarane qanana masu xaman banxa ko dalibai wanda suke qarqashin kulawar iyayensu balle abasu aure. In saurayi yazo wajen Mimi da wahalar gaske ya dawo inma ya dawo din baya wuce zuwa biyu xai dauke qafa dan kansa, kudan shekaru 6 kenan ana fama da wannan matsala, wadanda suka taso tare a yayan Baffa guda duk anmusu aure hardama yayan dangi na gurin uwa da uba, hakan ya janyo mata gori sosai ita da mama tun anayin abun cikin habaici har takai ana fitowa fili a gotanra musu, musamman inya kasance saurayi yayi musu hidima, (lokacin axumi ko toshin sallah) lamarin dake saka mimin qunci ta shige daki tayi ta kuka ba domin tana musu hassada ba saΓ dan ta rasa yadda zatasa kanta taji, tunda take bata tabacin ficikar namiji da sunan yana sonta ba to inama samarin suke??? Domin saita shafe shekara ko karen mota be leqo da nufin neman auranta ba. Ta rasa wani irin al amari ne wannan, ko a dangi anasamun masu goranta mata ta haryar shagube da cewa ah! Kedai Mimi kinqi aure kina jiran me kudi ko? To ai kwayi auran tare da yayanmu, abun takaicin da yawa daga masu goranta mata yan uwantane na jini kuma na jiki wanda ya kamata ace sun jajanta mata sai dai aduk lokacin da irin hakan ta kasance yaya Faty intana gurin takan kare mimin da cewa aure ai lokaci ne, ita Mimi nata lokacin baiyiba.
A bangaren mama AL AMARIN Mimi na mutuqar daure mata kai, domin Mimi macece Abida (mai yawan ibada) domin da ace ibada tana bada miji da Mimi bata rufe shekaru ashirin ba tare da aure ba, amma da yake aure AL 'AMARI ne na Allah sai gashi shiru, ta bangaren kyau, tsafta,gayu,nutsuwa da gwarjini badan ita ta haifi Mimi ba xata iya cewa ta dade bataga mace irin haka ba. Ta rasa a inda matsalar take amma ta tattara ta barwa ubangiji lamarinsa itadai kullum goshinta a qasa tana roqawa Mimi da ma masu irin matsalarta Allah ya kawo musu mafita. Duk da xuciyar mama tasha shawartar maman akan taje ta samu daya daga cikin yan uwanta maxa su hada mimin aure da yayansu kodan saboda matsin lambar da mimin ke fuskanta a gurin Baffa, amma abu daya ke taka mata burki wannan Abu kuwa shine : kada auren ya tabbata daga baya mijin ya wulaqanta Mimi saboda bashi ya nema ba, bashi ita akai, kuma dama ance matar shige bata daraja. Kuma inta xurfafa tunani sai taga da daya daga cikin yayan yan uwan nata sunso ai da sun furta San auran Mimi tunda duk SΓ‘ anin ta na bangaren jikokin mal SULAIMAN anmusu aure. Tana mutuqar tausayin Mimi, yarinyar bata da qoshin lfy amma tana da qarfin xuciya, indai Mimi na gida to mama aikinta xamane kawai ko kuma tayi dinkinta abunta sai taso xata taya Mimi da aikin girki kona shara amma duk aikin da mace ya kamata tayi a gidan miji Mimi ta daukewa mama hakan ya qara xafafa qiyayyar mimin a gurin Umma da Anty wato kishiyoyin mama matan Baffa, badan basu da yayan da xasuyi musu ba sai dai dan basu yiwa yayan tarbiyar temaka musu ba.
A bangaren Baffa kuwa shi babu ruwanshi domin aganinshi iya shegene ya hana Mimi fitar da mijin aure, saboda shi Allah bai taba jarrabashi da dadewar yaya agabansa ba babu aure da sun fara jami a kamar jira suke Allah yake kawo musu miji. Hakan yasa ya dau lamarin Mimi iya shege. " in har baki fitar da miji ba har kika kammala makaranta to tabbas xan cire hannuna daga kanki domin naga abun naki ya koma iskanci, neman xubarmun da mutunci kikeyi a unguwa gandamemiyar budurwa dake kina yawo a gari ko kunya bakiji tun kina xuwa auran sa anni kin koma xuwa na qanne." wannan shine fadan Baffa Kullum akan Mimi, wanda yau da gobe tasa mimin haddacewa kaf, kuma hakance ta faru domin bayan graduation din Mimi anyi sallah qarama ba dadewa kuma a wannan sallah Baffa ko sisi baibawa Mimi da sunan kudin kayan sallah ba lamarin da yayiwa matan gidan da yayansu dadi kwarai, kuma wannan alamarce ta nuna tabbas Baffa ya cire hannu akan Mimi kamar yadda ya alqawaranta, ko gaisheshi tai a ciki yake ammasawa shi a lallai yana fushi da ita kan abunda ba ita ta dorawa kanta ba (Allah sarki).
A yanxu haka da take shirin tafiya law school, a gidanma shirin aurar da mutum 3 biyu mata wadanda mimin ta girmesu da shekaru 3 sai namiji 1 yaya Ali, wanda ya kasance da na biyu a jerin yaya mazan gidan, domin dan Baffa namiji na farko (yaya jafar) wanda kuma ya kasance dan Umma yana kaduna yana aiki , kuma da shine yake nuna kamar yanason Mimi duk da bai furtaba amma daga baya maganar tabi ruwa tun bayan samun canjin gurin aiki daga kano xuwa kaduna. A duk lokacin da Baffa zai aurar da yaya mama ce keyi musu labulaye da xannuwan gado na alfarma a matsayin gudummmawa, wanda hakan ya zamewa Baffa jiki a tun bayan Koyan labulaye da xanin gado da mama tayi yayi bankwana da siyansu a harkar bikin yayansa, kawai in aure ya tashi xa a bata kalar kayan falon da xa ai wa amarya ita kuma zata zauna ta qure basirarta Ta tsantsara labulaye da bed sheets set uku uku ta bayar da sunan gudummawa kuma a karba bako godia kamar kudin suka bata kuma hakan bazaisa ana jimawa kadan aiwa yarta gorin aureba. Domin matan Baffa hamshaqan jahilai ne, jahilci irin wanda aka denashi saboda sauraran radio koda bakaje makaranta ba to yana existing a gidan tunbama suna fada akan yaya ba sai kaji kamar ka binne kanka, wannan yasa yayansu basu da tarbiyya ko kadan.
Gidansu Mimi gidane na kwalliya koma ince competition dinta ake da yake duk wacce ta gama karatu Baffa na samar mata aiki, hakan yasasu qarya daga yan matan gidan har wadanda ke gidan miji, yawancinsu suna da mota koma ince dukkansu wasu su suka siya wasu kuma mazajensu suka saya musu, acikinsu kuwa harda yaya Faty wacce ya Ahmad ya siya mata tun kafin ya siyawa kansa. Hakan yasa gidan ake gasar saka suttura da kwalliya da kuma shiga mota. Ta bangaren sutura Mimi kan sai hamdala tufa dai akwaita mama tayi mata, yaya Faty tayi mata, hajia kakarta ta wajen uwa wacce taci sunanta itama Kullum a hanyar yiwa takwararta sutura take , sannan mummy (Adda halima) yayar mama tayi mata sutura kam sai dai ta jira Mimi, ba Mimi ta jira ba. Hakan yasa koda Baffa bai mataba bata damuba.
Ana saura sati biyu bikin gidan ta tafi law school wanda yan gidan suka danganta haka da baqin ciki suka dunga sakin maganganu marasa dadi, domin Anty cewa tai ai dole aqirqiri tafiya law school domin da kunya a xauna to! za ayiwa yara aure ga gyatuma xaube ajabe agida.
Mrs Muhammad π
[9/30, 1:04 PM] βͺ+234 706 296 6299β¬: ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
AL' AMARIN MARYAM
ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
πFANTASTIC STARS WRITERS
{F S W }
Writing & story by
Rahma Muhammad {hajia}
Editing by
mmn khairat π
Page 1β£2β£
Yammacin ranar juma a ne rana gaf take da faduwa, a zaune akan tabar rila ta gidansu Mimi matasa ne guda biyu zaune akan tabarma suna jiran Baffa dake daga cikin sitroom din yana sallamar wasu baqi. Badaru sunan babban mai shekaru 33 sai Badamasi qaramin kenan me kimanin shekaru 30 a duniya, yayan abokin Baffa ne ya turosu gaida Baffa kamar yadda yake a al adar mahaifinsu (alh Inuwa) yakan turosu gaida abokin nasa aduk sanda ya kasance Badamasi na gari, saboda ba a garin kano yake aiki ba. Fararene tas kana ganinsu kaga fulani amma babban wato Badaru yafi Badamasi haske sai dai Badamasin yafishi jiki da kuma cikar zati irin ta maxa, sannan kuma yafishi alamar wayewa da kuma kwarjini, kodan hakan yanada nasaba da ilimin boko da Badamasin yafi Badaru oho.
Tafe take cike da gajiya saboda tafiyar da tayi daga Law skul (makarantar koyar da aikin lauya) xuwa gida sakamon samun hutu 1 wk da sukayi tazo gida domin yin hutun, sanye dake cikin suit baqaqe riga da skirt kamar yanda yake ga dokar makarantarsu, sai dan Baby hijab dake maqale a wuyanta kayan sun mata cif sun fito da surarta, qafarta sanye cikin rufaffen takalmi (cover shoe) baqi sai jakar goyo irinta dalibai itama baqa, ataqaice dai hijab dintane kawai fari a jikinta, jakar na goye a bayanta wacce ke dauke da yan kayan da xata iya buqata kamarsu brush, charger da kuma system din ta ( wato laptop) sai wayar dake riqe a hannunta. Duk da gajiyar da tayi hakan bai hana kyanta fitowa ba, babu kwalliya ko digo a fuskarta sai gashin gaban goshinta wanda baya iya rufuwa koda ta kwatanta rufeshi fatarta tayi tas ta kuma yin kyau saboda zama guri daya data samu. Mimin mama da Yaya Faty kenan .
Harta qaraso cikin rilar wacce xata sadata da sorayen gidansu bata kula da wanxuwar su Badaru a cikin gurin ba, wanda su kuma tunda ta tunkaro gidan suke kallonta harta shigo cikin rilar shigowarta yasa suka sauke ajiyar xuciya atare suka kuma shagala da kallonta ganin tana shirin shigewa cikin gidan yasa Badamasi tashi da hanxari ya qarasa inda take tare da cewa "Assalamu alaikum" . Yayin da Badaru ya kashingida ya cigaba da kallonta bako qiftawa. Bayan sun dan gaisa da Badamasi sama sama saboda ta qagu ta qarasa gida, ya kalleta a karo na barkatai sannan yace kamar daga makaranta kike ko? Taqanyi yaqe tace eh, ok wace skul kike? Ina Law skul ne dake nan jihar kano, ta bashi amsa a gajarce. Kai π³ kice da Barrister nake tare, yasunan malamar? Maryam ta bashi amsa tana murmushi π. Barrister maryam gaskiya kin burgeni inason inga mace tayi karatu me xurfi haka. Well naga a gajiye kike ni sunana Badamasi wancan na kwance yayanane sunansa Badaru munxo gurin Babanki ne, kuma ina fata daga yanxu xumunci ya shiga tsakaninmu. Tace to nagode bari na qarasa, Ok to Mimi sai nazo karki manta sunan Badamasi da haka suka rabu ta shige gida.
Bayan ta kwana biyu da xuwa ne kuma ta shirya xuwa gidan Rashida da Rahana (wato amaren gidan da akai biki bayan batanan) ta Ware 10k da nufin ta bawa ko wacce 5k a cikinsu. Mama sam batazo xuwan Mimi gidan Rashida ba saboda Rashida (yar Anty jamila)